Hausa Novels

Dashi Nafi Dacewa Hausa Novel Complete

Written by mynovels

DA SHI NAFI DACEWA

 

It’s romantic love story

 

Story & written by

mommyn fareesa

 

 

GODIYA*

Alhmdllh Ala kully halin” godiya ta musammun ga Allah S W A daya nunamun na fara wannan littafi lafiya”yah Allah yadda na fara lafiya Allah ka bani Aron rai da lafiya na gama lfy….

 

*GARGAD’I*

wannan littafin k’irk’irarran labarine banyi shi dan wata kodan waniba idan yayi daidai da rayuwar wasu Arashine”Aguji sauyashi ta kowace siga sbd hakkin mallakata ne….

 

*Special gift for*

 

Hjy maimuna sadeeq (mommy)

mamah G

Aisha lawal

Sameerah gusau

Hjy kulu mohd zagi

Zainab sulaiman(mmn waleed)

Hjy husainq Ibrahim

Hjy Salma Abbah

Oum farouq

Mlm hauwa Abubakar

sa’idat shehu(Afrah)

Fatima Ahmed Alhassan

Dr nafeesa

mmn Abdussamad

Aisha mohd

Aisha kyari wulgo

Raudah mohd sokoto

Zainab h wada

Mrs barrister

Nafisa dallatu

Maryam mohd

Mmn Afrah

Daduk Wanda beji sunansa ba

 

*Dedicate to* hjy maimuna Umar sadeeq mommy❤️🥰

 

BISSIMILLAHIR RAHAMIR RAHEEM

 

Page 1&2

 

KT STATE ! *Anguwar madoji G R A*……da yammacin yau Asabar dako wane Ma’aikaci ke gida sbd samun Hutun k’arshen mako”Adaidai wannan lokacin da marecen yayi gwanin dad’i da ban sha’awa sakama kon fara zafi da Akayi “Ayanzun kuma garin ya d’auki sanyi na marece”zafafan motoci ne guda ukku ke tafe kan babban titin Anguwar har suka shigo cikin wata babbar center “wanda ke d’auke da maka makan gidaje na Alfarma….

 

Abayan kowace mota An rubuta *SADEEQ MAWASHII !!* da manyan harrufah”gaba d’aya wa’annan maka makan manyan motoci Kai tsaye wani gida dake side na gefen haggu wanda shine farko daka shigo center Anan suka nufa”gidan ya gaji da had’uwa”yanada white & Ash colour paint”sannan get d’in gidan black ne”wanda gaba d’aya kaf Anguwar babu gida mafi kyau,burgewa da ban sha’awa kamar wannan babban katafaren gidan”Anan motocin duk suka tsaya suna dannah horn”babu b’ata lokaci get man ya bud’e get,motocin duk suka shigo sukayi parking “motar dake tsakkiya fara wacce tafi kowace kyau da tsada”itace Aka bud’e front sit da sauri “wani saurayi ya fito ya bud’e back sit yana wani kwantar da kai dake nuna ladabi….

 

 

bud’e k’ofar yayi daidai da wani irin gawurtaccen k’amshi me sanyi da kashe zuk’ata ya dira Awajen”Kafin Ahankali Aka zuro wata doguwar k’afa me sanye da takalmi sawu ciki coffee brown “tun dg kan santala santalan k’afafuwan sa idan ka kallesu zaka tabbatar da cewa” mamallakin su ingarman namiji ne me cikar zati da tsayi”Anutse ya ida fitowa daga cikin motar yad’an kalli farfajiyar haraban gidan”fuskarsa sanye da eye glass black”riga da wondo ne k’ananu da hula p cap Ajikinsa duk black ne masu masifar kyau da tsada “sun kuma haska fatar jikinsa matuk’a”fari ne Amma ba ja bane”lips nasa masu rownd pink colour ne”yanada gashin bak’i daya zagaye bakinsa zuwa gemunsa dake d’auke da k’asumbar data zagaye Masa fuska “sajen yayi bak’i ya kwanta “ya kuma fito Masa da tsananin kyawun cikar kamalar sa”karan hancinsa ya fito sosai saidai ba’a ganin k’wayar idanunsa”yayinda giransa sbd tsabar cika ta kusan had’ewa da y’ar Uwarta”be cika barin suma ba”ya kanyi Aski normal da gyaran fuska”tunda ya fito be furta ko A ba”tsayayyan mutum ne da kallo d’aya zaka yima k’iran jikinsa kasan k’arfaffa ne shi”be kuma d’aukar wargi”saidai baida jiki sosai Amma Akwai manyan k’wanji da wuya me tsoka…lolx”wanda Kai tsaye zamu iya kiran K’iran jikinsa irinta y’an kokawa(restealig)….

 

fuskarsa babu walwala da Alama be cika fara’a ba”Anutse ya duba wristwatch d’insa coffee brown dake d’aure saman tsintsiyar hannunsa yaga 4:25 pm”yad’an tab’e baki yana zura dogon hannunsa guda cikin Aljihun wondonsa ya wuce ba tare daya kula mutanan da suke tare dasu ba”*PA Ahmed* yayi saurin cewa” y’allab’ai zakaje buga ball d’in mu jiraka ne??….beyi mgn ba be kuma juyoba”hakan ya tabbatar Masa da cewa bazai jeba kuma be sallame suba”kasancewar duk week end yana tare da hadimansa”….cike da shan k’amshi da nutsuwa yake nufar interest d’in shiga cikin gidan nasu”dukda ba sauri yakeba Amma kasancewar yanada dogon tak’i sai gashi ya iso A gaggauce…yana turo k’ofar yaji k’arar TV “murmushin gefen baki ya saki wanda yayi masifar fito Masa da kyawun fuskarsa”cikin farin ciki ya k’araso sbd ya tabbatar mahaifinsa na gidan”Assalamu Alaikum! ya furta cikin k’asaitacciyar muryansa me kauri da idan yaga dama yake mayar da ita me k’arfi idan yana masifah….Anutse ya rufe k’ofar yana tunkaro had’add’en parlourn da idan ka shigo zaka zata ba’a Nigeria kake ba….

 

lolx”matashin babban mutum dake zaune wanda bazai wuce 60yrs ba” ya d’ago kansa ya Amsa sallamar tasa fuskarsa d’auke da murmushi”farar jallabiya ce da glass fari medical Asaman fuskarsa”yad’an mik’e k’afafuwansa saman center table”idan ka kallesa zaka zata be wuce 52 yrs sbd jin dad’in rayuwa “kalar fatarsa wankan tarwad’a ce”tun d’azun yake jiran shigowar tilon d’an nasa guda daya mallaka A duniya….

 

tamkar wani k’aramin yaro haka ya iso da gudu ya fad’a jikin Daddyn daga gefensa….yah salam! *sadeeq* ! miye haka kakeyi? kada ka karya mun miji “k’aramin yaro ne Kai da zaka fad’a Masa irin haka?? wai sai yaushe zaka girma ne?35 yrs gareka Amma kullum kana Abu gabanmu kamar d’an 10yrs….cewar wata kyakykyawar mace fara”wacce suke yanayi da *sadeeq* da kuma daddynsa”tana sanye da sutura ta Alfarma Ajikinta”hannunta rik’e da tray”kasancewar daga kitchen ta fito”shagwab’e fuska uban gayyar yayi zai tashi Daddy ya rik’e hannunsa guda yana fad’in Dr zamu b’ata dake”komai girman mutum wajen iyayensa yaro neshi”bayan haka kinsan bashida k’ani ko k’anwa miye Amfanin kiyi Masa surutai??…..”Ai dama Alh ba son laifin sadeeq kake ba”to Allah yau na shiryama duk wata fitinarku Agidan nan”badai dama duk week end haka nake fama daku ba”daga wannan yace kaza yake so sai wannan yace kaza yake so”tayi maganar tana Ajiye tray d’in hannunta saman center table ta zauna gefen sadeeq daketa ciccin magani ya d’auke fuska”Daddy yace”koma miye zakice munji”my friend Ina kaje har 4:30 pm baka dawo gida kayi lunch ba??….mun fita zumunci dasu bash nefa Daddy”yayi maganar yana dafa kafad’ar iyayen nasa”cikin tsananin k’aunar su”mommy ta murd’e Masa kunne tana fad’in tashi kaje kaci Abinci”yad’an saki k’ara “Dr me kika Masa?”mommy tayi murmushi ba tace komai ba “Daddy me mommy ta girka mana??….Abinda baka sone”wato Abincin gargajiya”kasan kuma Abinda mijina keso shine zan girka”idan kana son cin Abinda kakeso Aure zakayi matar ta dafa maka”yayi shiru yak’i yin mgn”kinga ki rabu dashi pls”mommyn ka na tsokanarka ne tayi maka fevorite food naka”sadeeq ya saki ihun murna yana rungume mommy”gaba d’aya sukayi murmushi “Ahankali ya zare eye glass d’in”Atake dara daran manyan idanunsa farare suka bayyanah”saidai Ayanzun Akwai d’an sirkin ja cikin su”SADEEQ!…uhmm mommy”*zaitoon* tazo wajenka sbd kuyi fira “data gaji da jira baka dawo ba saita tafi”nasan kuma sbd kasan tana nan shiyasa kak’i dawowa gida da wuri tunda yau ba office”toka sani ,bakada wata mata sai zaitoon kaji na gaya maka….bece komaiba ya tashi fuuuuuuu zai nufi wata k’ofa dake gefen dining Area “inda idan ya shiga upstairs ne zai sadashi da side nashi……SADEEQ! Daddy ya dakatar dashi murya babu Alamar wasa “jeka yi lunch kafin ka hau saman”ke kuma karki bari na koma miki mgn ta ukku Akan zancen zaitoon”yafad’a fuskarsa babu walwala yaci gaba da cewa”ba’a mun Auren dole ba kema haka”to d’ana bazan masa ba”duka nawa yake? Aure lokaci ne da yayi zaizo yakawo mun sarkuwata na Aura Masa”so karma na koma jin zancen wata zaitoon”ta tsaya matsayinta na k’anwarsa kawai Amma tunda baya sonta Abar maganar”shikenan Allah yabaku hak’uri”ta k’are maganar tana zuba Masa drink’s “taci burin muddin sadeeq ya kwaso mata y’ar talaka wlh bazata bari ya Aure taba”dukda tana likita gani takeyi kamar d’an nata beda lafiya”sbd ganin kofa budurwa be tab’a yiba”ko friends mata beda su”hidimar neman kud’i kawai yasaka gaba…. sadeeq kuwa zuciyarsa fes ya zauna yayi serving kansa kafin yafara lunch nasa”ya lura inba rashin mutunci da nunama zaitoon Asalin kalarsa yayiba bazata shafa Masa lafiya ba”yasan SO gaskiya ne Amma har yanzun bega wacce yake soba”yana so ya Auri mece me Aji marar tsoro wacce bata cusa kai ga mazaje”sannan wacce keda masifah kamarsa”beson kuma meson Abin duniya wacce zata Auresa sbd dukiyarsa”shiyasa har yanzun yakasa gane kan matan”ko ita kanta zaitoon y’ar k’anwar mommy ce ita” yasan badan Allah take sonshi ba”bayan haka shi bata Masa ba”yana wannan tunanin Kiran babban Amininsa *jabeer* ya shigo cikin babbar wayarsa”yana gani yak’i d’auka saima Ajiye spoon d’in hannunsa yayi ya zuba ruwa A glass cup yasha ya tashi ya wuce saman…..tun daga cikin parlourn har zuwa k’awataccen bed room d’in nasa gyare yake K’al yanata k’amshi”yasan kuma Aikin mommy ne”sbd tasan beson masu Aiki na gyara side nashi”yasan shid’in d’an gata ne gaba da baya “hakan yasa yanada son yara sosai sbd gidan su babu”Amma da yake d’an renin wayo ne be nunawa”hasalima ko bak’i Akayi yaga Akwai yara be d’aukar su”beson kuma danginsu na zuwa Hutu musammun mata”har kuma ga Allah Yana k’aunar iyayensa zai iya rasa ransa sbd su”Amma Akwai halayen mommy da baya so”shine nak’in son talaka”yadda kuma yakeso idan har Allah ya Amince Masa shine matarsa ta zama bame y’ar masu kud’i ba”yafiso ya Auri wacce ba kullum take cin nama ba Agidan su”idan tazo gidansa yabata kullum”zataji dad’i tayi Alfahari da Aurensa “Amma ya lura mommy ita bata duba tsari ko tarbiyar mata”ita dai kawai y’ar me wadata….ita kanta zaitoon y’ar k’anwar tace”kuma mahaifinta Abokin Daddy ne”Anan gidan su Abbanta ya had’u da mahaifiyarta hjy khadijah har sukayi Aure….cak! tunaninsa ya tsaya sbd fad’awarsa saman lallausan royel bed nasa”da yaji shimfid’u na Alfarma”Anutse ya kwanta rigin gine yayi matashin Kai da hannunsa guda “gudan hannun nasa ya d’auki k’aramar wayarsa yafara dealing na number d’in *bash*…..bugu biyu ya d’auka da ladabi yana yin sallamah”uban gayyar be Amsaba sai cewa da yayi jabeer yazo?”Ah Ah yallab’ai “idan yazo ya jirani”ka sanarwa Ahmed da Auwal kar suyi nisa zamu fita nanda 40minit”in sha Allah yallab’ai”daga haka sadeeq ya yanke wayar yana tab’e baki sbd yasan jabeer mayen mata ne” maybe yana can ya lalace wajen mace bazai fito ko inaba tunda week end ne”yana wannan tunanin ya tashi tsaye yafara zare kayan jikinsa….Masha Allah! Irinsu sadeeq Ake kira one in million “yanada k’iran murd’add’an jiki me mutuk’ar d’aukar hankali”gaba d’aya jikinsa nasa duk gashi ne musamun faffad’an kirjinsa “jikin nasa kuma yafi kyakykyawar fuskarsa haske”saidai me?”yana gama d’aura towel yaji gabansa ya fad’i ! Amma sai yayi Addu’a ya wuce bath room…..

*Goruba road*

gida ne plat madaidai ci irin na masu rufin Asiri “get d’in gidan orange ne”daka shigo k’aramin tsakar gida ne daga gefe tape ne da wajen yin wanke wanke “inda yaji tiles fari”sai y’ar k’aramar baranda da k’ofar shiga cikin parlourn take”wanda d’akunan bacci ne guda biyu cikin parlourn ,sai dining Area da kitchen”matar gidan me suna *munnirah* tana zaune da tsohon cikinta na fari tana y’an ciye ciyenta”Ahaka wata kyakykyawar budurwa jajir da ita ta fito d’aya daga cikin dakunan “tana sanye da riga da siket na Atamfa cotton chiganvy” rigar har gwiwa tazo mata,siket d’in me tsaga ne daga baya”sun zauna sosai kayan Ajikinta”tana rik’e da hand bag k’arama da wayarta k’iran *infinix hot 60 i*……tanata zuba k’amshi gwanin burgewa”tayi d’aurin d’an kwali ture kaga tsiya “wanda ya bayyanah tulin gashinta da tayi parking Abaya “ta yafa mayafi sky blue irin kalar Atamfar”jajir take har yellow yellow takeyi”tanada kyau na tashin hankali”danma bata yin make up”ko yanzun kwalli ne bak’i ta shafa babu ko powder saman baby face nata”yatsun hannayenta sunsha Adon lalle ja na hausa”ta saka zobba golden guda 2 A yatsun hannun “ta kuma d’aura Agogo me kyau black” kyakykyawar budurwa ce ita Ajin farko”bazata wuce 22yrs da haihuwa ba”ba doguwa bace ba kuma gajera bace”tana tsaka tsakkiya ne….wow ! *Jiddah*! badai fita zakiba? cewar munnirah tana zuba mata ido”saida ta turo bakin tsiwar tata kafin tace”fita zanyi mana Anty “tunda dai week end ne zan d’ebe kewa ne”Amma meyasa bazaki zauna muyi fira ba”sannan Sweet heart idan yadawo bakya nan kinsan zaiyi fad’a ko?? nafa kira yayan na sanar Masa zan fita”ta k’are maganar tana zaro face masks zata saka….matsalata dake kenan”wai miye ribar b’oye fuskarki da kike yi?babu komai Anty “hmm”ni Aganina ki dena sbd ita budurwa A kasuwa take Koda yaushe”dukda Akwai *Ayub* dake sonki da *Alh Iliyas* “Koda saka muku rana Akayi be kamata ki rufe fuskaba….Anty ! Da zaki gane yadda na tsani mutumin can Alh Iliyas wlh da bazaki mun maganar saba”shi kansa Ayub bana jinsa A Raina yanxun….. munnirah na tab’e baki tare da cewa”to Allah ya kiyaye keda waye zaku fita?nafef zan hau mu had’u da Abidah bakin titi mu d’auketa”hmm! wlh idan zaki Ajiye wannan Ak’idar taki ki kori kyawunki garama ki Ajiye “dubeki dan Allah”son kowa k’in wanda ya rasa “kinfi buk’atar yin teaching Awata 70k “sai siyar da snacks ?? Shima ba kullum ba??”inda kin yadda kin Auri Alh Iliyas inaga duk wata sai kin fita k’asar waje yawan hutawa”Acc naki cike da kud’i muma mu dan gwali Arzik’i “na rasa shin talaka kikeso kome?”koshi kanshi Ayub gabana yasha kiranki Akan me kikeso ko kike buk’ata ?Amma sai kice babu…..Anty !! nagaji da iri wa’annan kalaman naki nason zuciya”kinsan yaya beso shiyasa gabansa baki fad’a mun”ba irin wannan tarbiyan yabani ba shida mahaifiyar mu”na rasa meyasa da yawan mutane suka d’auka kud’i sune jin dad’in rayuwa?”zancen gaskiya kina son b’ata mun tarbiya “hakan ya koma maimaita kansa wlh zan gayawa yaya *yaya mukhtar*!….eyeeeee?? ba shakkah ! Laifina ne ke kika sani”banza jiddah tayi mata ta nufi k’ofa ta fita”saida ta baro cikin center tasu kafin ta fito bakin titi “Adaidai lokacin taheer ya iso kan mashin nasa roba roba zai wuce”kasancewar yasan dama kusan irin haka take shigarta”shiyasa yayi saurin ganeta….hjy jiddah manyan gari sai Ina kuma?? yafad’a Yana shan gabanta”ya zuba mata ido cike da burgesan data keyi”saida ta yamutsa fuska tare da kauda kanta kafin cike da Aji cikin zazzak’ar muryarta me sanyi tace”Ina wuni?”lafiya qlau ya gidan? Alhamdulillah “zan d’an fita ne”okay inane saina mik’a ki ko?”karka damu nagode sosai yaya taheer”daga haka ta wuce Abinta “tana mamakinsa daga mak’ota yaketa son manne mata”lura da yanada tarbiya da mutunci shiyasa take girmamashi”sannan beda makusa kawai y’an gidan Su da mahaifiyarsa ke basuyi mataba shiyasa tak’i bashi duk wata damar dazai furta mata kalmar so…..tana tafiya bata tsayaba harta samu nafef “lokacin kuma biyar da wani Abu ta wucema”basufi mintina 5 suka tsaya bakin titi ta kira Abidah k’awarta “babu b’ata lokaci ta fito daga layinsu tazo ta shigo”itama bah laifi ta had’u saidai bazama A had’asu da jiddah ba harta wajen hali da kuma ra’ayi “sannan ita ba masifaffah bace kamar jiddah….tana d’an murmushi ta kalleta tace”*beautyn Ayub*! Irin wannan kyau haka??banza jiddah ta mata sbd gabanta kawai taji ya fad’i “ga zuciyarta nata bugawa”kasancewar sun saba had’uwa suyi fad’a kafin su rabu A shirya sai Abidah ta shareta”Ahaka suka iso wani k’ayataccen wajen hutawa “wanda side ukku ke Akwai cikin garding d’in”Akwai wajen wasanni ,Akwai wajen hutawa da ciye ciye “sannan Akwai wajen shan shisha…..nawane kud’in ka??cewar jiddah da suka fito daga cikin nafef d’in tana zuge Jakarta”jin shiru yasaka ta kalli me nafef d’in taga gaba d’aya ita yake kallo….mittsuwww! mlm nawane kud’in ka?in kuma kallon nawa zakayi saina k’ara gaba”miyayi zafi hjy ?ku bada 1k”batayi mgn ba ta zaro ta mik’ama Abidah “sbd batajin zata iya tsayawa ta bashi dan wani irin haushi taji yana bata”itadai Abidah karb’a tayi tana girgiza kanta ta bashi suka wuce bakin get “Anan ma kud’in shiga jiddah ce ta biya suka wuce”kai tsaye wajen wasanni suka nufa”jiddah itace daga gefe Abidah na kusa da ita”Ahankali Abidah tace”gobe zakiyi snacks d’in??….jiddah na k’ok’arin mgn taji saukar kwalin hollondia saman fuskarta ya daki hancinta da gefen bakinta “da duk ta rufe da face masks”yayinda y’ar sauran dake ciki ta fantsalar mata saman mayafin ta sky blue….. subahanallahi! cewar Abidah tana juyowa ta kalli gefen dataga Anwurgo kwalin”Maza ne matasa guda 5 duk suna zazzaune kan wasu kujeru ga drinks gabansu”mutum guda ne daga tsakkiyar su da Alama ya d’an girmesu”kansa kuma na’a k’asa”kallo d’aya zaka yima guys d’in ka fahimci y’an boko ne masu rufin Asiri “Abidah na k’ok’arin mgn matuniyar taku data kai k’arshe wajen d’aukar zafi da fusata ta nufi inda gardawan samarin masu jini Ajika suke” bakinta fal tsiwa da masifah”tanaso taga wane d’an kutumar uba ne ya jefeta tayi Masa rashin mutunci??…..Abidah na dakatar da ita Amma tayi mata banza bata saurare taba”ta wuce kamar zata tashi sama tana huci ta dira gaban su…….✍️

 

Bazasuji komai daga bakina ba sai sai mun iso next page”iya Abinda na sani wannan book d’in shine one in million Acikin books d’ina 🤣😂Maza hjy tah ki biya kud’inki k’alilan sbd Adama dake free page beda yawa…..

About the author

mynovels

Leave a Comment