WhatsApp Join WhatsApp Channel
Littafan Hausa Novels

Maleeyah Hausa Novel Complete

Written by mynovels

Maleeyah Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

If you should come across this post plss say a prayer for my late father, Allah ya sabunta masa rahama, ya gafarta masa da duk musulman da suka riga mu gidan gaskiya, Allah ya kyautata makwancinsu gaba daya, ya sa mutuwa hutu ce a garesu, Allah ya yafe masu kurakurrensu, Allah ya bamu guzurin tar da su* 🥺

**All thanks to Allah S.W.T for the chance and privilege to commence this new book, yanda muka fara lafiya Allah ya sa mu idar lafiya*

 

 

💥💥MALEEEYHA💥💥

 

_By Khaleesat Haiydar_✍️

 

1…..

Zaune take a gefen gado ta jinginar da kanta jikin furniture din gadon tana kallon windan dakin babu ko kiftawa alamar tayi nisa tunanin da take, yarinya ce budurwa da baza ta haura shekaru ashirin ba a duniya, aka bude kofar dakin ta juya a hankali tana kallon kofar, lokaci daya ta sauke ido bayan wata matashiyar da baza ta haura shekaru talatin da shidda ba ta shigo dakin, matar ta karaso har inda take ta zauna gefenta tana kallonta cikin kwantar da murya tace “Maleeyha ki tashi ki koma gida kin ga har karfe shidda yanxu kar mutanen gidan su kara kira” A hankali Maleeha tace “Ni a nan zan kwana” Matar ta girgiza mata kai tace “A’a Maleeyha, haka jiya kika sa nayi masu karya” Maleeha tayi shiru bata ce komai ba tana kallon farin bedsheet din dake shimfide saman gadon da suke zaune, Matar tace “Maleeyha” Maleeha ta daga manyan fararen idanuwanta tana kallonta, Matar tayi kasa da murya tace “Ki min alkawarin baza ki sake komawa inda kika je ba jiya Maleeha” Lokaci daya hawaye suka kawo idanuwan Maleeha, ta sa hannu ta rufe fuskarta tana kokarin ganin bata fashe da kuka ba, cikin dakewa muryar ta na rawa tace “Don Allah kiyi hakuri, i will do one last thing if it doesn’t work shikenan bazan sake ba i promise” Sosai jikin matar yayi sanyi ganin hawayen idon Maleeha wanda in dai ka gansu to she is really hurt kenan, a hankali matashiyar matar tace “In dai na isa in gaya maki ki ji to na ce kar ki sake komawa inda kika je jiya, dama ni ba ki gaya min ba kika tafi da bazan bar ki ba, babu wani mafita a yanxu sai dai mu yi addu’a, ke ba er kowa bace Maleeha ina tsoron kar ki je ki saka kanki a matsala” Maleeha tayi shiru don in dai ta bude baki maimakon tayi magana kuka zata fara yi, she felt her heart broke into pieces, a hankali ta zame hannunta daga fuskarta ta juya tana kallon wayarta dake vibrate, kasa daukar wayar tayi tana ta kallon screen din, Matar dake ta kallonta tace “Ki tashi ki tafi gida kin ga an fara kiran ki” Maleeha bata ce komai ba, cike da karfin hali ta mike ta dau dogon hijab dinta dake linke ta warwaresa ta saka, a hankali tace “Na tafi” Matar ta sauke wani boyayyen ajiyar zuciya tace “To Allah ya tsare, ki gaida mutanen gidan” Maleeha tace “Za su ji” Daga haka ta fita daga gidan tana tafiya a hankali, kamar ko da yaushe unguwan shiru sosai, zuwa yanxu kam ta saba da shirun wasu daga unguwannin Arewacin Najeriya, sai kaga kamar babu mutane a gidajen unlike inda aka haifeta ta taso, Absentmindedly take tafiya tana jan kafa zuwa bakin titi inda zata samu adaidaita sahu, tunani iri iri ne cunkushe a zuciyarta da yayi mugun karaya a wannan gaɓar da take ciki na rayuwa, all of a sudden taji duniyar tayi mata zafi a ɗan kankanin lokaci, wasu hawaye taji sun kawo idonta, da sauri ta goge da bayan hannunta sanin kuka ba mafita bane, ta zo wuce wani tinted black car da aka yi parking a layin kawai lokaci daya taga an bude back seat din motar, bata ankara ba sai gani tayi an fincikota da karfi ana ƙoƙarin jawota cikin motar, bata gama recover daga wannan shock din ba aka bude driver seat wani baƙin mutumi ya sauko da sauri ya turata cikin motar ta karfi sannan ya kulle motar ya koma driver seat ya ja motar yayi zoom off daga layin kamar zai tashi sama, ko sararin ihu Maleeha bata samu ba don ƙaton mutumin dake back seat ya damki bakinta da hancinta ya matse su da karamin towel din hannunsa har tana jin kamar numfashinta zai dauke, kokuwa ta fara yi da shi amma yafi karfinta, cikin kankanin lokaci ta fara loosing consciousness.

*Previously….*💭

✍️
“Tunda ke kince muguwa ce azzaluma mara imani da tausayi, duk hanyar da za ki bi ki cuceni ki saka ni asara kin sani, to wallahi idan zuciya ta debe ni idan ban kore ki a gidan nan ba shegiya nake, in kuma shegiyar uwarki ce ke wahalar nema min kudi da zaki dinga min almubazzaranci da kayan sana’ata sai in ji, Wannan tumatirin da kika walakanta min sai ya isheki cin abinci na sati daya a gidan nan” Cewar wata mata da bazata haura shekaru hamsin da biyar ba kenan tana huci, Yarinyar da take ma fada dai bata kalleta ba kai kace ba da ita take ba don sai ɓare tulin maggin dake gabanta take tana ajiyewa a wani roba, a fusace matar ta figi kwanon stainless dake gefenta ta jefa ma yarinyar tare da kunduma mata muguwar ashariya tana cewa “Ba da ke nake magana ba don kaza kazan ki kika yi min shiru ga tsinanniya na magana ko?” Da sauri yarinyar ta kauce ma kwanon sannan ta mike tsaye bata dai ce komai ba tana komawa baya tana kallon matar idonta babu alamar nadama ko tashin hankali, dai dai nan aka kwankwasa kofar net din dakin, matar ta kalli kofar har sannan fuskarta a murtuke da harshen yarbanci tace “Tani ẹ? (Ma’ana wanene)” muryar wata makociyarsu er Edo taji da turanci tana cewa “I have been waiting for you to come back since Iya Habu, come out and see for your eyes, come out and see ooo” Tunda yarinyar taji muryar neighbor dinsu da suke ce ma Momy Sabrina gabanta ya fadi, a hankali ta koma ta rakube jikin bango tana zare ido, Iya Habu ta mike ta nufi net din dakin ta bude tana kallon Momy Sabrina dake rike da hannun er ta Sabrina da bazata wuce shekaru sha biyar ba, Iya Habu ta daure fuska tace “Ehen? Wetin happen?” Cikin bacin rai Momy Sabrina ta fara magana da harshen turanci tana cewa “Kin ga abinda Mary-Ann tayi ma yarinya ta har sai da muka je pharmacy daxu ko? to bazan yarda ba dama jira nake ki dawo gidan nan….” Iya Habu tayi ta kallon Sabrina da aka saka ma plaster a goshinta, sai kuma ta juya ta kalli yarinyar da ta makale da bango tun zuwan su Momy Sabrina, yarinyar ta sauke manyan idanuwanta tace “She’s been entering my trap since last week, ni kuma na mata duka daxu” cikin harshen turanci a mugun fusace Momy Sabrina ke cewa “Yanda kika zubar ma yarinyata jini kema sai na zubar maki da jini, bazan taɓa yarda ba, idan ba haka ba kuma mu tafi police station kawai” Tana fadin haka ta bankado net din zata shigo dakin, Iya Habu ta hankadata waje da karfi tace “You dey mad Momy Sabrina, I say u dey mad, na my pikin you wan beat for my front? (‘ya ta zaki doka a gabana? waye bai san yanda Sabrina ke da tsokana ba a yard din nan?)” Nan suka hau zage zagen juna har ana neman dambe, Iya Habu ta fixgo gajeran wandonta dake kan katifar dakin ta saka tana kunduma ma Momy Sabrina zagi, kan kace me kowa ya fito daga dakinsa kuma babu wanda yace su ci kansu duk aka tsaya ana kallonsu, yarinyar dai har sannan tana rakube inda take tsaye a dakin ita ma tana kallon komai, sai ga wata makociyarsu inyamura da ta tashi daga gidan ko sati biyu ba ayi ba ta shigo passage din gidan, da kyar inyamurar ta raba fadan, ta ja Iya Habu suka dawo cikin daki ta kulle net din da Hausar ta mara daɗi tana cewa “Haba Iya Habu, habaaa, meye zaki kula Momy Sabrina da kowa yasan mahaukaciya ce a yard din nan, ogogoro fa take sha, why you go answer her?” Iya Habu na huci tace “Wallahi Momy Chinaza na fi Momy Sabrina hauka, nima ai na taɓa shan burkutu a da, ba ta ce zata kai ni police station ba ina jira ta kai ni, ina zaman zamana ta min knocking wai Mary-Ann ta fasa ma er ta kai, to waye bai san er ta Sabrina da neman tsokana ba a gidan nan? Duk unguwan nan an san Sabrina da tsokana, Yaushe da yaushe Maleeha ke zaman gidan nan da har zata biye wata Sabrina in dai ba Sabrinar bace ta tsokaneta? Ni nasan Maleeha bata dukan kowa sai in an tsokaneta” Momy Chinaza ta kalli Maleeha dake makale da bango har sannan tace “Mary-Ann me ya hadaki da Sabrina?” Iya Habu ta figi wani kwano a kusa da ita ta jefa ma Maleeha da karfi tace “Shegiya fita ki ban waje er iska kawai, idan baki dauko min magana ba baki ji dadi ba, kullum ni kenan fada akan ki, ko kwana biyar ba ayi ba da kika kama Goodness kika mata duka har sai da kika ji mata ciwo kika bar ni da dambe da uwarta, to wallahi sai dai ki kashe uwarki ba ni ba, fita nace ki ban waje kar in maki illa a dakin nan, ni babu abinda na hada ke” Maleeha ta durkusa ta kinkimi maggin da take barewa ta fita daga dakin, Momy Chinanza ta bi ta da kallo tace “Meye ne yasa baki jin magana ne Mary-Ann?” Iya Habu na huci tace “Ki kyaleni da ita ai dama kwana biyu ban mata dukan tsiya ba, to da kyar yau idan ban taɓa lafiyarta ba wannan maganar da ta dauko min, ko kuma kawai in koreta taje duk inda ma zata in huta, kullum ni kenan fada da mutane a unguwan nan akan Maleeha? Which kind wahala be this” Momy Chinaza tace “Amma ai tana temako naki ta sayar da abinci a kasuwa, ta siyar da na safe da na dare” Iya Habu tace “Abincin da take ba ƙattin banza yan okada da masu barrow bashi tana dora min gbese a kai? ai muguwa ce yarinyar nan kamar uwarta, ni ban ma taɓa ganin yarinya karama da ƙeta irinta ba, jiya fa sauran miyan da muka rage daga kasuwa ta zubar min da gangan tace ya bare, ai ko nayi mata ɗan banzan duka na kulle kofata ta kwana a passage, ko shekaranjiya a passage din ta kwana cikin sauro, da zan lissafo maki mutanen da ta ba abinci bashi a kasuwa suka ki biyana za ki sha mamaki Momy Chinaza, muguwa ce yarinyar nan kina ganinta fa, tafi uwarta mugun hali, kuma bazata taɓa maki laifi ta baki hakuri ba sai dai ta zuba maki ido kamar mujiya tana kallon ki, in ma dukanta za kiyi ki doketa, tana bani wahala wallahi” Momy Chinaza tace “To ke kina siyar da abincin ki da kanki mana a kasuwa, ita kuma ki dora mata talla ta dinga bin street by street, naga ai har da kubewa da dawa-dawa da busasshen kayan miya kina siyarwa, ki dora mata tallansu ta dinga bin street by street kawai tana hawking” Iya Habu ta rike haɓa tace “Ta je a tsokaneta ta min watsi da farantin kayan miya ta hau dambe? tabdijam asara kawai zan ja ma kaina” Momy Chinaza tace “Ba karamin aikinta bane kuwa” Iya Habu tayi kasa da murya tace “Kin san bana boye maki komai Momy Chinaza, to wallahi na yanke shawara ne zan kai ta gidan gala satin nan da za mu shiga in sha Allahu, kin ganta kyakkyawa fara doguwa ga hanci da idanuwa, kuma ga ta er yarinya she is just 15 years old, tuni zata samu karɓuwa a wajen galan nan ta zama star, gashi tana da wayewa and she is very very wise” Momy Chinaza ta gwalo ido tace “Ta iya rawa ne?” Iya Habu tace “Tabdi, sai kace ba a Lagos din nan aka haife ta ba ke kuma Momy Chinaza, akwai wata yarinya Lawiza da na san uwarta a Igando yanxu haka tana can gidan gala sai tayi wata biyu ma bata dawo gida ba, sai kin ga kudin da uwar tace tana kawo mata, wallahi uwar ta siya masu fili a arewa har guda biyu da kudin gala” Momy Chinaza tace “To ke kin san gidan Galan ne?” Iya Habu tace “Haba ga wani can a Alaba rago, akwai ma a Jakande, kai har wajajen Seme Border ma akwai, amma na Alaba ragon dai zan kai ta don ina da kwastomomi a can tunda na kan je in saro shinkafa, sai in ce su min hanya in mikata gidan Galan” Momy Chinaza ta gyara zama ita ma tayi kasa da murya tace “Ni ma kinsan bana hiding maki komai ko my friend, akwai wani Chief a can garin mu Umuahia, duk sanda zai shigo Lagos sai ya sa in nema masa very young girl da zan kai masa hotel, baya son yarinya da ta kai 20 years ma, little girls nake kai masa da basu wuce 16 to 19 years ba, idan na kai masa kuma har dubu dari da hamsin yana ba yarinya a dare daya, ni kuma ya ban dubu dari kyauta, baki ga shi yasa na barku a one room apartment din gidan nan na kama self contain ba, amma nayi maku karya nace Baban Chinaza ne ya siyar da farm dinsa a village muka kama hayar self-contain? To a cikin wata uku na tara kudin Self-contain din nan da kika gani, every month Chief yana zuwa sau uku Lagos” Iya Habu ta saki baki tana ta kallon Momy Chinaza tunani iri iri na yawo kanta, a hankali tace “Dubu dari da hamsin fa kika ce a dare daya Momy Chinaza? Just like that?” Momy Chinaza tayi wani murmushi tana kada kai tace “Zan maki karya ne kawata? I go lie for you? To yanxu haka on Saturday zai zo Lagos har na nemo yarinyar da zan kai masa hotel da zai yi lodging a can Lagos Island, wata yoruba girl zan kai masa, i no dey stress my self to sell vegetables for Iyana Iba yanxu faa” Iya Habu ta marairaice tace “Haba Momy Chinaza amma kin san ina da yarinya er karama irin wanda yake so kika ki gaya min? ita fa ko 16 years din ma bata kai ba, kinga kuwa dai dai kenan” Momy Chinaza ta bude ido tace “To ai naga ku Hausawa ba ku yin irin wannan harka, na im let make i no tell you oo” Iya Habu ta wani kalleta tace “Wa yace maki? To bari in gaya maki wasu suna yi a boye, idan na fara lissafa maki yaran Hausawa nawa ke yin wannan harka a boye cikin unguwan nan sai kin bude baki, ni dai kawai ki min hanya kawata, kuma tsakanina dake ne wannan nasan baza ki je ki fada a wani waje ba, ni idan an bada dubu dari da hamsin din ma zan cire maki dubu ashirin a ciki wallahi” Momy Chinaza tace “Ina suspecting ma Mary-Ann virgin ce ai ko?” Iya Habu ta zaro ido tace “To da fa? Maleeha bata san komai ba wallahi, na small pikin she be nahh” Momy Chinaza tana murmushi tace “To ai farin ciki zai sa Chief ya bata ko dubu dari biyar ne akan ita virgin ce, kin san yana da kudi sosai fa, he is very very rich, kuma yayi ta cewa shi virgin girl yake so amma yara ƙanana yanxu su ma duk sun lalace suna iskanci, yarinya karama amma ba virgin ba” Iya Habu ta girgiza kai tana murmushi tace “Ni dai yarinyata Maleeha virgin ce wallahi bata san komai ba, bar ta da rashin jin ta da maganar da take dauko min tana dukan yaran mutane idan suka tsokaneta, amma she no know anything, yanxu yaushe kika ce Chief din zai shigo Lagos?”

07087865788✍🏻
[8/26, 6:52 PM] +234 803 216 9283: 💥💥 MALEEEYHA 💥💥

 

Daudar Gorah Hausa Novel Complete

 

By Khaleesat Haiydar ✍🏻

 

 

 

2…..

Iya Habu ta kara yin ƙasa da murya tana kallon Momy Chinaza tace “Kuma inji dai ba unguwan nan yake sauka ba dai ko?” Momy Chinaza tace “Haba, me zai yi a wannan local unguwan? Ai can Lagos Island yake biyan hotel room ya sauka, business trip ne yake kawo sa Lagos fa, amma sai ya huta da yarinya kafin ya koma” Iya Habu tayi wani murmushi zata yi magana aka bangaje kofar net din dakin, duk suka juya da sauri, Habu ne ya shigo dakin yana tangal tangal ya tafi ya fada kan er katifar dake dakin, Iya Habu ta rike haɓa tana ta kallonsa cike da takaici, rabonta da shi yau kwana hudu bata san inda yaje ba, gashi yanxu ya shigo mata a buge, tana magana zai hayayyako mata kamar zai mata duka shi yasa kawai ta ja bakinta tayi shiru, ta kalli Momy Chinaza tana taɓe baki, tuni karamin dakin ya gauraye da warin taɓar wiwi, tashi Iya Habu tayi ta tafi ta bude windan dakin, Momy Chinaza ta mike tana sosa uban gashin dokin dake jibge kanta da hannu biyu tace “To Iya Habu bari in je gida kila baban Chinaza ya dawo daga kasuwa, make i go turn Eba for am, Ina da sauran soup din jiya” Iya Habu na murmushi tace “To shikenan Momy Chinaza gobe muna gama siyar da abinci da safe zan zo gidanki sai mu karasa maganar mu, ko zaki kai Ugwu da water leaf kasuwa?” Momy Chinaza tace “A’a gobe sai da yamma zan je kasuwa, kin san yanxu na dena stress din kaina da yawa, i get where money dey enter from….” Iya Habu ta kyalkyale da dariya ta bata hannu suka tafa sannan tace “To sai na shigo dai goben, a gaida min su Chinaza da Ngozi” Momy Chinaza tace “Za su ji my friend” Daga haka ta fita daga dakin, Iya Habu ta koma ta zauna tana ɗan murmushi kudin da Momy Chinaza ta ambata na mata yawo a kai, har dubu dari da hamsin fa?? Tabdi, ashe ta kusa dena wahalan siyar da abinci, mikewa tayi ta fita daga dakin, ta tafi bayan windan ta inda take girka abincin siyarwan ta, bude ido tayi ganin iccen baya ci gashi lokaci ya wuce, ta fara waige waigen inda zata ga Maleeha, amma bata ga alamarta ba, a fusace ta zaga zuwa gaban compound din gidan nasu da ake kira da Face me i slap you, wanda ke dauke da dakuna kusan talatin dake facing juna kuma ɗakunan ba wasu masu girma ba, sai public toilet hudu for the whole compound. Tsaye ta ga Maleeha bakin rijiya tana dibar ruwa ta cika roban fenti manya hudu, ga few compound people zaune frontage din gidan suna hira, rai bace Iya Habu tace “Tun daxu uban me kike baki debo ruwan ba sai yanxu?” Maleeha ta daga kai ta kalleta da hausanta da bai gama nuna a bakinta ba tace “Fetching pail (Guga) ya fada cikin rijiya, shi ne na nemo hook in cire, kuma ina yin aiki tun daxu” Iya Habu ta cire takalmin kafarta ta jefa mata tare da kunduma mata zagi tace “Kina yin dambe da Sabrina dai, er iska kawai” Maleeha tayi shiru bata ce komai ba tana jan fetching pail din da ta zura cikin rijiyar, Iya Habu tayi wani kwafa tace “Zan yi maganin ki nan ba da dadewa ba wallahi, sai kin san kin dauko min magana har ana cewa za a kai ni police station” Daga haka ta juya ta bar wajen ko kallon tenant din gidan dake zaune suna bin ta da ido bata yi ba, Momy Solomon tayi kasa da murya tana kallon Iya Adaku tana mata magana da yarbanci, Maleeha ta dau bucket din ruwan ta daura a kai ta bi bayan Iya Habu, Momy David ta kyabe baki tace “Tufiakwa….” Karfe hudu da yan mintuna na yammacin ranan Iya Habu ta iso inda suke sayar da abincinsu a wani busy semi market, Mai barrow dake dauke da kulolin abincin ya dinga saukar mata da su kasa, Maleeha dake wajen tun karfe uku da rabi har ta share ko ina, kawai jiran isowar Iya Habu take, ta mike daga inda take zaune ta tafi zata sauke kananun cooler da zata iya dauka a cikin barrow, Iya Habu ta dinga gaisawa da Hausawa en cirani dake cike a wajen da masu kabu kabun machine, cikin yan mintuna suka gama jera duk abincin siyarwan kan teburi da taimakon wasu gardawan maza, Iya Habu na adjusting babban Umbrellan dake masu rumfa tace “To don uwarki kin tafi kin amso min kudadena gun Kolo ko kuma ke da shi kuna da gado na ne?” Maleeha ta girgiza kai tace “I went to Bala’s shop but I did not meet him there” Iya Habu ta kankance ido tace “Heheee, za ma kiyi meet dinsa a shop din ne don uwarki tunda ban aike ki basa bashi ba, duk inda zaki samo min dubu uku na a yau ba matsalata bace in kuma ba haka ba kar ki dawo min gida wallahi, ya wuce ace ya gudu garinsu tunda ance yan sanda sun kwace masa machine din da yake kabu kabu sai zaman shagunan mutane kawai yake babu aikin yi, wallahi duk inda zaki je ki samo wannan kudin ki je ba matsalata bace, bazan dinga ciyar dake ba kuma kina ja min asara” Ita dai Maleeha tayi shiru bata ce komai ba tana ta kallonta, Iya Habu ta fara sallaman masu zuwa siyan abinci don har sun fara taruwa a wajen, tafi minti talatin tana ta siyar ma jama’an da suka cika gaban teburinta abinci Maleeha na taya ta, bayan wani lokaci Iya Habu ta bar ma Maleeha siyar da abincin ta dau er jakarta tace “Zan tafi amso danyen shinkafa yanxu, saura ki min ba dai dai ba kafin in dawo, ko kuma don mugunta ki dinga cika masu abincin tunda uwar ki ce ta ban jari, ni ai nasan nawa ne adadin abincin da muka kawo kasuwa yau, ko biyar ne babu a kudina na sani, kuma sai kin biya ni” Tana kai wa nan ta tafi ta tsayar da machine a bakin titi ta hau don Allah Allah take ta je gidan Momy Chinaza taji yanda ake ciki, sai da Maleeha ta tabbatar ta sallami jama’an da suka zo siyan abinci sannan ta dau robobin zuba abinci ta fara zuba ma mutanen da kullum ka’ida ne sai sun siyi tuwo a wajensu kuma ita take mika masu tuwon a shagunansu, tana ta sauri kafin customers su kara taruwa, ta daga kai ganin wanda yake tahowa towards direction din teburin abincin nasu, wani matashi ne da bazai wuce 28 years old ba, ya karaso gaban teburin ya sauke hular rigar sanyin jikinsa yace “Kolo ya baki kudin nan kafin ya tafi?” Ta ɗan bude ido tana kallonsa with fear written all over her face jin abinda ya ce, lokaci daya ta bata fuska tace “Ya tafi arewa ne?” Matashin me suna Usman yace “Ya tafi garin su, bai baki kudin ba?” A hankali ta girgiza masa kai tace “No, he gave me nothing” yace “Nawa ne kudin?” Tace “3000” Usman yace “Ohk” Maleeha dai tayi shiru bata ce komai ba, Allah kadai yasan abinda Iya Habu zata mata akan 3k din nan, ta ci gaba da zuba tuwon da take a roba tana tura baki, ya ciro dubu takwas a aljihunsa, ya mika mata yace “Ki cire kudin kolo, sai ki sa min abincin 2000, ke kuma ki ci na 3000” Ba tare da ta kallesa ba tana rufe abincin da ta zuba a roba da ledoji tace “I ate at home” Daga haka ta mika hannu ta amshi kudaden da yake mika mata ta cire dubu uku ta mayar masa tana kallonsa, yace “Ki ci abinci na ce” Tace “I never told you I have not eaten” Ya mika hannu ya amshi kudin da take mayar masa ya saka a aljihu, Benchin dake wajen ya tafi ya zauna, ita kuma ta dau abincin da ta zuzzuba zata kai ma mutane a shagunan su, An dau kusan minti goma kafin Maleeha ta dawo wajen siyar da abincin nasu, ta tarar da masu siyan abinci suna ta jiran ta gaban teburin abincin, sai da ta fara sallamansu gaba daya sannan ta juya ta kalli Usman tace “What are you buying?” Yace “Shinkafa da miya” Ta dau takeaway ta zuba masa abinci wanda zai kai na dubu uku ga uban nama da ta ɗora masa a kai, sannan ta rufe takeaway din ta saka masa a leda ta sa masa cokalin roba ta tafi ta mika masa, ya amshi abincin ya bude yana kallo yace “Na dubu biyu nace, ko baki gane bane? Kuma ban ce ki sa nama ba” Tace “Eh ni na baka a haka” Yace “Kina so ki samu matsala wajen Iya Habu” A takaice babu yabo babu fallasa tace “Just be going to where you are going” Daga haka ta koma ta ci gaba da abinda take, zuwan wani bahaushe da ake kira Jagaba da abokinsa Rabilu wajen yasa Usman ya mike yayi tafiyarsa don Jagaba mutumin Iya Habu ne sosai, kowa a kasuwan ya sani, Maleeha na kallon Jagaba tace “Me za a baka?” Sai da Jagaba yaga Usman ya hau machine dinsa ya wuce sannan yace “Ke, yi min hadin dubu biyu da dari biyar amma ba tuwo ba don yau bana jin cin tuwo, Rabilu kuma a basa tuwon dubu daya da dari biyar” Ta mika hannu ba tare da ta kallesa ba alamar ya bada kudi, Ya wani kalleta yayi gefe da bakinsa ya karkace yace “Ke kar ki kawo min rashin kunya mana, ya haka? guduwa zan yi da kudin halan?” Bata ce komai ba ta juya ta koma kan kujeran da take zaune ta zauna har sannan taki kallon inda yake ta dau literature book dinta me suna ‘Without a silver spoon’ da ta taho da shi daga gida ta bude tana duba page din da ta tsaya, ya mata wani tsawa a fusace yana zare ido yace “Kee ni zaki bari a tsaye ki tafi ki zauna? Ni zaki kawo ma raini? Kaiii abincin Iya Habun ne baza ki bani bashi ba don baabarki, ko baki san yanda mu ke da Iya Habu bane” A takaice Maleeha tace “You have to wait for her to come back and sell for you on Credit” Tana magana ne ba tare da ta kalli inda yake tsaye ba, Wani zagi ya kunduma mata yace “Wallahi sai na ɓaɓɓallaki idan baki tashi kin zuba min abinci ba don baabarki” Sai a sannan ta wani kallesa tace “Lallai… Tunda ga sugar cane ko? to bazan zuba ba don Iya Habu ta hanani siyar da abinci on credit” A fusace ya nufeta Rabilu yayi saurin rikosa yace “Ka rabu da ita kawai Jagaba, dama ai kowa yasan bata da kunya a kasuwar nan, har ita ma Iya Habun ta sani, ka bari kawai Iya Habun ta dawo tayi maganinta, yanxun nan kana taɓa ta sai ayi maka caa, kyaleta kawai da yawarta mu tafi….” Maleeha ta ci gaba da karatun literature dinta kamar bata san da su a wajen ba, Jagaba sai zagi yake zunduma mata yana cewa zai yi maganin rashin kunyan ta a kasuwan nan, gaba daya attention din mutane ya komo kansu, Rabilu ya ja Jagaba suka bar wajen yana basa hakuri kar a basu rashin gaskiya, sai a sannan Maleeha ta bi su da wani shegen kallo ta ja tsaki, mikewa tayi ta dau kwanon roba ta debi abincin da zata ci, kadan ta zuba don ba wani yunwa take ji ba tunda suna gama girki a can gida wajen karfe biyu da taga Iya Habu na ta shirga baccin gajiya shine ta debi abincin ta cika cikinta kan ta taho kasuwa ba tare da Iya Habun ta sani ba, nama yanka uku ta dora kan abincin da ta zuba yanxu, sannan ta koma can lungu ta juya baya ta fara cin abincin da hanzari kafin Iya Habu ta dawo. Kafin karfe bakwai da rabi na dare Maleeha ta gama siyar da abincin Iya Habu tass, ta share wajen teburin nasu bayan duk ta harhada manyan kulolin abincin waje daya sannan ta fara wanke robobin siyar da abincin, duk wannan aikin da take jakar kudin Iya Habu na makale jikinta sanin idan tayi sakwa sakwa da shi wani sai ya sure bata sani ba, ta gama wanke wanken kenan sai ga Iya Habu ta dawo da buhun shinkafa da wake rabin buhu sai gero, Maleeha ta mike zata amshi ledan hannunta, Iya Habu dake duba ko abincin siyarwanta ya kare ta warce ledan ta gwaleta tace “Kiyi min uwar me da shi, dalla ni tafi ki nemo min Safiyanu me Barrow ya zo ya kai min gero da shinkafar nan gida, yanxu kina nufin miyan ata (tumatir) duk ya kare?” Maleeha tayi shiru tana kallonta da manyan idanuwanta, Iya Habu tace “Dama nasan ai sai kin min mugunta kan in dawo, da ni ce na siyar da abincin nan ta yaya ma miyar zai kare? Ai dole sai na maida saura gida” Maleeha ta juya bata dai ce komai ba zata je kiran Safiyanu, Inda masu Wheel barrow ke zama a kasuwar ta tafi don tasan yana can, kamar ko da yaushe babu wanda ta gaisar cikin Hausawa yan ciranin dake zaune wajen suna bin ta da kallo gaba dayan su, tana kallon Safiyanu a takaice ta gaya masa sakon Iya Habu, Tanimu ya yar da guntun taɓar hannunsa yace “Wato ke riƙaƙƙiyar mara kunya kin fi karfin ki gaida mutane ko? Duk wata yarinyar mace dake siyar da abinci a wajen nan babu me mana rashin kunya da fitsara da ji da kai sai ke, haka daxu Jagaba yace kin masa rashin mutunci akan yace ki zuba masa abinci bashi, to me kike takama da shi da kike ma mutane wannan iskancin haka? Mansura ma da ta fi ki kyau da diri a kasuwar nan tana gaida mu ayi wasa ayi dariya har ta zauna cikinmu ayi hira, amma ke kina kwailar ki sai rashin kunya da rainin wayo….” Ko kallonsa Maleehaa bata yi ba kamar ba da ita yake ba ta juya ta bar wajen, Kallamu yace “Ina ga takamar ta Usman Zaki…” Habibu yace “Ko Usman Damusa ne ba Zaki ba, shi Usman din uwar me yake takama da shi a garin Legas” Kallamu yace “Karfi mana, takamar sa karfi, ko ka taɓa ganin wanda ya kada sa a gidan dambe?”

+2348138491099✍️
[8/27, 1:34 PM] +234 803 216 9283: 💥💥 MALEEEYHA 💥💥

 

 

By Khaleesat Haiydar ✍🏻

 

 

3…….

Maleeha ko juyowa bata yi ba duk da tana jin abubuwan da suke cewa ta ci gaba da tafiya abun ta, Kallamu yace “Ai ba a cin Usman wasa duk karfin mutum, akwai wasa tsakaninsa da Garbati ma sati me zuwa, kowa jiran wannan rana yake, to ina ga da shi take takama take ma mutane iskanci tunda yana kulata, kuma duk mun san asali baya kula yan matan kasuwan nan, bai ma siyan abincinsu, sai na Iya Habu, gashi dai fa ba shiri suke da Iya Habun ba” Habibu yace “An fa ce asiri Usman yake ba haka nan kawai yake nasara a ko wani wasa ba, fatana Garbatin Kano ya ci wasar nan don shi ma ai karfaffa ne kuma duk wasannin da yayi a Kano shi ke nasara, Allah dai ya basa sa’a kan Usman ya karya alkadarinsa” Safiyanu ya mike daga kan Wheel barrow dinsa da yake zaune yace “Ku dai bi a hankali don babu abinda Usman bazai yi kan wannan yarinyar ba, kwanaki a kanta haka ya ma Jamilu duka ya fitar masa da jini daga ya zage ta taki basa bashin abinci” Maleeha na komawa inda suke siyar da abinci taga Jagaba tsaye da Iya Habu yana gaya mata abinda tayi masa cikin bacin rai, Iya Habu ta juya tana kallonta tayi mitsi mitsi da ido tace “Don kaza kazan ki dama rashin kunya na ce ki dinga yi ma jama’a a kasuwar nan idan bana nan? Korar min customers dina za ki yi? Baki san wanene Jagaba a wajena ba ne da har zaki hanasa abinci?” Maleeha tace “But you said I shouldn’t sell food on credit…” Iya Habu ta suri tsintsiya ta jefa mata tace “Shi Jagaban ne baki sani ba a kasuwar nan da baza ki basa credit ba?” Maleeha tayi shiru bata ce komai ba ta tafi tana harhada abubuwan da za su tafi gida da shi, rai bace Jagaba yace “Wani tashen rashin kunya take jin yi ma mutane Iya Habu, kwata kwata bata da mutunci bata da tarbiyya yarinyar nan, ta raina kowa” Iya Habu tace “Duk gun shegiyar uwarta ta gado wannan, don shi dai ubanta babu ruwansa wallahi, ko yatsa ka zura masa a baki bazai ciza ba, ai ku kun sani ba sai na tsaya ɓata bakina ba, baƙin halin uwarta sak ta kwaso….” Ta gefen ido Maleeha ta wani harari Jagaba tana ci gaba da harhada kayan da take, Jagaba yace “Duk wajen nan fa korafi ake a kanta, idan mutum ya zo zai amshi abinci zuwa dai kafin ku tashi da daddare ya bada kudinsa sai ta hanasa kememe, kadan ya rage ta kashe maki kasuwa bari in gaya maki gaskiya Iya Habu babu boye boye” Iya Habu tace “Ka kyaleni da ita mu koma gida zata gaya min abinda yasa ta walakanta ka yau, kuma wai baka gaura mata mari ba don girman Allah Jagaba” Jagaba yace “Wallahi ba don Rabilu ba dukan da zan mata daxu sai Allah” Iya Habu tace “Da kuwa ka kyauta min tunda tace ita er iska ce mara mutunci” Jagaba yayi kwafa ya kama ma Safiyanu buhun shinkafa suka dora saman Barrow, Iya Habu tayi sallama da Jagaba ta tsayar da okada biyu da zai maida su gida, ta hau daya da wasu Kuloli tayi gaba abun ta, Maleeha na hararan Jagaba ta hau daya da sauran kayan mai machine din ya bi bayan su Iya Habu. Maleeha na zaune one room apartment dinsu da tuwon da Iya Habu ta zuba mata cikin wanda take ragewa a gida kafin ta kai na siyarwanta kasuwa, tura tuwon kawai take da kyar don a koshe take, ana kiran Magrib sai da ta kara cin shinkafa a kasuwa wajen siyar da abinci kafin Iya Habu ta dawo don tasan suna dawowa tuwo zata hadata da shi, ita kuma ta tsani cin tuwo, Iya Habu ta gama kirga kudaden cinikinta da take taga yau ribar kusan dubu sha tara suka samu, har tayi mamaki don ribarsu baya wuce dubu sha biyar ko sha shidda, ta maida kudin cikin karamin purse ta sokesa a mara kar Habu ya tona mata asiri, sai kuma tayi kasa da murya tana kallon Maleeha tace “Ke wai daxu da rana me ya hada Momy David da mijinta ne a gidan nan?” Maleeha bata daga kai ba tana tura tuwon gabanta tace “Dambe ne suka yi” Iya Habu ta kyalkyale da dariya tana gyara zama tace “Ki ce kallo ya bar ni ina nan ina ta shirga baccin gajiya, me yasa baki zo kin tasheni ba, to sai aka yi yaya?” Maleeha tace “Ya yaga mata kaya, yaji mata ciwo a kai, shi ne aka kai ta pharmacy da sauri” Iya Habu ta kara tuntsirewa da dariya tace “Dama gashi haka take yawo babu pant a gidan nan, ba dai bata da aiki sai gulman mutane a Yard din nan ba kadan ta gani, shi yasa bana shiga harkar kowa don a rayuwata bana son mutane munafukai magulmata, ai kwanan nan Allah zai bani kudi mu tashi gidan nan ko er self-contain ne irin na su Momy Chinaza mu koma abun mu, cikin kwanan nan za mu tashi daga gidan nan” Maleeha dai bata ce komai ba, Iya Habu ta hade rai tace “Kin ce kin amso min bashin kudina wajen Kolo, ina kudin yake?” Maleeha tace “Na hada kudin ai a jaka” Iya Habu ta ɗan yi shiru, wato shi yasa taga kudin ya kama dubu sha tara, duk da haka sai tace “Karya kike yi wallahi, Jagaba ya gaya min tun jiya Kolo ya bar garin nan da asuba” Maleeha tace “Brother Usman paid the money, you can ask him tomorrow” Iya Habu tace “To dai gwara da ɗan wahalan ya biya don wallahi ba yarda zan yi ba, da duk inda zaki samo min kudina sai kin samo, shi kuma Jagaba kin min dai dai da kika hanasa abinci, ai ba ni na kawo sa Lagos ba da zan dinga basa bashin abinci, sau biyu yana ci min abinci bashi baya biyana ɗan iska kamar ya ci abincin kanwar uwarsa, don haka kar ki kuskura ki ce zaki basa bashi idan ba haka ba ke zaki biya ni kudina babu ruwana wallahi” Maleeha ta ɗaga kai tana ta kallonta, Iya Habu tace “In kuma yace zai taɓa ki ki tara masa mutane a wajen kiyi ta ihu kina birgima ki ce ya mare ki, ai ba abincin sadaka na ke kai masu kasuwar ba” Maleeha tace “But few moment back you said I should be giving him food on credit” Iya Habu ta galla mata harara tace “Ke baki san siyasa ba? Shi ya hada min jarin abincin da zan dinga basa bashi don uwarsa” Maleeha ta sauke kanta kasa, Iya Habu na kallonta da tuhuma tace “Wai ya naga kina gajaljala min tuwon ne, ko dai kin ci min abinci a kasuwa ne?” Da sauri Maleeha ta ɗaga kai tana zare ido tace “A’a ban ci komai ba, I am having stomach pain shi yasa na kasa ci” Iya Habu tace “A haka nan zaki tura sa don ban ga uban wa zaki bar ma ba, tuwon dari biyar kenan na baki….” Maleeha dai bata ce komai ba ta ci gaba da tura tuwon, Iya Habu ta ciro jakar da ta sakala a maranta ta ciro naira dari biyu ta jefa mata tace “Ya zan yi tunda Allah ya dora min, sai ki je chemist ki siya Gelusil, in ban fiddo kudin ba uban wa zai baki magani ko zaki mutu” Maleeha ta dauki kudin tace “Nagode” Sai kusan karfe sha daya na dare Safiyanu ya iso gidan da kayan abincin Iya Habu a barrow, Maleeha na zaune compound tana ta jiran isowarsa duk sauro sun cijeta ga wani bacci da take ji amma bata isa ta kwanta ba har sai Safiyanu ya iso da kayan abincin su daga kasuwa, bayan an shiga da kayan abincin daki ta kalli Iya Habu dake ta minshari ga Habu shi ma sai minsharin yake a dakin a er katifar dake ƙasa, ta kulle kofa tayi shimfida a lungun da take kwanciya a cikin dakin sannan ta kwanta ta takure waje daya, nan da nan bacci ya dauketa. Karfe uku da rabi na Asuba ana ruwa sosai Iya Habu ta tada Maleeha ta hanyar maka mata duka tace “Tashi ki fita, don iskanci kullum sai an tashe ki ke baki san lokacin tashin ki ba ki tashi don kanki, idan kika kwanta bacci kamar an ajiye gawa, tashi ki fitar min a daki” Maleeha ta mike da sauri tana murza idonta ta fita daga dakin, Iya Habu ta koma ta kwanta ta ci gaba da baccin ta, Maleeha na fita ta makale a passage din gidan don garin yayi sanyi sosai, haka nan dai daga karshe ta shiga ruwan da ake tsulawa ta wanke fuskarta sannan ta tafi karkashin rumfar da suke girki don aza wutan da za ta daura ruwan koko, bayan ta hura wutan ta daura ruwan ta dau babban roba ta tafi debo waken da zata wanke, duk ta jiƙe jagab da ruwan sama don a rijiya ta jawo ruwan da ta daura kan murhu, a duk karfe shidda da rabi na duniya suke fita kasuwa siyar da koko da kosai da dankalin Hausa, zuwa karfe goma sun gama siyarwa sannan su dawo gida a daura abincin da za su kai kasuwa da yamma, sam Maleeha bata da lokacin hutu don hatta asabar da lahadi sai sun yi abincin siyarwa har ta saba da wannan wahalan, karfe hudu da minti arba’in Maleeha ta taso Iya Habu dake ta bacci tace “Mama the water is boiling” Iya Habu ta tashi da sauri ta fita zata dama koko, zuwa sannan ruwan saman da ake ya ɗan tsagaita. Karfe tara na safe Iya Habu ta mike daga gaban randan kokonta da ya rage kadan a kasuwa ganin jama’a masu siyan koko da kosai da dankali sun ragu, tana kallon Maleeha dake juya kosan karshe dake cikin man gyada a kasko tace “Zan je unguwa yanxu, idan kin gama siyar da komai ki tattara ki tafi gida ki wanke min kayan miya a markada ki dora min kan murhu kafin in dawo, kuma ki tafasa min nama ki yanka min alaiyyahu, saura in dawo in ga ba dai dai ba ki ga ikon Allah” Maleeha tace “To” Iya Habu ta dau roba ta zuba koko ludayi uku ta mika mata tace “Ki debi dankali uku ki hada da kokon nan ki sha ai ya ishe ki” Maleeha ta amshi kokon tace “Nagode” Iya Habu ta dau jakarta ta tafi ta tsayar da Okada da zai kai ta gidan Momy Chinaza, Maleeha ta gama kwashe kosan ta kashe wutan murhun sannan ta dau plate ta debi kosai bakwai ta mayar mata da dankalinta uku cikin roba alamar bazata ci ba, ta bude randan kokon ta kara akan wanda ta dibar mata, ta debi wanda zai isheta sannan ta koma can gefe ta zauna ta fara cin abun ta, sai da ta gama sannan ta koma ta ci gaba da siyar da sauran koko da kosai da dankalin da suka rage, kafin karfe tara da minti arba’in ta gama siyar da komai ta fara wanke robobin koko da randar kokon, ɗaga kai tayi ta kalli Usman da zuwan sa wajen kenan, ya karaso ya zauna kan Benchi ya sauke hular rigar sanyin jikinsa yace “Ke kadai kika zo yau” Maleeha na ci gaba da aikinta ta girgiza masa kai tace “No” Bayan ta gama dauraye robobin ta tashi ta dauko wani roba me dauke da koko da ta rufe, sai wani leda daban me dauke da kosai cikin takarda ta tafi ta kai masa, yace “Bai kare ba” A kan Benchin ta ajiye masa bata ce komai ba ta tafi ta zauna a inda take zama tana jiran ya gama ta nemi Okada din da zai maidata gida, yace “Na nawa ne?” Tace “The way u use to buy” Sai da ya fara shan kokon sannan yace “Ke kin ci?” Tace “Eh” Sai kuma ta rungume hannunta ta daure fuska tace “I want you to warn Tanimu and his clique, idan suka kara shiga trap dina I will insult the hell out of them” Usman ya kalleta yayi shiru, sai kuma yace “Me yayi maki?” Ta kara daure fuska tace “He insulted me because i didn’t greet them, I have no business with them in this market why will i be greeting them? shi kuma Jagaba har da cewa zai karya ni because I refused to give him food on credit” Usman ya ci gaba da shan kokon hannunsa bai ce komai ba, bayan wani lokaci ya ajiye roban ya mike yace “Yaushe zaki tafi gida?” Tace “I am leaving now” Yace “Mu je in ajiye ki” Ta kalli inda yake ajiye machine dinsa, tashi tayi ta fara harhada kayan da zata tafi gida tare da su, ya ciro dubu biyu ya mika mata kudin kosai da koko da ya sha, ta karba ta saka cikin jaka, ya dau kayan da ta harhada ya nufi mashin dinsa ta bi bayansa. Iya Habu na zaune parlon Momy Chinaza bayan ta gama sauraron bayanin Momy Chinaza, tayi kasa da murya tace “To ni abinda nake son in fahimta Momy Chinaza wa zai kai ta Lagos Island din? Ko ni zan kai ta?” Momy Chinaza ta wani kalleta tace “I no understand…. Ina kika san Chief din zaki kai ta? Na me dey carry her go there now, ai ni nake kai girls din” Iya Habu ta gyada kai tace “Na true… to kamar karfe nawa zan shiryata in kawo ta gidan ki?” Momy Chinaza tace “Just bring her around 4pm, kafin mu je Island night go don reach, kin san da nisa daga nan” Iya Habu na murmushi tace “To Allah ya kai mu Momy Chinaza, wallahi naji dadin wannan hanyar arzikin da kika min my dear friend, May God bless you for me, ba kowa ne yake yi ma mutum hanyar arziki ba” Momy Chinaza tana murmushi ita ma tace “You are a friend indeed Iya Habu shi yasa kawancen mu ya dade ai, idan ma ta ba Chief cooperation nasan ko yaushe ita zai ce na dinga kai masa idan ya shigo Lagos, there was a time da yayi sticking to one Edo girl da na kai masa, sunan yarinyar Sandra, in gaya maki tayi saving enough money from chief ta koma Benin City tana University yanxu, the girl is just 18 years fa, har mota tana da shi” Iya Habu ta sauke ajiyar zuciya tana jin kamar ta jawo asabar ya zo, Momy Chinaza tace “So how are you going to convince Mary-Ann about this?” Iya Habu ta hade rai tace “Convince her? Wa yace maki tana da iko da kanta? Ai a yanxu bata da gata a duniya sai ni, kuma komai na ce tayi bata min musu take yi, so i no get issue with her at all, she go cooperate well well” Momy Chinaza tace “I thought as much, nasan bazata ce a’a ba tunda tana jin maganar ki” Iya Habu tayi murmushi tace “In sha Allahu kuwa, balle ma karamar yarinya ce fa da bata san komai ba, na this one go be her first time, daga nan kuma zata saba ta zama er gari ita ma” Momy Chinaza tace “To how we go take share the money?” Iya Habu tayi dariya ta ja hannun Momy Chinaza tace “This woman you too like money, make the money enter our hand first before we share am nahhh” Momy Chinaza na dariya ita ma tace “Tow no wahala, just make sure she is very neat that day, chief too like neat girls walai” Iya Habu tace “Maleeha no get issue with neatness at all, duk lattin da za mu yi na zuwa kasuwa sai tayi wanka kafin ta fita, wani lkcn har dukanta nake yi ince lokaci ya wuce wankan uban me zata yi, amma ko a boye ne sai ta shiga toilet tayi wanka, even her cloth dey always neat, kullum sai tayi wankin kayanta, shey u dey see her if you come sometimes, even before you pack comot for our yard you suppose don notice her since na” Momy Chinaza tace “Na true, Mary-Ann is neat” A haka Iya Habu ta sallami Momy Chinaza zata koma gida saboda abincin siyarwar da za su kai kasuwa anjima da yamma, cike da farin ciki ta kama hanyar gida tana jin ina ma ta jawo ran asabar, a ranta har ta kuduri kudin farko da Maleeha zata fara kawo mata hayar self-contain zata kama don ta gaji da one room apartment din da take ciki….

07087865788
+2348138491099✍️

About the author

mynovels

2 Comments

Leave a Comment