Akan Mijina Hausa Novel Complete
ππππππ
*AKAN MIJINA*
ππππππ
NOT EDITEDβ
Written by
Minertβπ»
Dedicated to
Hrtbeath
Matsayin Ki Bawai Cikin Littapi Neh Kawai Ba Har Cikin Zuciya Da Gangar Jiki Sonki Yabi Jini Ya Tsaga Proud Of Yuhh Fatima Abbakarπ
Am Back Again Mah Pan’s Gaskiya Ina Kara Jinjina Muku Bisa Irin Zallar Kauna Ba Algus Da Kuke Nunamin Allah Yabar Zumunciπ€π»ππ―
IT’S ALL ABOUT LUV AND CARINGπ
More Comments More Typingβπ»
Bismillahir Rahmanin Raheem
Pg 1&2
Babban Estate ne Wanda ya gaji da haduwa girma da tsarin gidan kadai ya isa kasance cewa an narka makudan kudi wajan tsara gidan part biyu ne cikin estate din Koh wanne off stairs ne Idan ka kalli tsarin gidan zakayi tunanin a turai ne tsabar irin kyan da yake dashi.
Duk inda ka juya manyan Sojoji ne da manyan bindiga fuskar’su babu alamun Rahama kiris Kawai suke jira Mutum yayi mistake kasha suburbuda
Abban Sojoji Hausa Novel Complete
Wata kyakkyawar mata na gani sanye da shiga ta alfarma tana zaune akan lallau’san kujerun parlon rike take da iPhone S max da alama chatting take domin ta mayar da hankalin’ta akan abinda take
Kare mata kallo Nayi zatakai shekara 27 sedai hutu dajin Dadi yayi tasiri wajan boye shekarun’ta fara ce sedai ba sosai ba tana da kananun ido haka zalika bata da tsayi sosai komai nata Dan daidai ne da alamu bata da kirki ko kadan
Jiki yana rawa Indo ta sunkuya har kasa cikin tsantsar ladabi tace ranki ya dade ur food is ready bata dago kaiba bare tasan da zaman Indo a wajan takai almost 15minute kafin tace Ok kina iya tafiya
Ta b’ata tsahon lokaci tana zaune kafin ta haura Off stairs fitowar shi daga toilet kenan Yana tsane sumar kanshi da karamin da towel dama ganshi seda na tsorata domin Nayi tunanin Koh gamo nayiπ€£π·
Allah yayi masa halitta irin ta sadaukai jarumai kyakkyawa ne ajin karshe domin Yana da zubin yan etopia godo sosai jikin’shi a murde yake Yana da Sexy eyes gashin kan’shi yana kwance luf luf Fuskar’shi doguwa ce hade da pink lips sedai miskiline sosai Bai fiye wayan magana ba Sam Sam baya Dariya idan kaga Yana doguwar magana tabbas Yana tare da Ammyn shi a k’alla Zaiyi 38 years IRFAN NASSER DIKKOH kenan
Bai kalli site din da Aisha take ba shiryawa yayi cikin kakinsa na Sojoji ba karamin kyau yayi ba Duk da baya Dariya Amma hakan Bai hana Zallar kyawun da Allah ya masa fitowa ba
Tana zaune akan Bed harya gama shirin sa koh breakfast bai yiba haka ya fita tun kafin ya karasa parking space masu tsaran lafiyar shi suka dinga Sara masa hannu Kawai yake daga musu bude masa motar sukayi get man ya wangale musu motocin da suke binsu sunkai guda 10 har suka isa Billa gidan gwamnati
Minertβπ»
πππππ
*AKAN MIJINA*
πππππ
NOT EDITEDβ
Written by
Minertβπ»
Dedicated to
Hrtbeath
IT’S ALL ABOUT LUV AND CARINGπ
Bismillahir Rahmanin Raheem
Pg 3&4
Ya d’auki tsahon lokaci suna magana da President kafin ya tafi Office dinshi Escort dinsa suna tare dashi domin babu damar yayi tafiya komai kwankwantar ta batare da Escort ba domin kasancewar shi Babban mutum Kuma Wanda talakawa suke Jin Dadin shi hatta mai Girman shugaban kasa ya bala’in Respecting din IRFAN NASSER DIKKOH
Allah yayi masa kwarjini da cikar zati
Sedai Kuma ya hadu da Mata Jarababbiya ga masifar kishi ta Kori house sunfi goma domin Koh kallon IRFAN kayi by mistake daga ranar ka Dena aiki a gidan
Sam bata wani kula dashi kamar ba Mijin Auren taba ita dai barta a fannin kishi ko Bed din da suka kwanta house girl ce take gyarawa shi kuwa IRFAN Mutum Bai kyankyami shiyasa bai cin abincin gidan sedai yaje wajan Ammyn shi da kanta take masa girki
Haka a fannin Auratayya IRFAN kwarzo ne wajan iya sarrafa mace cikin lokaci kadan zaisa ki manta wacece ke Yana da feelings me karfi sedai Aisha sosai take nuna masa ragwanci dakyar take yarda yayi 2 round hakan ma ta dinga masa mita kenan Wannan abin abin Yana Daya gada cikin abin da yake kona zuciyar IRFAN sedai baka cika Gane fushin Saba domin bamai yawan magana da son Hayaniya bane
Aisha Yar Business ce sosai tana zuwa Dubai da England sometimes takanyi 1 week acan kasuwancin ta ya fiye Mata kula da miji
Kafin yayi having Sex da ita se tasha Pills batare da IRFAN ya saniba dalilin Daya hanata samun ciki kenan shi kuwa Mutum mai son Yara
Koda yaushe Yana cikin yin Azumi domin bazai iya kusantar Zina ba
Wasu Yan Mata guda Biyu na gani suna tafiya suna Hira ko wacce da tulu a hanun’ta da alama Rafi zasu marar Jikin ce ta kalli medan Jikin murya a rau nane tace Ilham ciwon Abba Yana damuwa koda yaushe Yana kwance Gashi bamu da kudin kaishi Asibiti kullum Anna cikin Kuka take wallahi na rasa yadda zanyi
Domin Sam bana son ganinta cikin damuwa hakan Yana taba zuciyata cikin kwantar da hankali Ilham tace AMATULLAH hakuri zamuyi Allah ya fimu sanin halin da muke ciki wata Rana sai LABARI kwantar Mata da hankali Ilham ta dinga yi har suka debo ruwan
Assalama tayi cikin Dan karamin gidan nasu Wanda da gani kasan talauci yayi musu yawa dakuna biyu ne se karamin kitchen da Bayan gida ginin kasa ne
Wata kyakkyawar mata ce ta amsa Mata da gani ita ce Mahaifiyar AMATULLAH domin kamar Daya sedai ita tadan manyan ta kallo daya zaka Mata ka Gane Buzuwa ce gashin kanta har baya tana da jiki kadan fara ce sol sedai rashin wadata yasa skin din’ta dishewa a k’alla zatayi shekara 40
Da sauri AMATULLAH ta karaso wajan Abba da yake kwance kamar wani mattatce da alamu Yana Shan wahala sosai rike hanun’shi AMATULLAH tayi tace Abba sannu kaji Allah zai baka lafiya gyada Mata Kai Kawai yayi
Minertβπ»
[23/07, 17:08] Marubuciyan Jini Daya: πππππ
*AKAN MIJINA*
πππππ
NOT EDITEDβ
Written by
Minertβπ»
Dedicated to
Every Body
Kuyi Hkr Na Rashin Jina Har Yanzu Bana Jin Dadi Neh Pls I Need Ur Pry Sister’sππ»
*ALLAHU*
IT’S ALL ABOUT LUV AND CARINGπ
Bismillahir Rahmanin Raheem
Pg 5&6
Tana rike da hanun’shi har wajan 30 minutes idon’ta cike tab da kwallah na tausayin Rayuwar su Musamman Abba wanda yakai shekara guda cif a kwance har yanzu Allah bai basu kudin kaishi Asibiti ba
AMATULLAH Yarinya ce kyakkyawa f’adar irin kyanda take dashi b’ata Lokaci ne tana da hankali da nutsuwa Duk da kasancewar ta karama Amma tunanin manya gareta shekarun’ta 15 tayi saukar Qur’ani sau biyu Allah ya hore mata ilimin Arabi tana jin Larabci sosai Fannin Boko ma gwana ce domin bata da wani buri d’aya wuce tayi karatun Likita tayiwa Abbanta magani
Tun Daga Js 3 ta Dena zuwa School saboda Rashin kudi
ASALIN SU
Musa shine Asalin sunan mahaifin ta Dan Asalin garin Yole fulani ne sosai tun Yana da shekara 15 iyayen sa suka mutu dangin Mahaifin shi suka cinye Dukiyar gadon wani Dan karamin gida Kawai suka bashi Musa akwai zuciyar neman na kan’shi baiyi kasa a gwiwa ba ya fara bin Babbar motan da suke zuwa Nigar a hankali ya fara samun taro da sisi kullum ya samu kudi boyewa yake
Shekarar su goma suna zuwa Nigar lokacin Yana da shekara 25 Allah ya hadashi da Ameenah har suka fara soyayya Ameenah Yarinya ce kyakkyawa ne domin akwai samarin da suke son’ta Amma fir taki ita lallai Musa t’ake so iyayan ta basu hanata ba
Domin a zamanin yanzu a Dena Auren dole suka ce Musa ya turo magabatan sa Bai boye musu komai game da tarihin Rayuwar Saba ALHAMDULILLAH basu nuna masa kyama ba domin da mai kudi da talaka duk Allah ne ya halicce su
Anyi bikin Musa Da Ameenah lafiya inda aka kawota garin Yole a kauyen su da ake Kira RUGAR ARDO har fenti yayiwa Dan karamin gidan
Suna zaman su lafiya da kaunar juna Gashi Allah Yana rufa musu Asiri Musa ya fara saida kayan koli dashi suke Managing Rayuwar su har Allah ya bawa Ameenah ciki sunyi murna sosai
Cikin’ta Yana wata Tara ta haifo santaleliyar yarta mai kama da ita sak sedai ta debo colourn mahaifin ta ranar suna akayi mata huduba da sunan Maman Musa ZAYNAB AMATULLAH
Haka sukaci gaba da rainon Amatullah kullum kara girma take Yarinyar akwai tsantsar kyau gata bul bul da ita gwanin sha’awa tun daga kanta Ameenah bata sake haihuwa ba
Back To Story
Ilham ita kadai ce kawar ta Duk fadin rugar su tare suka taso tun suna Yara
Sanadin ciwon Musa wata Rana ya fito daga bayan gida ya yanke jiki ya fadi tun daga lokacin Bai sake samun lafiya Wannan dalilin ne yasa Rayuwar tayi musu kunci Gashi Sam Yan uwan sa bata temaka musu da komi
ABUJA
Yana zaune a katafaran parlon shi aiki yake a laptop Dinshi kirar iPhone hankali sa kwance. Aisha ne tazo ta kwanta a jikin’shi cikin Kissa tace Honey I’m tired please muje muyi bacci tun dazu fa nake jiran ka Bai kalli inda take ba kamar bada shi take magana seda ya gama abin da yake yace ki shiga kitchen ki hadomin Coppe
Zare ido Aisha tayi tace Haba Honey wane Coppe Kuma da wannan Daren Gaskiya ni gaji tana magana ba wani respect girgiza Kai Kawai yayi ko uffan baice Mata ba yasa tattausan lisifas dinshi ya nufi site din Ammy
Yana fita harabar gidan Escort Dinshi suka biyo shi daga musu yayi alamun baida Bukata cike da tafiyar kasaita irin ta Sadaukan Maza ya isa site din Ammy Yana murda handling din Door din ya bude
Babu kowa a parlon Bedroom din’ta ya shiga tana zaune akan Praying mat tana lazimi sallama yayi cikin Husky Voice Dinshi wata kyakkyawar Farar dattijuwa ce ta amsa bisa alamu ita ne Mahaifiyar shi domin suna matukar kama a k’alla zatayi shekara 50
Hutu dajin Dadi ya samu wajan Zama a jikinta baza kayi tunanin takai wannan shekarun ba
Zama yayi a bakin Loyal Bed din ya shakwabe fuska kallon’shi tayi cike da kauna tace Habeebee lafiya kuwa lumshe oily eyes Dinshi yayi ya bude a kanta suna kallon juna Ammy Coppe
Yunwa nakeji shiru Ammy tayi kamar me tunani kafin ta shiga Kitchen da kanta ta hada masa Coppe a Dora masa akan karamin Tiray se turiri yake a hankali ya fara sha yaci Chips din kadan
Se wani shafa ciki yake Ala dole yayi over feeding girgiza Kai Ammy tayi
Kwanciya yayi a jikinta tana shafa lallausar suman kan’shi a Haka bacci mai Dadi yayi gaba dashi kura masa ido Ammy tayi cikin tausayi tace IRFAN Allah ya hadaka da Ballagazar Mata wacce bata son ya ake kula da miji ba Business din’ta ya fiye Mata komai
Allah ya baka wacce zata kula dakai domin nafi kowa sanin wanene Kai



Ba wai