Kuyi Mana Adalci Hausa Novel Complete
*KU YI MANA ADALCI*
NA
Sadiya Abdulrazak
Page 1
Marubuciyar
Aure A Yau
Sandar dukan uwargida
Ranar Kuka
Miji goma
Zuciyar mace
Iya ruwa
Wani auren
Da Walakin
Wutar Ƙaiƙayi
Matar shige. Dss
Duniya juyi-juyi, kawaɗo ya faɗa a ruwan zafi, ina yawan tunawa da wannan karin maganar cikin zuciyata, saboda a yanzu dai yana taka ta shi rawar a cikin rayuwar aurena. A baya idan wani ya ce mini zan iya yin bacci ba a kwance a ƙirjin mijina ba alhalin muna kwance a gado ɗaya, zan shiga shakkun tabbatuwar hakan, inda a ce wani ya taɓa faɗa mini akwai ranar da za ta zo muna gida ɗaya da mijina mu raba ɗaki kowa ya kwana shi kaɗai a na shi ɗakin wallahi nan take zan daka tsalle na musa cikin isa, amma sai ga shi zamani ya jujjuya da rayuwar aurenmu ya watso mu ƙadamin da muke ciki a yau, wanda ya fi kama da rayuwar maƙiya ba masoya ba.
Juyi na yi a makeken gadon nawa, na lalubo filo na rungume, ina sane da hasken wayata da yake ta kawowa a karo na babu adadi, alamun mai kiran wayar har yanzu bai gajiya ba, na mirgina na kalli wayar, ba don neman sanin mai kiran ba, don na san wannan, agogon wayar na duba wanda ya nuna ƙarfe sha biyu na dare da minti goma, idan na yi rantsuwa ba zan yi kaffara ba, sai yanzu Sadam ya gama waya da chatting ɗinsa da matan da yake ganin sun fi ni daraja a halin yanzu, wanda nake ƙarfafa zargin sun kunna shi ne, yake neman yadda zai kashe wannan wutar ta wajena, don haka na ƙudure ba zan iya amsa kiransa ba, duk da ban manta da hukuncin matar da mijinta ya kira ta shimfiɗarsa ta ƙi amsa kira ba.
Ina sane ƙofar ɗakina a buɗe take, don haka shigowarsa ba ta ba ni tsoro ba, amma ta ba ni mamaki, nan take na tuna da rantsuwar da ya taɓa yi mini a ranar da nake kuka ina tabbatar masa ba zan sake kwana a ɗakinsa ba, ya ce”Na rantse da Allah Sayyada babu macen da ta isa na bi ta ɗakinta na kwana da ita, kuma tun da ni mijinki dole ki amsa kirana a duk lokacin da na buƙaci hakan”.
Shin na karya masa rantsuwarsa ne tun ba a je ko’ina ba? Lumshe ido na yi kamar mai bacci, daidai lokacin da ya kai hannu ya kunna globe ɗin ɗakin, ya taka a hankali ya ƙaraso ya zauna a gefen gadon “Sayyada, Sayyada”.
Ya shiga kirana da taushin murya kamar munafiki, ban ko motsa ba, don haka ya kai hannu ya fara taɓa fuskanta, na janye hannun na shi da sauri tamkar wanda ya taɓa ni da bakin wuta, ya riƙe hannun nawa ƙam ya jijjiga shi sannan ya ce”Tashi mana, ina ta kiran wayarki ashe kin yi bacci”.
Na fizge hannun na ce”Ban yi bacci ba, zuwa ne ba zan yi ba! Kenan ba ka yarda ba da na ce maka ba zan sake kwana a ɗakinka ba ko?”
Ya sauke numfashi, har yanzu da wannan sanyin muryar wanda yake yaudarata da shi a da, ya ce”Haba Sayyada, na zata wannan ya wuce ai”.
Na ce”Ba zai wuce ba har abada”.
Ya ce”Yaushe kika koyi gardama ne? Yaushe kika koyi musu da ni?”
Kamar zan yi kuka na ce”Tun ranar da ka nuna mini matsayi da darajata sun ɓare a wajenka”.
Tsaki ya ja, a wannan karon sai ya canza murya ya kaurara ta ya ce”Dalla tashi ki wuce mu je”.
Na yi banza da shi, zuciyata ta fara yi mini zafi, ina tuna miyagun kalamansa a kaina.
“Ki tashi mu je ki ba ni hakkina Malama!” Ya maimaita mini cikin daka tsawa.
Ni ma ɗin a tsawace kuma cikin kuka na ce”Ba zan bayar ba! Na ƙarfi ne”.
Ya tashi tsaye yana ce”To ai ina da ƙarfin”.
Ƙarfin kuwa ya saka ya fizgo ni daga gadon, abinka da ‘yar ƙarama mai ƙaramin jiki ba tsayi ba ƙiba, shi kuma dogo mai ƙiba ƙaƙƙarfa, nan take ya ɗauke ni cak, duk shure-shuren da nake yi da dukansa bai sare ba har sai da ya dangana ni da gadon ɗakinsa, irin abin da ya faru a daren da na ce ba zan sake shiga ɗakinsa ba shi ne ya faru a yau ma, fyaɗe Sadam ya yi mini karo na biyu a tsayin zaman aurenmu, duk miyagun kalaman da na dinga jifansa da su ba su saka ya sare ba, har sai da ya kai inda yake son zuwa, na yi laƙwas a gadon ina kuka mai sauti, irin mai cin rai ɗin nan, na yi mai isa ta babu mai rarrashi, sanda na taƙaita na rarrashi kaina kuwa shi tuni ya yi bacci, na kalle shi ta hasken ɗakin, baƙi ne mummuna, amma a yanzu na gane hakan, domin kuwa a shekarun baya kafin zamanmu ya hargitse wallahi gani nake yi ko gasar kyau Sadam ya shiga zai iya shiga sahun farko-farko, ashe soyayya tana ɓoye muni? Tirr! Ni Sayyada na la’anci kalmar soyayya da masu bauta mata indai a haka ƙarshenta yake ƙarewa kowa.
Na daɗe kwance a haka hawaye yana gangara ta gefen idona, ji nake zuciyata ta yi mini nauyin da nake jin kamar babu macen da ta fi ni shiga ƙunci, a hankali na yunƙura na tashi, na ɗauki yaloluwar rigar baccina da ya yaga rabinta na bar ɗakin. Bayan na yi wanka na kwanta sai na fara jin ciwon kai kaɗan-kaɗan, tsallen da na yi na afka kogin tunani kuwa ya ta’azzara hauhawar farashin ciwon kan, wanda dama tuni ya zame min jiki.
Sautin kiran sallar farko da ya karaɗe unguwar ne ya ankarar da ni tabbas yau na kwana ban runtsa ba, idan aka cire baccin da na samu tsakanin bayan sallar isha’i zuwa ƙarfe goma da dawowar Sadam ɗin ta tashe ni, sai da na yi sallar asuba sannan bacci ya ɗauke ni a kan sallayar. Sai wajen ƙarfe tara na tashi, na yi wanka na saka doguwar rigar leshi na faɗa kitchen, a raina ina addu’ar Allah Ya sa bai fita ba, ruwan shayi kawai na dafa, na ɗakko biredi da bota na ajiye a dining, na haɗa nawa shayin na koma falo na zauna ina sha.
Ban yi nisa da fara sha ba ƙamshin turarensa ya cika hancina, hakan ya tabbatar mini da fitowarsa, na juya a hankali na kalle shi, fes yake fuskarsa da walwala alamar bai tashi da wata damuwa ba, ina kallon shi muka haɗa ido, ya sakar mini murmushi ya ce”Morning”.
Duk yadda na so na mayar masa murmushin na kasa yi ko da kuwa na gefen baki, amma dai na amsa masa da faɗin”Morning”.
Sannan na tashi na ƙarasa dining ɗin, ya zauna, ni kuma na tsaya na haɗa masa shayin na tura masa gabansa, zan bar wajen ya riƙo hannuna ya ce”Idonki ya kumbura, sorry”.
Na gyaɗa masa kai alamar na ji, sannan na zame hannun na koma ɗakina, mayafi da jaka na ɗauka na saka wayata a ciki, na zura takalmi, na dawo falon na zauna, ina jira ya gama na ji yadda za mu kwashe, duk tunanin da na kwana ina yi jiya mafita ɗaya na samu a kan burin gyaran rayuwata, shi ne na ziyarci asibiti a yau na fara gyara kuskurena, don a yanzu shi ne kuskuren da ya fi damuna kuma ƙarami cikin kura-kuran da na aikata.
Yana gamawa ya zo ya saka kai zai bar falon, bayan ya yi mini kallo ɗaya, na tashi da sauri na bi bayansa, tun da na lura hauka yake son manna mini, ai dai ya sani gari banza ba zan saka mayafi da takalmi har ma da jaka don na ji daɗin zaman falo ba.
“Amma dai ka san ba haka kawai na saka mayafi ba ko?” Na faɗa a gadarance.
Ya yi tsaki ya ce”Allah wadaran naka ya lalace, na ga ranar da za ki iya magana da miji ke dai”.
‘Idan ya zama dole sai na kira ka da miji to dole na ƙara da faɗin mijin ƙaddara’ Na faɗa a raina, a fili kuma kau da kai na yi ƙwalla tana kawo idona na ce”Ka sauke ni a asibiti”.
“Ba ki da lafiya ne?” Ya tambaya hankalinsa na kan wayarsa da ya ciro daga aljihu.
Na ce”E, ba ni da lafiya”.
Ya ce”Mene ne yake damunki?”
Na ce”Tsakanina da likata ne”.
Ya ce”Ok, idan na fita zan turo likita sai ki yi masa bayani”.
Na ce”Asibitin nake son zuwa”.
Kai tsaye ya ce”Ba za ki je ba”.
Da sauri na sha gabansa a harzuƙe na ce”Na gaji! Na gaji da wannan mulkin mallakar da kake yi mini, na gaji da yadda kake tauye ni, ba zan zuba ido ka kashe min rayuwa ba fa, na gaji da zama babu haihuwa, ina son ganin jinina, don na gane a yanzu su ne gatana kuma abun ɗebe kewa ba kai ba!” Na rushe da kuka ina tuna girman kuskuren da na yi na biye wa namiji cikin guguwar soyayya, wacce ba ta juye ni a ko’ina ba sai cikin karmamaki.
Tsaki ya yi, ya raɓe ni zai wuce, ai kuwa na daka tsalle na tsaya a gabansa ina cewa”Ya zama dole na haihu Saddam, ya zama dole ka je ka ƙaryata cewar ni juya a idon duniya, ko da kuwa ba za ka fasa ƙara aure ba”.
Da sigar rainin hankali ya ce”To kin tanadi loud speaker da zan yi sanarwar?”
Takaici ya sa na ji kamar na zage shi tass, amma na kasa, ina sane mijina ne, ina sane ina yi masa kalaman da ba su kamata ba, ni dai har na fara tunanin ko da aka ce mata sun fi maza yawa a wuta, to silar mazan mata za su kasance a wuta.
Ina yi masa wannan kallon na tsantsar takaici ya fice daga falon yana cewa”Na aiko likitan ko dama rashin lafiyan naki na manufa ne?”
Na ce”Ba na so, kar ka aiko min kowa, ni zan yanke nawa hukuncin”.
Ya ɗaga murya ya ce”To idan kin tashi yanke shi hukuncin ki wasa wuƙar”.
Ina kallon shi har ya shiga motarsa, waya kare a kunnensa, mai gadi ya buɗe masa gate ya bar gidan.
Da baya da baya na koma na zauna a kujera, na fashe da kuka, kukan kewa, ina kewar haihuwa da son ganin yarana, a wannan karon na shirya fito na fito da Sadam indai a kan haihuwa ne, ko ya bar ni na haihu ko kuma na haƙura da auren bakiɗaya, ai ana cewa mace ta yi haƙuri ta jure baƙinciki namiji ne saboda tunanin makomar yaranta, to ni kuma babu yaran ballantana na ce zamansu nake yi, na kai kamar minti ashirin a zaune kafin na tashi, na ɗauki jakar tawa na share hawaye na kama hanyar fita tsakar gidan, a bakin gate din na tsaya na gaishe da dattijon mai gadin, ya amsa yana mayar min da gaisuwar,ganin ba shi da niyyar yunƙurawa ta buɗe min yasa na ce”Baba zan fita ne”.
Ya ɗan diririce kafin ya ce”A! Amma…Hajiya cikin girmamawa nake sanar da ke cewar Alhaji ya ce kar na sake bari ki fita, ki yi haƙuri, a gafarce ni,umarni ne daga sama”.
Na ce”Don Allah ka buɗe min, ba ni da lafiya ne, asibiti zan je, kuma ba zan bari ya ga laifinka ba wallahi”.
Cikin damuwa ya ce”A dai yi haƙuri Hajiya, a kan aikina nake”.
Huci kawai na yi na juya na koma cikin gidan da gudu, kitchen na nufa don na gama yanke hukuncin da nake ganin shi ne mafitata a halin yanzu, wuƙa na zaro sabuwa dal na cire ta daga gidanta, zuciya tana ƙara zuga ni da ingiza ni na aikata kawai, tare da gudunmawar tunawa da irin tauye ni ɗin da aka yi aka cutar da ni, don haka na ji dole na ƙwatarwa kaina ‘yanci.
08028966015
[03/10, 8:10 pm] Sadiya Abdulrazak: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LnQJ26F7GLvLHNQHkwpWw1
*KU YI MANA ADALCI*
NA
Sadiya Abdulrazak
Page 2
Assalamu Alaikum my people dafatan kunanan cikin aminci sunana ummuh sayyeed traditional medicine center Zaria dealer in all kinds of magungunan mata turarukan wuta sudaniss dilka skin care products
Alhmdulillah call 09065504546 Ina mai farin cikin sanar da Yan uwana mata ni yar mutan Chadian zan muku promo 🎤🎤🎤🎤
Tundaga gobe__ 9/19/2025__ harzuwa end of this month dinnan in Sha allahu
Ina matanda sukefama da rama
Ina masu fama da lalacewar nono
Ina matanda sukefama da rashin gashi da lalacewar gashi
Ina Maison taga komai nata cifcif
Ina Mai
Hmmm kukanki yazo karshe dakila wadda ita batasan
Dadin jima’ba shin kinsan ko mijinki ne bai baki abinda kikeso wato baida kuzari munada maganin da zamubashi
Ga kayan dazamu yi promo Nan akan 4,500 kacal 👌👌
Maganin sanyi 1,k
Tsumin bom 1,500
Madarar tabaje 1k
Gumbar Milo 1k
Garin yaukayauka emergency 1,500
Garin kinfi kaza 1,500
Hmmm duk waddanan kayanfa ,naira
4,500 💃 munamaraba damasu siyan Daya ko sari
Buɗe damtsen hannuna na yi, na ajiye wuƙar na fara matsa hannun nawa don jin yadda zaman implant ɗin yake, na ci alwashin yau ba zai kwana a hannuna ba, ko da kuwa zan mutu ne wajen azabar cire shi, na ɗora wuƙar a daidai wajen zan yanka hannun, tsoro da tausayi kaina suka kama ni, zuciyata ta ce mini ‘A’a fa Sayyada wannan kasada ce, idan kika yanka kanki jini ya ɓalle miki komai zai iya faruwa, ƙila azaba ta sa ki kasa fita daga ɗakin ma ballantana ki nemi agajin Baba mai gadi, shikenan sai ki mutu a banza burin Sadam ya cika, ya ji daɗin auren shi’.
Wata zuciyar kuma ta shiga zuga ni da faɗin’Babu abin da zai faru, ki daure kawai ki yanka ki zare tsinke, ya zo ya same miki cikin jini dole hankalinsa zai tashi ya san tura ta kai ki bango, ƙila silar haka ya fara yi miki adalci.
Na dawo falo na zauna da wuƙar a hannu, na yi zuru ina tunanin na yi ko kar na yi? Na san dole akwai zafi, kuma yanzu safiya ce, awa nawa zan yi a cikin azabar nan? Sai dab da magriba yake dawowa fa, na daɗe ina ƙullawa da kuncewa kafin na bar shi a kan zan yanka ɗin, amma sai na ji dawowar shi gidan, yadda ba zan sha wuya sosai ba, da haka na mayar da wuƙar, na fara gyaran gidan, na gama na nemi waje na kwanta ina ta tunanin rayuwa, zuciyata cike da kewa, sai a yanzu ne da Sadam ya canza min hali ya juya min baya kaɗaici yake damuna, kaɗaicin haihuwa da na abokin shawara ko ƙawa.
Wayata na ɗakko na kira mahaifiyata muka gaisa, mun jima muna fira, amma na kasa faɗa mata damuwata, na san idan na faɗa mata planing na yi a duk tsayin shekaru ukun nan da aurenmu ya yi, shi yasa ban samu ciki ba za ta ga laifina sosai, kuma za ta yi min faɗa, musamman ganin yadda ta fi kowa nuna damuwa a kan rashin samun cikina, bayan mun gama na kira Babana, shi ma suka gaisa, sannan na kira ƙanwata Salma ita ma mun daɗe muna fira, ita dai Salma kamar ita ta tsarawa kanta, ba ta da wata matsala a gidan aurenta, kullum cikin yabon mijinta take yi, ga kuma ɗansu mai shekara ɗaya abun sha’awa, daga nan na kira Anisa, ƙawata kuma ‘yar’uwarta, yau sai na ji kamar na bayyana mata damuwata, da kuma abin da nake shirin aikatawa ko za ta ba ta shawara, amma kuma ba na son a ga laifinta, don ni kaina sai yanzu nake raina wayona, na yi nadamar biyewa daɗin bakin namiji, kodayake umarni ma zan ce, tun da a lokacin ba na iya tsallake umarninsa shiyasa na amince da tsarinsa.
Ƙalau na gabatar da wunin ranar, na yi girki da yamma na ci, amma iya cikina, dab da zai dawo gidan na ɗakko wuƙar na zo falo na zauna, har da saka riga mara hannu don na ji daɗin gabatar da aikina, idan na tuna azabar da zan yi wa kaina sai hawaye ya ƙwace min, dab da magriba na ji ƙarar buɗe masa gate, na ɗauki wuƙar da sauri na runtse ido zuciya na ƙara zuga ni, na luma ta a daidai saman inda tsinken yake na yanka da ƙarfi, nan take kuwa na saki wuƙar ta faɗi, na ƙwalla ƙarar azaba ina fashewa da kuka, babu jira jini ya wanke min hannu, duk yadda na so na zaro tsinken haƙura na yi, saboda zafin da nake ji ba zai bari na taɓa wajen yankan ba, kwanciya na yi a wajen ina kuka riƙe da hannun.
Shi kuma kamar ya san tana neman taimakonsa, ya nemi waje ya zauna a baranda, Safna ta kira shi yana hanya ya ce mata idan ya ƙarasa zai kira ta, Safna ƙawarsa ce wacce ita ta maye gurbin Sayyada a yanzu ta fannin neman shawara da tattauna muhimman batutuwa, uwa-uba kuma matar da zai aura, sun shaƙu sosai, a asibitin da take aiki suka haɗu, lokacin ya shiga ganin likita, yanzu ma fira kawai suke yi tana jaddada masa yau a gidansu zai ci abincin dare, ya tabbatar mata da zai halarta, daga nan suka cigaba da fira.
Ina can kwance ina kukan azaba, shiru bai shigo ɗakin ba, ga shi ba na so ya gane ina nadamar yanka hannun nawa ballantana neman taimakonsa, sai da ya gama wayarsa a tsanake ya shigo ɗakin, kukana ne ya fara sauka a kunnensa, kafin ya gan ni riƙe da hannu jikina ya wanke da jini, zuciyarsa ta doka, ya saki wayar hannunsa da sauri ya ƙarasa inda nake yana cewa”Sayyada! Ke mene ne ya same ki?”
Ban ce komai ba sai kukana da ya tsananta, yana ganin wuƙar tsoro ya ƙara kama shi, da ƙarfi ya ce”Me ya same ki!? Kar ki ce mini yanka hannunki kika yi”.
Cikin kuka na ce”Na gaji, wallahi yau ba zan kwana da tsinken cutarwar nan a jikina ba, cire shi zan yi, ko da zan mutu, indai kai a tsarinka ba ka son haihuwa da ni har abada to sai dai yau ka sake ni, na gama planing har abada”.
Na kai hannu zan ɗauki wuƙar, ya riga ni ɗauka, duk ya firgice ya ce”Kin fara shaye-shaye ne Sayyada? Ko taɓin hankali kika samu?”
Duk da a raina na san ƙarya nake yi ba iya sake saka wuƙar zan yi a jikina ba, amma haka na daure na yunƙura da nufin ƙwacewa ina cewa”Ka ba ni! Ka ba ni na ƙarasa aikina Sadam, kuma ka sake ni na gaji da zama da kai”.
A raunane ya ce”Ki yi haƙuri don Allah, mu ke na kai ki asibiti, jininki yana ta zuba fa”.
Da ƙarfin hali na ce”Babu inda zan je, na fi so na mutu”.
Ya rasa ma ta ina zai fara, ya tuna idan ya kaita asibiti za a zargi wani abu, don haka ya kira likitansu a waya ya sanar da shi abin da yake faruwa, ya ce ya kawo ta asibitin shi yanzu zai je ya same su, ya ajiye wayar yana cewa”Sayyada tashi mu je asibiti kin ji, za a cire miki shikenan”.
Da ƙyar ya lallaɓa ni na yarda mu je asibitin, sai da na ga ran shi ya fara ɓaci, na ji tsoron ya yi zuciya ya rabu da ni, a mota muna tafiya yake cewa”Haba Sayyada ba ki kyauta min ba sam, wannan ai kin tona mana asiri, me yasa ba za ki faɗa min ke dole kin gaji da planing ɗin ba?”
Takaici kamar na buge bakinsa, da wane yaren yake nufin na nuna masa gajiyawata ya gane idan ba wannan fa na yi yanzu ba? Ban ce komai ba har muka ƙarasa asibitin, da yake asibiti ne mai zaman kansa kuma yana da hanya nan take aka shiga ba ni taimako ba tare da bin diddigin abin da ya faru ba.
Likitan sai nasiha yake mini bayan an gama yi mini ɗinkin, ina ta hawaye, ya saka min ruwa, ya kalli Sadam ya ce”Zan yi mata allurar da za ta samu bacci”.
Ya ce”Don Allah mu je gida ka yi mata”.
Ya ce”A’a ba zan sallame ta a yau ba fa, a ƙalla ta yi kwana uku sai ku koma gidan na cigaba da zuwa ina duba ta, amma yanzu dai ba zan yarda ku tafi gida ba, kuma yana da kyau ta yi bacci”.
Sadam ya shiga damuwa, ya ce”To tsaya mu yi magana da ita kafin allurar, la ba mu waje don Allah”.
“Ok” kawai ya ce ya bar ɗakin.
Ya zauna a gefen gadon yana kallona, kallon ma na kasa fassara shi, amma kamar ba na tausayi ba ne, sai dai kuma fuskarsa babu ɓacin rai sosai, ya ce”Amma wallahi ke daƙiƙiya ce, ban da hauka ta ya za ki aikata wannan shiryen? Yanzu idan ‘yan’uwa suka ji uban me kike so mu ce musu? Yanzu da aka ba ki gado wa za a kira ya yi jinyarki?”
Na ce”To ai ba na shakkar kowa ya ji abin da ya faru, tun da dai na rabu da tsinken nan shikenan, idan ma zancen ya fito kai ne da kunya, kai ne za a zaga a ce ka cutar da ni”.
“Ya isa haka!” Ya daka min tsawa, sannan ya dora da faɗin”Duk wannan shirmen da kike yi ba zai hana ni bin umarnin mahaifiyata na yi aure ba, ko ki mutu ko ki rayu zan yi aure, don haka kina da zaɓi, ko ki kwantar da hankalinki ki cigaba da bin uamarnina mu zauna lafiya, ko kuma ki tada hankalinki ki yi ta shiga ƙunci da damuwa, kina kallo kuma ni zan samu kwanciyar hankali da matata”.
Ina kuka na ce”Ba zan yi maka biyayya ba, ba zan sake bin umarninka ba, kuma ba zan sake kwana a gidanka ba matuƙar ka auri wata, sai dai ka sake ni wallahi, ai ba kai kaɗai ba ne namiji”.
Wannan karon dariyar rainin hankali ya yi ya ce”Ba ni kaɗai ba ne namiji, amma ni kaɗai ne namijin da za ki rayu da shi har abada, ke da zaman aure da wani sai a lahira idan ana yi, kuma aurena da ke ki saka a ranki takalmin kaza ne, mutuwa ce kaɗai za ta rabu, don haka nan gaba idan kin tashi azabtar da kanki a wuyanki za ki saka wuƙar ba hannu ba, shashasha!”.
Ya tashi yana harara ta ya ce”Kar ki sake ki kira wani ki ce za ki yi kuskuren sanar da shi, zan nemo wacce za ta kula da ke, saboda ba zan iya kwana a asibiti ba”.
Na ce”Ba na buƙatar taimakon kowa, kuma ka kawo min wayata!”.
Ya fita ba tare da ya sake ce mini komai ba.
Gida ya koma ya yi wanka, yana fitowa ya shirya ya nemi waje ya zauna ya riƙe kansa, bai taɓa tunanin ƙarfin zuciyar Sayyada ya kai ta aikata haka ba, ana wannan halin kiran Safna ya sake shigowa wayarsa, ya ɗauka a sanyaye yana faɗin”Baby”.
Ta ce”Beb lafiya ba ka ƙaraso ba?”
Ya ce”Sorry ba zan samu zuwa, a halin yanzu ba na cikin nutsuwata ma wallahi”.
Ta ce”Subhanallah! Mene ne ya faru?”
Ya yi guntun tsaki ya ce”Wannan mahaukaciyar yarinyar ce ta yanka jikinta”.
Gabanta ya faɗi ta ce”Ban gane ba, yankewa ta yi ba ta sani ba?”
Ya ce”Ba na faɗa miki ta takura min sai ta haihu ba?”
Ta ce”E ka sha faɗa min”.
Ya ce”To shi ne da na hana ta fita yau ta ɗauki wuƙa ta yanka hannun za ta cire”.
Safna a ranta ta ce’Matsiyaciya dama ta mutu, na huta’
A fili kuwa sai ta nuna alamar damuwa, ta ce”Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Amma dai yankan bai shiga sosai ba ko? Yanzu tana ina, na zo na duba ta?”
Ya ce”Ki kwantar da hankalinki ai ba abar tausayi ba ce, a kanta aka fara kishi?”
Ta ce”A’a bai kamata fa ka ce haka ba, ka san kowace mace da kalar nata tunanin wajen kishi, ka yi mata uzuri, ni wallahi tausayi take ba ni ma, yanzu kuna asibiti?”
Ya ce”Na dawo gida, ba ta isa ta saka ni kwanan asibiti saboda haukanta ba, tunanin wacce zan nema ta kwana da ita nake”.
Da sauri ta ce”I can! Ba sai ka nemo kowa ba ni zan zo na kwana da ita”.
Ya ce”A’a Safna, kar ki takura kanki, kuma kin san idan ta gane ke ce ba za ta ji daɗi ba”.
Ta marairaice ta ce”Na yi maka alƙawarin ba za ta gane ba, wallahi ba zan nuna mata komai ba, ko dai ba ka yarda da ni ba ne Beb?”
Ya sauke numfashi ya ce”Wallahi na yarda da ke, kawai dai na yi mamaki, na yi zaton kishi ba zai bari ki je ba”.
Ta ce”Wallahi tamkar yadda zan zauna da ƙanwata uwa ɗaya uba ɗaya haka zan zauna da Anti Sayyada”.
Ya ce”Na gode sosai my wife to be, amma a gida za a bar ki?”
Ta ce”Duk da dai yau ba dutyn dare gare ni ba, amma zan ce zan karɓawa ƙawata saboda ɗanta ba shi da lafiya, za a iya barina”.
Ya ce”Wow! To bari na zo na ɗauke ki ko?”
Ta ce”A’a, kar ka zo za a zargi wani abun, bari na zo kawai gidan sai ka kai ni”.
Ya ce”Za ki taho min da abincina da kika yi min? Yunwa nake ji”.
Ta ɗan yi shiru na sakanni kafin ta ce”A’a ba zai yiwu na taho maka da shi ba, za a zargi wani abun, ka ga an san kai na yi wa girkin, kuma yau ba ni da aikin dare, idan na yi ƙaryar zan karɓawa wata an yarda, ba za a yarda da ni ba idan na ɗauki abincinka”.
Ya ce”Good! Kina da tunani”.
Ta ce”Amma dai idan na zo zan dafa maka”.
Ya ce”Na gode sosai ina jiranki a bakin titi”.
Suka ajiye waya, yana sauke ajiyar zuciya.
Sannan ya tashi ya fita da mota, bayan ya ɗakko ta a hanya tana ta nuna jimaminta, kamar ta fi shi son Sayyada, da suka ƙarasa gidan ita ta gyara wajen da jinin ya ɓata, sannan ta shiga kitchen ta ɗora masa macaroni jollof, a falo ya zauna yana ta danne zuciyarsa, da kuma shaiɗan ɗin da yake ta ƙissima masa ya gwada sa’arsa a kan Safna, ta taimake shi ko da romance ne, lokaci ɗaya fitinanniyar sha’awa ta taso masa, duk da Safna ko hijjabi ba ta cire ba.
08028966015
[03/10, 8:10 pm] Sadiya Abdulrazak: *KU YI MANA ADALCI*
NA
Sadiya Abdulrazak
Page 3
In kunji ana wata miyar sai a maqota to ba ko ina bane sai kamfanin GHT🤩 Ka samu kudi dasu kuma ka qurewa cuta lamba duk dasu, ma’ana dai akwai magunguna tun daga na diabetes, malaria, infection zuwa gyaran jiki💃🏻 kuma zaka iya zama member na company a rinqa baka percentage kai har kyautuka, bonus ga kuma abinda zaka samu monthly.kunemi 👉🏻07064627917 ko kawai
dannan link don shiga group ɗina kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/DmQX0AKyyX8BODoIiLoKj8?mode=ems_copy_t
Allah Ya sani aurenta yake son yi, duk da mutum ba ya hana kan shi jin sha’awar wanda ya yi masa, amma a yanzu dai ba irin yanayin baya yake ji ba, ji yake kamar ya gwada ta ko za ta amince ko sumbatarta ne ya yi, wata zuciyar tana hana shi, tunawa da yadda daren farkonsu da Sayyada ya kasance, ya ci wa daren buri sosai, amma ƙarshe sai ga shi ya zo masa a baibai, a ranar ko sha’awarta bai ji ba, haka suka kwana ƙalau ba wani abu da ya shiga tsakaninsu, haka aka kasance babu wani marmari da shauƙin juna, to gaskiya yana son yin ƙara’i a wannan sabon auren da zai yi, don haka ya daure ya dinga yaƙi da shaiɗan har ya samu ya fi ƙarfin zuciyarsa bai nunawa Safna komai ba, a baki ta dinga ba shi abincin, kuma har vedio ta yi masa, dama ta yi wasu a kitchen, bayan ya gama ci ta ce ya ɗakkowa Sayyada wasu kayan ko za ta yi wanka, ya ɗakko suka tafi, da abincin da kuma ruwan zafi.
A hanya yake cewa”Allah Ya sa dai kar ta gane, don Allah ki yi iya yinki don ganin kin kaucewa yadda za ta sanki, tukuna ma me za mu ce mata? Ke wace ce?”
Ta ce”Sai mu ce ni ‘yar’uwarka ce, na zo zan kwana biyu, kuma za ka iya sirri da ni shi ne ka ce wa Momy na zo gidanka na kwana biyu kafin na tafi”.
Ya ce”Kai na gode Allah, da ya ba ni mace mai basira, i love You”.
Ta yi murmushi ta ce”Ai ka cancanci hakan ne Love”.
Lokacin da suka ƙarasa ɗakin bacci take yi, suka tsaya suna kallonta tana ta bacci, ya taɓe baki ya ce”Kin dai ganta, ga shirmen da ta yi abin da ya ja mata”.
Safna ta ce”Allah sarki, Allah Ya ba ta lafiya, kai ma kuma bai kamata ka kafe a kan ba za ta cire tsinken ba, yanzu ga shi ta cutar da kanta”.
Ya ce”Share ta”.
Ya fita ya siyo kayan shayi, biredi, kaza da fruit, ya kawo ya ce idan ta tashi sai ta saka ta ci abincin, suka zauna suna ta fira, yana tambayarta anya za ta iya kwana kuwa, dariya kawai ta yi ta ce ni da na saba kwanan asibiti, babu komai ka je kawai”.
Ya ce”To na gode sosai Baby, ku kwana lafiya”.
Ya fita yana waiwayenta yana murmushi, a ransa kuwa daɗi yake ji sosai, don ya fara hango yadda gidansa zai wanzu da zaman lafiya idan ya aure ta.
Bayan fitarsa ta bi Sayyada da kallon wulaƙanci, wayarta da ya ba ta ta ajiye mata ta ɗakko, a hakanli ta ɗago yatsan Sayyadar ta ɗora a wayar key ɗin ya fita, ta sauke ajiyar zuciya ta matsa gefe, lambarta ta fara ɗauka, sannan ta shiga cikin wayar ta fara bincike, ba ta ga komai na rashin gaskiya ba, don haka ta ajiye mata, sai ta dubo lambar tata a whatsApp ta tura mata vedion Sadam wanda take ba shi abinci a baki, da kuma wanda take yin girki a kitchen, ta tura mata shi amma ta once, yadda idan ta kalla sau ɗaya shikenan ba za ta sake kalla ba, ta haɗa da rubutu a ƙasan ta ce”Ya kamata ki gane miji irin naki ba wanda za ki nasaka kanki a kansa ba ne, kin dai gani kina asibiti shi kuma yana tare da wata, cewa ya yi ya ji daɗin baki gado da aka yi ma, sannan ba zai iya kwana da ke ba, yanzu haka yana can tare da wata, ta yi masa girki kuma za ta kwana a gadonsa, ban faɗa miki don ki tada hankalinki ba, sai don ki nutsu ki gane da wa kike tare, mijin ƙaton mane min mata ne”.
Tana ta kallo a wayarta, don ta kunna data ba ta ga Sadam online ba, dama ya ce mata da wuri zai yi bacci, har ta gama ta yi bacci, Sayyada ba ta tashi ba, ita ma ta kwanta a sallaya ta lulluɓa da hijjabinta, bayan ta zare layin da ta tura mata saƙon da shi daga cikin waya, ta fara baccinta hankali kwance.
SAYYADA
Sai ƙarfe ɗaya na dare na farka, na bi ɗakin da nake da kallo, zuciyata ta fara zafi, ƙwalla ta zubo min, tunawa da duk ni na ja wa kaina kasancewata a nan ɗin, na kalli hannu na da ke naɗe da bandeji, yana yi min zafi har yanzu, hawaye ya sakko min, cikin wayam yunwa nake ji, fitsarin da nake ji da kuma tunanin ban yi sallar magriba ba da isha’i ba, ya sa na yunƙura na tashi zaune, gabana ya faɗi ganin wata kwance a ƙasan gadon, tsoro kuma ya ɗan kama ni, duk da na yi tunanin Sadam ne ya aiko ta, to amma wace ce? Na san dai ƙanwarsa Amna ko mutuwa zan yi ba za ta zo ta zauna da ni ba, saboda tsanar da ta yi min, kuma ban da ita ba shi da wata ƙanwa, sannan ba zai iya zuwa ya faɗa a gidanmu ba ballantana na ce ko Khadija aka ba shi, wannan ma babba ce ta fi Khadija ƙanwata, da wannan saƙe-saƙen na yi hanyar banɗaki, sai kuma idona ta sauka a kan wayata, na ɗauka na buɗe ta, da text massage na fara cin karo, wanda ke ɗauke da cewar “Ki duba na ajiye miki saƙo a whatsApp mai muhimmanci”.
Da sauri na kunna data na shiga whatsApp ɗin, hannuna har rawa yake yi, saƙon da na gani da baƙuwar lambar na fara buɗewa, na danna vedios ɗin, wanda take ba shi abinci a ba ki na fara gani, ina karanta maganar kuma hankalina ya ƙara tashi, wallahi saura kaɗan fitsarin da nake ya kufce min, da sauri na ƙarasa banɗakin riƙe da wayar ina jin kamar na saka kuka, kafin na yi alwala sai da na karasa kallon sauran, tabbas na gane kitchen dina, ga kuma falona, kuma shikenan ba ni da damar sake kallon vedion ballantana na kafa shaida da shi, zargina ya zama gaskiya, yau dai ta tabbata mijina yana neman mata, kamar yana jira na bar gidan? Na fashe da kuka sosai, ina alwala ina kukan, sai da na fito daga banɗakin na share hawayen, na ajiye wayar a gadon na shiga tashin wacce take baccin.
“Baiwar Allah” Na faɗa ina taɓa ƙafarta, ta farka ta yaye fuskarta daga lulluɓar, gabana ya faɗi ganin ban santa ba, ban taɓa ganinta ba, za ta girmi tun a kallo ɗaya.
Safna ta ce”Anti Sayyada sannu, kin tashi ashe”.
Na ce”Yawwa, amma wace ce ke?”
Ta ce”Ƙanwar Yaya Sadam ce, zuwa ya yi gidan ya ɗakko ni zan kula da ke”.
Na ce”Na gode, ara min hijjabin zan yi sallah”.
Ta ɗakko jaka tana cewa “Ai ya haɗo miki ma da hijjabi a cikin kayanki”.
Na karɓa na saka, ta tashi ta ba ni sallayar na tada sallah, kafin na idar ta haɗa mini shayi, ta zuba min macaroni da kazar, zuciyata zafi take yi min, shi yasa na ɗaga hannu na daɗe ina ta addu’a Allah Ya sassauta mini abin da nake ji, har sai da na ji mai ciwon ya dame ni da zafi, sannan na sauke, ta kalle ni ta ce”Sannu Anti Sayyada ga abinci”.
Yunwa nake ji don haka na yunƙura zan ɗauka, amma da na tuna wai wata ce ta dafa abincin sai na koma na zauna, ƙwalla ta kawo idona na ce”Ya sunanki ke ɗin? Kuma ban san ki a ‘yan’uwan shi ba”.
Ta yi murmushi ta ce”Sunana Hafsa, kuma ni da babar shi da babata uwa ɗaya uba ɗaya suke, ina yawan zuwa gidan ai, don dai ba kya zuwa ne sosai, su ma kuma ‘yan gidan ban ga suna zuwa gidan naku ba shiyasa ba za ki san ni ba”.
Na ce”Ok, amma wannan abincin daga ina aka same shi?”
Ta ce”E to, ni dai ya kawo ne kawai”.
Na ji sam ba zan iya ci ba, ba zan iya cin abin da karuwarsa ta dafa ba, duk da yunwar da nake ji haka na ƙi ci, na sha iya shayin, na ci ayaba, ta ba ni magani na sha na koma na kwanta ina jin zuciyata tana yi min nauyi.
Sadam ya daɗe yana cutata, ya daɗe yana ƙuntata mini, tun kafin ya aure ni yake gana min azaba, sai yaushe ne zan fara morar garɗin soyayya wai? Bayan aurenmu na yi zaton shikenan ni da baƙinciki sai hange daga nesa, ashe zaman yana can a gaba, zuciyata dai ta dinga zuga ni a kan na bar asibitin nan kawai na tafi na je na rutsa shi da karuwar a yi wacce za a yi, ba tare da dogon tunani ba na tashi, na sauka daga gadon, na zura hijjabi, Safna ta kalle ni ta ce”Anti ina za ki je?”
Na ce”Gida zan tafi, ni na ji sauƙi”.
Sai ta tashi da sauri ta ce”A’a don Allah ki yi haƙuri ki zauna har sai an sallame ki, kuma yanzu dare ya yi ma”.
Tsaki kawai na yi, na buɗe ƙofar na fita, da gudu ita ma ta fito ta shiga ofishin likitocin, ta sanar da su, sai ga likitan ya fito da saurinsa ya taddo ni ya ce”Madam ya haka, mene ne ya faru?”
Na ce”Ka sallame ni kawai ni a gida zan kwana”.
Ya ce”Ki yi haƙuri ba zai yiwu na sallame ki yau ba, sai dai ko zuwa gobe, kin ga dare ya yi ai”.
Sai kawai na fara hawaye, sai yanzu ma na yi tunanin ba zan samu abun hawa ba ai, ya ce”Ki yi haƙuri ki koma pls”.
Safna ta kama hannuna tana ba ni haƙuri ita ma, ta ja ni sai na bi ta muka koma ɗakin, baccin da ban koma ba kenan, na ga tsayin daren sosai, na yi kuka na ƙoshi, na kuma tuna abubuwa da dama wanda a yanzu nake ndamar aikata su.
Da asuba Safna tana yin sallah ta ce za ta tafi gida, za ta dawo min da abinci, na yi mata godiya, da ta fita tsayawa ta yi ta kira Sadam a waya ta faɗa masa ta bar asibitin, ya kamata shi ya je, ya ce”Na gode sosai Baby, amma fa ni ba zan fita yanzu ba gaskiya, sai zan tafi aiki sai na leƙa ta”.
Ta ce”Amma fa ya kamata ka je da wuri, don jiyan ma cewa ta yi ba za ta kwana a asibiti ba da ƙyar ta haƙura, likitan ya ce yau zai sallame ta”.
Ya ce”Au haka ma za ta yi? Ai da ya bar ta ta dawo ɗin, ta zauna idan hannun ya riɓe aka yanke kin ga ni ba zan zauna da musaka ba ai”.
Safna ta yi dariya ta ce”Ba ma zai faru ba, ka je dai don Allah, sai ka kai mata abincin kari, jiya shayi kawai ta sha”.
Ya ce”Gaskiya ni za ta takura ni, bacci bai ishe ni ba, ina ta tunanin ya kika kwana”.
Ta ce”Ya na kwana ko dai ya matarka ta kwana?”
Ya ce”Wallahi ke nake tunani, an ɗora miki nauyin da ba naki ba, ga shi ina fargabar kar ta gano wace ce ke a samu matsala”.
Ta yi dariya ta ce”Idan ma aka gane ba na jin za a samu matsala ai na ga Antin tawa tana da haƙuri”.
Ya ce”Za ki jira na zo na ɗauke ki?”
Ta ce”A’a zan tafi a adaidaitasahu, zan yo muku girkin kai da ita sai na dawo”.
Ya ce”Me zai hana ki zo ki yi a nan gidan namu? Please”.
Ta ce”To bari na zo ɗin”.
Ta ɗan jima a tsaye kafin ta samu adaidaitasahu ta hau, ta kama hanyar gidan Sadam, da ta ƙarasa kiransa ta yi ya zo ya buɗe mata, suka ƙara gaisawa, ta shiga kitchen da sauri, ya bi bayanta yana jin yadda yanayinsa yake canzawa, sai dai yana ta ƙoƙarin dannewa, kayan ciki ta gyara ta ɗora sannan ta ɗora shayi, ta ɗakko doya tana firewa, shi kuma yana ta kallonta fa burgewa, ji yake ina ma a ce an yi auren matarsa ce, da babu abin da zai hana shi rungume ta ko zai ji sassaucin yadda sha’awarta take gigita shi, amma babu dama, a gaskiya bai taɓa gwada yi mata ko maganar batsa ba, bai sani ba ko za ta amince da romance, ya dinga sauke numfarfashi, yana amsa mata firar da take yi masa da e, ac, har dai ta ce”Beb ko ba ka da lafiya ne?”
Ya ce”Lafiya ba lau ba”.
Ta ce”Mene ne yake damunka?”
Ya ce”Ke ce, kewarki ce za ta kassara ni”.
Ta ce”Kewa kuma? Ba gamu a tare ba?”
Ya ce”Ba irin wannan kasancewar ba ai, zan so wacce ta fi wannan kusanci”.
Ta yi murmushi ta ce”Ni dai ban gane ba, kuma ba na so na na gane, pls mu bar zancen”.
“Ok” Kawai ya ce, ya tashi ya bar kitchen ɗin, ta bi shi da kallon tausayi cikin shauƙin so da ƙauna.
Har ta kammala komai bai dawo kitchen ɗin ba, ta zuba wanda za a kai wa Sayyada, ta zuba masa na shi ta fito falon, ta same shi kwance a kujera, ta ajiye tana cewa”Na yi zaton ma ka yi wanka kana karyawa sai dai kawai ka tafi kai mata?”
Ya sauke numfashi ya ce”Yanzu zan yi, za ki taya ni ko?”
Ta yi kamar ba ta ji shi ba, ta ce”Ka ci abincin”.
Ya ce”Ki zo mu ci mana”.
Ta girgiza kai alamar a’a.
Ya ce”Don Allah zauna mu ci, ya min yawa ma ai”.
Ta zauna suna ci suna kallon soyayya da murmushi, har wanke-wanke ta yi ta gyara komai tsaf, ta juyo za ta bar kitchen ɗin, ta gan shi tsaye ya tare hanya, kuma ba kamar ɗazu ba da yake da jallabiya a jikinsa, yanzu gajeren wando ne kawai a jikinsa, da alamar kuma daga wanka ya fito, tsoro ya kama ta, kafin ta yi magana ya ce”Safna can I give you a huge? Please my wife to be”.
SAYYADA
Na yi zaton tun asuba Sadam zai zo, na ji shiru har gari ya waye, ga yunwa ina ji, ina cikin jerin mutanen da ɓacin rai ko jinya ba ya hana su cin abinci, ko macaroni da ban ci ba jiya kishi ne, na ƙara haɗa shayi na sha, na ci kazar, don da na duba ta na fahimci gashin bakin titi ne ba ita ce ta gasa ba, ina ci ina hawaye, idan na tuna Sadam yau ya kwana da wata a gadonmu na sunna sai na ji kamar rayuwata ta zo ƙarshe, fitar numfashina har canzawa ya yi.
Wajen ƙarfe tara da rabi na gaji da jiran shi, na daure zuciyata na ɗauki waya ba kira shi, kira biyar bai ɗauka ba, zuciya tana ta raya min yana can tare da mace sun ɗora daga inda tsaya daren jiya, sai na ji ba zan iya cigaba da zaman asibitin ba, duk da da safen nan da likitan ya duba ni ya sake ba ni haƙuri ya ce na bari Sadam ɗin ya zo sai a ji yadda za a yi, sai ya dinga zuwa gida yana duba ni kullum, amma na kasa haƙuri na tashi na ɗauki wayata na saka hijjabi na fice, Allah Ya taimake ni har na bar cikin asibitin ba wanda ya gane ba ni da gaskiya.
Na tari adaidaitasahu na hau, a hanya ma sai hawaye nake yi, ina kuma fargabar abin da zan je na tarar, wallahi Indai ya tabbata da wata a gidan dole ya sake ni duk taurin kansa.
08028966015
[03/10, 8:10 pm] Sadiya Abdulrazak: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LnQJ26F7GLvLHNQHkwpWw1
*KU YI MANA ADALCI*
NA
Sadiya Abdulrazak
Page 4
Assalamu Alaikum my people dafatan kunanan cikin aminci sunana ummuh sayyeed traditional medicine center Zaria dealer in all kinds of magungunan mata turarukan wuta sudaniss dilka skin care products
Alhmdulillah call 09065504546 Ina mai farin cikin sanar da Yan uwana mata ni yar mutan Chadian zan muku promo 🎤🎤🎤🎤
Tundaga gobe__ 9/19/2025__ harzuwa end of this month dinnan in Sha allahu
Ina matanda sukefama da rama
Ina masu fama da lalacewar nono
Ina matanda sukefama da rashin gashi da lalacewar gashi
Ina Maison taga komai nata cifcif
Ina Mai
Hmmm kukanki yazo karshe dakila wadda ita batasan
Dadin jima’ba shin kinsan ko mijinki ne bai baki abinda kikeso wato baida kuzari munada maganin da zamubashi
Ga kayan dazamu yi promo Nan akan 4,500 kacal 👌👌
Maganin sanyi 1,k
Tsumin bom 1,500
Madarar tabaje 1k
Gumbar Milo 1k
Garin yaukayauka emergency 1,500
Garin kinfi kaza 1,500
Hmmm duk waddanan kayanfa ,naira
4,500 💃 munamaraba damasu siyan Daya ko sari
Page 4
Muna dab da ƙarasawa gidan na hangi wata mace ta fito daga gidan tare da Sadam, ƙirjina ya doka da ƙarfi, sai dai kafin adaidaitasahun mu ya ƙarasa tuni ta hau adaidaitasahun da ya zo wucewa an ja sun tafi.
“Tsaya! Sauke ni haka!” Na faɗa da ƙarfi don ganin Sadam ya juya da sauri zai koma cikin gidan, ko gama tsayawa bai yi ba na fito hakan ya sa na faɗi a ƙasa tim, ban damu ba na miƙe da sauri na cim ma Sadam da yake shirin shiga gidan, shi kuwa wata kunya ce da fargaba ta kama shi, saboda ya san dole ta fa Safna, kuma sai yake ji kamar za ta gane ya rungume Safna har ma ya yi kissing ɗinta a cikin gidansu.
Da sauri na fizgo jallabiyar jikinsa cikin ƙaraji na ce”Wace ce wannan!? Sadam da wa ka kwana a cikin gidana?”
Yana juyowa ya sharara mini mari, rai a haɗe ya ce”Ashe ba ki da hankali! Ni za ki yi ƙazafi a titi a bainan nasi?”
Na ci kwalarsa na fashe da kuka ina cewa”Ni za ka mara a kan hakkina? Ba zan sake yarda ka ci zarafina a kan gaskiya ta ba wallahi, wace ce wannan ka rako ta? Uban me ya kawo ta gidana da sassafe? Kuma uwar wace ta yi maka girki juya a cikin gidan nan?”
Da ƙarfe ya ƙara min marin, sannan ya fizge rigarsa, takaici da zafin zuciya suka saka ni zubewa a wajen na rushe da kuka, ga shi ƙofar gidanmu titi ne, masu ababen hawa har sun fara fakawa suna kallonmu, cak ya ɗauke ni ya yi cikin gidan da ni, ina ta zillewa ina zagin shi ina faɗin”Ka ajiye ni, wallahi yau sai ka sake ni, kuma ba zan taɓa yafe maka ba, ɗan iska, fasiƙi, mazinaci”.
“Kar fa ki fama hannunki, ba ki da hankali ne?” Ya faɗa kamar bai damu da zagin da nake yi masa ba.
Bai ajiye ni ba sai da ya sada ni da ɗakina, ya kulle ƙofar, duk da ba a hayyacina nake ba, amma idona tarr ya sauka a kan gadona, inda na ga pant yashe a gadon, an buɗe shi kamar wanda aka shanya shi, tashin hankali bai sa na tsaya na yi wa wandon kallon tsanaki ba, da tabbas zan gane nawa ne, na zauna a jikin ƙofar na ɗora hannu a kai na rushe da kuka ina cewa”Na shiga uku, Sadam ka cuce ni ba zan taɓa yafe maka ba”.
Duk wannan ihun da nake yi yana falo yana jiyo ni, shi ma kuma abun duniya ya ishe shi, ya yi nadamar gayyato Safna, Allah ne shaidarsa bai taɓa kusantar wata mace ba bayan Sayyada, duk ‘yan tsalle-tsallensa a iya waya yake ƙarewa, wannan ta san yana yi, yana yin sex chart har ya samawa kansa nutsuwa, amma ya sani a yadda soyayyarsa da Sayyada ta kasance kafin aure dole za ta iya zarginsa a yanzu, ai shi ne ya zubar da garinsa a wajenta, amma idan za ta yi masa adalci tun da bai zarge ta ba, bai kamata ita ma ta zarge shi ba, dalili kuwa shi ne ita da shi ɗin ƙwaryar sama ce ta daki ta ƙasa.
“Sayyada aurenki fa zan yi, an saka ranar aurenmu, ɗaurawa ne kawai ya rage, idan ba ki yarda da ni ba a yanzu sai yaushe? Ashe ba ni da wata alfarma a wajenki? Ba ni da matsayin da zan nemi abu ki ba ni? Please just romance, ki amince da ni, ba za ki taɓa danasani ba”. Na rintse ido tunawa da irin kalaman yaudarar da ya dinga yi mini, nuna mini yake duk matan duniya ma shi ƙyamar su yake, da ni kaɗai zai iya sex, ashe zai iya maimaitawa wata macen wannan kalaman da ya yi mini amfani da su har na amince? Kuma idan ta amince har ya aikata? Lallai duk wacce ta yarda da daɗin bakin namiji za ta sha giyar mamaki ta yi mankas har ta yi tuɓumle, ni Sayyada kura-kuran da na yi a kan Saddam sai dai na roƙi Allah Ya yafe mini kawai, amma na tabbata shugabar daƙiƙan matan duniya, a gaba za ku ji labarin kalar tawa soyayyar.
Na ci kuka na gode Allah, a nan ƙasan ɗakin bacci ya kwashe ni ban shirya ba.
Sai da ya daina jin kukana sannan ya buɗe ni, a zatonsa na yi haƙuri ne, sai ya same ni ina bacci, ɗaukata da ya yi don mayar da ni kan gado ne ya farkar da ni, na sauke idona a cikin nashi, na zabura zan dire sai na fama ciwona, na saki kukan azaba ina jin dama kawai na mutu na huta, don ganin Sadam yana azabtar da ni ba kaɗan ba.
“Sorry Sweetheart”. Ya kira ni da sunan da yake yi min daɗi a da, amma yanzu haushi na ji maimakon daɗin.
“Ka ajiye ni”. Na faɗa ina hawaye
Ya ce”Ok” Ya ɗora ni a gadon.
Na ce”Na tsane ka!”.
Ya ce”Ki dakata da wannan shirmen please, ya jikin naki?”
Na haɗiyi yawun baƙin ciki, ban da raini ni zai tambaya ta jiki? Na rufe ido kawai hawaye yana sake kwaranya daga idona.
Ya ce”Ki tashi ki ci abinci ki yi wanka ko za ki daɗin jikinki”.
Na yi shiru ban kuma buɗe idona ba, tabbas Allah Ya taimaki Sadam da ya ƙaddara wannan ciwon na hannuna, da yau ban san adadin haukan da zan nuna masa a cikin gidan nan ba, ganin na lumshe ido ya yi zaton bacci nake yi, sai ya tashi ya bar ɗakin, yana fita na tashi leƙa shi ta window, na hangen shi a falo yana waya, ba dai na jiyo abin da yake cewa, yana shiga ɗakinsa na saka hijjabi da takalmi da sauri ko wayata ban tsaya ɗauka ba, na fito cikin sanɗa na bar falon, Allah Ya taimake ni mai gadi yana cikin ɗakinsa, don haka na buɗe gidan na fita, Allah Ya sake taimakona na fita daidai adaidaitasahu ta ajiye maƙocinmu, na faɗa ina faɗa masa ya yi sauri ya ja mu tafi, ai kuwa ya bi umarnina ya fafake mu a guje yana tambayar lafiya? Na ce”Mahaukaci ne ta biyo ni, kuma gudu gare shi kamar babur”.
Ya ce”Subhanallah! Gaskiya to ba ki kyauta mini ba, salon ya yi jifa ya fasa kin glass?” Ya ƙara gudu sosai, cikin sakanni muka bar unguwar.
Na yi iya ƙoƙarina na ganin na saita kaina kafin na shiga cikin gidanmu, na shiga ɗaki na gaishe da Mama na ce ta ba ni ɗari biyu zan bawa mai adaidaitasahun, ta ba ni, na fita na kai masa, sannan na dawo ɗakin, na zauna na sunkuyar da kai.
Ta kalle ni ta ce”Sayyada lafiya kuwa? Na gan ki a hargitse me ya faru?”
Sai na fara kuka na ce”Babu komai”.
Ta ce”Babu komai za ki zo haka ba shiri ki saka ni a gaba da kuka? Ba za ki faɗa ba? Ko ke da Sadam ɗin ne?”
Na gyaɗa mata kai alamar e, don na shirya sanar da ita abin da yake faruwa, saboda a yadda nake ji a raina kawai na gama zama da Sadam, damuwa ta bayyana a fuskarta ta ce”Mene ne ya faru? Wani abun ya yi miki?”
Daidai nan kuma Baba ya yi sallama a ɗakin, na gaishe shi, bai amsa ba ya ce”Sayyada, kukan ne kike yi?”.
Mama ta ce”Ita da mijinta ne, yanzu nake son jin mene ne ya haɗa su”.
Nan take Baba ya haɗe rai kamar hadari, ya ce”Ba na son jin komai da ya shafi zaman auren Sayyada da yaron nan, don haka tashi maza ki koma ɗakinki”.
Mama ta ce”Amma Malam ba ta taɓa kawo ƙararsa ba, ya kamata a tsaya a saurare ta a ji da me ta zo”.
Ya ce”Ko da me ta zo ba mu da maganinsa, na dai shi ta zaɓa ba? To ta je ta rayu da shi, ko kashe ta ya yi sai dai na ce Allah Ya ji ƙanta, ba dai na ɗaga kai na yi masa kallon banza ba”.
Na fashe da kuka na ce”Baba don Allah ka yi haƙuri ka yafe min, wallahi na gaji da auren nan, kuma na yi nadama”.
Ya ce”Nadamarki ta zo a makare, kar ma ki sake ki furta abin da ya yi miki, ni sai dai ma na ce ya yi min daidai, kuma daga yau kar na sake jin wata matsala ta kawo ki gidan nan, tun daga ranar da na ba shi ke na faɗa muku kyauta ce ta har abada idan ya ga dama ya kwaɗa ki ya cinye, ko sakinki ya yi dama kar ki tunkaro gidana, tashi ki koma!” Ya karasa da daka min tsawa.
Na kalli Mama sai na ga ta kau da kai daga kallona, haka na fita ina gursheƙen kuka, ina tafe a hanya ina kuka kamar mara galihu ko wata ƙaramar yarinya, ba na ma kallon gabana kawai jefa ƙafata nake yi, a raina ina tambayar shin wace irin zuciya ce da babana? Allah mamallakin kowa da komai ma muna yi masa laifi ya yafe mana, shi Baba me yasa ba zai yafe min ba? Horn ɗin mota na dinga ji babu ƙaƙautawa ta bayana, don haka na waiwaya don na ga ta ina na tarewa mai motar hanya, sai na ga motar Sadam ce, na juya na cigaba da tafiya, ya fito daga motar da sauri ya sha gabana ya ce”Ki zo ki shige mu tafi, ai dama kin san ba ki da wani sauran matsuguni a gidanku, ina fata dai haukanki bai yi tsananin da har kika faɗa musu abin da ya faru ba”.
Ina kuka na ce”Abin da ya faru wanne daga ciki? To wanda kake gudun shi na faɗa musu, na faɗa musu kai mazinaci ne, fasiƙi”.
Ya ɗage kafaɗa ya ce”Fine! Ai dama sun san ni da ke mazinata ne tun tuni, don ba a mazinaci sai da mazinaciya”.
Na ji maganar kamar saukar aradu a kaina, kafin na nemi amsar ba shi, ya fizgi hannuna mai lafiyar ya ja ni zuwa wajen mota, ya buɗe ta ya tura ni, idan ma bai tura ni ba shigar zan yi wallahi, don yanzu na fahimci da gaske gidan nashi da nake ganin shi ne damuwata zaman cikinsa ya zame mini dole, sai ranar da baƙinciki ya yi ajalina zan bar shi, ya shiga motar ya ja muka tafi, na kifa kaina a cinyata ina ta rera kuka, bai yi min magana ba har muka ƙarasa gidan.
08028966015
[03/10, 8:10 pm] Sadiya Abdulrazak: *KU YI MANA ADALCI*
NA
Sadiya Abdulrazak
Page 5
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FfTzcn6WjGj4aBnWO0nMPi?mode=ac_t
Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/FeCWRcbOqP7AldNuwFmE0q
Albishirinku mutane na ayau ina gabatar muku wata shahararriyar me saida data akan farashi me sauki 1gb@#600 https://wa.me/+2347064743711 sannan tana sayarda kayan kitchen da atamfofi da sauransu kuma akan farashi me sauki da rangwame sannan tana bada sari (maman yasmeen) wacce take zaune agarin potiskum jihar yobe Tana tura kayanta kowane gari da yardan Allah
Maza kuyi join kude domin samun kayayyakinta akan farashi me sauki tana bada sarin kayayyaki kala kala mungode.
Shi ya buɗe min motar na fito, ya kama hannuna kamar gaske muka shiga falon, ya zaunar da ni a kujera, shi ma ya zauna yana riƙe da hannuna ya ce”Sayyada, Allah Ya sa dai ba ki faɗi abin da kike zargi a gidanku ba, wallahi dariya ma za a yi miki”.
Na ce”Au zargi ma nake yi kenan? Har yanzu kana da ƙwarin gwiwar da za ka kare kanka duk da shaidun da na gani da idona? Sadam wace ce ta zo ta kwana a gidan nan? Idan za ka yi zinarka ba za ka yi a waje ba sai ka ci mutuncina ka zo har cikin gida a gadona?”
Nan take yanayin fuskarsa ya juye daga na damuwa zuwa ɓacin rai, ya ce”Ke Sayyada kar ki sake danganta ni da zina, idan kuma zargina kike yi to ki fara saka minjaye, e ina nufin ni ma ina zarginki”.
Gabana ya faɗi na kalle shi hawaye yana sakko min na ce”Me na yi na zargi? Sai ka faɗi hujjarka”.
Sai ya yi tsaki ya ce”Kin ga ni ba na son tashin hankali, mu bar zancen haka, tabbas na kawo wata ta yi girki, amma wallahi babu abin da ya shiga tsakanina da ita, ni ba mazinaci ba ne Sayyada, wallahi ke kaɗai na sani a ‘ya mace”.
Na girgiza kai na ce”Faɗi wata maganar dai, don har abada ba za ka samo kalaman da za su wanke ka ba, tun da ba zargi nake yi ba na tabbatar”.
Ya ce”Kin tabbatar? Shaidar zina ba fa ba ƙarama ba ce Sayyada, kin taɓa kama ni turmi da taɓarya? Kuma kin kira shaidu sun shaida? To wallahi ki iya bakinki, ki kiyaye ni”.
Na tashi zan tafi ya janyo ni na dawo, sai na zauna ɗin na kifa kaina a kujera, ba kuka nake ba, kawai dai na rasa ma yadda zan yi, shiru na sakanni kafin ya sanyaya murya ya ce”Sayyada”.
Ban amsa, ya fara faɗin”Duk iya ƙoƙarin da zan yi don na ga mun zauna lafiya ba tare da shiga hakkinki ba ina yi, ina ta gudun cutar da ke amma ke kamar ba kya gani, idan kina wani abun sai na ga kamar kin manta wane ne ni a wajenki, kamar kin manta ramukan da kika tsallake kafin burinki ya cika ki same ni, a zatona ko ni ne na sake ki don raɗin kaina ba za ki iya cigaba da rayuwa ba, amma yau wai ke ce kike cewa na sake ki, to ba zan sake ki, don haka ki kalle Ni mu tattaunawa kowa ya gyara halinsa, ina so zamanmu ya dawo kamar na baya, ba na jin daɗin ganinki a damuwa”.
Na yi shiru ina ta hawaye, ya ɗago ni yana cewa”Ki yi magana don Allah, kin ji?”
Na ce”Sadam, za ka iya fasa wannan auren da kake shirin yi?”
Ya ce”Wallahi ba zan iya fasawa, ai na faɗa miki umarnin mahaifiyata ne, kuma ba na haɗa umarninta da na kowa a duniyar nan, ba zan iya bijire mata ba”.
Na ce”Duk da na san Momy ba sona take ba, amma a wannan karon ba don ta ƙuntata min ta sa ka aure ba, don ka samu haihuwa ne, kuma yanzu tun da an cire tsinken ai zan haihu, me zai hana ka ce mata ta ɗan ƙara maka lokaci? Idan na samu cikin sai ka ce mata kawai ka fasa, ai ba za ta ƙi ba, tun da haihuwar da take fata za a samu”.
Ya ce”Ita kuma ya zan yi na wanke ta daga ganin baƙinta da za a yi? Ina nufin su gidan su yarinyar da za a aura min ɗin, kin ga za su mayar da ita ƙaramar mace idan ta dawo ta ce an fasa, sannan auren nan saura watanni biyu, kina da tabbacin za ki samu a cikin wata biyun?”
Na ce”Idan na samu a cikin wata biyun za ka san yadda za ka yi a fasa auren?”
Ya ce”Ban yi alƙawari ba”.
Na ce”To tun da hakane babu amfanin na tsaya ina tattaunawa da kai, aure dai sai ka yi ko? Ka je ka yi, amma ka sani daga ranar da ka auri wata ba zan sake amsa sunan matarka ba”.
Sai ya yi dariya ya ce”Za ki saki kanki ne ko kuma kotu za ki je ta raba mu?”
Na ce”Ko da ina nan da aurenka ba za ka sake haɗa jiki da ni ba, na bar mata kai har abada”.
Ya ce”To shikenan, hakan ma ya yi indai za ki samu nutsuwa”.
Na tashi zan shiga ɗaki ya ce”Anjima kaɗan likita zai zo ya duba ki”.
Na gyaɗa kai, still ya sake riƙo hannuna, ya ce”Don Allah ki daina zargina, ban kwana da wata mace ba, amma wacce zan aura ta zo ta yi girki, kuma ita ce kika ga fitarta daga gidan ɗazu, Allah ne shaidata, ke ma kuma ki yi min adalci, tun da tare kuka kwana a asibiti da ita, yanzu ma ta dawo ne don ta yi miki abun karyawa, don Allah ki sassautawa zuciyarki”.
Takaicinsa ya linku a zuciyata, inda ya san zafin da zan ji da ya gwammace ya ɓoye min gaskiya, don wallahi a yadda nake da kishi har gara a ce wata karuwa can ya ɗakko haya a titi ta zo suka kwana a gidan, da a ce wacce zai aura ce ta zo ta yi mini girki a kitchen har ma ta zo ta taya ni kwana a asibiti, to idan da na san ita ce sanda na farka tana baccin nan da ban shaƙe shegiya ba na wuce lahira?
A tsayen da nake na rushe da kuka ina maimaita idan ka cuce ni Allah Ya saka min, Allah Ya bi mini hakkina”.
Ya yi tsaki ya shige ɗakinsa, ni ma nawa ɗakin na koma na zauna ina fashewa da sabon kuka. A hankali kuma na taƙaita kukan, kafin ma ya ɗauke cak kamar an yi ruwa an ɗauke, ƙwaƙwalwata ta shiga tariyo mini shuɗaɗɗun lokuta masu daɗi a wajena da akasinsu.
A asibiti muka haɗu da shi, lokacin Mama ba ta da lafiya an ba ta gado, shi kuma ranar ya je duba jikin abokinsa, Allah Ya ƙaddara haɗuwarmu, da fari ya fara ne da kallona yana faɗin na yi masa kama da wata Zainab a Kaduna, na faɗa masa ni ba ni da wata ‘yar’uwa mai suna haka a Kaduna, ya dage ya ce dole ‘yar’uwa ta ce tun da kamarmu ta ɓaci, har dai Anisa ta shiga zancen ta ce to ya nuna mana hoton Zainab, ya ce ba shi da hoton amma na ba shi lambata idan ya sa ta turo masa zai tura min, wannan ne silar haɗuwarmu da kuma faruwar komai, hoton Zainab kuma har yau bai nuna mini ba, ƙarshe dai ma ya sanar da ni babu ita, kawai yana neman link ɗin da zai jona alaƙarmu ne.
Kafin a sallami Mama ya yi zuwa biyu asibitin, bayan an sallame ta kuma ya zo gida ya sake duba ta, nan fa ya riƙe ni sosai a waya, muka saba, amma har lokacin bai yi zancen yana sona ba, sai dai fira kawai kala-kala, har ta kai duniya fira da shi ta fi yi min daɗi sama da kowa, shiyasa kuwa idan bai kira kira ni sai na ji kamar ba ni da laka duk na rasa kuzarina, iyayena duk a zaton su soyayya muke yi, kamar yadda ni ma na yi zato, domin kuwa zuwa lokacin na kamu da soyayyar shi da ƙarfi kuwa, a zatona tun da yana ta nuna mini alamomin soyayya ai ba sai ya furta ba, akwai ƙawata da take faɗa min ita ma daga gaisuwar mutunci da firar duniya, ba ta san lokacin da suka faɗa soyayya ba, kawai sun wayo gari ne sun tsinci kansu a matsayin masoya, tsakanin ita da shi babu wanda ya yi zama na musamman ya yi wa ɗan’uwan shi bayanin na ga ni ina so, za mu fara soyayya, ga shi yanzu har sun yi aure, shi yasa na yi zaton ni ma haka ce za ta kasance mana ni da Sadam, don haka na ƙara zura jiki, saboda ni idan ina yin soyayya ina yinta da duka zuciyata da ƙarfina, haka ma idan ina ƙin mutum, akwai Ashiru, wani ɗan’uwan Babana da yake sona tun ina yarinya, ni kuma na tsane shi, da fari ya dage ya ce zai iya zama da ni ko ba na son shi, amma da na matse lamba wajen nuna masa ƙiyayyata tsirara a hankali na fita daga ransa ya janye da kansa
Mun riga mun saba da Sadam, kullum muna tare a waya, duk ranar Alhamis da Juma’a da ba mu da islamiyyar dare yake zuwa mu sha fira, ganin shi shi ne babban farincikina, shi yasa nake alla-alla ranakun zuwan nashi su zo, dangi kowa ya ji na samu wanda zan aura, ballantana kuma ƙawayena wanda yanzu ba ni da wata fira sai ta Sadam, mun yi wata shida tare da shi sannan na yi kammala secondary, kuma a bisa tsarin Baba dama ‘yarsa mace tana yin Candy sai zancen aure, ko ɗar ba na ji, tun da na san ina da mijin da zan aura, sati na ɗaya da Candy Baba ya zaunar da ni da batun aure, ya tambaye ni akwai wanda nake so? Nan take na faɗa masa ina da Sadam.
Wata ranar Alhamis da Sadam ya zo, kafin na fita Baba ya tsare ya ce masa ya ba shi sati ɗaya ya turo magabatansa idan da gaske yake, ya ce masa to.
Da na fito sai na ga fuskar Sadam a murtuke ba kamar yadda ya saba ba, hankalina ya tashi, saboda ni fa farincikinsa shi ne nawa a lokacin, na ce”Yaya Sadam, me ta faru na ga kana ɓata rai?”
Ya yi shiru kamar ba zai ce komai ba, kafin ya sauke numfashi ya kalle ni ya ce”Ke Sayyada!”
Na yi mamakin jin yadda ya danganta sunana da ke, sannan ya kaurara murya.
Na gama can jinin jikina ni na yi masa laifi, gabana sai faɗuwa yake yi, kamar zan yi kuka na ce”Na’am”.
Ya ce”Mene ne alaƙata da ke?”
Wannan tambayar tasa sai ta saka ni a ruɗani da fargaba, na ce”Yaya Sadam, ai ka fi ni sanin amsar wannan tambayar da ka yi mini, akwai wata matsala ne? Duk na rasa gane kanka”.
Ya ce”Ina son jin amsar nan daga bakinki, saboda na lura yadda na ɗauke ki ba haka kika ɗauke ni ba, mene ne alaƙata da ke? Ina nufin mene ne ya haɗa mu, me muke yi?”
Na sunkuyar da kai na ce”Mutunci ne ya haɗa mu, daga baya kuma muka jone muka zama ɗaya, ina nufin soyayya muke yi ko?”
Ya ce”Tun da muke da ke na taɓa cewa ina sonki?”
Na ji kamar an rufto min wani abu a kaina, na ji kawai na fi kowa shiga muzanci a duniya, ga shi ba ya ko murmushi ballantana na yi tunanin wasa yake yi min, nan take idona ya tara ruwa suna dab da fara tsiyaya, shi kuwa ko a jikinsa ya sake maimaita”Na ce ina sonki ne? Dama soyayya muke yi?”
Na saki hawayen da rawar murya na ce”Dama ba ka sona Yaya Sadam, don Allah ba na son irin wannan wasan”.
Ya ce”Ba wasa nake yi miki ba Sayyada, ni fa kawai na ɗauki alaƙarmu ne a matsayin abota da kuma girmama juna, ki yi haƙuri gaskiya ban taɓa jin son ki ba ballantana na yi tunanin zan aure ki, don haka ki sanarwa iyayenki ba soyayya muke yi ba tun wuri”.
Daga haka ya shiga motarsa ya ja ya tafi ya bar ni tsaye kamar an shuka ni, na kasa ko motsi, zuciyata sai tiriri take yi, na ja ƙafa ina share hawayena na shiga gida, Allah ya taimake ni babu kowa a tsakar gidan, na faɗa ɗakinku na kwanta a katifa na fashe da kuka, ƙannaina suka shiga tambayata mene ne, na ce kaina ke ciwo, Mama ba ta yarda da ni ba, kuma tambayar duniya na ƙi faɗa mata, a wannan daren ban runtsa ba, ko da a ce zan iya haƙura da soyayyar Sadam to da wane kalaman zan sanarwa duniya silar rabuwarmu? Sai na ce dama ba sona yake ba ni ce nake haukana?
Washegari na tashi jiki ba ƙwari, dayake ranar Asabar ce na tafi Islamiyya ta safe, idan muka dawo ƙarfe ɗaya shikenan ba a komawa sai kuma ta dare, a makarantar ma yau ban tsinci komai ma, kifa kaina a benci kawai na yi na ce ba ni da lafiya. Ƙaramar magana da ta zama babba, ta tabbata Sadam da gaske yake ba wasa yake yi mini ba, tun da ga shi bai sake kirana ba har dare ya yi, na kasa jurewa na kira shi, sai ya kashe ya kira ni kamar yadda ya saba, na ɗauka da rawar murya, shi kuma muryarsa ba kamar yadda ya saba ba, sam babu walwala ya ce”Sayyada ya aka yi?”
Na ce”Don Allah idan wani laifin na yi maka ka sanar da ni”.
Ya ce”Laifi ai ke ce kika yi min, a kan me za ki faɗawa mahaifinki soyayya muke yi, har ya tare ni da zancen ya ba ni sati ɗaya na turo iyayena? Na ce ina sonki ne?”
Na fara kuka, na kasa cewa komai, zuciyata kamar za ta buɗe ƙirjina ta fito.
Ya sassauta murya ya ce”Sayyada”.
Da ƙyar na ce”Na’am”.
Ya ce”Sona kike?”
Na ce”Ka yi haƙuri idan na yi katsalandan a cikin rayuwarka, ba laifina ba ne, laifin zuciyata ne, kuma ni a nawa tunanin duk wani namiji da zai nunawa mace irin kulawar da kake ba ni sonta yake yi, shi yasa ma ban kwaɓi zuciyata ba, ashe na yi kuskuren fahimta, ina sonka Yaya Sadam, ina tsoron halin da zan shiga idan da gaske ba ka so na, don Allah mene ne aibuna?”
Ya sauke numfashi ya ce”Ba ki da wani aibu, kuma zan iya soyayya da ke wannan ba wani abu ba ne, sai dai ni gaskiya ina da sharuɗan da na tanadarwa duk wacce zan yi soyayya da ita kafin ma a kai ga auren, kina ganin za ki iya bi?”
Aka ce wanda yake ruwa idan aka miƙa masa takobi kamawa yake yi, a yanzu neman mafita nake yi, don haka na ce”Na amince”.
Ya ce”To saboda muhimmancin maganar, mu bar wa gobe in sha Allah zan zo sai mu tattauna baki da baki”.
Na ce”Allah Ya kai mu, na gode”.
Ya ce”Ni ma na gode, ki yi bacci mai daɗi”.
Zan iya cewa tun daga wannan ranar da Sadam ya karɓi soyayya rayuwarmu ta canza, rikiɗa ya yi ya koma kamar wanda ban san shi ba, kamar ba wannan wanda muka yi sabo muka zama abokan juna ba, sai ya yi ta sha min ƙamshi yana zuba izza, ni kuwa kullum soyayyarsa ƙara faɗi take yi da tsayi a zuciyata.
Dokokin da ya kafa mini su ne, duk wani umarni da ya ba ni ya zama dole na bi, aurena zai yi, don haka bin umarninsa a yanzu shi zai tabbatar masa da ya yi dacen mace, kuma bayan auren za ta iya bin umarninsa, akasin haka kuwa tana nuna ko an yi auren bai isa da ita ba, don haka babu batun ya auri wacce ba za ta yi masa biyayya ba, cikin biyayyar nan har da sharaɗin tambayar shi duk inda zan je, dole sai ya san shige da ficena, ko da kuwa iyayena ne suka aike ni, sannan yana da damar ya bar ni na fita, yana da damar hana ni idan ya ga fitar da zan yi ba ta dace ba, na ce na amince.
Sannan ya ce ba zan sake saka gyale ba, babu ni babu kwalliya sai dai idan zai zo zance, duka na amince, ya ce idan ya gan ni da wani saurayi ko ana gobe ɗaurin aurenmu ne ya fasa, na ce na amince, a haka muka gina soyayyar kuka ta fara tafiya sannu a hankali, ina ta ƙoƙarin bin dokokin nashi, sai da ta kai har Mama za ta aike ni idan na faɗa masa ya ce ba zan je ba, kuma ba zan je ba ɗin, sai dai na yi ƙaryar ba ni da lafiya saboda na kaucewa aiken, daga karshe ko unguwa na je shi zai ba ni lokacin da zan dawo gida, idan aka samu matsala na wuce ba ƙaramin ɓaci raina yake yi ba, sai na ta bin kansa kafin na samu ya yafe min mu shirya, shi yasa nake taka-tsan-tsan da duk abin da zai sa na karya dokarsa.
Tun a cikin satin da Baba ya yanka masa ya turo Iyayensa aka saka ranar aure watanni takwas, shiyasa yanzu duk dangi kowa ya tabbatar da shi zan aura.
08028966015
[03/10, 8:10 pm] Sadiya Abdulrazak: *KU YI MANA ADALCI*
NA
Sadiya Abdulrazak
Page 6
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LnQJ26F7GLvLHNQHkwpWw1
Assalamu Alaikum my people dafatan kunanan cikin aminci sunana ummuh sayyeed traditional medicine center Zaria dealer in all kinds of magungunan mata turarukan wuta sudaniss dilka skin care products
Alhmdulillah call 09065504546 Ina mai farin cikin sanar da Yan uwana mata ni yar mutan Chadian zan muku promo 🎤🎤🎤🎤
Tundaga gobe__ 9/19/2025__ harzuwa end of this month dinnan in Sha allahu
Ina matanda sukefama da rama
Ina masu fama da lalacewar nono
Ina matanda sukefama da rashin gashi da lalacewar gashi
Ina Maison taga komai nata cifcif
Ina Mai
Hmmm kukanki yazo karshe dakila wadda ita batasan
Dadin jima’ba shin kinsan ko mijinki ne bai baki abinda kikeso wato baida kuzari munada maganin da zamubashi
Ga kayan dazamu yi promo Nan akan 4,500 kacal 👌👌
Maganin sanyi 1,k
Tsumin bom 1,500
Madarar tabaje 1k
Gumbar Milo 1k
Garin yaukayauka emergency 1,500
Garin kinfi kaza 1,500
Hmmm duk waddanan kayanfa ,naira
4,500 💃 munamaraba damasu siyan Daya ko sari
Tun ina ɓoyewa makusanta yadda Sadam yake juya ni, ni kuma nake bin umarninsa kamar shi haife ni, har abun ya bayyana kowa ya gane, ba ƙaramin faɗa nake sha a wajen Mama ba, ƙawaye ma suna ta ganin baikena, ni kuwa ko a jikina don ji nake indai Sadam zai yarda da ni ya yi farin ciki da ni na wuce wajen. Zuwa gidan biki ko na ‘yan’uwa sai wanda ya ga dama yake barina, ballantana na ƙawaye, haka kowa zai tafi, a bar ni ni kaɗai a gida, kuma sam ba na damuwa, Anisa ƙawata ce kuma ‘yar’uwata, amma lokacin aurenta haka ya hana ni zuwa wajen dinner, ranar na yi kuka, musamman na gorin da na sha a wajen ‘yan’uwa, haka aka dinga caccake ni, ana tsinewa soyayyar tamu, kuma a daren sai da ya zo zance, saboda ma ya tabbatar da ban je ɗin ba, yana ganin fuskata babu walwala shi ma ya haɗe tashi fuskar, ya shiga yi mini faɗa yana cewa”Sayyada saboda na hana ki zuwa wajen wannan shirmen shi ne za ki ɗauki fushi da ni? To ko da na hana ki zuwa ai umarni ne na ba ki, kina da damar bijirewa, tun da ban ɗaure ki ba, yanzu ma ki tafi ai ba ki makara ba, ban yi miki dole ki bi umarnina ba, amma kin san sharaɗin da soyayyarmu ke saƙale da shi ko? Idan kin ga kin zaɓi rabuwar fine!”.
Daga haka ya bar ƙofar gidanmu, na kasa bacci sai da na kira shi, ya ƙi ɗauka duk nacina, haka ita ma Anisa na dinga kiranta ta ƙi ɗauka, sai da ta yi mini massage sannan na haƙurwa, cikin saƙon take ce mini, tun da na zaɓi wani ɗan iska a kanta kar na sake nemanta, gobe ma ba ta gayyatata, don kar na je ya tsine min na bi duniya, na share hawaye a fili na furta”Ba za ku gane ba”.
Washegari da sassafe sai ga kiran shi, na ɗauka muka gaisa sama-sama, ya ce”Kin tafi gidan biki ko kina gida?”
Na ce”Ina gida”.
Ya ce”To ki je, amma ki tabbata a gidanku kika yi sallar isha’i, duk wani shiririta da shirme da za ku yi kar ki sake ya wuce magriba, ki koma gida zan zo”.
Kamar zan yi kuka na ce”Amma fa akwai kai amarya, kuma Mama ta ce yau a can zan kwana, tun da wajen kai amaryar za a iya kai wa dare”.
Ya ce”Ni dai ga abin da na faɗa miki nan, ra’ayinki ne ki ji ko ki yi watsi da shi”.
Daga haka ya kashe wayar, na runtse ido ina jin kamar zan yi ihu, na rasa manufar wannan takunkumin da yake saka min, mutane suna yawan faɗa min idan mun yi aure ba ƙaramin kulle zai yi mini ba, ana ta nuna min takaicin da matar kulle take ƙunsa, amma ni gani nake indai mijina yana sona yana faranta mini muna zaune lafiya kuma zai ɗauki duka ɗawainiyata mene ne don ya yi mini kulle? Idan aka cire wannan dokokin da yake kafa min wallahi yana da daɗin sha’ani ya iya nuna soyayya da kalaman kulawa, a takaice dai gani nake ni ce na fi kowa dacen mijin aure.
Ban ajiye wayar ba na ji shigowar saƙo, na duba na ga alert ne daga gare shi, na dubu hamsin, wani saƙon ya sake shigowa, na karanta faɗa min yake yi kuɗin gudunmawa ne na bawa Anisa, na tura masa da saƙon godiya, anko kala biyu aka fitar a bikin, kuma duka shi ya siyo min, ya kawo min a ɗinke kowanne da kalar takami da jaka da zai dace da shi, har da mayafai da set ɗin sarƙa mai kyau sosai, sannan ya haɗo min da dubu goma ya ce na yi liƙi, ban taɓa kuɗin ba, Baba na tambaya ya cika min na siyawa Anisa wani Jug me kyau na bata. Mama ta tafi gidan bikin tun asuba, sai ƙannaina da suke gab da gama shiryawa, dama umarni nake jira tun da na samu izini ni ma tuni na tashi na shiga wanka, na ce su jira ni, muka tafi tare, Na samu Mama na faɗa mata zancen kuɗin da ya ba ni na bawa Anisa, ta ce na ba ta dubu ashirin na bawa babarta talatin ɗin, na fita na je na ciro na bawa Umma na ce inji Sadam, nan fa aka dinga jinjina ƙoƙarinsa ana godiya, har na ji daɗi a raina, ya kankaro min mutunci.
Na samu Anisa a ɗakinta cikin ƙawayenmu na makaranta, ta kalle ni ta kau da kai, na faɗa jikinta ina dariya da faɗin”Allah Ya huci zuciyarki”. Da ƙyar ta sauko daga fushin, na ciro kuɗin na ba ta na ce inji Sadam, ta taɓe baki ta ce”Ai ni ko miliyan zai ba ni bai burge ni ba, kuma ba na so ki mayar masa”.
Na sauke numfashi ina tunanin ko ya za ta ji idan ta san ba zan je kai amarya ba? Kafin dai yamma ta yi ta saki jiki da ni, ta karɓi kuɗin har ma ta yi masa godiya ta wayata, kafin mu yi sallama ya sake jaddada min bayan magriba na dawo gida, na ce to, ai kuwa ana idar da sallar magriba na zame daga cikin ‘yan biki na shiga ɗakin Umma na haye gado na lulluɓa da mayafina, kowa ya shigo sai ya tambaya sai na ce ba ni da lafiya, a dole Mama ta saka ni a gaba muka koma gida, raina babu daɗi saboda na so a ce na raka ƙawata ɗakinta.
A haka muka cigaba da soyayya, yana nan yana kafa min dokoki ni kuma ina ta biyayya saboda gudun ɓacin ransa, idan na kuskure na ga tijarar da har sai na yi nadamar aikata laifin. Ko da wasa wani saurayi ya tsayar da ni a hanya ce masa nake ni matar aure ce, don kada ma tsautsayi ya sa a ce masa an gan ni da wani na shiga uku. Kwanci-tashi aka samu wata biyar da saka rana, arenmu ya rage watanni uku, a lokacin ne kuma Sadam ya fara fito mini da wasu sabbin halaye wanda na kasa gane musu, zuwa lokacin ya siya min babbar waya muna yin chatting, kuma mun fi yin na dare, saboda ya ce sai daren yake da lokaci, ya fara da tura min stickers na kiss da hug, da na nuna ba na so sai ya nuna min ba komai ba ne, ni kuma sai na yarda da babu komai ɗin, tun da ba wani tsaraici ba ne ake bayyanawa, gaba-gaba kuma sai ya fara tura min ta romance, babu kunya sai ya turo min hoton ƙinjin mace, har ma ya dinga tambayata nawa irin wanne ne? Tun ina ƙin amsa masa har dai na fara, saboda gudun ɓacin ransa, kuma yana maimaita min don yana sona ne yana tare da ni, wai idan bai tura min ba wa nake so ya turawa? Sai ka ce dole aka yi masa sai ya turawa wata.
A ranar da ya fara tura min blue film hankalina ya tashi, saboda ban taɓa kalla ba ko da wasa, kuma na kasa jurewa har sai da na faɗa masa ba na so kar ya sake tura min, kashe wayar ma na yi sai da na yi kwana uku ban kunna ta ba, har ji nake yi kamar zan yi zazzaɓi, a cikin kwanaki ukun bai zo ba, a rana ta huɗu na kunna wayata ban ga saƙon shi ba, ban sani ba ko ya kira ni, gaskiya ya ɓata min rai kuma na fara zarginsa ma, idan ba yana yawon bin mata ba waye yake tura masa? Wata zuciyar take ƙila ɗakkowa yake yi a internet, ina kallon shi online bai yi min magana ba, sai na kasa jurewa ni na yi masa sallama, ya amsa ya ce lafiya? Na ce lafiya ƙalau, sai ya danna voice note ya ce min”Sayyada ba lafiyar jikinki nake tambayarki fa, tambayar dalilin yi min magana nake yi”.
Na ce”Yanzu sai da dalili zan yi wa mijin da zan aura magana?”
Ya ce”To ai ba ki ɗauke ni a matsayin wanda zai aure ki ba, ban da haka kawai don na tura miki vedio shi ne za ki kashe waya? Kenan idan da zan ce ki zo ki taya ni wuni ba za ki amince ba ko?”
Na yi shiru na rasa me zan ce masa ma, amma na shiga fargabar me Sadam yake nufi da ni?
Ya sake yin voice ya ce”Na rasa irinki wallahi idan kina wani abu kamar haihuwar ƙauye, ban da shirmenki mene ne a cikin wannan? To gaskiya ni ba zan iya soyayya da mace irinki ba, ballantana kuma aure, don irinki idan mutum ya aure ki ma takaici zai kwasa wallahi, don haka kina da zaɓi guda biyu, ko ki koyi yadda za mu dinga gamsar da juna ta haka ko kuma a fasa auren nan kawai, sai ki je ki nemi ustaz ki aura tun da na ga ni kallon ɗan iska kike yi mini”.
Kamar zan yi kuka na ce”Ni fa ba haka nake nufi ba”.
Ya kira ni a waya, ina ɗauka ya ce”Ki buɗe baki ki yi mini bayanin me kike nufi? Wane kallo kike yi mini?”
Na ce”Ba komai wallahi, kawai dai ni na tsorata ne, ba na son gani”.
Sai ya sanyaya murya ya ce”To me kike so?”
Na ce”Da dai za ka daina turo min”.
Ya ce”Kina so na turawa wata kenan ko? Idan ba mu saba da wacce zan aura ba tun yanzu sai yaushe? Ko so kike sai bayan auren na dinga fama da koya miki abubuwa? Ni ba haka na tsara ba, amma ba zan yi miki dole ba shi yasa na ba ki zaɓi”.
Ya kashe wayar, a ranar na kasa bacci ina ta tunani na san dai haramun ne, amma da ya dinga tsara ni da kalaman yaudara, da na barazanar fasa aurena sai na amince, sannu a hankali muka saba da wannan mummunar ɗabi’a, tsakar dare wani lokacin bayan na yi bacci na farka, wataran kuma ba na yin baccin sai na jira shi, zan tashi zaune mu yi ta dirty chat, yanzu na saba da kallon vedion, kuma idan na kalla ina shiga wani yanayi sosai na buƙatuwa, yadda muke yi idan ya turo bayan na gama kalla sai ya ce mu yi sharhi a kan vedion, tun ina jin kunyar cewa komai har na saba na saki jiki, a hankali Sadam yake faɗaɗa min sha’awata, ta kai har na matsu a yi auren.
Daga wannan kuma sai ya fara kwaɗaita kasancewarmu a zahiri, a nan ne dai na tirje duk kuwa ni ma zuwa lokacin ina jin sha’awarsa sosai, duk kalaman yaudara da ya dinga yi mini na ƙi yarda da shi, ya yi fushin ya gama ya dawo duk ban yarda ba, don na san wannan zina ce, ba shi da wasu kalaman da zai yi amfani da su wajen canza kalma, ni kuwa ba na fatan na aikata zina a rayuwata.
Daga baya ya bar yi min zancen, sai dai muna nan tare a waya, aurenmu ya rage wata ɗaya, lokacin har an fitar da anko ‘yan’uwa ana ta yi, ya ce Momynsa ta ce na je na gaishe ta, tana so ta gan ni saboda za su haɗa lefe, na ce masa zan tambaya a gida idan za a bar ni, ya ce ba sai na tambaya ba, saboda idan na tambaya za a iya cewa sai na je tare da ƙanwata, ita kuma Momy ba ta son haka, zan yi musu ya dakatar da ni da faɗin”Kin ga Sayyada idan fa ba za ki je ba babu dole, ai mahaifiyata ce dama ban ce ki kalle ta a matsayin uwa ba, sai dai kuma ki sani ba ni da kamar Momy a duniyar nan, duk macen da za ta nuna ba ta ɗauki maganar uwata a bakin komai ba wallahi ban ga amfanin cigaba da mu’amala da ita ba”.
Da sauri na ce”Ni fa ba da wata manufar na faɗa ba, shikenan yaushe zan je?”
Ya ce”Ko gobe ma”.
Na ce”To zan tambayi zuwa gidan Anisa daga can sai na wuce ko?”
Ya ce”Allah Ya kaimu”.
Washegari kuwa na je gidan Anisa tun safe, na wuni a can, ana yin sallar la’asar, na tafi, muka haɗu da Sadam a titin unguwar, ya ɗauke a motarsa muka kama hanyar gidansu, babban gida ne sosai, don iyayen shi masu rufin asiri ne, ya shiga da mota cikin gida, muka fito, gidan part biyu ne, na yi zaton babban part ɗin za mu shiga, sai na ga mun nufi ƙaramin, ya buɗe da mukullinsa muka shiga, falo ne madaidaici, sai sai ɗakuna guda uku, na zauna a kujera ina raba ido, gabana yana faɗuwa, saboda zan gana da surukata, ya fita, babu daɗewa ya dawo da drinks da snacks ya ajiye min, ya ce “Sorry babu kowa a gidan fa”.
Gabana ya faɗi na ce”Kamar ya?”
Ya ce”E yanzu na shiga na ga ba kowa, sai na kira ta take ce mini ta tafi asibiti dubiya, wai ƙawarta aka kwantar, kuma na san za ta iya kaiwa dare ba ta dawo ba”.
Na ɗauki jakata na miƙe na ce”To gaskiya tun da hakane kawai zan tafi gida, wani lokacin sai na dawo”.
Ya ce”To jira na ɗan watsa ruwa sai na kai ki”.
Na zauna a tsorace, saboda yadda nake jin salon tantirancin Sadam a waya dole zan ji tsoron keɓewa da shi mu biyu a gida, har ya tafi ya dawo ya ce”Ko za ki taya ni wankan?”
Da sauri na ce”A’a, don Allah ka yi sauri kar Mama ta ga na daɗe”.
Ya yi murmushi ya ce”Amma ai za ki taya ni shafa mai ko?”
Na sunkuyar da kai ban ce komai ba, zuciyata tana ta bugu, ya shiga ɗaya daga cikin ɗakunan dake falon, don tsoro ko ruwa kasa sha na yi, saboda zarginsa kawai nake yi, kar ya zuba mini wani abu a ciki na sha ya cim ma buƙatarsa a kaina, sannan na fara tunanin karya yake yi dama ya san Momyn ba ta nan, so yake kawai ya yaudare ni.
Ina nan zaune da zulumi na ji yana ƙwala min kira daga cikin ɗakin, na daga murya na amsa, ya ce”Zo mana”.
Gabana ya faɗi, na ce”Na’am me ka ce?”
Ya ce”Zo ki ga wani abu”.
Na ce”Don Allah ka zo ka mayar da ni gida, bai kamata na shiga ɗakinka ba fa”.
Na ji motsin buɗe ƙofar ɗakin, ina juyawa na gan shi daga shi sai boxer, ya nufo ni, kafin ya ƙaraso na tashi na ɗauki jakata ina cewa”Ni zan tafi kawai sauri nake yi”.
Ya ƙaraso ya riƙe hannuna, da irin muryar nan ta cikin waya ya ce”Babyna, kenan da kike cewa kina kewar kasancewa da ni duk na ƙarya ne? Tun da ga ni yanzu mun samu dama me zai hana mu farantawa junanmu?”
Ƙwalla ta kawo idona na ce”A’a don Allah, mu bar wannan har sai mun yi aure”.
Nan ya tisa ni a gaba da zantukan yaudara da daɗin baki yana nuna min ba komai ba ne wannan, wanda ba su da tabbacin za su auri juna ma suna yi ballantana mu da kwanaki ya rage aurenmu, bai ƙyale ni ba har sai da na amince na shiga ɗakin, ya yi yadda ya so da jikina, sai da ya nemi wuce gona da iri sannan na lura ni ma na shagala da yawa, na farga na taka masa burki, bai yi fushi ba sai ma godiya da yake ta min yana nuna min kulawa da soyayya, ya saka na yi wanka shi ma ya sake yi, sannan ya mayar da ni gida, jikina duk a sanyaye ina ta tsarguwa, gani nake kamar duk wanda ya kalle ni zai ga abin da na aikata liƙe a goshina.
08028966015
[03/10, 8:10 pm] Sadiya Abdulrazak: *KU YI MANA ADALCI*
NA
Sadiya Abdulrazak
Page 7
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LnQJ26F7GLvLHNQHkwpWw1
Assalamu Alaikum my people dafatan kunanan cikin aminci sunana ummuh sayyeed traditional medicine center Zaria dealer in all kinds of magungunan mata turarukan wuta sudaniss dilka skin care products
Alhmdulillah call 09065504546 Ina mai farin cikin sanar da Yan uwana mata ni yar mutan Chadian zan muku promo 🎤🎤🎤🎤
Tundaga gobe__ 9/19/2025__ harzuwa end of this month dinnan in Sha allahu
Ina matanda sukefama da rama
Ina masu fama da lalacewar nono
Ina matanda sukefama da rashin gashi da lalacewar gashi
Ina Maison taga komai nata cifcif
Ina Mai
Hmmm kukanki yazo karshe dakila wadda ita batasan
Dadin jima’ba shin kinsan ko mijinki ne bai baki abinda kikeso wato baida kuzari munada maganin da zamubashi
Ga kayan dazamu yi promo Nan akan 4,500 kacal 👌👌
Maganin sanyi 1,k
Tsumin bom 1,500
Madarar tabaje 1k
Gumbar Milo 1k
Garin yaukayauka emergency 1,500
Garin kinfi kaza 1,500
Hmmm duk waddanan kayanfa ,naira
4,500
A sanyaye na shiga gida da siyayyar da ya yi mini a hanya, na miƙawa Mama kamar yadda na saba na ce inji shi, ta ce”A ina kuka haɗu? Ko shi ya kai ki gidan dama?”
Na ce”A’a, yanzu zan shigo gida na gan shi, sai na ce masa kaina ciwo yake, shi ne ya ba ni ya tafi”.
Ta ce”To ciwon kai kuma? Ki ci abinci ki sha magani, kar dai ki kwanta sai kin yi sallah, ya Anisan take?”
Na ce”Lafiya lau, tana gaishe ku”.
Na shiga ɗaki na kwanta, gabana sai faɗuwa yake yi, ina ta hango yadda kasancewarmu ta faru, na rasa ma me nake ji, Allah Ya sa ni ba da son raina ba ne, sai da aka fara kiran sallah na fita na yi alwala na yi sallah, na kasa cin abincin ma, ballantana magani dama lafiyata ƙalau babu ciwon kan, na kwanta lamo a katifa ina ta tunani, fatana dai Allah Ya sa kar Sadam ya sake neman mu aikata wannan abun, da daddaren mun yi waya da shi, amma na ce masa ba ni da lafiya, don haka ba mu yi irin chart ɗin da muka saba ba.
Amma washegari muka ɗora daga inda muka tsaya, har ma yana yi min sharhin kasancewarmu, ni ma kuma a hankali sai nake jin daɗi idan na tuna yanayin, don haka a tare muke yin sharhin, kuma har ma ina jin ina ma mu ƙara kasancewa haka, amma fa idan mun yi aure nake nufi.
Haɗuwarmu ta biyu gidan yayarsa ya ce za mu je, abun mamaki bai sake yi mini zancen zuwa gaida Momy ba, nan ma dai ƙarya na yi da zuwa gidan su wata ƙawata, ya zo ya ɗauke ni a hanya, wannan dai kai tsaye ya faɗa min ba gidan yayarsa za mu je, don kasancewa da ni yake yi, don haka hotel za mu je, hankalina ya tashi na ce”Hotel? Sai ka ce wata karuwa? Don Allah ka rufa min asiri, wallahi ba zan iya ba, don Allah ka mayar da ni gida, sati biyu fa ya rage aurenmu, muka yi haƙurin watanni masu yawa sai na sati biyu ya gagare mu?”
Nan take ya ɓata rai sosai, ya ce”Shikenan ki je kawai, na gode, tun da ni ba ni da wata alfarma a wajenki a matsayina na wanda zai aure ki”.
Na fara hawaye ina tunani,ko a hasashe ban taɓa tunanin zuwan ranar da zan je hotel tare da saurayi da nufin aikata masha’a ba, a wannan lokacin dai ban yarda ba, na buɗe murfin motar na fita, ina saka ran ko da za mu zauna yana fushi da ni ba zan yarda ba, tun da sati biyu ya rage auren ko bai huce ba har lokacin idan aka kai ni ɗakinsa zai huce, adaidaitasahun na shiga na tafi gidan ƙawar tawa da na yi ƙaryar zan je, fira muke yi amma hankalina ba ya jikina, ina can ina tunanin halin da yake ciki.
Can na ji shigowar saƙo wayata, na duba na ga shi ne, da sauri na fara karantawa, “Sayyada wallahi kin ji na rantse ba zan iya auren wacce ba ta girmama ra’ayina ba, tun daga waje na bawa wacce zan aura umarni ta karya ina ga an yi auren? Ki sani a yau na yanke hukuncin fasa aurenki, kuma wallahi da gaske nake, ba zan dai fito ƙarara na ce na fasa ba, amma zan ta ɗagawa har a gaji a san cewar na fasa ɗin, don haka na ƙara watanni uku a yau”.
Tsoro ya kama ni, zuciyata ta yi rauni na fara tunanin anya Sadam don gaskiya yake yi mini kuwa? Ban yarda da gaske yake ba, sai da daddare da Baba ya yi baƙi, bayan sun tafi ya zaunar da ni yake ce min iyayen Saddam ne suka zo, kuma sun nemi a ƙara masa watanni uku, don bai gama shiryawa ba, a ranar na ci kuka, haka na kira shi ina kuka, ni gani nake abun kunya ne ‘yan’uwa da ƙawaye sun gana yin anko da shirin aurena kuma su ji an ɗaga saboda bai shirya, na kira shi na dinga yi masa kuka, shi kam ko a jikinsa, ƙarshe dai na ce na amince, ya ce ma ba ya so, sai kuma bayan kwana uku ya yarda muka haɗu, amma ya ce sam ba zai yiwu ya janye ɗagawar ba har sai ya ga gudun ruwana.
Tun daga lokacin muka jone a wannan sabgar, mun yi nisa sosai, bayan zuwana gidan na farko na sake zuwa sau uku, duk ranar da babu kowa a gidan sai ya kira ni na je gidan, mai gadi dai ya san da zuwana, amma ina tunanin ko tsoron tonawa Sadam asiri yake, ko kuma yana ba shi cin hanci ne, daga baya ma sai ya siya katifa ya saka a gidan shi, muke zuwa can, an gama ginin gidan komai tsaf, shi yasa nake mamakin dalilin da ya sa ba za a yi auren a wuce wajen ba.
Lokacin da auren ya rage saura wata ɗaya Saddam ya shigo min da babbar buƙatarsa, ya nuna yana buƙatar kusantata romance ya daina gamsar da shi kawai daurewa yake, kuka na saka masa da roƙon a bar wannan maganar, ya nuna min ba komai ba ne tun da dai aure za mu yi, dama abun nashi ne, don ya nema tun yanzu ba zai zama matsala ba, da na nuna ban yarda ba sai ya ce zai fasa auren ko kuma a ƙara ɗagawa, ni kuma a lokacin wallahi wata irin ƙaunarsa nake yi, ko ɗagawa ba na so a yi ballantana a kai ga fasawa, ga shi ni ma ya sabar min da romance ɗin, tsananin sha’awar shi tana neman kassara ni, shi yasa na matsu a yi auren.
Ban san da gaske yake ba sai da Baba ya kira ni a wani dare, ransa a ɓace yake tambayata abin da saurayina yake nufi, jikina ya fara rawa fa na ji wai jiya ya ce sai dai a ƙara ɗaga auren nan, a ƙara wata biyu ya zama saura wata uku a maimakon wata ɗaya, Baba ya ce ya gaji, idan bai shirya ba na watsar da shi na bawa wani dama a yi da shi, wallahi ranar tashin hankalin da na shiga Allah kaɗai ya sani, na ci kuka na gode Allah, na gaji da gorin da ake yi mini na wannan ɗage-ɗagen auren da ake yi, wasu har suna cewa kuɗin ne ba shi da shi, alhalin ni dai ban ga babu a tare da Sadam ba, maimakon na yi karatun ta nutsu na gane Sadam jikina yake so ba ni ba, amma ina, na kasa fahimta, sai nake ganin laifina ne da na ƙi bin umarninsa, don haka na amince da sharaɗin ba za a sake ɗaga auren ba, ya ce ya amince.
Na yi ƙaryar zuwa wani gidan, ranar muka haɗu a gidan shi, gabana yana ta faɗuwa, shi kuma Sadam yana ta rawar jiki da zumuɗin kasancewa da ni, irin wanda ango yake yi a daren farko, a ranar, a wannan gidan, wanda dai ya kasance gidan aurenmu a yanzu , a cikin ɗakin da yake nashi ne a yanzu, a kan ƙaramar katifa da filo guda ɗaya Sadam ya samu nasarar shiga hurumina, ya kawar da budurcina, ya mayar da ni cikakkiyar mace, na sha wahala daidai gwargwado, na ci kuka, haka ya mayar da ni gida wajen bayan isha’i, inda a ce Mama ta mayar da hankali sosai a gare ni za ta ga yadda tafiyata ta canza, duk da ina ta daurewa ina ƙoƙarin haɗe ƙafafuna, na kuma daure na ci abinci na yi sallah na kwanta, amma da safe na tashi fuskata a kumbure saboda kukan da na ci, idona sun jawur, ga shi na kasa haɗe ƙafata na yi tafiya kamar yadda na saba, da safen dai Mama tana ganina gabanta ya faɗi ta shiga tambayata mene ne ya same ni? Na ce mata ciwon kai nake yi da zazzaɓin, don kuwa da zazzaɓin na kwana, da yake lokacin sanyi ne, sai ta ce sanyi ya kama ni, shi ya kumbura min fuska, haka dai aka siyo min maganin zazzaɓi da ciwon kai na sha, na yi jinyata ni kaɗai, sai Sadam da yake yi mini sannu a waya sosai, tare da alƙawarin ba za a sake ɗaga aurenmu ba.
Sati ɗaya da faruwar haka ya sake nemana, ya kalamance ni har na sake amincewa da shi muka haɗu, tun daga lokacin kuma shikenan, ya zamana duk sati sai ya neme ni sau biyu, ni ma yanzu abun har ya fara yi mini daɗi.
Na sakankance, muka saba da Sadam sosai kamar wasu ma’aurata, a haka har lokacin bikin ya sake zuwa, ya rage saura sati biyu, shiru ba a kawo lefe ba, ga shi a wannan karon Baba ya ce indai aka sake ɗagawa to ya zare hannunsa a lamarin auren gabaɗaya, kullum cikin fargaba nake, duk da na san dai ina bin shi a yadda ya ce, sanda aka shiga satin bikin aka yi masa zancen lefe, sai ya ce a yi masa haƙuri a ɗaga auren zuwa wata ɗaya, nan take Baba ya ce sai dai a fasa, Sadam ya ce ba fasawa ya yi ba, yana ta ba da haƙuri ya tafi, a daren nan na ci kuka, na dinga kiran wayarsa ba ya ɗauka.
Washegari tun safe Baba ya wakilta abokansa da yayansa ya ba da kuɗin auren da Sadam ya kawo a mayar da shi gidansu, abun mamaki da tashin hankali ne ya faru sanda suka ƙarasa gidan, domin iyayen Sadam uwa da uba cewa suka yi babu wanda ya san yana neman aure, ƙarshe dai na taƙaice muku labari Sadam iyayen bogi ya samu suka kawo masa kuɗin aure, ranar na ga tashin hankali, Baba ya fusata sosai, ya kira Sadam a kan ya zo ya karɓi kuɗinsa ya ƙi zuwa ya ce ya bar min, ban gama tsinkewa ba sai da ya yi mini massage ya ce na yi haƙuri mu haƙura da juna kawai, har ya ƙara da faɗin babana ba shi da kirki, shi kuma ba zai zauna a wulaƙanta shi ba, kiran duniyar nan ya ƙi ɗaukar waya, ni dai ranar a asibiti na kwana saboda zazzaɓi ne ya rufe ni ruf.
Sai da na yi kwana uku a asibiti aka sallame ni, da na dawo gida babu zazzaɓin amma fa an kasa samun kaina, gabaɗaya na rikice, Sadam ya daina ɗaukar wayata gabaɗaya, duk na rame na ƙare, abinci ma yafita kawai nake, abu biyu ne ya haɗar min, ga zafin rabuwa da shi, ga kuma tunanin na riga na ba shi kaina ya gama buɗe ni, me zai faru idan na auri wani ba shi ba? Idan ya tambaye ni game da yadda ya ji ni kamar bazawara me zan ce masa? Auren wanda ya lalata ni shi ne kawai mafitata, ko da kuwa zai sake ni a sati ɗaya, duk wanda ya sake aurena daga baya ai ya san dama sunana bazawara, bazawara kuwa kowa ya san hanya ce daga Kano har Maiduguri.
Kullum a kwance nake kamar ruwa, tun Mama tana kyarata da yi min faɗa a kan yadda na kasa mantawa da Sadam har ta daina, ta fara jana a jiki tana yi min nasiha da nuna min Allah zai kawo min wanda ya fi shi, amma inaa! Duk da haka na ƙi kwantar da hankalina, wallahi ban san abin da ya sakawa Mama zargina ba, kawai wataran sai ta zaunar da ni take tambayata ko dai Sadam ya taɓa sanina a ‘ya mace? Ko na ba shi jikina? Na fara kuka ina girgiza mata kai alamar a’a, ba ta sake cewa kowa komai ba, sai washegari da safe ta ce na ɗauki hijjabina na fito, na ce”Mama ina za mu je?”
Ta ce”Siyar da ke zan yi”.
Na ja bakina na yi shiru na saka hijjabin muka fita, muka shiga adaidaitasahun, ba mu tsaya a ko’ina ba sai asibiti, ban san bayanin da Mama ta yi musu ba, kawai dai na ga wata Nurse babbar mace ta kira ni, ta zaunar da ni take tambayata a tsanake wai lokacin da muke soyayya da saurayina wani abu ya taɓa shiga tsakaninmu ne? Na ce mata a’a, ta ce na faɗi tsakanina da Allah, na dinga hawaye har da rantsuwa ta, na ce wallahi babu komai, aka yi min gwajin ciki da na HIV, kowanne nagative, ta ce to na hau gado za ta duba ni, gabana ya yanke ya faɗi, na fara roƙonta kar a yi haka wallahi lafiya ƙalau nake, sai da ta ɓata rai sannan na saddaƙar na hau gadon bayan na cire pant ɗina na ajiye, da ta duba ba ta ce min komai ba, amma a gabana ta yiwa Mama bayanin ba daɗe da sanin namiji, a ranar na ci kuka, don kukan da Mama ta yi ya tada hankalina sosai, haka muka koma gida ni ina gursheƙen kukan nadama, ita tana share hawaye.
A wannan ranar dai na ga ta kaina, domin Baba bulala ya saka ya zane ni, da ƙyar aka ƙwace ni, kuma ya ce ya zare hannu a lamarina gabaɗaya, babu shi babu ni, cewa ya yi ma sai dai na bar masa gidansa, duk yadda aka ba shi haƙuri ƙin haƙura ya yi, sai gidan yayansa na tattara na koma wato mahaifin Anisa.
08028966015
[03/10, 8:10 pm] Sadiya Abdulrazak: *KU YI MANA ADALCI*
NA
Sadiya Abdulrazak
Page 8
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LnQJ26F7GLvLHNQHkwpWw1
Assalamu Alaikum my people dafatan kunanan cikin aminci sunana ummuh sayyeed traditional medicine center Zaria dealer in all kinds of magungunan mata turarukan wuta sudaniss dilka skin care products
Alhmdulillah call 09065504546 Ina mai farin cikin sanar da Yan uwana mata ni yar mutan Chadian zan muku promo 🎤🎤🎤🎤
Tundaga gobe__ 9/19/2025__ harzuwa end of this month dinnan in Sha allahu
Ina matanda sukefama da rama
Ina masu fama da lalacewar nono
Ina matanda sukefama da rashin gashi da lalacewar gashi
Ina Maison taga komai nata cifcif
Ina Mai
Hmmm kukanki yazo karshe dakila wadda ita batasan
Dadin jima’ba shin kinsan ko mijinki ne bai baki abinda kikeso wato baida kuzari munada maganin da zamubashi
Ga kayan dazamu yi promo Nan akan 4,500 kacal 👌👌
Maganin sanyi 1,k
Tsumin bom 1,500
Madarar tabaje 1k
Gumbar Milo 1k
Garin yaukayauka emergency 1,500
Garin kinfi kaza 1,500
Hmmm duk waddanan kayanfa ,naira
4,500 💃 munamaraba damasu siyan Daya ko sari
Yayan babana shi ne ya tsaya min tsayin daka, bayan ya gama yi min nashi faɗa da nasihar, ya ce hannunka ba ya ruɓewa ka yanke ka yar, sannan ba za a bar Sadam ya ci bulus ba, ya zama dole ya aure ni, shi ya shige gaba ya je gidan su Sadam ya sanar da su ya riga ya lalata ni, don haka auren nan babu fashi, idan kuma ya ce ba zai aure ni ba to za a yi ƙararsa a kan lalata min rayuwa da ya yi, shi ne mahaifinsa ya ce ba damuwa zai aure ni, yayinda mahaifiyarsa ta yi tsallen baɗake ta ce ba zai auri mara tarbiyya ba, aka dinga kai ruwa rana, ƙarshe dai aka fi ƙarfinta, aka sake saka ranar aure sati biyu masu zuwa, Baba ya ce ko ya shirya ko bai shirya ba za a ɗaura idan ma a kafaɗa zai yi yawo da ni sai dai ya yi, da aka sanarwar babana sai ta ce babu ruwan shi fa a magana, kuɗin kayan ɗaki dama ya daɗe a wajen kafinta kuma aka yi sa’a Baba bai karɓe ba, kayan kitchen ɗina ma tuni an gama haɗa komai, don haka ba a da matsala ta nan ɓangaren.
Kuma wani abun mamaki Sadam shi ma ya amince da auren, bai nuna mini wani ɓacin rai ba, firarmu muke yi hankali kwance, sai yake nuna min shi fa dama ba auren ne ba ya so a yi ba, kawai dai ƙaryar da ya yi tun farko ne bai faɗawa iyayensa zai yi aure ba, ya sa shi fargaba, hakan ne ya ja komai, ni dai kawai bin sa nake da kunne, amma ina tsoracewa kaina kalaman da aka yi ta faɗa min na cewar ko an yi auren ba zan yi daraja ba a idonsa, ba na fatan hakan ta tabbata, bai kawo lefe ba, kuma ba wanda ya tambaye shi, saura kwanaki uku auren dai ya kawo kaya a ɗinke kala biyar, da takalma biyu jaka biyu, sai mayafai da sarƙa, ya ce na yi fitar biki.
Haka aka ɗaura auren, ba a yi wani taro ba, sai ‘yan’uwa na kusa ne kawai suka zo, aka je aka jera min kayana a gidan, an tarar ma ya zuba kujeru masu kyau, kayan kallo da babban firji a falo, haka ɗakinsa ma ya saka gado, aka jera sauran kayan a ɗakunan da suka yi saura, a daren da za a kai ni ɗakina Maman Anisa ta saka ni a gaba zuwa gidanmu don na nemi yafiyar iyayena, Mama ta ce ta yafe min ita dama ba ta ƙullace ni ba, yayin da Baba ya ce ba zai sake cewa komai a kaina ba, amma dai na sani ya bar wa Sadam ni har abada, kar na sake na ce zan zo gida na kwana ko da ziyara ce ballantana yaji, idan zai dinga yankar naman jikina yana ci kar ma a faɗa masa ballantana a yi tunanin zai ɗauki mataki, tun da har na iya yin watsi da tarbiyyar gidansa to na je na rayu da wanda na zaɓa rayuwa ta har abada.
Na ci kuka a ranar kamar babu gobe, na san na yi laifi, ban yi wa iyayena adalci ba, amma a ganina ko ma me na yi bai kamata Baba ya yanke wannan hukuncin mai tsauri ba a gare ni, tun magriba kowa ya watse, wajen ƙarfe tara Sadam ya zo shi kaɗai ya ɗaukata duk an yi zaton ma dai gobe ne kai amaryar, tare da Baban su Anisa muka tafi ni ina bayan mota shi yana gaba, sai da ya raka ni har ɗakina, ya haɗa mu ya yi mana nasiha, sannan Sadam ya mayar da shi gida, ina zaune ina ta share hawaye ya shigo gidan, hannunsa ɗauke da ledoji, ya ajiye, sai na ga jikinsa a sanyaye fuska babu yabo babu fallasa, sam babu wani zumuɗi na angwaye, ya zauna a kusa da ni muka yi shiru na ɗan lokaci, kafin ya ce”To Sayyada daga ƙarshe dai aurenmu ya tabbata, sai mu ce Alhamdulillah! Allah Ya ba mu zaman lafiya, Sayyada ina son ki, kuma ina fatan za ki cigaba da bin ra’ayina a komai, idan kika yi min biyayya a zamanmu na yi miki alƙawarin samuna yadda kike so, ba ana cewa wasu mazan mijin ta ce ba? To ni kam zan zame miki kan ta ce”.
Ni dai na kasa cewa komai, ya ce”Kin yi shiru, ko dai ni kaɗai nake farinciki da wannan ranar?”
Sai na fashe da kuka sosai, na kwanta a jikinsa na riƙe shi na ce”Ni amana ce a wajenka, Babana ya ce ya zare hannunsa a lamarina ya sallama maka ni, ya ce ko yanka ni kake yi bai amince na koma gidansa ba, ballantana yaji, ziyara ya ce ba zan sake zuwa na kwana ba, Sadam kai kaɗai ne da ni a yanzu, ka dubi Allah ka yi mini adalci a zamanmu, ka yi wa iyayena adalci ka kula da ni, ko haka zai wanke musu ƙuncin da na saka musu a zuciyoyinsu, don Allah ka rufa min asiri mu bawa maraɗa kunya”.
Ya fara shafa bayana yana cewa”In sha Allah Sayyada zan yi iya yina na ganin na yi miki adalci, in sha Allah babu wanda zan bawa damar yi miki dariya, za mu zauna lafiya matuƙar za ki cigaba da yi min biyayya”.
Mun ɗan dade a haka kafin ya ɗago ni ya ce na je na yi alwala mu yi sallah, bayan mun idar ya miƙo min ledar da ya shigo da ita, na kai kitchen na juyo mana kaza a faranti tare da kofina, muka ci muka ƙoshi, raina duk babu daɗi, jiki a mace, shi dai ban san mene ne a zuciyarsa ba, bayan mun kammala ya shiga ɗakinsa ni ma na shiga nawa, na sake yin wanka, na saka rigar bacci mai ɗaukar hankali, tun da a yanzu babu wata kunya tsakanina da shi, na koma ɗakin nasa na tarar shi ma ya fito daga wankan, ya saka kayan bacci ya kwanta yana cewa na kashe hasken ɗakin, shiru na yi bayan na kwanta ina jiran ta inda Sadam zai fara taɓa ni ko ya matso kusa da ni kamar yadda na san zai yi wuya ango ya kasance a daren farko bai ko kai hannu jikin amaryarsa ba, amma sai na ji shiru, a zatona yadda yake mararina idan mun haɗu a yau da na zama mallakinsa zai yi fiye da kullum, sai na ga saɓanin haka, sai ni ce na ja na matsa kusa da shi, na kwantar da kaina a jikinsa, a haka bacci ya ɗauke mu.
Da asuba ya tashi, ya tashe ni, sannan ya tafi masallaci, bayan ya dawo ya sake kwanciya, ni kuwa zaune na yi ina ta tunanin wannan sabuwar rayuwa da na shiga, ina kuma istigfari har gari ya waye, na tashi na shiga kitchen na haɗa mana abun karyawa, komai na kayan abinci akwai a store ɗin dake kusa da kitchen ɗin, ina kammalawa na gyara gidan sannan na yi wanka na yi kwalliya na je tashinsa, na same shi yana shiryawa, na yi masa murmushi na ce”Ashe ka tashi”.
Shi ma ya mayar min da murmushin ya ce”Na tashi, ai na makara ma, zan je wajen aiki”.
Na ce”Aiki? Ina alƙawarinmu da kai, na cewar za ka ɗauki hutun sati ɗaya idan mun yi aure?”
Ya ce”Ban manta ba, abun ne ya zo babu shiri kin ga ai, ban kammala wasu ayyukan ba, ga shi Abba yana gari, idan ya ga ba na zuwa Company za mu samu matsala”.
Na marairaice na ce”Kuma ni kaɗai za ka bar ni a gidan?”
Ya ce”Ki yi haƙuri, next zan ɗauki hutun sai mu huta”.
Ya kammala shirin ya fito, muka ci abinci na raka shi ƙofar falo ya tafi, na koma na yi wanke-wanke na kwanta ina ta tunanin yadda zaman aurena zai kasance.
A ranar dai ya kusance ni, abun dai kamar yadda muka saba, amma bambancin ɗaya ne a baya idan mun gama zai ta yabo na, da nuna jin daɗinsa, yau kuma sam bai yi wannan ba, washegari ma hakan ce ta faru, mun kammala na fito daga wanka yake cewa”Ni wai Sayyada ko irin gyaran amaren nan ba a yi miki ba a gidanku? Ta ya zan ji ki yadda na saba jinki a waje?”
Na yi shiru na ji duk na kunyata na muzanta, sai yanzu ma na tuna ya kamata na gyara jikina, amma ai a ƙa’ida buduruwa gyarata ake yi ba ita za ta nema da kanta ba, wata zuciyar ta ce min ai ke kin zubar da garinki shiyasa, kuma na yarda da hakan.
A sanyaye na ce”Kenan ba wani daɗi da ka ji?”
Ya ce”Ina fa daɗi abu salam? Dama haka ake amarya? Gaskiya ya kamata ki gyara ko ki ce a gyara ki”.
Na ce”To a yadda auren namu ya kasance wane ne zai yi tunanin gyara ni? Kuma yanzu kowa yana jin haushinta wa zan tunkara da batun gyara?”
Ya ce”To ki san dai yadda za ki yi, don idan aka tafi a haka ni fa sam ban mori amarci ba, ji nake ga maganin nan ana ta tallansa, ki nemi inda za ki siya zan ba ki kuɗin”.
Na ce”To zan nema in sha Allah”.
Na kwanta jikina duk ba ƙwari, sai ya matso kusa da ni ya kwantar da kansa a jikina, saitin kunnena da shu’umar murya ya ce”Baby, don Allah ina neman wata alfarma”.
Na ce”Allah Ya ba ni ikon yi maka”.
Ya ce”Yanzu idan kin gyara jikinki sabuwar rayuwa za mu buɗe mu dinga shan amarcinmu daidai gwargwado, haka kuma ba zai yiwu ba muddin kika samu ciki, gaskiya dama ni a tsarina na fi so sai mace ta yi shekara ɗaya mu huta da juna sosai mun sake fahimtar juna mun ga tsara zaman mu sannan ta fara haihuwa”.
Gabana ya faɗi, na nutsu tsam ina ta auna kalamansa a raina, ya ce”Kin ga ba mu san da wane yanayi cikin zai zo ba, ƙila ki yi ta laulayi duk ki rame ki fita a hayyacinki kuma kin san idon danginki yana kanmu, yanzu sai a fara yi miki dariya ana zaton wahala kike sha a gidan, amma idan kika huta kika yi ƙiba muka sha soyayyarmu idan haihuwar ta zo ma sai mun fi marmarinta, amma ya kika gani?”
Na ce”Amma anya babu matsala kuwa? Ni a ra’ayina ko haihuwa ɗaya ce na yi kafin planing”.
Ya ce”To ni dai ga yadda na tsara mana, idan kuma ke ce mijin ni matar sai ki yi naki tsarin”.
Ya janye jikinsa ya juya min baya, hawaye ya sakko min, Allah Ya jarabce ni da ƙin son ganin Sadam yana fushi da ni, a raunane na ce”Ni fa ban ce ban yarda ba, amma kamar wata nawa za mu yi planing ɗin?”
Ya ce”Shekara ɗaya ma ya isa, indai kika bi umarnina Sayyada za ki ji daɗin zama da ni wallahi, na faɗa miki babu wata mace a waje da za ta sake ba ni sha’awa ballantana ma har na aure ta, saboda ni ma ina sane samun irinki sai an tona”.
Ya ce”Kin amince?”
Na ce”Na amince, ina sonka mijina, so ne ya sa na aure ka, kuma zan yi ta maka biyayya a kodayaushe, fatana dai ka yi mini adalci a zamanmu, don Allah kar ka butulce mini, kar ka kawo wata cikin rayuwarmu ta rage mana farinciki, ba zan iya raba ka da kowace mace ba, kishi ne zai saka zuciyata ta yi bindiga”.
Ya ce”Na yi miki alƙawarin hakan ba za ta faru ba My Baby”.
Ya kashe ni da daɗin baki sosai har na daina fargaba na amince har zuciyata, washegari kuwa ya ɗauke ni muka je wani private hospital, amma na yi mamakin ƙaryar da ya yi musu, ya ce matarsa ce ni, haihuwata uku duk CS ake yi min ana ciro yaran babu rai, shi ne muke buƙatar na yi planing na samu hutu kafin samun wani cikin, kuma implant yake so a saka min, saboda an yi min allura ta saka ni zubar jini, ƙwaya kuma ba na jurar sha mantawa nake yi, haka na yarda aka saka min tsinke na shekara biyar, da zummar idan ya yi shekara ɗaya za a cire shi, Sadam ya dinga lallaɓa ni, a cikin kwana ukun da aka ce kar na yi aiki da hannun komai shi yake yi, har wanka yi min yake, sannan bai kusance ni ba, ya ce sai na gyara jikina.
Anisa na tambaya inda ake siyan maganin mata, ta haɗa ni da wata mata ta ce kayanta suna da kyau sosai, na yi mata magana na ce ni bazawara ce zan yi aure ta yi min haɗi mai kyau, ta ce na kawo dubu ɗari za ta haɗa min komai har maganin sanyi ingantattu, na turawa Sadam account numberta, nan take ya saka mata kuɗin, a ranar kuma aka aiko min da kayan, na hau amfani da su ka’in da na’in.
Kafin na yi rabin kayan ni kaina na ji canji a jikina sosai, ranar kuwa da ya dawo min shi ma ya faɗa ya ce sai yanzu ya san ni amarya ce, wannan gyaran da na yi ma ya ƙarawa zamanmu amarshi, daga nan muka sake sakin jiki da juna, muka cigaba da shimfiɗa rayuwar aurenmu cike da soyayya.
Ƙalubale ɗaya shi ne ba ni da wata alaƙa da danginsa, sau ɗaya ya taɓa ɗaukata muka je gidansu, ai kuwa sai da na yi nadama, saboda yadda Momy ta yayyanka min maganganu ta ce kar ta sake ganin ƙafata a gidanta, ba ta sona, ba ta son aurenmu, ba ta alfahari da kasancewata matar ɗanta, kuma ba za ta taɓa yi min kallon suruka ba, na ma daina sakawa a raina ina da suruka indai ita ce, ina hawaye muka bar gidan, Sadam yana ta kwantar min da hankali, tun da kuma ban sake zuwa gida ta ba shikenan babu wani abu da take yi mini da nufin ƙuntatawa, kowa sabgarsa kawai yake yi, shi dai Sadam kullum sai ya je gidan, ina zuwa gidanmu, ina samun tarba daga wajen Mama, Baba ne dai sai dai kawai ya amsa gaisuwata fuska babu walwala, ban sake fira da Baba ba tun daga ranar da ya san na ɓarar da mutuncina.
Haka rayuwar ta yi ta miƙawa, ko na ji kewar samun ɗa ko ‘ya sai Sadam ya wanke min wannan tunanin, da soyayyarsa me tsayawa a zuciya, mun yi zaman lafiya sosai, har na tsayin shekara biyu, duk lokacin da na yi masa maganar cire tsinke sai ya ce mu ɗan ƙara lokaci, muna shiga shekara ta uku mahaifiyarsa ta fara saka mana ido da tambayar ƙalau nake kuwa? Me yasa ban haihu ba har yanzu, sai dai ya ce mata Allah ne bai kawo ba, ni mamaki ma ta dinga ba ni, tun da a ganina tun da ba ta sona ma ai ba za ta so ɗanta ya haihu da ni ba, a hankali ta fara matsawa da zancen rashin haihuwata, na ce masa to a cire mana kawai na samu cikin nan, firr ya ƙi, sai ya zamana ma indai ina so mu yi faɗa to na yi masa batun a ajiye planing ɗin nan, yanzu zai birkice min na kasa gano kansa, shi yasa na rabu da shi don na ga gudun ruwansa, ai kuwa ƙarshe na gani.
A hankali na lura ya fara bawa wayarsa muhimmanci, ko fira muke yi hankalinsa na kan waya, sotari sai na yi bacci na barsa yana danna waya, ko tsakar dare na farka na same shi a falo da waya, da na so yin ƙorafi sai ya taka min burki da faɗin ban isa da na tsara masa rayuwarsa ba, shi ba lusarin namiji ba ne, na ja baki na yi shiru, sau ɗaya na taɓa ɗaukar wayarsa na duba, ai kuwa na ga yadda yake lalata da mata a waya, abun har ya ƙazanta, a ranar saura kaɗan kaina ya fashe, wani ɗan ƙaramin yaƙi aka yi a gidan, don birkice masa na yi na dinga hauka da ihu, shi kuma tun yana kare kansa har ya fara cewa ya yi ɗin na ɗauki mataki, nan fa zagi da gore-gore ya ɓarke a tsakaninmu, yana jifana da kalmar mara tarbiyya ni ma ina faɗa masa shi ne mara tarbiyya, ban taɓa ɗaga masa murya ba sai a ranar, don haka ya faffala min mari, wanda hakan bai kashe bakina ba, tun daga ranar kuma bakina ya buɗe, idan ya faɗa min baƙa ni ma sai na mayar masa, tun da na lura shi bai san halakci ba, na yi zaton irin sadaukarwar da na yi masa tun kafin aurenmu zai saka ya yi mini kara idan halin nasu na maza ya motsa, sai ya nuna min sabo da kaza ba ya hana yankata.
LITTAFIN NAN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 700, KAFIN NA GAMA FREE PAGES MAI SO ZAI SAKA 500, WANNAN DISCOUNT ƊIN NA ‘YAN KWANAKI ƘALILAN NE, DON FREE PAGES SUN KUSA ƘAREWA.
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay
08028966015
[03/10, 8:10 pm] Sadiya Abdulrazak: In kunji ana wata miyar sai a maqota to ba ko ina bane sai kamfanin GHT🤩 Ka samu kudi dasu kuma ka qurewa cuta lamba duk dasu, ma’ana dai akwai magunguna tun daga na diabetes, malaria, infection zuwa gyaran jiki💃🏻 kuma zaka iya zama member na company a rinqa baka percentage kai har kyautuka, bonus ga kuma abinda zaka samu monthly.kunemi 👉🏻07064627917 ko kawai
dannan link don shiga group ɗina kai tsaye
https://chat.whatsapp.com/DmQX0AKyyX8BODoIiLoKj8?mode=ems_copy_t
*KU YI MANA ADALCI*
NA
Sadiya Abdulrazak
Page 9
Ban tashi sanin na yi ganganci ba, sai da na ga da gaske Sadam yanzu ba ya ta ni, kuma aurensa zai yi, duk yadda nake yi masa bambamin sai na cire tsinken jikina ya ƙi, a ganina wannan ai mugunta ce, kenan ni ya mayar matar ado, zai auro wacce za ta dinga haihuwa, shi yasa ƙarshe na ɗauki matakin da na ɗauka.
A sanyaye ya shigo ɗakin, na sauke idona a kan shi, sai hawaye suka fara zubo min, ya ce”Ki fito ga likitan nan ya zo zai ga hannun”.
Ya juya ya fita, na tashi, na ɗauki mayafi na yafa na fita, bayan ya gama dubawa ya yi mini faɗan na daina yawan motsa hannun, bayan ya tafi na tashi zan koma ɗakin, Sadam ya ce”Sayyada, ki dawo ki zauna mana, ba fita zan yi ba, zan ɗan ɗauki hutun aikin saboda na kula da hannun naki”.
Na ce”Ba na buƙatar kulawarka, ka je ka kula da wanda suka damu da kai”.
Na wuce ɗakin, ya biyo ni, na hau gado na kwanta, shi ma ya hau gadon, ya kamo hannuna me lafiyar yana matsawa ya ce”Jikinki akwai ƙwarin da za ki iya karɓa ta? Ina buƙatarki”.
Takaici ya sake kama ni, na ce”A’a, sai dai ka yi min fyaɗe”.
Ya yi murmushi ya ce”Ai babu fyaɗe tsakanin mata da miji”.
Na yi shiru don magana da shi ma na so nake ba, ballantana na tsaya na shi hujjojin da zai tabbatar akwai fyaɗen.
Na yi ƙoƙarin ƙwace hannuna ya riƙe ni tamau ya ce”Tashi ki sha maganinki”.
Ya fita ya ɗakko maganin da ruwa, yana cewa”Na haɗo miki shayi?”
Na ce”Na sha a asibiti”.
Ya ɓallo maganin ya ba ni na sha, sannan na koma na kwanta, ya sanyaya murya ya ce”Kin ga Sayyada wannan zaman namu ba zai haifar mana da ɗa mai ido ba, ba na son rashin kunya da neman fitina, ke kuwa yanzu shi kika saka a gaba”.
Na ce”Sadam ni fa indai ba fasa auren nan ka yi ba wallahi ba wani abu da za ka faɗa min na saurare ka”.
Ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya ce”To shikenan Sayyada, zan saka a ɗaga auren zuwa wata uku, indai kika samu ciki a cikin wata biyu na yi miki alƙawarin zan fasa auren”.
Na ce”Da gaske”.
Ya ce”Na rantse miki zan fasa indai kin samu ciki nan da wata biyu zan fasa auren nan”.
Sai na ji hankalina ya fara kwanciya, na ce”In sha Allah zan samu, Allah Ya ba mu mai albarka”.
Ya ce”Amin, amma kin san samun ciki ba zai yiwu kina guduna ba ko?”
Na ce”Na daina, dama ai don ina takaicin za ka yi auren ne shiyasa”.
Ya ce”Fine! Yanzu na matso kenan?”
Na ce”Haba don Allah, ba ka ga halin da nake ciki ba ne? Ina laifin ma a bari zuwa sanda ciwon nan zai warke?”
Ya ce”Shikenan, Allah Ya ba ki lafiya”.
Na amsa da amin, sai kuma ya ce”Don Allah ki yi min shikenan za mu zauna lafiya, kin fitini kanki duk kin rame, ba ki taɓa zuwa gida da zummar kina fushi da ni ba sai a wannan karon, don Allah ya zama na ƙarshe kin ji?”
Na ce”Idan ka so zai zama na ƙarshen in sha Allah, zan yi bacci”.
Ya ce”A tashi lafiya” Ya fita ya bar min ɗakin.
Tun daga ranar Sadam ya dage da kulawa da ni, kullum sai Mama ta kira ni ta ji lafiyata, don na faɗa mata ba ni da lafiya, amma ban ce mata ga abin da ya same ni ba, a yadda na lura duk ta yi zaton laulayi nake yi, har yanzu ba ta taɓa zuwa gidana ba, kuma ina zargin Baba ne ya hana ta zuwa. Bayan na warke muka cigaba da zaman lafiya da Sadam, kamar gaske ya rage yin chatting ɗin dare, yana ba ni lokacinsa kamar baya, a yadda ya ce min ya dakata da kula Safna har sai wata biyun ta yi an ga yadda zan kasance, sosai na hana idona idona baccin dare, rabin dare Sadam ya yi yadda ya so da ni, rabi kuma na raya shi da sallah, haɗi da addu’ar Allah Ya ba ni haihuwa mai albarka, sannan ina ta lallaɓa Sadam, ina kyautata masa, ado da kwalliya kuma na linka a kan wanda nake yi, bayan wata ɗaya ina ta addu’a da fatan Allah Ya sa kar na ga period ɗina, ai kuwa sai ga shi ya zo, ranar har kuka na yi, saboda a yadda nake sakarwa Sadam jikina wallahi ban yi zaton ba zan samu ciki a watan ba, ashe ba daga nan take ba, sai na tsananta addu’a, har sadaƙa nake kaiwa islamiyyar kusa da mu, haka nake turawa Mama kuɗi na ce ta sa a yi min sauka a islamiyya Allah Ya cika min burina, da ta ritsa ni da tambayar burin nawa na faɗa mata Sadam ne zai ƙara aure saboda ban haihu ba, yanzu kuma ga sharaɗin da laƙanya min, shi yasa nake fatan samunta ido rufe.
Haka wata na biyu ya zo, ina ta fargaba wallahi har ramewa na yi, saboda abinci ma ba ni da nutsuwar ci yadda ya dace, watarana muna zaune da shi nake tambayarsa “Wai yanzu a ina kuka kwana da batun yarinyar?”
Ya ce”Ai na faɗa miki sakawa na yi a ɗaga auren ko? Idan kuma ba ki samu cikin ba sai a yi a lokacin da aka saka tun farko, kin ga yanzu saura sati biyu kenan”.
Na ji na sare, saboda ban ga alamar ina da ciki ba, kuma a lissafi wani satin al’adata za ta zo, na ce”Don Allah ina neman alfarmarka”.
Ya zuba min ido bai ce komai ba.
Na ce”Idan ban samu ciki a watan nan ba, ka dubi girman Allah da manzonsa ka ƙara min wasu watanni biyun”.
Ya ce”A’a, ko kwana ɗaya ba zan iya ƙara miki ba Sayyada, indai ba ki samu cikin nan ba shikenan kawai ki yi haƙuri a yi auren nan a wuce wajen, ni ban ga dalilinki na tada hankali fa ba ma, ba fa gida ɗata za ku zauna ba, tana gidanta kina naki, kuma ba wai zan canza miki don na yi aure ba, ƙalau za mu zauna idan kika so”.
Kamar zan yi kuka na ce”Ai ba zan iya zama da kishiya ba ne, me zan yi ka fahimci ba zan iya haɗa miji da wata ba? Kamar yadda na yi maka biyayya a baya na so abin da kake so, don Allah ka yi min alfarma ni ma ka ba ni dama ko da ‘yar kaɗan ce, duk fa kai ne silar komai, da tuni na yi haihuwa biyu”.
Ya ce”Hmm! Allah Ya zaɓa abin da ya fi zama alkhairi kawai”.
Tun daga ranar bai sake tattaunawa da ni game da aurensa ba, ko maganar nake yi sai dai ya yi shiru, na ƙaraci kukana ba zai ce min ƙala ba, ana haka al’adata ta zo, tabbacin dai na karya wannan sharaɗin, ta tabbata ban samu ciki ba, hakan yana nufin auren Sadam sati ɗaya ya rage babu fashi.
Na fara al’ada ranar Juma’a, ranar Asabar yake ce min”Sayyada, na lura kamar jiya kin fara al’adarki ta watan nan ko?”
Na gyaɗa masa kai alamar e, na ce”Amma don Allah ka taimake ni ka ƙara min lokaci”.
Na ce”Ba zai yiwu ba, Sayyada ki yi haƙuri kawai ki ɗauki ƙaddara, Allah Ya sa hakan shi ya fi alkhairi”.
Na ce”Ta ya kishiya za ta zama alkhairi? Kishiyar da aka yi ta don a ƙuntata min? Sadam don gaskiya Allah ka sake ni”.
Ya ja tsaki ya ce”Wallahi Sayyada kukan daɗi ma kike yi, ta ya zan ta baki da lallaɓa ki kamar wata jaririya? To ki je ki tambaya ki ji, ki tambayi matan da mazan su suka ƙara aure, haka suke yi musu komai a tsanake suna kwantar musu da hankali? Wallahi samu kika yi ma”
Na ce”Ai da ni da sauran matan ba ɗaya ba ne?”
Ya ce”Ok ke da gwal aka sassaƙa ki ko?”
Na ce”Ba halitta nake faɗi ba, halacci da sadaukarwar da na yi maka, azabar da ka gana min kafin ka aure ni”.
Ya ce”To Sayyada kin yi min halakci na butulce miki, a je a hakan sai me? Idan kin so ai kina iya rama butulcin, a iya sanina duk wani adalci da ya kamata na yi miki na yi, ko na ce ina kan yi, amma tun da kina ganin ban yi miki daidai ba to ki ɗauki mataki”.
Cikin kuka na ce”Ai matakin yana hannunka! Ka sake ni mana”.
Ya ce”Za ki iya sakin kanki ai ko?”
Na ce”Kana nufin ka bar min igiyar sakin a hannuna?”
Ya yi banza da ni ya fice daga ɗakin, babu jimawa ya dawo da akwati ‘yar tsakiya, ashe dama tana cikin motarsa, na saki baki ina kallon akwatin, ya ajiye min ya ce”Ga kayan faɗar kishiya nan, an kai kayan lefen Safna tun sati biyu da suka ce, saboda dama na san ba samun cikin za ki yi ba, wannan tsinken wasu idan aka cire musu shi, sai sun yi wata shida kafin su samu ciki, duk da an ce akwai masu samu da zarar an cire, don haka gara ma ki kwantar da hankalinki, kawai ki cigaba da addu’a idan Allah Ya dube ki ya ba ki shikenna sai mu gode masa, idan sex ne ke saka a samu ciki ai da azabar da kika gana min cikin wata biyun nan sai kin samu cikin ‘yan biyu, don haka na daina ɓata lokacina, kuma ki daina mafarkin zan sake ki, idan kika cigaba da cewa na sake ki wallahi wataran sai na fasa miki baki, shashasha kawai, za ki ga alert, sai ki yi ɗinki da shi”.
Daga haka ya shiga ɗakinsa ya rufe ƙofar da mukulli, ya bar ni tsaye ina kokawa da numfashi, sai da ƙyar na samu na daddage na rusa ihu, kuka kuwa ya ɓarke min, na tashi a haukace a buɗe akwatin, na shiga fito da kayan dake jere a ciki ina watsi da su a falon ina faɗin”Wallahi Sadam sai ka sake ni, ba zan zauna da kishiya ba!”.
Ko sake fitowa falon bai yi ba, na je na dinga buga ƙofar ɗakin nasa ya ƙi buɗewa, da na leƙa ta windo sai na hango shi a tsakiyar gado yana waya haƙoransa a waje, da alama yana cike da shauƙi, ni ya mayar mahaukaciya, na durƙushe a wajen ina ta kuka, na yi mai isata na ta shi na shiga ɗakina, da asuba ina jin dawowarsa daga masallaci na fita na tare shi a falo, na ci kwalar rigarsa zan fara sababi, ai kuwa ya fincike ya wancakalar da ni a ƙasa, na shiga zaginsa ina yi masa Allah Ya isa, ya dinga dukana ta ko’ina, har ƙafa ya saka ya dinga tattaka ni yana zagina shi ma da faɗin, tun da haukan na zaɓi a yi ai shi ma ya iya mu zuba mu gani, tass ya yi min jikina ya yi tsami sosai, ya shiga ɗaki ya yi wanka na fice daga gidan, takaici ya hana ni motsawa daga kwancen da nake ina yin kuka kamar marainiya.
Sai da yunwa ta fara damuna sannan na tashi, siket ɗin jikina duk ya ɓaci da period saboda gumurzun da muka yi, don haka wanka na fara yi na gyara kaina, na shiga kitchen na ɗora indomi, na haɗa shayi, na karya, na sha maganin zazzaɓi don na fara jin alamaunsa, ciwon kai kuwa dama tuni ya dirar mini.
Haka na wuni cikin ƙunci, da rana na yi girki ɗan kaɗan na ci na rage na dare, yau ko shara ban yi ba, kayan nan na faɗar kishiya a falon suka wuni a warwatse, na so na kai ɗakinsa na watsa su, sai na tarar ya rufe da mukulli, ina jin dawowarsa na koma ɗakina na kulle, sai ga shi bai ma neme ni ba, hakan kuma sai ya ƙara ƙona zuciyata, na rasa ta yadda zan nunawa Sadam son shi da nake yi ne ya sa ba zan iya haɗa shi da wata ba, amma shi ya kasa fahimta, ni dai na san zan iya mutuwa idan ya auri wata, shi yasa nake yin iya yi na, amma na lura nema ake a ci ni da yaƙi.
Washegari sai ga Anisa ta zo gidan, ta tarar da ni kamar mahauciya, saboda yadda nake a firgice, ga falona har yanzu da kayan lefen a baje, har da akwatin, hankali tashe take tambayata abin da ya faru, na fashe da kuka na ba ta labari, amma ban ce mata planing na yi ba, sai ta rufe ni da faɗa ita wai laifina ma take gani, nunawa ta yi tun da har na shekara uku ban haihuwa ba to rashin adalci ne zai saka na hana mijina aure, kuma tun da ba wulaƙanta ni yake yi ba ai ya yi min da sauƙi, na kasa fahimtar da ita domin na ajiye wannan planing ɗin da na yi a matsayin sirri, haka ta ƙaraci nasiharta wacce take shiga ta fita daga kunnena, ɗaya ban ɗauka ba, tun da asirin ciki sai hanji, ni kaɗai na san wane ne Sadam.
Kafin ta tafi sai da ta gyara gidan tsaf, ta yi girki mai yawa, ba ta tafi ba sai da na yi mata alƙawarin zan haƙura mu zauna lafiya da shi, amma da ta tafi na watsar.
Kwana uku kenan muna ‘yar ɓuya da shi, sai a na huɗun ne ya yi dadowar bazata, da azhar ya dawo, kuma ya bar motarsa a waje bai shigo da ita ba, don haka ban ankara ba ya ritsa ni a kitchen, ina yin meat pie, kawai sai shigowarsa na ji, duk na diririce, kuma na ɓata rai, ya tsaya yana kallona da idanunsa da suke burge ni a baya, amma wallahi yanzu Allah na tuba sai na ga idon kamar ma a shagiɗe, “Sayyada” Ya kira sunana a sanyaye.
Na yi kamar ban ji ba, na zuba mai a kasko zan kunna gas din, ya shigo ya riƙe hannuna ya juyo da ni, ya ce”Kwana biyu ya gida?”
Na fara ƙoƙarin fizgewa, bai ba ni dama ba ya ce”Ki yi haƙuri da abin da ya faru rannan, wallahi kin kai ni bango ne, ki dinga tunawa ni fa mijinki ne, wasu abubuwan da kike yi suna yawa”.
Na fara ƙoƙarin sakin hawaye, amma ina ta dagiya da su dai ba su zubo ba, ya ce”I miss You, mu je ki ba ni hakkina ko?”
Na ce”Ai har abada! Tun da dai ka samu me ba ka, sai ka je ta ba ka, dama ai ba yau ta fara baka ba”.
Ya ce”Ba na son saka miki ƙarfi fa sai dole, Kodayake kin ce ma wai fyaɗe ne ko?” Ya ƙarasa da dariya.
Ya ɗaga min gira ya ce”Mu je? Kin ga idan amarya ta zo za ki huta da ni”.
Na fizge na ce”Wallahi ba zan sake haɗa shimfida da kai ba, kuma ya zama dole ka sake ni”.
Ya yi tsaki ya ɗauke ni cak, ina ta dukan bayansa, da na ga dai ya kusa cim ma ɗakin nasa na fara faɗin”Ka ajiye ni, ni ka ajiye ne, ban yi tsarki ba fa, period nake”.
Ya ce”A tunaninki hidimar auren za ta saka na manta da kwanakin period ɗinki kenan”.
Ya dire ni a ɗakinsa, ya biya buƙatarsa, ya yi wanka ya fito ya ce”Tashi ki fita Malama zan rufe ɗakina”.
Kallonsa kawai nake ina hawaye na ƙi tashi, ya zo ya ɗauke ji da tarkacen kayan da ya cire min yana cewa “Na daina barinki a ɗakina, kar aljanunki su tashi ki kassara ni”.
Ya watsa ni kan doguwar kujera ya fice daga gidan.
LITTAFIN NAN NA KUƊI NE A KAN NAIRA 700, DAGA YANZU ZUWA LOKACIN DA ZAN GAMA FREE PAGES ZA A SAKA 500
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay
08028966015
[03/10, 8:10 pm] Sadiya Abdulrazak: *KU YI MANA ADALCI*
NA
Sadiya Abdulrazak
Page 10
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/IQSfA0FWVmPL04MXpXtLfd
Assalamu alaikum
Kuna ina? Ku zo na zo muku da kyakkyawan albishir💃🏻kuna da labarin shahararriyar mai siyar da kayan nan, wato OUMMU RA’IS COLLECTION? Tana siyar da leses, jakununa, takalma, sannan kuma tana siyar da kayan yara, tun daga new bornhar zuwa 15 years, domin samun kayanmu cikin sauƙi ku shiga group ɗinmu, ko kuma ku tuntuɓe mu a kan lamba kamar haka 09138243082 sai kun zo.
A yau dai na ji kamar tun da aka yi aurenmu Sadam bai taɓa tozarta ni irin haka ba, zuciyata ta dinga zafi, na daɗe kwance a hakan ina tunanin me na yi masa da na cancanci haka a gare shi? Ba na tuna komai sai sadaukarwa da na yi masa, da kuma tarin cutarwar da ya yi mini, ko da iya fushin da mahaifina yake yi da ni aka bar ni ai ya cuce ni, na rarrashi kaina na tashi, na yi wanka na saka kaya, na koma kitchen na ƙarasa abin da nake yi, na haɗa da lemo na ci meat pie ɗin, da na daidaici ya kusa dawowa gidan na ɗauko sauran daga kitchen ɗin na ɗauki yogurt na koma ɗakina na rufe, alƙawari na yi ba zai sake gani na ba, idan ya gaji ya ga babu amfanin zaman auren namu ƙila zai sake ni, aikuwa na yi ƙoƙarin kauce masa ɗin, bai gan ni ba, amma kullum sai ya zo ya leƙa ni ta window yana ta tambayata ina lafiya? Banza nake yi da shi, a wannan zaman ɗaki da nake yi addu’a kawai nake Allah Ya kawo min ƙarshen zaman ƙuncin nan, Sadam ya sake ni na huta, ba mu haɗu ba har sai ranar ɗaurin auren da safe, kwana na yi ina sallar dare, hakan ya sa na makara, sai ƙarfe bakwai na yi sallar asuba, kuma na tashi da yunwa, amma haka na daure ina jiran ya fita, tun da sai takwas da rabi yake fita, tun da lokaci ya yi nake baza kunne ban ji fitowarsa ba, sai na tuna ƙika ya fita tun sassafe tun da dai yau ake ɗaura aurensa, hakan ya sa na fito, daga ni sai wata guntuwar rigar bacci iya cinyata, ina fitowa na ji an fizgo ni, na firgita na ƙwalla ƙara, na yi mamakin ganin ko shiryawa bai yi ba, na fara fizgewa ina cewa “Sake ni, ka sake ni!”.
Ya ce”Haba Sayyada, wai ke sai yaushe za ki sassautawa kanki ne? Kishi hauka ne? Ba fa duka za ta kwace miki ni ba, sammata za ki yi, idan kika duba tsarin nan ke ce matar so, ita matar haihuwa ce da rainon ‘ya’ya”.
Na ce”Kenan dai har yanzu ba ka fatan na haihu ko Sadam?”
Ya ce”Wallahi ba haka ba ne, kawai dai ina nuna miki yadda nake sonki ne”.
Na ce”Cika ni don Allah”.
Ya ce”A’a taimakona za ki yi, ki ɗan rage min zafi, kin ga anjima ina gidan amarya, na san za ki yi kewata, sati ɗaya da yawa, shin za ki iya kwana ke kaɗai ma kuwa? Shi yasa na so na haɗa muku gida, amma gudun fitinarki na canza ra’ayi”.
Na ce”Sadam ba zan ma zauna a gidanka ba, ballantana na yi maka fitinar, in sha Allah zan bar maka gidanka, wallahi na tsane ka, ba zan sake son ka ba har abada”.
Na fizge na yi hanyar kitchen ɗin, ya ruƙo ni ya ce”Ki so ni ko kar ki so ni wannan zaɓinki ne, amma zama da ke ko rabuwa zaɓina ne, ban da ma ke shashasha ce na ga ni ne gatanki? Ke da ubanki ya sallama mini ke kamar baiwa, har mene ne abun sha’awa a ki kashe auren ki koma gidansa, Sayyada ko da na sake ki ki saka a ranki ke da jin daɗin zaman aure har abada, ni ɗin da kika tsana kika raina wallahi ni ne gatanki”.
“Tirr! Ai kuwa Allah wadai da wannan gatan, indai kai ne gatana wallahi ni ce shugabar asararru ta wannan zamanin, kuma mugun fatanka ya tabbata a kanka, In sha Allah za ka sake ni, kuma zan auri miji na gari, na yi rayuwar aure mai ‘yanci, in sha Allah sai na rayu da wanda ya san darajata, mugu azzalumi, butulu”.
Ya ji zafin maganata ko a yanayin fuskarsa, ya yi murmushin gefen baki, sannan ya cije leɓensa ya jinjina kai ya ce”Shikenan, mu zuba mu gani, yanzu za ki ba ni hakkina ne ko kuwa sai na saka ƙarfin?”
Cikin kuka na ce”Ka saka ƙarfin, don Allah kar ka bar ni har sai na ja numfashin ƙarshe, ka kashe ni don Allah”. Na rushe da kuka
Bai ji tausayin kukan nawa ba, ya tura ni kan kujera, ban yi wani yunƙurin hana shi ba kamar yadda na saba, haka ya yi yadda ya so da ni, ina ta kuka mai cin rai, ya gama ya yi tsaki yana cewa”Allah wadaran naka ya lalace, ban da ma dai amaryar ta tabbatar min a cikin period take me zan yi da ke a yau Sayyada?”
Ban ce masa komai ba, ya koma ɗaki, na tashi ni ma na koma ɗakina, na fito daga wanka na zauna a bakin gado, zuciyata na zafi, ina ta tunanin matakin da ya kamata na ɗauka a kan Sadam, saboda har zuciyata na gaji da zaman auren nan, ina nan zaune ya shigo ɗakin cikin shirinsa na angwaye, ransa fess yana ta murmushi ya ce”To Sayyada, ni fa zan wuce, bayan ɗaurin auren zan shigo kafin na tafi ɗakin amarya”.
Na yi shiru ban ce komai ba.
Ya ce”Kina buƙatar wani abu ne? ‘Yan uwanki za su zo? To idan za ku yi girki ki faɗa min, kodayake bari na saka miki kuɗi sai ki yi abin da za ki yi, ni na tafi, so sorry Baby love”.
Ya tafi, na bi shi da kallo kamar sokuwa, yadda zuciyata ta yi rauni haka gangar jikina ma ta yi, ba ni da ƙarfin da zan dakatar da shi, na san ƙarshe dukana zai yi ma.
Waya na ɗakko na kira lambar Anisa ba ta shiga ba, na kira Mama, muka gaisa, ta ce”Sayyada ya ƙarfin jikin naki? Kina lafiya ko?”
Kamar ina jira na rushe da kuka sosai, ta ce”Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Mene ne ya faru? Me ya yi miki?”
Na ce”Yau ne! Mama yau ne, wallahi yau ne ɗaurin auren Sadam, ya tafi, ya tafi zai auro wata, Mama ko ku bar ni na dawo gida ko kuma na mutu, ba zan jure ba wallahi zuciyata ce za ta buga a yau ɗin nan”. Na tsananta kukana sosai
Mama ta ce”La haula wa la ƙuwwata illa billah! Haba Sayyada, ke kuwa wane kalar kishi ne da ke? Kishiya kanki farau? Waɗanda aka yi musu ɗin mutuwa suka yi? To wallahi ki kiyaye ni Sayyada, ko dai ki kwantar da hankalinki ki yi haƙuri, ko kuma ki ƙarasa ɓarar da garinki a wajen mijinki, domin yanzu yadda ya yi sabuwar amaryar nan babu abin da ba za ki gani ba”.
Na kashe wayar na ajiye, ina ji tana kira na ƙi ɗagawa, to me za ta ce min? Na gama lura babu wanda ya san yadda nake ji, ba za a fahimce ni ba, faɗin kukan da na sha a ranar ɓata baki ne, fuskata ta kumbura ta yi ja, ga shi Sadam bai dawo ba, babu wanda ya zo gidan a dangina ko ƙawaye, kodayake wa ba gayyata? Dama Anisa ce nake tunanin zuwanta, kuma ba ta zo ba, ta ma kashe wayarta, nan take na ayyana ƙila ma don ni ta kashe don kar ta zo, haka ba wuni cikin wani hali, amma hakan bai sa na ƙi jin yunwa ba wajen ƙarfe uku, ni dai na ga baƙincikin da zai sa na kasa cin abinci, shayi da biredi na sha tsaye a kitchen, na nemi waje na zauna a ƙasa dirshan, kawai gani nake duk duniya babu mai sona a yanzu sai Mama, ita kuma ba ta iya ja da maganar Baba, don haka ita ma ba ta da wani tasiri idan ba addu’a da take cewa tana yi mini ba, da na yi tsam na yi tunani sai na ga to idan haka ne mene ne amfanina? Ba ni da wani sauran amfani, idan na mutu ni kaɗai ce na yi asarar rayuwata, Sadam dai ba shi da asara tun da yana da wata matar a yanzu wacce ya ma fi so, iyayena suna da wasu ‘ya’yan bayan ni, wanda nake da tabbacin yanzu sun fi son su fiye da ni, tun da su ba su saɓa musu ba suna yi musu biyayya, sannan ni ba ɗa ba ballantana jika, da na haihu shi ne nake da tabbacin yarana za su koka idan na mutu, tun da kuwa ba mai damuwa da mutuwata ai ya kamata a ce na mutu kawai, sauke idona da na yi a kan wuƙa ya yi daidai da tunawa da hukuncin wanda ya kashe kansa, kafin ma na mutu na tarar da wannan hukuncin ita kanta azabar da zan sha na tuna ta, tun da ban manta raɗaɗin da na ji ba lokacin da na yanka hannuna, ba zan kashe kaina ba, ba zan sake cutar da kaina a kan Sadam ba, don bai cancanci haka ba, sai dai na cutar da shi, ‘Kashe shi zan yi?’ Na yi wa kaina tambayar a zuciya, wata zuciyar ta ce’Mene ne ribarki idan kin kashe shi an kama ki kin ƙare rayuwarki a gidan yari?’
A fili na furta “Babu! Shikenan kawai ya riga ya cuce ni”.
Gidanmu kawai zan tafi, ko kashe ni Baba zai yi sai dai ya yi, amma ba zan iya wannan zaman ba na takaici, na ɗauki waya na kira Mama, tana ɗauka na ce”Mama ki yafe min, don Allah ki cewa Baba ya yafe min”.
Mama ta ce”Sayyada ai mun yafe miki, me kuma ya faru?”
Na ce”Gani nan a kitchen riƙe da wuƙa zan kashe kaina na huta, tun da babu mai sona babu wanda ya damu da rayuwata, Mama zan kashe kaina fatana kawai ku yafe ni”.
A matuƙar ruɗe Mama ta ce”Innalillahi wa inna ilaihi! Sayyada! Kar ki yi, kar ki sake ki aikata wannan babban kuskuren, don Allah kar ki cutar da kanki, ki kamo hanya ki taho gida, Babanki zai karɓe ki, ki tuna rainon ciki da zafin haihuwa, ki tuna shayarwa da rainonki da na yi har zuwa girma, ina son ki har gobe, har abada, idan kika illata kanki ba ki yi mini adalci ba, kuma sai Allah Ya yi mana hisabi da ke” Ta fara kukan da ya tashi hankalina.
Ni ma cikin kukan na ce”Shikenan Mama, na fasa, ki daina kuka, zan haƙura na zauna har ciwon zuciya ko na damuwa ya yi ajalina, zan zauna da Sadam baƙincikinsa ya kashe ni Mama…” Na rushe da kuka.
Ita ma kukan take yi ta ce”Sayyada ki taho gida na ce, ki haɗa kayanki ki taho gida”.
Na ce”Ba na son abin da zai ja miki matsala da Baba, Mama ba na so…”
Ta daka min tsawa ta ce”Na ce ki taho gida!”
Da sauri na ce”To, gani nan”.
Na hau haɗa kayana a babbar jaka, na tattara komai nawa me amfani na saka hijjabi na bar gidan, mai gadi bai hana ni ba, tun da ba a ba shi wannan umarnin ba, ina zuwa ƙofar gida na tarar da Baba yana alwalar sallar la’asar, gabana ya fara faɗuwa, haka na daure na tunkare shi, ina hawaye, na duƙa na gaishe shi murya a dashe, ya bi ni da mugun kallo kafin ya ce”Ina za ki je da wannan uwar jaka?”
Na ce”Gida na dawo Baba, na gaji da auren nan, don Allah ku yafe ni, na tuba, wallahi na gane kuskurena”.
Baba ya ce”Maza ki koma inda kika fito, wallahi ko sakinki ya yi na faɗa miki ba ki da matsuguni a gidana, ni da ke har abada! Sayyada cutarwar da kika yi min ki sani sai Allah Ya yi mini hisabi da ke, ki koma inda kika fito, kuma idan kika je gidan wani ɗan’uwana ban yafe miki ba!”.
Ya tafi masallaci ya bar shi tsaye ina kuka, ga masu wucewa zuwa masallaci sai kallona suke yi, ban ji maganarsa ba, haka na ja ƙafa na shiga gidan ina ƙara sautin kukana, Mama ta zo ta rungume ni tana kukan ita ma, ta ce”Sayyada duk na jiyo tattaunawarku, ba ki da wajen zuwa da ya wuce nan gidan, so yake ki shiga duniya ko kuma zama za ki yi ɗan iskan mijinki ya kashe ki?”
Ta tura ni a ɗakinmu na yara, ina kuka, ta zaunar da ni, tana cewa”Idan har ya hana ki zama to ni ma ba zan zauna ba, sai dai mu tafi tare, me yasa maza ba su san ciwon mace ba? Ai ni dama na sani, mijinki ba zai taɓa daraja ki ba, saboda kin cuci kanki ki ɓarar da darajarki a idonsa”.
Zuciyata ta cika da fargabar hukuncin da Mama take son yankewa, na ce”Mama don Allah kar ki yi haka, kar ki bari Baba ya yi fushi da ke, tun da kuka haife ni na taso ban taɓa ganin kun samu saɓani ba sai ta silata, idan aurenki ya mutu ta dalilina wallahi na cika asararriya, ba zan yafewa kaina ba, rayuwata ma ba za ta yi albarka ba, zan tafi Mama ki yi min addu’ar fatan alkhairi, na yi miki alƙawarin ba zan taɓa sake aikata kuskuren da na aikata a baya ba, zan tsare mutuncina a duk inda nake”.
Mama ta ce”Me da me yake yi miki ne? Abun ya yi tsananin da ba za ki iya haƙuri ba?”
Na ce”Komai ma yi min yake ma, abubuwan ba za su faɗu ba”.
Ta ce”Ki zauna, ko yaya ne ki ba shi iska, zan faɗawa Babanki ba ki shigo ba, sai ki bari sai ya fita sannan za ki dinga fitowa tsakar gida”.
Na gyaɗa mata kai alamar na amince.
Ta tashi ta bar ɗakin. Baba yana dawowa daga masallaci ya fara faɗa yana tambayar ina nake? Da sauri na ja jakata na laɓe a bayan ƙofa, ina ji Mama tana ce masa ban shigo ba, ya cigaba da sababi yana cewa ko gidan wani nashi bai amince na je ba, gawata kawai zai gani ya yafe min abin da na yi masa, na guntse baki ina sakin kuka, yanzu idan ya riga ni mutuwa fa? Hakan na nufin ya tafi bai yafe min ba? Wace irin zuciya ce da Baba?
Da daddare Mama ta kawo min abinci na ci, ta zauna tana ta kwantar min da hankali. A haka na yi sati ɗaya cir a gidanmu, ba na taɓa fitowa sai Baba ba ya gidan, na yi mamakin yadda Saddam bai kira ni ba, na sake tabbatarwa ba ni da wani sauran mutunci a idonsa, wato ya samu amarya har ya manta da ni, hankalina har ya fara kwanciya, saboda da gaske fa ba na son ganin Sadam ballantana aurensa.
Ashe shi duk bai san wainar da ake toyawa ba, yana sane ya ƙi kirana, ya ƙi zuwa gidana, saboda ya hukunta ni da hakan, bai taɓa zaton ba na gidan ba, sai da ya gama sati ɗayansa da amarya cikin kwanciyar hankali, a ranar da ya dawo gidana ya ga ba na nan, mai gadi yake faɗa masa ai tun ranar aure da na fita ban dawo ba, hankalinsa ya tashi.
A ranar ina kwance ina bacci da safe ina jiyo firar Mama da Baba a tsakar gida sai ga kiran Sadam ya shigo wayata, da yake a silen take ban sani ba, sai da ya yi kira uku, a na huɗun ne na ga waya tana haske, ina ganin sunan shi gabana ya faɗi, na kashe wayar bakiɗaya, babu jimawa kuma na ji sallar yaro, tare da faɗin”Wai Sadam yana sallama da Sayyada”.
Ƙirjina ya doka da ƙarfi, har sai da na dafe shi, Baba ya ce”Ka je ka ce babu Sayyada a gidan nan”.
Yaron ya dawo ya ce”Wai ya ce mijinta ne, yau sati ɗaya ba ta gidansa”.
Mama tuni gumi ya fara yanko mata, ta ɗauki buta ta shige banɗaki, Baba kuma gabansa ya faɗi ya yi tsam da jin ashe ban koma gidana ba, amma ya maze ya ce”Ka ce masa ba ta zo nan ba”.
Ina ɗaki a tsaye a bayan ƙofa ina ta gumi sai jin sallamar Sadam na yi ya shigo cikin gidan, na ƙara ruɗewa, ya gaishe da Baba ya amsa a taƙaice, Saddam ya ce”Baba dama Sayyada ce…”
Baba ya katse shi da faɗin”Ba na son jin komai! Ta zo nan amma ko gidan ba ta shiga ba ta koma, don haka sai ka san inda za ka tafi nemanta”.
Saddam ya ce”Don Allah Baba ka yi haƙuri, na san tana gidan nan, kawai dai ranku ne ya ɓaci, ba za ta je ko’ina ba ban da nan, don Allah a yi haƙuri, zan gyara idan laifi na yi mata”.
Baba ya ce”To ban san kuma da wane yaren zan yi maka magana ka fahimta ba, yanzu ni na yi maka kama da wanda zan yi maka ƙarya kenan? To kai ma ka sani, ko sakinta ka yi ba ta da wajen zama a gidana, ballantana kuma yaji, don haka ka tashi ka bar min gida”.
Sadam ya shiga ɗaga hanci yana shaƙo numfashi kamar sabon maye, ya ce”Amma Baba kamar fa ina jin ƙamshinta, ina nufin turarenra”.
Ya tashi tsaye, ai kuwa ya ga ashe a kusa da hijjabinta dake kan igiya ya tsugunna, ya gane hijjabin kuma ya tabbatar da ƙamshin, ya ce”Wallahi Baba Sayyada tana cikin gidan na , don Allah ku fito min da matata mu tafi, Wallahi zan gyara, wasu abubuwan kuma laifinta ne”.
Baba ya rasa abun cewa, can kuma sai ya tashi ya leƙa ɗakin Mama, ya dawo ya leƙa ɗakin da nake, ina bayan ƙofa ni da kayana, amma wayata tana yashe a tsakar ɗakin, ya ƙarasa cikin ɗakin ya ɗauki wayar da Sadam ya kira ko zai jiyo ringing a cikin gidan, ya ce”Wannan wayar…”
Ido huɗu da muka yi ya sa ya ƙarasa maganar, na fashe da kuka ina cewa “Baba ka yafe min”.
IN SHA ALLAH GOBE ZAN KAMMALA FREE PAGES, GOBE BA ZAN KARƁI 500 BA, DISCOUNT ZAI ƘARE A YAU, 700 NE LABARIN NAN
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay
08028966015
[03/10, 8:10 pm] Sadiya Abdulrazak: *KU YI MANA ADALCI*
NA
Sadiya Abdulrazak
Page 11
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/IQSfA0FWVmPL04MXpXtLfd
Assalamu alaikum
Kuna ina? Ku zo na zo muku da kyakkyawan albishir💃🏻kuna da labarin shahararriyar mai siyar da kayan nan, wato OUMMU RA’IS COLLECTION? Tana siyar da leses, jakununa, takalma, sannan kuma tana siyar da kayan yara, tun daga new bornhar zuwa 15 years, domin samun kayanmu cikin sauƙi ku shiga group ɗinmu, ko kuma ku tuntuɓe mu a kan lamba kamar haka 09138243082 sai kun zo.
Da matuƙar mamaki mai haɗe da tsantsar ɓacin rai ya ce”Sayyada!?”
Na maƙale a jikin bangon ina maƙerƙeta, saboda na yi zaton dukana zai yi, amma sai na ga ya fita yana ƙwalawa Mama kira, ta fito daga banɗakin da ta ɓuya ita ma tana karkarwa ta ce”Na gaji, na gaji da yadda rayuwar ‘yata take ƙunsar takaicin namiji me yasa maza ba kwa yi mana adalci ne?”
A fusace Baba ya ce”Au haka kika ce? Ni ne mara adalcin? To ki tattara ‘yar taki ku bar min gida, wallahi sai kun bar gidan nan, idan Sayyada ta sake kwana a gidan nan a bakin aurenki!”.
Na fito da sauri ina kuka na duƙa a gaban Baba na kama ƙafarsa zan fara yi masa magiya, ya yi min wata ƙafa sai da na gangara, Sadam ya taho da sauri ya tada ni tsaye ya rungume a ƙirjinsa yana cewa”Baba don Allah ka yi haƙuri”.
Na fara ƙoƙarin janyewa daga jikinsa ina cewa”Ka rabu da ni, ya dake ni ɗin indai zai wuce, don Allah Baba ka kashe ni idan na zama gawa na san na zama free za ka yafe min”.
Mama ma kukan take ta ce”Na yarda zan bar maka gidanka, gara na haƙura da auren na zauna da ‘yata na jiɓanci lamarinta, Allah ma muna yi masa laifi ya yafe mana ballantana kai ɗan’adam”.
Na ce”Don Allah Mama kar ki yi haka, ni ban cancanci ki ɓata aurenki saboda ni ba, zan tafi kawai amma wallahi ba zan cigaba da rayuwa a gidan Sadam ba, idan kuma aka matsa min komai zai iya faruwa” Na fashe da kuka sosai.
Sadam ma idonsa ya yi ja, ya ce”Baba Sayyada fa ‘yarka ce, a duniya na tsani na ga wani yana tozarta ta tun ranar da na aure ta, ko ba ka kore ta ba dama wallahi ba zan bari ta zauna ba, ai ba sakinta na yi ba, kuma ba zan sake ta ba, ko mutuwa na yi yau na bar wasiyya kar Sayyada ta dawo gidan nan, ta zauna a gidana na mallaka mata shi halak malak daga yau, ke ki wuce mu tafi!” Ya ƙarasa da daka min tsawa rai a ɓace.
Sam bai burge ni ba, haushi ya ba ni soyayya, domin wannan abin da Baba yake yi min bai saka na ji ba na son shi ba, abu ɗaya na sani na yi masa babban laifi shiyasa ya kasa yafe min, na ce”Kar ka sake ka ce za ka faɗawa mahaifina magana, kuma aurenka na ce na gama shi, don haka dole ka sake ni”.
Ya ce”Ina kayan naki suke?” Bai jira amsata ba ya shiga ɗakin ya ɗakko jakar.
Ya kalli Baba ya ce”Ba dai ba ka son ganinta ba? In sha Allah ba za ka sake ganinta ba daga yau”.
Sannan ya kalli Mama ya ce”Mama ki yi haƙuri ki zauna ki riƙe aurenki, ko kin kashe aurenki ba za ki rayu da Sayyada ba, don wallahi babu kotun da ta isa ta saka na sake ta ballantana mutum, amma ki saka a ranki ‘yarki tana cikin aminci, idan ta shiga ƙunci ita ta so”.
Ya kalle ni ya ce”Sayyada mene ne amfanin zama a inda ganinki a wajen zai haddasa husuma da ɓace-ɓacen rayuka? Na yi miki alƙawarin kyautatawa daga yau, wallahi zan zauna da ke bisa adalci idan a baya ina yi miki abubuwan rashin adalci yanzu zan gyara zan yi miki adalci”.
Ya riƙe hannuna yana cewa”Mu je gida, mijinki yana tare da ke har ƙarshen numfashinsa”.
Na firge, ya sake damƙar hannuna ya fizge ni zuwa waje, ya jefa ni a motar ina ta kuka ya ja muka tafi, ban tsagaita da kukan ba shi ma bai rarrashe ni ba har sai da muka ƙarasa gida, ya faka motar ya ce”Ki fito”.
Na ce”Wallahi Sadam cigaba da rayuwa tare da ni ba zai yi maka daɗi ba, za ka yi danasanin dawo da ni gidan nan”.
Ya ce”Na ji na yarda, indai ke zai yi miki daɗi ai shikenan”.
Na ce”Na tsane ka Saddam, ka kiyayi zama da wanda ya tsane ka musamman ma mace”.
Ya yi shiru yana kallona, ni ma shirun na yi ina jin yadda tsanarsa ke ta’azzara a zuciyata wallahi ji nake shi ne wanda na fi tsana a duniya, sai yanzu nake ganin girman cutar da ya yi min, ina zan kai fushin mahaifina?
Ya ce”Sayyada, ki yi haƙuri kin ji? Amma idan kika duba ba ki da wata mafita wacce ta fi mu cigaba da rayuwar aurenmu, in sha Allah za ki samu haihuwa idan ma don ita ce, kuka kishiya babu ruwanki da ita, wallahi ba zan rage komai da nake yi miki na kulawa ba a matsayinki na matata, ni fa ba mahaukaci ba ne, ba kuma ba ni da zuciya ba ne, wannan ƙiyayyar da kike nuna min da rashin kunya abun yana yi mini zafi sosai, kawai ina daurewa ne saboda na san a baya na cutar da ke, sai nake ganin na dawwama da ke na riƙe aurenki da amana shi ne zai wanke ni a zuciyarki da kuma idon iyayenki, amma kin ƙi ba ni haɗin kai, ya zan yi ne? Me kike so na yi miki ki yarda da ni?”
Na ce”Ka sake ni, sakina kawai za ka yi na yarda kana sona kuma ka yi min halakci, don Allah idan kai ɗan halak ne ka sake ni Sadam”.
Ya yi huci mai zafi, ya fita daga motar, ya zagayo inda nake ya fito da ni, cak ya ɗauke ni ya dire ni a falo, ya ce”Kina jin yunwa ne?”
Na yi banza da shi ina ta kuka.
Ya zauna ya riƙe hannuna yana ta wasa da shi, ya ce”Sayyada”.
Ban amsa ba, ya cigaba da faɗin”Don Allah ki dakata da wannan shirmen, ina sonki, kina sona…”
Na katse shi da faɗin”Gyara kalamanka, ka ce dai a da na so ka, amma wallahi ban da yanzu”.
Ya ce”Yanzun ma kina sona, ɓacin rai ne kawai, kuma na san za ki huce, yanzu dai ina so zamanmu ya dawo kamar farko, mu rayu cikin farinciki don Allah”.
Na daka tsaki na ce”Ko za ka kwana ka wuni kana magana abu ɗaya kawai nake jin kana maimaitawa, kalmar saki kawai za ka furta min na san an samu cigaba a kalamanka”.
Ya ce”Ai kuwa ba za a samu cigaban ba, ni dai Allah Ya sani na yi iya yina, tun da taurin kai ne da ke ki je ki yi duk yadda kika ga dama, amma kar ki manta ni mijinki ne, aljannarki tana ƙarƙashin ƙafata”.
Na ce”Ai ba miji irinka ake nufi ba”.
Ya ce”Ok, ko me za ki yi, ki yi, ga wajen nan”.
Yana gidan a ɗakinsa ni ina falo ina ta ƙunar zuciya, har aka kira sallar azhar, ya fita masallaci, na tashi na ɗauki jakata na fito ba don na san inda zan je ba, amma kawai burina na yi nesa da shi, na gujewa aurensa, na ji daɗin ganin Baba mai gadi ba ya nan, da sauri na ƙarasa, sai dai ina zuwa na ga kwaɗo a jikin ƙofar, na san dai ni ake tsarewa, tun da don zai tafi sallah ba ya rufe ƙofar ta ciki, na ja jiki na koma ina hawaye, ni ma sallar na yi, na zauna ina ta tunanin mafita, wata zuciyar ta ce na haƙura na zauna da Sadam mu gyara zaman, wata kuma ta ce idan ban bar gidansa ba baƙincikinsa ne zai kashe ni, saboda duk daɗin baki yake yi mini ba zai canza hali ba, kuma na fi yarda da ba zai canza ba ɗin, tun da tun yaushe muke tare? Tun yaushe yake cuta ta?
Bai dawo da wuri ba, saboda sai da ya je ya siyo mana abinci, ya shigo fuskarsa babu yabo babu fallasa ya ajiye min, na shige ɗakinsa da na shi, wajen la’asar ya fice daga gidan bai kula ni ba, bayan magriba ya dawo da abinci a kula, ya ajiye min, nan take na fara tunanin daga gidan shegiyar matarsa ya karɓo, don haka na ce”Ka ɗauke ba zan ci ba”.
Ya ce”Ok”.
Ya matsar da shi daga gabana, ya ce”Sayyada, yau na dawo ɗakinki, kuma kwana biyu za a dinga rabon kwanan, ai ya yi ko?”
Takaici ne ya hana ni cewa komai, ina raba shi da kiwon kyalle yana kyalle ta haihu? Ya ce”Sayyada”.
Ban amsa ba, ban ma kalle shi ba, ya ce”In sha Allah daga yanzu ba zan sake takura miki ba, amma ba zan sake ki ba, sai dai kuma ba za ki sake fita daga cikin gidan nan ba har sai na gamsu da yadda kika karɓi zaman aurenmu, komai kike so ki faɗa min zan kawo miki, sabga kuma idan ta tashi ki dinga Allah Ya sanya alkhairi a waya, ba zan gajiya wajen yi miki addu’ar nema miki shiriyar Allah ba, sannan zan fara yi miki ta gujewa fushin Allah, ni mijinki na yafe miki”.
Daga haka ya tashi ya fita daga gidan, ina nan zaune a falon ya dawo can bayan sallar isha’i, ya wuce ni yana waya ya shiga ɗakinsa ya rufe, har sha ɗaya ina nan a zaune, bacci da yunwa sun addabe ni, haka dai na buɗe kular na ga faten doya ne da kifi, na tashi na je kitchen na ɗakko faranti na zuba na ci, ni ce har da ƙari, kamar na manta daga hannun kishiya ya fito, na shiga ɗakina na yi wanka na canza kaya ka kwanta, nan take bacci ya yi gaba da ni.
Washegari ya dafa shayi ya karya, ya yi tafiyarsa aiki, ni ma guntun shayi da biredin na ci, wajen sha biyu ya aiko da cefane mai yawa, a raina na ayyana wato dai shi ya dage ni da shi zama daram ko? Na yi girki iya cikina, na ci, na kai wanda zan ci da daddare ɗakina, na wanke komai kamar ban yi ba, don ba na so ya san na yi ɗin, so nake ya gane da gaske ba na zaman auren nan, ko zai sake ni na huta.
Bai dawo ba sai bayan sallar isha’i, ina ɗakina ya turo ya shigo, ya ce”Sayyada na ki yi girki ba ne?”
Na ce”Ban yi ba, ai ni da girki a gidan na. Har abada!”.
Ya ce”To Allah Ya raba ki da cutar yunwa”.
Ya fita, ina jin sanda ya fice da mota daga gidan, ya dawo ya shigo ya ajiye min takeaway na ƙi kula shi, a nan ya zauna ya ci na shi, ya sha ruwa, sai na ga yana rage kayan jikinsa, ya gama ya hau gadon, da sauri na tashi zaune ina cewa”Ka fitar min daga ɗaki”.
Ya ce”Ba zan samu hakkina ba? Gobe fa zan bar gidanki, wai kar na barki da kewata”.
Na ce”Allah Ya kiyaye, wacce ta damu da kai ita ce za ta yi kewarka, har abada ba zan sake baka haɗin kai, sai dai idan fyaɗen da ka saba za ka yi”.
Ya sauka gadon ya ce”Ai na daina yi miki har abada, sai da safe”.
Ya fice daga ɗakin.
Washegari duk da yana ɗakin Safna sai da ya zo gidana da safe, ganina kawai ya yi bai ce komai ba ya tafi, washegari ma haka. Ranar dawo ɗakina ma haka ba ya shiga harkata, kuma ranar da zai bar ɗakina ya sake zuwa ya ce zan ba shi hakkinsa? Na ce a’a, sai ya ce Shikenan duk ranar da na ji ina bukatarsa na sanar da shi, shi dai ba zai sake nema na ba, daga ranar kuwa bai sake nema na ba, har tsawon wata ɗaya haka muke zaman kowa ya yi ta kansa, ya riga ya saba ba na ba shi abinci, iya cikina nake girkawa.
Wata ranar Lahadi da ba zan taɓa mantawa da ita ba, ranar ba ma ni ce da kwana ba, a gidan Safna yake, ina ta bacci wajen sha biyu, na ji shigowar mutum ɗakina, ya kunna hasken ɗakin, Sadam ne tsaye daga shi sai ɗan wando, ya yi min murmushi, na ɓata rai, ya ƙaraso ya zauna a bakin gadon ya ce”Yau fa Safna ba ta nan, aikin kwana take yi, kuma dama tana period, ni kuma na kasa jurewa, shi ne ta ce ta amince na zo gare ki”.
A harzuƙe na ce”Ni ban amince ba, kenan ma ba ka faɗa mata na bar mata kai ba har abada?”
Ya ce”Don Allah Sayyada mene ne matsalarki? Kin san fa ba daidai kike aikatawa ba, ya kamata a ce zuwa yanzu mun wuce wajen”.
Na yi banza da shi.
Ya ce”To ya za ki yi da ni yanzu? Za ki ba ni ne?”
Na ce”Ka ƙwata mana! Ko dama da ka ce ka daina yi min fyaɗe kana zaton na yarda ne?”
Ya ce”Yanzu idan za a ba ki zaɓi za ki zaɓi na je wata a titi ta ba ni?”
Na ce”Ai dama ka saba!”
Ya ce”Na yafe miki duka ƙazafin da kike yi min”.
Ya janyo ni jikinsa, duk duka da yaƙushin da nake yi masa bai rabu da ni ba, sai da ya cim ma muradinsa, zuciyata ta dinga zafi, ya shiga ya yi wanka a banɗakina, ya kwanta bacci ya kwashe shi.
Na tashi zaune ina fashewa da kuka, kallonsa da nake yi ne ya dinga ta’azzara ƙiyayyarsa a zuciyata, shikenan haka zan cigaba da rayuwa cikin rashin ‘yanci? Sam ban san inda na dosa ba fa, ba zai yiwu ba, Saddam ya yi kaɗan na kashe rayuwata saboda shi. Ina wanka ina kuka, na gama na saka doguwar rigar atamfa, na haɗa kaya a jaka, na fice daga ɗakin, ga mamakina ƙofar dai a kulle take ta ciki, na shiga ƙwanƙwasawa mai gadi, ya buɗe ya fito daga ɗakin nasa, na durƙushe a ƙasa ina kuka na ce”Baba indai kai uba ne ka yi tunanin yadda za ka ji idan ‘yarka ta kasance a halin da nake ciki, don girman Allah ka buɗe min ƙofar nan na tafi gidanmu don Allah”.
Baba ya ce”Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Ki yi haƙuri ‘yata, komai ya yi zafi maganinsa Allah, ki yi ta faɗawa Allah, idan yana cutarki shi zai yi miki kyakkyawar sakayya, ba zan iya buɗe miki ƙofar nan ba, amma na lura kina cikin tsanani, yanzu dare ne, gobe da safe na yi miki alƙawarin zan buɗe miki ki tafi ‘yata”.
Na ce”Don Allah Baba ka buɗe min yanzu, zan iya mutuwa idan na kwana a gidan nan”.
Ya ce”Ki yi haƙuri, yadda ba zan iya bari ‘yar da na haifa ta fita daga gidan cikin daren nan ba, haka ke ma ba zan bar ki ba, da yau da gobe duk ɗaya ne, awa ne ma ya rage mu ga wayewar garin? Ki yi haƙuri kin ji? Ki je ki ɗaura alwala ki yi sallah, Allah zai kawo miki sassauci”.
Na gyaɗa masa kai, na ja jakar kayana na koma ciki, amma sai dai kash, ƙaddara ta riga fata, inda na yarda na ɗauki shawarar Baba mai gadi ƙila da abubuwa da yawa ba su faru ba cikin rayuwata, cikin ɗakin na koma na zauna a falo na fashe da kuka sosai, zuciya ta dinga yi mini ayyane-ayyane, a haka ne ta ayyana min me zai hana na kashe Sadam? Ai dai ba wanda zai min tilas ɗin zama da gawa ko? Ba tare da tsayawa tantance shawarar zuciyata ba, na yi kitchen na ɗakko wuƙa na tafi ɗakin nawa.
Yana kwance ya baje sai sharar bacci yake yi hankali kwance, na tsaya ina kallon shi da wuƙar riƙe a hannuna, wallahi na kasa tuna kyautatawa ko guda ɗaya da ya yi min, sai tarin ƙuntatawa da cutarwa ne suke ta zuwa kaina, zuciyata tana ta faɗa min shi ne matsalata, kuma ina da maganin matsalar, na kashe shi kawai na huta.
Duk taku ɗaya da nake yi na matsawa kusa da shi, ƙara bugun zuciyata ake yi, gabana sai faɗuwa yake, haka har ya zamana na matsa dab da shi, babu wani sauran taku, na ɗaga wuƙar cike da zugar zuciya da ta shaiɗan, sai dai na kasa daɓa masa ita a ciki kamar yadda na san zan fi kashe shi cikin sauƙi, sai kuma na sauke, sai da na ɗaga wuƙar sau biyu ina fasawa, a na uku da na ɗaga na daddage na caka masa a santaleliyar cinyarsa, na finciko ta da sauri, ya zabura ya saki wani gigitaccen ƙara sannan ya fara salati, tuni jini ya fara malala a gadon, na sake ɗagawa kamar zan caka masa na ce”Sadam za ka sake ni ko sai na kashe ka?”
Zare ido yake cikin azabar ciwo da mamaki, ya ce”Sayyada? Kashe ni za ki yi?”
Na ce”Za ka sake ni ko na ƙarasa ka?”
Yana fizgar numfashi ya ce”Na…na…na sake ki, Na sake ki Sayyada”. Ya fara kwarara ihu yana riƙe ƙafar.
Jikina ya hau rawa, na fita da gudu ina ƙwalla kiran mai gadi, “Baba! Baba ka zo ka taimake ni, zai mutu”.
Ya fito da sauri, ya yi cikin gidan ni kuwa cikin farincin yau gidan a buɗe yake na buɗe na fice da gudu, ina ta haki, na yi nisa da gidan rigata ta harɗe ni na faɗi, daidai lokacin kuma na ji marata ta murɗa, na saki kukan azaba da nadama, da ƙyar na tashi ina jin ruwa mai yauƙi yana bin ƙafata amma ban fasa sauri ba, don na kasa yin gudu.
Yau dai Sadam ya sake ni, amma tun a ranar na kasa jin farincikin da na yi tsammani, a tunanina rabuwa da Sadam ita ce hanyar buɗe shafin farincikina, ashe shafin ƙunci ne zai buɗe min, ku biyo ni don jin yadda rayuwata ta kasance.
.
Sadiya Abdulrazak


