Gurguwar Tafiya Hausa Novel Complete
๐๐จ๐ฅ๐๐จ๐ช๐๐ฅ ๐ง๐๐๐๐ฌ๐
๐๐๐๐๐ฅ๐/๐ฅ๐จ๐๐จ๐ง๐๐ช๐
๐๐๐๐๐ช๐๐๐ฌ๐๐ฅ๐ ๐๐๐ ๐๐ ๐ ๐จ๐’๐ญ๐จ
(๐ฅ๐จ๐๐๐ฌ)
** *ุจุณู ุงููู ุงูุฑุญู ู ุงูุฑุญูู *
*_____________________________________*
*๐๐ฐAINUWA ๐ผRITER’Sโ๐ผ*
*๐ฆSSOCIATION๐ค๐ป*
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
**
๐ถ๐ฐ๐ฑ๐ฐ๐๐ฐ๐๐๐ฐ
๐ณ๐ ๐๐๐๐๐ ๐ฐ๐๐๐๐ ๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐, ๐๐๐ ๐๐๐ ฦ๐๐.
๐ณ๐๐๐๐๐ ๐ข๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐ข๐ ๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐ฐ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐ ๐๐๐ ๐ ๐๐๐ ๐๐๐๐๐, ๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐ฐ๐๐๐๐ ๐๐ ฦ๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐ฐ๐๐๐๐๐ ๐ผ๐๐๐๐๐๐๐ (๐.๐ฐ.๐), ๐๐ ๐๐ข๐๐๐๐ ๐๐, ๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐, ๐๐ ๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐, ๐ฐ๐๐๐๐ ๐๐ ฦ๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐ข๐๐ข๐ข๐๐ ๐ผ๐๐๐ฃ๐๐ ๐ฐ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐ฐ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐.
Yankan Baya Hausa Novel Complete
๐น๐๐-๐๐๐๐
๐น๐๐-๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐ข๐๐ข๐ ๐๐, ๐ฐ๐๐๐๐ ๐ข๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐, ๐ฐ๐๐๐๐ ๐ข๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐ ๐๐๐.
๐ฑ๐ ๐ฃ๐๐ ๐๐ษ๐ ๐ ๐๐๐๐ ๐ ๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐ n๐ ๐๐ฦ๐ ๐๐๐-๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐ข๐๐’๐๐ ๐๐๐ n๐, ๐ฐ๐๐๐๐ ๐ข๐ ฦ๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐ฃ๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐ณ๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐ข๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐ ๐ ๐๐ ๐ข๐๐๐๐๐ .
๐น๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐
๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐ ฦ๐๐ฦ๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐๐, ๐๐๐ ๐ข๐ ๐๐๐ ษ๐๐ ๐๐๐ ๐ฃ๐๐๐๐๐๐ ๐ ๐๐๐ ๐๐ ๐ ๐๐๐ ๐๐, ๐๐๐๐ ๐ข๐ ๐ข๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐/๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐ ๐๐๐๐, ๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐ ฦ๐๐ฦ๐๐๐ ๐๐ ๐๐, ๐๐๐ ๐๐ข๐ ฦ๐ฦ๐๐๐๐ ๐๐ข๐๐๐๐ ๐, ๐ฐ๐๐๐๐ ๐ข๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐ ๐ข๐ ๐๐๐๐๐ข๐๐ ๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐ข๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐ข๐.
๐ฑ๐๐ ๐ข๐๐๐๐ ๐ ๐๐๐ ๐๐ ๐ ๐๐๐ ๐ข๐ ๐๐๐ข๐ ๐๐๐ ๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐ , ๐๐ ๐ข๐๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐ ๐๐ ๐๐ ๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐ข๐, ๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐ฃ๐๐๐ ๐๐ ๐๐, ๐ ๐๐๐ข๐๐ข๐.
๐๐ ๐บ๐ฎ๐๐๐ผ ๐ธ๐ ๐ท๐ถ ๐ค
๐ช๐ฎ๐ป๐ป๐ฎ๐ป ๐น๐ถ๐๐๐ฎ๐ณ๐ถ๐ป ๐๐ฎ๐ป๐ฎ ษ๐ฎ๐๐ธ๐ฒ ๐ฑ๐ฎ ๐๐ฎ๐น๐ผ ๐ป๐ฎ ๐ฏ๐ฎ๐ป ๐บ๐ฎ๐บ๐ฎ๐ธ๐ถ, ๐๐ฎ๐น๐ผ๐ป ๐๐ฎ ๐ฑ๐ฎ ๐๐๐ฎ๐ฟ๐ถ๐ป ๐๐ฎ ๐๐ฎ ๐ฏ๐ฎ๐ป๐ฏ๐ฎ๐ป๐๐ฎ, ๐ฐ๐ถ๐ธ๐ฒ ๐๐ฎ๐ธ๐ฒ ๐ฑ๐ฎ ๐๐ฎ๐๐๐ฎ๐๐ถ, ๐๐ฎ๐๐ฎ๐ณ๐ฎ๐ฟ ๐๐ผ๐๐ฎ๐๐๐ฎ, ฦ๐ถ๐๐ฎ๐๐ฎ,๐ฟ๐ฎ๐๐๐๐ฎ๐ฟ ๐ฎ๐ฟ๐๐ถ๐ธ๐ถ ๐ฑ๐ฎ ๐๐ฎ๐น๐ฎ๐๐ฐ๐ถ, ๐ด๐ฎ ๐๐ฎ๐ฟ๐ธ๐ฎ๐ธ๐ถ๐๐ฎ ๐ธ๐๐บ๐ฎ ๐บ๐ฎ๐ถ ๐๐๐๐ฎ๐ป ๐๐ฎ๐ฟ๐๐ฎ๐ฟ๐ฒ๐๐ฎ, ๐๐ฎ๐ฑ๐ฎ ๐ฑ๐ฎ๐ถ k๐ ๐ฏ๐ฎ๐ฟ๐ถ ๐ฎ ๐ฏ๐ฎ๐ธ๐ ๐น๐ฎ๐ฏ๐ฎ๐ฟ๐ถ, ๐ธ๐ ๐ฏ๐ถ๐ป๐ถ ๐๐ฎ๐ป๐ป๐ ๐ฎ ๐ต๐ฎ๐ป๐ธ๐ฎ๐น๐ถ ๐ฑ๐ฎ๐ป ๐๐ฎ๐ฟ๐๐ฎ๐ฟ๐ฒ ๐บ๐๐ธ๐ ๐ฑ๐ฎ๐ธ๐ถ -๐ฑ๐ฎ๐ธ๐ถ .
๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ
๐ ฟ๐ ฐ๐ ถ๐ ด 1 & 2
Tafi minti talatin a durkushe a wajan da suke wanke -wanke,wasa ta ke yi da kumfar da ta kaษa da wani ษan ฦaramin kofi da ke hannun ta, haka ta ke ษaga kumfar kamar wacce ta samu shayi mai kauri, yayin da zuciyarta bata tattare da ita,wasa kawai ta ke da kumfar amma hankalin ta da tunanin ta sun yi nisa yayin da zuciyarta ta cunkushe da tunane-tunane marasa amfani ษalle makama.
Saukar ludayi taji a gadon bayanta wanda ya sa ta miฦewa a kiษime ba tare da ta shirya wa hakan ba abinka da shgwaษaษษiya tuni har kwalla ta cika idanun ta, Mahaifiyar ta ce ta kalle ta cike da faษa tana faษin
“Ke wai Umaimah wacce irin yarinya ce da ba kya jin magana? Kullum akan wanke -wanke anyi ta fama da ke kamar wata yarinyar yar shekara goma? To wallahi na baki minti goma ki kammala inba haka ba… ” Kwafa tayi ba tare da ta karasa maganar da za ta yi ba ta wuce, Umaimah bata iya cewa komai ba ta tsugunna ta fara wanke -wanken kamar zata fashe da kuka dan ita a rayuwar ta babu abinda ta tsana sama da aiki to gwara ma tayi shara sau dubu da tayi wanke -wanke, tana zumษura baฦi dai har ta samu ta kammala domin tafi kowa sanin halin Mahaifiyar ta, duk da tsananin son da ta ke mata hakan baya hana ta hukunta ta indai ta aikata laifi ko kuma tayi ma ta faษa, hakan ya sa ta ke shakkar Mahaifiyar ta sossai.
Cikin sauri ta share wajan da ta yi aikin tare da tattara kwanukan cikin kwando ta kai cikin ษan madaidaicin kicin ษin su, zuba kwanukan ta ke yi cikin kwandon tana mita ฦasa -ฦasa
“Dubi yadda kwandon nan ya fashe dan Allah, kaiii wlh talauci bai yi ba, Allah ma yaga zuciyata a bisa dole nake iya rayuwa a gidan nan dan babu yadda zan yi ne kawai,amma komai baya min kyau, mtseww” ta karashe zancen da jan doguwar tsuka ta fice a kitchen din domin kullum sai ranta ya ษaci, a nata ganin tafi ฦarfin wannan rayuwar,kamata ya yi ace kamar ita tana daga zaune tana bama masu aiki umarni,tafi so ace komai yi ma ta ake yi tana daga zaune, irin rayuwar masu kuษi take buri,bata son talauci ko kaษan, ko da ta fice a kitchen ษin wani daฦi ta nufa tare da kwanciyar a wata yar yololuwar katifa tana faษin
“Wash Allah!! Na gaji wlh, Allah ka raba ni da yin wanke -wanken nan, na san duk randa nayi sati ban yi aiki ba sai an kalle ni an sake kallo saboda kyan da zan ฦara yi” a bayyane ta ke maganar ta cikin nuna gajiyawa da aikin da ta ke yi a gidan nasu kullum, wayar ta kirar goinee P32 ta dauko ta fara dannawa,gaba daya wayar ta fice a hayyacin ta, har ga Allah tana jin kunyar shiga mutane da wannan wayar musamman ganin kusan ko wacce yarinya iPhone 13 pro max ne a hannun ta idan ta leฦa shafin sada zumunta, harta kawayen ta tampatsa-tampatsan wayoyi ne da su…
“Umaimaaah” Mama ta kwalla kiran ta da karfi wanda hakan ya sa ta jefar da wayar da ta ke dannawa a gefen katifa ta fito waje tana bata rai kamar za ta kurma ihu, a taskar gida ta tarar da Mama tana kokarin daka yajin barkono, cikin tsawa Mama ta ce :
“Uban waye zai dora miki abincin rana naga kin koma ษaki kin kwanta, baki da aiki sai kwanciya? Ke dai ki kwanta dai kamar manja, to Allah ya shirya “, Ba tare da Umaimah tace komai ba ta juya ta tafi wajan kitchen, taliya yar murji taci karo da shi a wata yar roba a ฦofar shiga kitchen ษin hakan yasa ta ja wani dogon tsaki “mtseww” ba tare da ta shirya ba, kunkuni ta shiga yi tana tura baki gaba tana faษin “Ni ni wallahi na gaji da cin taliyar hausa, haba ayi ta cin fulawa kamar me, salon mutum ya yi ta narka ฦiba ta ba gaira ba dalili, ni dai gaskiya na gaji” cike da ฦosawa da gajiyawa ta ฦarashe fadin haka tare da figar robar tayi cikin kitchen ษin ta fara kokuwar haษa icen da zata dafa abincin da shi.
Tana gama dafa taliyar ta ษora ruwan zafi a kan gaushin da ya rage, fitowa ta yi ฦofar kitchen ษin ta ja kujera yar tsugunno ta zauna gami da share zufa, gaba ษaya idanun ta sun chanza launi saboda hayaฦin da ta shaฦa, sai murza idanu ta ke yi tana cewa a fili
” Ni wallahi ficewa ma zan yi a gidan nan, sabuwar Atamphar nan da na dinka zan dauka na kira Musa ya kaini ta anguwar G.R.A ya min hotuna na samu na status kwana biyu”
Tana gama fadin haka ta saki murmushi mai sauti wanda ya bayyana annurin dake fuskar ta karara, miฦewa ta yi ta koma cikin daki da yake mallakin ta, tana ci-gaba da saฦa irin hotunan da Musa zai mata na kece raini da ษaukar hankalin masu bibiyar ta a shafukan sada zumunta.
Suhail ne ke bacci hankali kwance, daga shi sai singlet da shorts, ga sanyin AC yana ratsa shi ta ko ina, daga yadda numfashin shi ya ke sauka zaka fahimci lallai ba ฦaramin jin ษadin baccin ya ke yi ba, cikin magagin bacci yaji karar wayar shi, ba shiri ya miko hannu ya ษauka gami da kashe ta gaba ษaya,domin baya son abinda zai takura mai ko ya katse mai jin daษin baccin shi.
Sai da ya shafe sama da awa uku yana bacci sannan ya buษe ido a hankali gami da lalubo wayar yana kunnawa, ko da ya kunna wayar bai kuma duba wanda ya kira shi yana bacci ba ya mike zuwa cikin toilet ya watsa ruwa, bayan ya fito ya zauna yana goge jikin shi da towel, yana cikin shafa mai kenan yaji wayar tana sake ฦara, dauka ya yi ba tare da yace komai ba, sai da ya gama jin me ake fada daga ษayan bangaren bai ce uffan ba ya kashe wayar gami da jan wata doguwar tsaki tare da jefar da wayar a gefe, ya ci-gaba da shiri cikin wasu baฦaฦen kaya, shirt da wando, dake lokacin yamma tayi sossai, duk saurin da yake yi kokari kawai yake yaga ya bar gida, so yake ya je ya tarar da abinda aka fada a waya domin hakan ne kaษai samun kwanciyar hankalin shi domin yanzu kawai daurewa ya ke yi yana controling kan shi har ya gama shiryawa, key’n motar shi ya ษauka ya fice ta kofar baya dan baya son kowa ya gan shi ballantana ya tsayar da shi har a bata mai lokaci.
๐ง๐ฎ๐ธ๐ ๐ฎ ๐ธ๐ผ๐ฑ๐ฎ ๐๐ฎ๐๐๐ต๐ฒ
๐๐ฎ๐ฑ๐ฎ๐๐ฒ๐ฒ๐๐ฒ๐ฟ๐ต


