Uncategorized

1000+ Free Hausa Novel Books Download, Littafan Hausa Novels Kyauta

Written by mynovels

1000+ Free Hausa Novel Books Download, Littafan Hausa Novels Kyauta

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Littafan Hausa Novels

 

Zumuncin zamani

 

Na

Nazeefah Sabo Nashe.

 

(Typing: Fadimatu sabi’u d’ankaka jazakillahu bil jannah.)

 

Not edited a karanta da hak’uri Ba ni da lafiya.

 

Dubai Part 1 and 2 Hausa Novel Complete

 

Saeed ko girgixa kai ya yi ya zabga tsaki kafin ya ce “ba ma tilas ta hak’ura da auren sa ba, ai ko shi ne autan maxa ba xata aure shi ba.”

 

Umman su kuwa tana d’aki ta zabga uban tagumi Abba mustapha ya girgiza kai “yanxu fisabillah umman sauda ba za ki yi shiru da hawayen nan ba? Kada kii manta, ita fa rayuwar nan yanzu haka take sai kana dashi sannan kake xama mutum idan kuwa ba ka da shi kare ma yafi ka daraja Shi yasa yanxu mutane idonsu ya afu da Neman kud’i ko ta wace hanya wanda nake rok’an Allah ya kare ni daga fad’awa sharrin zuciya. Ina son don Allah ki jajirce ki zama mace jaruma kada wanann abun ya dame ki…

 

Amfanin Soyayyar Aure Hausa Novel Complete

 

Girgixa kai umma ta yi tace “Abban sauda dubi fa irin cin mutunci da mutumin nan ya yi mana ya ilahi me mutane suke son su mayar da zumunci ne?”

Abba ya girgiza kai ya ce “babu komai, kansa ya yi wa. Ina rok’on Allah Kuma ya ganar da shi gaskiya” daga haka ya janyo carbinsa ya ci gaba da laziminsa hakan ya tabbatar wa da umma da ba ya son magana a lokacin

 

Jikin umma a salu’be ta mike ta bar d’akin zuciyar ta cikin zafi da matuk’ar K’una

Shi kuwa Hisham tunda ya yi parking ya dire mahaifinsa a sukwane ya ja motar ya bata wuta, bai zame ko ina ba sai wani park, flat ya kwanta a kan ciyayi, zuciyar sa naci gaba da yi masa wani tukukin bak’in ciki idan ya tuno kalaman da mahaifin nasa ya yi amfani da su wajen cin mutuncin bayin Allah nan me suka yi masa? Kawai dalilin talauci sai mutum ya zama abin gudu abin wulak’antawa da tozartawa?

 

Sexxies House Hausa Novel Complete

 

Ya rintse ido kafin ya ciro waya ya kira wayar saudat sai dai haka tayi ta ringing ba a d’auka ba shi kenan ya sani saudat ta rabu da soyyarsa, bai ga laifinta b kuma ko wacece ce ma kuma xa ta aikata, ya ayyana hakan a ransa tabbas idan har bai auri sauda ba shi kenan farin cikin sa ya k’are a rayuwa, ya zai yine? Kuma a ina zai samu mafita?

 

Alhaji hamza kuwa ko da ya shiga gidansa dariya ya shiga kyakyatawa tamkar wani zararre, matarsa balaraba ta dube shi kafin ta ce “lafiya Alhaji?

Ya yi tsaki had’e da cewa “ni da wad’annan matsiyatan mutanan ne su sun zata da gaske neman aure na je har da wani malala min tabarma. Ni kuwa na zage su tass na ci musu mutunci”

 

Hajiya laraba ta saki murmushi ta ce “ai ni na zata da gaske kake ina nan ina ta tsuma ina jiran ka dawo naji dalilinka na aikata haka.”

Alhji hamza ya ce “ni mahaukacin ina ne zan yarda d’ana ya jajaibo min tsiyar dangi ke ko a mafarki aka ce miki zan yarda za ki amince? Wai ni na yarda Hisham ya auro min dangin tsiya.”

Hajiya laraba tace “ai shi na gani,abin ya yi matuk’ar d’aure min kai, da naji kai ne ka amince

Alhaji ya girgiza kai “yanzu abin da zaa yi, tashi zakiyi kije ki bawa mahaifiyar yarinyar hak’uri,ki sanar da su maganar banza yake, ki dai san yadda kika yi kika shawo Kansu.”

Hajiya ta ce “yanxu kuwa, ai ba a bori da sanyi jiki”

 

Alhaji hamza ya ce. “A to, kin dai sani da bazarsa muke taka rawa, idan Hisham ya k’i auren y’arsa na tabbata duk wasu kwangiloli da suke shigo min dainawa zai yi, yadda yake ji da yar nan tasa tamkar gold”

 

Haj laraba cewa ta yi, “to ba dole ya ji da ita ba ita kad’ai ce fa tamkar ajali”

 

Alhaji hamza ya girgiza kai kafin ya ciji baki ya ce “don haka ki sake jawa yaronki kunne a game da yarinyar nan don wallahi matuk’ar ya k’i bin umarnina sai dai ya sake wani uba amman ba ni hamza ba” ya fad’a Yana nuna kansa..

Hajiya laraba kuwa cewa ta “In sha Allahu ma ba zai k’etare umarinka ba, ai Hisham tun Yana yaro ba dai muka saka masa doka ya k’etare”

Ya sake girgiza kai had’e da cewa “Ah to, na dai fad’a miki, bin umarnina shine kwanciyar hankalinsa a gidana,sab’anin haka kuwa ke ma kin san sauran” daga haka ya mik’e ya shige d’aki hajiya laraba kuwa mi’kewa ta yi ta nufi gidan su fareeda don ta ba mahaifiyar ta hakuri…

 

Fareeda na zaune ita da maminta, daidai lokacin hajiya laraba tayi sallama cikin kwantar da murya saboda ta san gidan da ta zo daman haka lamarin yake kafi wani wani ya fika.

Maman fareeda a wulak’ance ta amsa sallamar saboda ita sam ba ta san dalilin da da yasa mijinta son auren ba, sam a nata tunanin ba su da dukiyar da har za a yi rububin had’a zuria da su,to ka ji fa, wannan fa shi ake kira gaba da gabanta!! Aljani ya taka wuta ita a son ta a nemi wani hamshakin mai kud’i a bashi auren d’iyarta ko ma d’an shugaban k’asa,amma ba wannan ba wanda mahaifinsa yake samu daga taskar mijinta.

 

A shagube ta amsa gaisuwar daga haka ta ja bakinta ta tsuke. Ita kuwa fareeda ko kallonta bata yi ba, ta mik’e ta shige d’aki.

Hajiya laraba ta sake rusunar da kai ta ce “hajiya daman hak’uri nazo na baki tabbas na san Hisham ya b’ata muku amma a yi hak’uri yaran yanzu ne ka haife su ba ka haifi halinsu ba”

 

Da saurii hajiyar ta dakatar da ita,fuskarta a had’e sosai ta ce, “wasu yaran ba, wad’anda ba su da tarbiyyah to ki sanar da shi in dai fareeda y’ata ce to daga yau na haramta masa aurenta, kuma za ki san na isa da ‘yata dama duk alhaji ya jawo,idan ban da haka ai wannan had’in sam bai yi min ba. to me na sama ya ci balle ya ba na k’asa? Ai babban goro sai magogin k’arfe,don haka ni na yi farin ciki da abinnan ya faru, ya je can ya k’arata .Allah raka Taki gona yo ma banda iskancin wane ne Hisham da har zai wulak’anta min ‘ yah, to an fasa ya je ya auri ko wace ce amma y’ata ba kalar kishiya ba ce.” Daga haka ta shige d’aki

Hajiya laraba na sake ba ta hak’uri amma ko waiwayen ta bata yi ba haka nan jikinta a sanyaye ta mik’e ta bar gidan zuciyar ta cike da tunanin tsagwaran rashin kirkin mamin fareeda

Ko da ta koma gida alhaji hamza yana nan yana tsimayin ta. fuskarta babu walwala ta shiga gaya masa yarda suka yi da mamin fareeda

Alhaji hamza ya girgiza kai ya ce “mata kenan rabu da ita shi honourable d’in zan samu na san zai fahimce ni”

Hajiya laraba ta ce ai kam matar nan tasa bata da mutunci wallahi ko kad’an” alhaji hamza ya girgiza kai ya ce “duk ba kowa ne ya jawo wannan matsalar ba sai Hisham”

 

Tun da safe da ta mike take ta share- share a gidan, zuciyarta sai matuk’ar suya take mata, ga shi umman tata ta tafi asbiti kasancewar ba ta jin dad’i kanta ya matsa mata da ciwo.

 

sai karfe goma ta gama share_sharen sananan ta shiga wanka,da sauri take komai kasancewar karfe 11 safe take da (lecture).

Bayan ta kimtsa tsaf duk da ba wata shahararriyar kwalliya take ba, yanxu ma riga da zani ne na wata koriyar atamfarta ta kamfanin NOUVA , ta yafa wadataccen mayafinta mai kaurin gaske, sannan ta shiga d’akin mahaifinta yana zaune yana lazimi har k’asa ta durk’usa ta sanar dashi zata tafi makaranta.

Addu’a ya yi mata sosai, sannan ya ce “Àllàh ya bada sa’a sai an dawo saudat.”

Jikin ta a sanyaye tafito daga gidan don ko ficika ba ta da shi na shiga mota. Don suna da test ne yau kam da babu abinda zai sata zuwa makaranta.to wa yake ta karatu ana ta abin da zaa saka a ciki?gaba dayan su yau azumin suka tashi da shi saboda babu wadataccen abincin da za a iya yin ci biyu da shi a rana bama uku ba.

 

Littafan Hausa Novels

Gaba d’aya rayuwar tasu ta sake canjawa,tun bayan da Allah ya sake saukar da iftila,in gobara, bayan Hisham babu wanda ya kawo mak’idan kudi ya ba su sai ko inna Maryam da ta kawo musu kayan abinci su ma din tafi_tafi sun cinye su kaf.

Tafiya take kawai ba tare da ta san inda take jepa k’afarta ba, ba, saboda tunanin da ya cushe mata kwanya, ji ta yi ana yi mata wani mahaukacin horn, hakan ya sa ta yi saurin juyowa, don ta ga dalilin, tunda dai ita ta san ba a kan hanya ta ke ba, cak ta tsaya ganin Hisham ya fito dga motar cikin suit bak’ak’e fuskarsa saye da bak’in gilas ya Yi masa matuk’ar yi masa kyau.

 

Tamkar ta juya ta ci gaba da saurin, sai dai sam ta kasa, ba don komaii ba sai don tuna halaccinsa gareta,

a hankali ya iso har inda take fuskarsa d’auke da mayalwacin murmushi, ita kuwa sam kasa sakin murmushi tayi saboda tunanin da ta yi yanzu shi kenan ta rasa shi, tana tsananin k’auanr sa amman Sam ba za ta iya jure wulak’ancin danginsu ba.

Cikin slow voice yace “zo na kai ki mana please!”

Da sauri ta girgiza kai ta ce “uhm_uhm Yaya Hisham ka bar shi kawai”

Zare gilas d’in idonsa ya yi cikin wani salon kallo ya ce “why sauda? me ya sa za ki yi min musu duk da tarin soyayyar da muke wa juna? Ko kina nufin an raba mu?”

 

D’ago Kai ta yi tace. “Y. Hisham kenan rabuwa kam ai ta zama dole tunda dai kana jin furucin da mahaifinka ya yi a gidan mu.Y. Hisham ta ya ya kake tunani za mu iya auren juna?”

Hisham ya girgiza kai ya ce,”No saudat,da ikon Allah nine mijinki babu abunda Zai rabamu ina nan ina neman mana solution. Yanzu ki zo muje ma k’arasa maganar a mota.”

Jikinta a mace ta bi shi ta shiga motar don sam ba za ta iya yi masa musu ba.

Suna tafiya ya sake dubanta sosai kafin ya furta kalamansa,” sauda please ki taimaka min don Allah ki min alk’awarin komai rintsi ba za ki rabu da ni ba, wallahi sauda ina miki wata irin soyayyah mai matuk’ar wahalarwa”

 

Littafan Hausa Novels

Ko da ya sauke ta kalamin da ya dinga jaddada mata kenan.

Da kai take amsa masa kawaii don ta san abu ne mai matuk’ar wuya har ta fita ya kira ta ta juyo a hankali, ya yi mata nuni da son ganin Jakarta.

K’in ba shi tayi.

Ya d’an dube ta “me yasa saudat so nake na ga kina mayar da hankali a makaranta.”

Hakan da ta ji ya sa ta mika masa jakar, rafar yan #500 ya zuba mata a cikin jakar.

Sam ba ta lura ba, har ya miko mata, yana murmushi yace “A sha karatu lapia.”

Ita d’in ma da kai ta amsa masa don ba ta son ta sake kwallafa shi a ranta, ta san aurensu abu ne mai matuk’ar wahala saboda su kansu y’an gidansu sun d’auki zafi musamman yayyenta….

 

Jikar Nashe ce!

About the author

mynovels

Leave a Comment