Meefrah Hausa Novel Complete
MEEFRAH
“`Mafarkin kaddara“`
Elegant online writers
_STORY AND WRITING_
“` Maryam Muhammad Ussaini
(Nazlarh ce)“`
~~~~~~
*بسم الله الر حمن الر حيم*
__________________
Page 1&2
MEEFRAH!! “Na’am Ummee”, “Me kikeyi ne a tsakar gida har wannan lokacin bakije kin kwanta ba?”, Meefrah ta ce “Ummee banajin bacci ne kuma gashi idan ina daki sai na dingajin tsoro”, Ummee cike da haushi ta ce “Maza ki tashi kije ki kwanta bana fada miki cewa ki dungayin addu’oi kafin ki kwanta ba”.
Maryama Hausa Novel Complete
Meefrah tashi ta yi tana wik’i-wik’i da ido ta ce “Tom Umme tana fad’in haka ta tashi ta shiga k’aramin dakinta wanda karamin kati fane a ciki sai jakan kayanta a ciki.
Kwanciya tayi akan katifar tare dayin addu’oi ta shafa a jikinta sannan ta rufe idonta.
Bacci ne ya kwashe lokaci kad’an.
Bacci takeyi hankalinta kwance, wani mummunan mafarki ta farayi, wata mata tana gudu cikin duhun daji ga k’atan ciki a jikinta ihu take tana neman te mako saka makon wasu k’atina dambobi da suke binta a bayan wanda basu da suffa masu kyau gasu bak’ak’ene wulik ko fuskansu baza ka iya ganewa ba.
Gudu take tana nishin wahala, wani jikin bishiya ta boye, tana wani nishin saboda tagaji da gudun da takeyi, wani wahalallen na k’uda ne yafara taso mata cike da azaba, hawayen ke zubowa daga saman fuskanta, tana yarfe hannunta don azaba ga zufa na keto mata tako inna gashi tanajin ihun wa inna dodanni da suka biyota ga gurnanin su na kara tsorata ta, hannu tasa ta rufe bakinta tana kuka hawaye yana zubo mata dafe cikinta ta yi saka makon kulle mata da maranta ya yi.
Ji tayi daya daga cikin wa inna dodanni ya dafata tana daga idonta tayi arba da mummunan kwayar idonshi hak’ori ya kafa mata a dai-dai wuyanta, ya fara zukan jininta take jariri ya kwala ihu alaman ta haihu don azaban wannan cizon da wannan damban yayi mata, take numfashinta yadauke.
Wani gigitaccen ihu Meefrah tasaki tana fad’in “Innalillahi wa’inna ilaihim raji’un”.
Wanda yayi dai-dai da fadawon jariri a jikinta, wani zufa ke keto mata tako ina hawayen shab’e shab’e a fuskarta, kukan jariri taji a gabanta wanda tana kallon jaririn ta ganta cikin jini kuma wannan jaririn shine wanda matar nan ta cikin dajinnan ta haifa.
Meefrah take ta sume a wurin saboda mugun tsorata da tayi.
Umme kuwan tashi ta yi, saka makon jin ihun Meefrah da ta yi a dai-dai lokacin taji ana kiran sallah Asuba.
Ummee tashin Abban Meefrah ta farayi, yana bude ido ta ce “Abban Meefrah bakajin ihun Meefrah ba?”, Abban Meefrah kuwa ya ce “A’ah ni banji ba”.
Ummee ta ce “Wllh naji ihunta don Allah tashi muje mu dubata tunda ankira sallah kar wani abu ya sameta”.
Abban Meefrah bece mata komai ba ya sakkon daga kan katifar su dake kwance a tsakar dakin, suka fita a dakin.
Direct dakin Meefrah suka wuce, Ummee ta kunna karamar tough-light dake hannunta, tana haska Meefrah taganta kwance cikin jini ga jariri sai rafka ihu yakeyi abunshi.
Ai Ummee batasan lokacin da tasaki fitilar hannunta ba ta kurma ihu da sauri ta nufa kusa da Meefrah.
Abba kuwa mutuwan tsaye yayi ya kasa ko d’aga k’afa daga inda yake.
Ummee ta riko Meefrah ta fara girgiza ta hankali a tashe, amman ba alaman motsinta, da sauri ta ce “Abban Meefrah kawo ruwa don Allah da sauri”.
Abba kuwa da yayi suman tsaye a firgice ya fita a dakin ya d’ibo ruwan a cikin wata kwanan sha.
Ummee kwara mata ruwan ta yi wanda ya yi dai-dai da farfad’owan Meefrah daga doguwar suman da ta yi.
Ummee ta kallin Meefrah da ta zuba ma wannan jaririn ido, yana ta faman kuka, Hawaye yana zubowa daga idonta, dah taji tsoron daukan jaririn saboda yadda komai ya kasance a wannan mafarkin, hannu tasa ta daukeshi ta rungumeshi a kirjinta jikinta yana rawa, cikin ikon Allah jaririn yayi shiru.
Ummee da Abba kuwa kawai sun zuba ma Meefrah ido suna kallon ikon Allah.
Ummee hannu tasa ta fisge jaririn a hannun Meefrah cikin b’acin rai ta ce “Meefrah meye haka taya haka ya faru daman kina da ciki ne tun yaushe kike da ciki kike boyewa bamu sani ba?”.
Duka wannan tambayan Ummee ta jero ma Meefrah da ke kallon jaririn, yadda yake tsala kuka a jikin Ummeeta, tashi tayi duk da tasan jikinta a b’ace yake da jini ta k’wace jaririn a hannu Ummeeta, ta rungumeshi sosai a jikinta tanajin wani masifan kaunar jaririn yana shiganta.
Take jaririn yayi shiru abinshi, Meefrah ta kalli Ummeenta da Abbanta ta ce “Abba nima bansan taya hakan ya faru ba…..ai bata gama rufe baki ba taji saukan mari gudu uku masu zafi a kuncinta.
Saurin dafe jaririn tayi saboda yadda yakusan fad’uwa saboda zafin marin da taji, Ummee kuwa wuyanta tashak’o tana “Meefrah fadamin waya miki ciki taya aikai kuka haihu daman kina da cikine bamu sani ba kike boye mana?”.
Hawayen masu zafi ne suke fitowa daga idon Meefrah ga azaban marin da Abba ya yi mata ga azaban shak’e mata wuya da Ummee ta yi ga jariri a hannunta wani wahalan ihu tasaki ta kwace kanta da k’arfi ta zube a k’asa rungume da jariri a hannunta, cikin kuka ta ce “Ummee ni bani da ciki a salima ban taba kusanta wani d’a namiji ba Ummee Abba ku yarda dani nima bansan taya hakan ya faru ba kawai dai nayi mafarki ne a cikin wannan mafarki…….wani zafafan mari taji wanda yayi sanadiyar kasa karisa maganarta, Abbanta cikin zafin rai ya ce “Meefrah karya kikeyi fadamin waya miki ciki?”, ko kuma na kashe ki kowa ya huta, cikin kuka ta riko k’afan Abbanta ta ce “Abbana ka yarda dani bansan komai a kaiba wllh a mafarkina naga wannan jaririn ni banta ba aikata zina ba”.
Ummeeta kuwa hannu tasa ta fara kai mata duka tako ina ga jaririn sai kuka yakeyi saboda har dashi Umme take had’awa da sauri Meefrah ta rufe jaririn duk dukan da Ummee take mata ihu kawai takeyi tana bata hak’uri da magiya akan ta yarda da ita bata aikata wani zunubi ba, amman ina Abba kuwa d’ago da Meefrah yayi wacce gaba daya farin matar ta sai da suka koma sukai jawur don azaba fuskan duk ya kun bura.
Abba ya ce “Meefrah kitashi ki fita min a gida daga yau muba iyayenki bane, maza kitashi tun kafi gari ya waye yan garin suga abin kunyar da kika jawo mana, abinda zai zubar mana da mutunci a idon jama’ah”.
Cikin kuka Meefrah take rok’on Abbanta da ya hak’uri yabarta ta zauna, “Abban wllh idan kuka koreni bansan ina zanje ba nasaba rayuwata da ku don Allah karku min haka bazan iya rasaku ba kunne gatana kune farin cikina”.
Ummee cikin fushi ta d’auke Meefrah da mari, ta ce “Wllh Meefrah saikin bar gidan nan kije wurin d’an iskan saurayin da ya yi miki ciki, kiyi rayuwa dashi tunda kin fifitashi akan mu harki kika bashi kanki duk tarbiyar da muka baki kin zubar”.
Ummee itama kukan ta fashe dashi, Meefrah tarasa ina zatasa kanta kuka take sosai ga jikinta sai rawa yakeyi ga jaririn shima kukan ya keyi, tashi ta yi bakinta narawa ta ce “Ummee!!Abba!! kuya femun don Allah banyi abinda kuke tunani ba idan na tafi bansan ina zani ba”.
Abba cikin b’acin rai ya ce “Meefrah idan baki tashi kin fitar min a gida ba kika k’ara magana tom na tsine miki, wani irin kuka da ihu Meefrah tasaki ta zube a k’asa a wurin, Abba ya ce “Meefrah tashi kifita tun kafin wani yasan abinda ya faru kuma idan kika tafi karki tsaya nan kusa kitafi can ki manta mu iyayenki ne, idan kika bari na fito masallaci na sameki wllh saikinyi mamakin abinda zan miki”.
Yana gama fadin haka ya fita a d’akin, Ummee kuka takeyi sosai ta tashi zata fita da sauri Meefrah ta rik’e mata k’afa ta rushe da kuka, ta ce “Ummee karki guje yar da kika haifa a cikinki kinsan irin tarbiyar da kika bani bazan aikata abinda ba dai-dai ba, don Allah Ummee ki saurareni karki gujeni bani da kowa bayan Allah saiku mai yasa bazaki yarda dani ba Ummee”.
Ta k’ara fashewa da kuka Ummee kuwa fisge kafarta ta yi ta fita a dakin da gudu tana sharan kwallah.
Meefrah kallon jaririn tayi yadda ya zuba mata ido yana kallonta wani kukan bak’in ciki ne ya kuma zuwa mata ta fashe dashi cike da ciwon abinda iyayenta sukai mata, ta ce “Wannan wani irin Mafarkin kaddara ne?”, kuka takeyi kamar ranta zai fita gashi bata da wani mafita a yanzun, daya wuce tatashi tabar gidan kafin Abbanta ya dawo………
Hummm shin wani irin mafarkin kaddara ne haka Meefrah ta yi?
Wacece Meefrah?



[…] Meefrah Hausa Novel Complete […]