Kannywood

Suwaye Iyayen Ummi Rahab

Written by mynovels

Suwaye Iyayen Ummi Rahab?

 

 

Ummi Rahab (wacce ake kira Rahab Saleh a rayuwa ta gaskiya) na daya daga cikin fitattun jaruman Kannywood da suka yi fice a masana’antar fina-finan Hausa.

Duk da shahararta, mutane da dama suna tambaya: waye iyayenta?
Asalin Rayuwa
An haifi Ummi Rahab kuma ta taso a cikin birnin Kano, wanda yake daya daga cikin cibiyoyin harkar Kannywood a Najeriya. Tun tana karama take da sha’awar harkar fim, wanda daga baya ya kai ta ga samun daukaka.

Iyayenta Su Waye?
A gaskiya, Ummi Rahab ba ta bayyana sunayen iyayenta a fili ba. Wannan yana daga cikin dalilan da suka sa mutane ke ta bincike a kai.

Jaruman Kannywood da suka fi tashe

👉 Abin da aka sani kawai:
Iyalan ta Hausawa ne masu mutunci
Sun ba ta goyon baya wajen shiga harkar fim
Ba su yawan bayyana a kafafen yada labarai
Dalilin Boye Bayanin Iyayenta
A yawancin lokuta, jaruman fina-finai suna boye bayanan iyalinsu ne domin:
Kare sirrin iyali
Gujewa matsin lamba daga jama’a
Tsare mutuncin iyaye daga shaharar ‘
ya’yansu
Ummi Rahab ma na iya kasancewa cikin wannan rukuni.
Rayuwarta a Masana’antar Kannywood
Duk da rashin bayanai game da iyayenta, Ummi Rahab ta yi suna sosai a masana’antar Kannywood. Ta fito a fina-finai da dama tare da manyan jarumai, kuma tana da masoya da yawa a Najeriya da ma kasashen waje.
Kammalawa
A takaice, babu cikakken bayani a bainar jama’a game da iyayen Ummi Rahab. Amma abin da ya fi muhimmanci shi ne irin nasarar da ta samu a rayuwarta da kuma yadda ta zama abin koyi ga matasa da dama.

 

INA IYAYEN UMMI RAHAB?

 

Daga Datti Assalafiy

 

Satin da ya gabata na ga wani labari dake cewa shahararren ‘dan wasan Hausa film Adam Zango ya kori wata matashiyar ‘yar Hausa film mai suna Ummi Rahab saboda wasu dalilai da ba’a bayyana ba

 

Sannan sai jiya kuma naga wani labarin wai Ummi Rahab ta cewa Adam Zango “Na ji kana fada cewa wai kana so ka bani tarbiyya amma na bijire maka, idan ka cigaba da neman bata mini suna da wannan sharrin wallahi zan tona maka asiri”

 

Jaridu sun ruwaito wannan labarin a matsayin raddi da gargadin da Ummi Rahab ta yiwa tsohon Maigidanta Adam Zango, ba wanda ya san me ya hadosu, idan labarin ya tabbata gaskiya, nafi ganin tausayin Ummi Rahab akan Adam Zango, yarinyace mai kyawun sura wanda idan batayi hankali ba tsoffin kuraye mayu zasu ragargaje mata rayuwa su watsar kamar yadda suka yiwa Maryam Boot

 

Yara ‘yan mata kanana irin wannan, a lokacin da suke tashen balaga, suna falli sakamakon hulda da suke da manyan mutane kudi yana shiga musu ta kowani lungu da sako, ji suke tamkar kasa ba zata iya daukar su ba saboda girman kai, basa jin nasiha da shawara, sun fi yadda duniya ta koya musu darasi ba mutane ba

 

Ina iyayen Ummi Rahab? mu yasa kuka bar ‘yar ku ta shiga Hausa film?

Danyar yarinya kamar wannan ba daidai bane iyayenta ku kyale ta tana yawon gararamba ba tare da idonku yana kanta ba

 

Idan labarin nan ya tabbata gaskiya Ummi Rahab ta yiwa Adam Zango gargadi da barazanan zata tona masa asiri to akwai abin dubawa anan

 

Wani irin boyayyen asiri ne ga Adam Zango wanda ta sani idan ta bayyana zata wargaza masa lissafi?

Zina yayi da ita ta dauki bidiyon sa kamar yadda artificial karuwai na yanzu suke yi?

Ko kuma ciki ya mata ya zubar shiyasa tayi barazanan tona masa asiri kamar yadda aka ruwaito?

ba laifi bane ayi irin wannan tambayar

 

Ku bata shawara taje tayi aure ya fi mata rufin asiri da kima da mutunci, sana’ar film ba inda zai kaita sai tashar da na sani marar amfani

About the author

mynovels

Leave a Comment