WhatsApp Join WhatsApp Channel
Littafan Hausa Novels

Bara A Kufai Hausa Novel Complete

Written by mynovels

Bara A Kufai Hausa Novel Complete

*bara a kufai*

*zeey kumurya*

1.

bright pens 2026

yota id 003

bismillahir rahmanir rahim.

dare mahutar baya da kowanne ɗan adam yake yada haƙarƙarinsa a ƙasa domin ya huta, musamman a irin wannan yanayin na tsakiyar damuna.

misalin ƙarfe ɗaya da rabi na dare, gari ya yi tsit, mutane da dabbobi kowa ya nemi gurin fakewa saboda ruwan saman da ake kamar da bakin ƙwarya.

duk da karfin ƙarar ruwan da yake sauka hakan bai hana nishin da take yi cika ɗan ƙaramin ɗakin ba.

idan aka ce mata akwai wani raɗaɗin ciwo a duniya da ba taɓa ɗanɗana shi ba take za ta ƙaryata ba tare da ta bari wanda ya furta ya gama rufe bakinsa ba, saboda tarin raunukan mabanbantan ciwuka da ta rayu da su a cikin zuciyarta, wanda a kullum suke cikin famuwa maimakon waraka. amma a yau da take durƙushe a kan gwiwoyinta cikin azabar ciwon da ba ta taɓa jin irinsa ba a rayuwarta komai ya goge mata, ta kuma tabbatar mutuwa za ta yi, ranar barin ta duniya ce ta zo shi ya sa har ta nemi waɗancan ciwukan na baya ta rasa sai wannan kawai take ji.

duk wani ƙarar saukar ruwan saman da yake zuba a rufin kwanon ɗakin da take, ji take tamkar a kanta yake zuba yana ƙara mata azabar da take ji.

“innalillahi wa’inna ilahiraji’un!” la’ilaha’illallhu muhammadur rasulullahi!

ta furta cikin wata iriyar murya tana jujjuya kanta a matuƙar galabaice.

“ku taimake ni don allah! ku kai ni asibiti!” ta ƙara faɗa numfashinta na sama kamar zai bar gangar jikinta.

tsaki matar da ke zaune a gefen gado tana kallon ta a wulaƙance ta ja tare da keɓe fuska ta ɗauke kanta daga gurinta, fuskarta babu alamun tausayi ko kaɗan.

murɗawar da cikinta ya yi mata ya sa ta buɗa murya ta zabga salati, saboda azabar ciwon da ta ji da ya zarce na baya, wani irin gumi ne yake tsatstsafowa a jikinta, ƙarfen gadon dakin da take riƙe da shi ta ƙara damƙewa tamkar za ta ɓalle shi, cikin fitar hayyaci ta damtse leɓenta na ƙasa tare da sakin nishi da ƙarfi.

ganin yanayinta ya sa matar da ke bakin gadon saurin sakkowa ta ware ƙafafunta ta fara taimaka mata cikin zafin nama da mugunta har jaririn ya fito duniya, a take kukansa ya cika ɗakin. ƙaƙƙafar ajiyar zuciya ta sauke ta yi baya ta zauna sharaf tana mayar da numfashi, kamar an zare gashi daga tandar mai haka ta nemi ciwon ta rasa, duk da ba ta ga abin da ta haifa ba bare ta san wanne jinsi ne amma kukansa da ya cika mata kunnuwa ya haifar mata da wani abu mai girma a cikin zuciyarta, ta ji ta yi mata nauyi kamar an ninka mata ita biyu, ta ji ƙaunar shi na bin duk wani lungo da saƙo na jikinta tana samar wa kanta mazauni.

a hankali ta ɗaga kanta ta zuba masa idanunta da suka yi mata nauyi, dishi-dishi take kallon matar da take goge masa jiki da wani farin yadi. hannunta ta ɗaga da yake yi mata ƙaiƙayi saboda zumuɗin ganin shi a jikinta, ta saita shi tana jira kawai ta ji ta sako mata shi kamar yadda take jin labarin ana yi.

turo ƙofar ɗakin da aka yi a haukace aka shigo ya sa ta mayar da idonta gurin ƙofar, wata mummunar faɗuwa gabanta ya yi ganin wadda ta shigo, da sauri ta ɗauke kanta tare da fara ambaton sunan allah a cikin ranta.

“goge-gogen me kike yi haka ne?” ta faɗa a tsawace tana kallon mai riƙe da jaririn.

ba ta jira amsar ta ba ta ƙara faɗin. “abin da ya fito daga jikin wannan najasar kike ƙoƙarin tsaftacewa kamar kowanne ɗa? ko kin manta ɗauɗar da take tattare da ita ne? wadda ko ruwan duniya za a tara a wanke ta da shi ba za ta taɓa fita ba.”

mai riƙe da jaririn ba ta ce komai ba ta kwantar da shi a ƙasa. hakan ya sa wadda ta shigo jan ƙwafa, a fusace ta ƙaraso ta fizgi hannunta ta miƙar da ita tsaye a wulaƙance, cikin galabaita ta ja zanin jikinta da ƙasansa ke jiƙe da jini ta tallafe shi a ƙirjinta da ɗayan hannun, idonta duka a waje cikin tsananin tsoro. jan ta ta fara yi kamar farin shigar layya ya siyo rago, ta so turjewa ko don ta ɗauki abin da ta haifa da yake ta tsala kuka, amma kasancewar jikin nata babu kwari ko kaɗan ya sa hakan ya gagara. ganin sun fice daga ɗakin ya sa ta tsaya duk da jirin da take ji, a raunane ta ce. “duk da ban san inda za ki kai ni ba amma don allah ki bari na ɗauki ɗana.” ko tsayawa ba ta yi ba bare ta juyo ta kalle ta, ta ci gaba da jan ta a cikin ruwan kamar mushen dabba, a soro suka tsaya ta zare sakatar gidan ta hankaɗa ta waje, cikin kakkausar murya tana zare idanunta masu ban tsoro ta ce. “na sha faɗa miki abubuwa da yawa a baya amma kina ɗaukar su wasa, to yau zan tabbatar miki da bana faɗar abin da na san ba zan iya aikatawa ba, a cikin daren nan, a cikin ruwan nan na kore ki daga gidana da rayuwarmu kora ta har abada, don haka ki san inda dare ya yi miki, kar na ƙara buɗe gidan nan na gan ki, wallahi! wallahi idan ba ki tafi ba kika tsaya ni kaɗai na san abin da zan yi miki!” daga haka ta tura ƙofar gidan da ƙarfi kamar za ta ɓalla ta, ta mayar ta rufe.

da sassarfa ta koma ɗakin da suka baro, ganin matar da suka bari da yaron ta kuma ɗaukar shi ya sa ta yi mata wani kallo tare da faɗin. “na lura kamar tausayi ya fara ratsa zuciyarki akan wannan aikin ko?” da sauri ta girgiza mata kai ta ce. “ko ɗaya.” sai da ta zauna a kusa da ita tana kallon jaririn sannan ta ce. “tunda mun samu jinin haihuwar ita kuma na kore ta je ki cilla abin da aka haifa cikin rijiya.” ba ta amsa ba, ba kuma ta yi musu ba ta miƙe ta fice daga ɗakin.

wani murmushi ta saki ta ja farin yadin da aka goge jinin jaririn ta nannaɗe ta miƙe ta fice da shi a hannunta, ba tare da ta damu da jiƙewar da jikinta ya yi ba.

***** ***** ******

*mafari*

katon guri ne da ya kasance a rufe ruf wanda aka gina shi da zallar mulmulallen dutse mai ƙyalli da ɗaukar ido. babu komai a cikinsa sai wasu mutane su bakwai tsirara da ɗaurin jan ƙyalle a ƙugunsu. suna tsaye riƙe da wani baƙin zare sun zagaye wani rami da yake fitar da hayaƙi yana turniƙe su. a hankali hasken da ke gurin ya fara ɗaukewa, duhu ya mamaye su, tartsatsin wuta ya fara fesowa daga cikin ramin gami da sautin magana cikin wani irin amo mai razanarwa.

“jini da jini sun haɗu sun ƙosar da ƙanzula! amma ƙanzula na buƙatar jinin goɗiya mai jan tauraro! wadda ke shaƙar numfashi ɗaya da ɗaya daga cikinku! ku yi gaggawar kawo ta ga ƙanzula! za ku yi farinciki da haka! za ku samu abin da ba ku taɓa samu ba daga ƙanzula! ƙanzula na buƙatar godiyar nan da gaggawa!”

daga haka sautin ya ɗauke ɗif! hasken gurin ya dawo, zaren hannunsu ya fara komawa cikin ramin da kansa, tartsatsin wuta da hayakin suka ɗauke kamar ba su taɓa wanzuwa ba, ramin ya haɗe kansa ya rufe ruf ba tare da ya bar wata alamar ƙofa ba.

a hankali suka juya suka yi layi, idanunsu a rufe suka nufi wata siririyar hanya, bangon gurin kawai na gaban ya shafa ƙofa ta bayyana ta buɗe kanta, ba tare da sun buɗe idanun ba suka shige.

ƙaton ɗaki ne mai yalwar haske, na farkon ya zura hannayensa biyu cikin wata jakar fatar zaki da ke maƙale a bango ya ɗauko wata ƙwarya da ke zagaye da harsuna a manne a jikinta ya kafa bakinsa ya fara ɗiɗɗikar baƙin jinin da yake ciki. sai da suka sha ɗaya bayan ɗaya sannan suka nufi wata ƙofa a cikin ɗakin suka fice suna karanta wasu irin ɗalasumai.

wani makeken parlour da ya ji komai na kayan alatu suka ɓulla, sai a lokacin suka buɗe idanuwansu, kowa ya nufi inda ya ajiye tufafin jikinsa ya ɗauka ya fara suturta jikinsa. a take su shida suka fito cikin shiga ta kamala, manyan rigunan jikinsu suka ƙara fito da haibarsu, hulunan kansu suka ƙawata fuskokinsu zuwa ta manyan alhazai masu madafan iko, tamkar ba su ba ne naked a mintina ƙalilan ɗin da suka shuɗe.

“an ja shekaru ƙanzula tana batun wannan goɗiyar amma har yau mun gagara samo ta, abin da bai taɓa faruwa ba tun kafuwar wannan ƙungiyar, anya kuwa babu wanda yake shirya wata manaƙisar a cikinmu a ɓoye? tunda a kullum sai ƙanzula ta faɗa mana yarinyar nan tana kusa da ɗayanmu.”

ɗaya daga cikinsu ya faɗa yana saka glasses a fuskarsa.

kallon shi suka yi a tare kafin wani guntu mai sanƙo ya jijjiga kai ya ce.

“kuma fa ka zo da magana abar dubawa janwuya, ban da haka me ƙanzula ta taɓa buƙata daga gare mu muka gagara ba ta? wa ne namu ba mu bayar ba? sai wannan ce kawai za ta gagara?”

janwuya ya yi taku biyu yana yi musu kallon ƙasan ido ɗaya baya ɗaya, cikin tsanaki ya ce. “na fara tunanin ko ma wane ne ya gano wace ce goɗiyar, ya ƙi bayyana mana ita ne kawai saboda yana da wani plan nasa a kanta, ko yana so ya kawo wa ƙanzula ita a sirrance ya samu tagomashin da ta ce shi kaɗai, ko kuma yana yi mata soyayyar da ba zai iya bayar da ita ba.”

“koma yaya ne, ko a ina take ni sai na nemo ta na kawo ta! wannan alƙawari ne na ɗaukar wa kaina!”

wadda ta kasance mace ɗaya tal a cikinsu ta furta tana wani irin murmushi.

jinjina janwuya ya yi mata ya ce. “duk abin da kika faɗa tabbatacce ne a gurinmu saboda sanin ƙwazonki, na san za ki iya, muna nan muna jiran zuwan wannan ranar da ƙanzula za ta yi farincikin da ba ta taɓa yi ba, ƙungiya ta samu abin da ba ta taɓa samu ba, baƙin dage ya yi kalaci da jan tauraro da ya yi shekaru yana tsumayi, dakarun baƙin gida su yalwata da arziƙin da ba su taɓa samu ba, ke kuma ki samu ƙarin girman da kowa yake ƙulafuci!”

jinjina suka yi mata a tare fuskokinsu ɗauke da fara’a, ban da mutum ɗaya da ya ƙura mata ido fuska a haɗe yana jifan ta da wani irin kallo.

***** ***** ******

ahayan

gida ne ginin ƙasa mai babban tsakar gida da aka jera masa ɗakuna daga farkon gidan har ƙarshe a kowanne bango na kudu da arewa suna fuskantar juna. daga can ɓarin yamma kuma rijiya ce a hannun dama sai banɗaki daga hannun hagu, ƙofar shigowa da ɗakin soro na maza kuma daga ɓangaren gabas.

ita kaɗai ce a durƙushe a bakin rariya tana wanki, kamar baƙuwar gidan haka take bin ko’ina da kallo tana hasaso yadda gidan zai kasance a cikin ranta duk ranar da aka ce babu waɗannan rakwacam ɗin shirgin da ko lokacin damuna ba a kwashe su duka. numfashi ta sauke ta ɗauke idonta daga kan tukwane kusan shida da suke kusa da ita da ragowar kayan wanke-wanke, ta sauke idanun nata a ƙofar ɗakin inno da shi kaɗai ne a gyare kaf gidan, sabuwar filasta da fentin da aka yi masa suka ƙara ƙawata shi, ga tiles masu ɗaukar ido da aka shafe ɗan tudun da ke ƙofar ɗakin da shi.

motsin fitowar da ta ji ya sa ta saurin kallon inda take jigo sautin. zeenat ta ce ta fito sanye da ɗaurin ƙirji tana hamma, ta taho fakam-fakam ta wuce ta shige toilet bayan ta bangaje ta. ba ta ko ɗaga ido ba ta ci gaba da wankin da take.

“ahayan! ahayan!”

muryar umma lantana ta karaɗe kunnuwanta. da sauri ta tsame hannunta ta ɗauraye tana amsa mata.

“wanke mini tukunyar da na yi tuwo jiya zan ɗora ɗumame, ban san rana ta yi haka ba ga shi zeenat za ta je makaranta.”

ahayan ta amsa mata cikin girmamawa sannan ta janyo tukunyar ta fara ƙoƙarin wankewa.

daidai lokacin inno ta buɗe ƙofar ɗakinta ta fito cikin tafiyar ƙasaita tana cika da batsewa, fuska babu annuri take duban ahayan a wulaƙance.

“ke!”

ahayan ta ɗaga kai da sauri ta kalle ta, duk da a tsugunne take amma sai da ta ƙara rankwafawa, a ladabce ta ce. “ina kwana?”

“janyo mini ruwa ki cika mini bokitin can!”

cewar inno cikin gadara tana hure hanci ba tare da ta bi ta kan gaisuwar da take yi mata ba.

da sauri ahayan ta ajiye tukunyar hannunta ta nufi gurin rijiya ta kama igiya ta fara janyowa.

“idan kika janyo ruwan nan ba ki gama abin da na saka ki ba wallahi sai na tura ki kin bi gugan cikin rijiyar, idan ya so sai ki zuƙo mata ruwan ta baki da hanci.”

umma lantana da ta tunkaro inda take ta faɗa a fusace tana gyara ɗaurin zanin jikinta.

a tsawace inno ta ce. “ke yi mini abin da na saka ki kafin na saɓar miki, kin kuma san bana son yawa maimaita magana ko?”

tsayawa kawai ahayan ta yi tana kallon su cikin tsoro, ta san halin kowaccensu da kalar muguntarta, babu abin da ya faru ma sun gana mata azaba ina ga sun samu dalili. a marairaice ta ce. “don allah ku yi haƙuri, duk zan yi muku abin da kuke so yanzu.”

“to fara yin nawa tunda ni na fara saka ki!”

cikin izza inno ta taka zuwa kusa da umma lantana, lokaci ɗaya ta ja baya kamar wadda aka tsikara tana toshe hanci, a wulaƙance ta ce. “wallahi sai ta zuba mini ruwan nan sannan za ta bar gurin nan, ke har kin isa a gidan nan na saka abu ki ce sai na jira an yi miki naki sannan za a mun? wace ce ke? ƙazama da ke kina fama da warin hammata da kwantsar ido ki ce da ni za ki dinga takara? to ki kama kanki kafin na kama miki shi da igiyar da za ta wujijjiga rayuwarki, ki kuma fita a sabgata na faɗa miki!” ba ta jira cewar umma lantana ta kalli ahayan a fusace ta ce. “za ki yi abin da na saka ki ko kuma?” idon ahayan cike da ƙwalla ta gyaɗa mata kai da sauri cikin tsoro ta fara jan ruwan. kamar wadda aka cilla haka umma lantana ta yi tsalle ta damƙo rigarta ta baya ta janyo ta, ta hankaɗa ta. a ɗimauce ahayan ta saki gigitacciyar ƙarar da ta cika gidan.

****

haseenah

matashiyar budurwa ce zaune a ƙaramin tsakar gidansu tana latsa wayar hannunta, a hankali ta yi zooming status ɗin ƙawarta da ta saka hotunan anniversary na iyayenta, yadda suka jeru a ƙaton parlon gidansu ba ƙaramin burge ta ya yi ba, gabaɗaya matan suna sanye da baƙar rigar abaya da ta ƙara fito da hasken fatarsu, a fili ta furta “wow.” tare da ƙara faɗaɗa murmushin fuskarta ta ci gaba da kallon status ɗin.

“hasina! hasina!”

ɗago kanta ta yi tare da amsawa, lokaci ɗaya murmushin fuskarta ya ɗauke, ta tsaya kawai tana kallon amma da take ta fama da hura wutar ice, ta haɗa gumi ta yi sharkaf sai share idonta take saboda hayaƙi.

fuskar amma a washe ta ce. “ki je ki gani idan an gama markaɗen ƙosan ki karɓo mini.” baki hasina ta zunɓura tare da cunkushe fuska, cikin ƙunƙuni ta ce. “gaskiya amma ki nemi almajiri, da girmana da class ɗina kawai a ga ina ɗauko markaɗe a ƙaton bokiti? salon duk wanda na haɗu da shi ya san ƙosai ake siyarwa a gidanmu?” baki amma ta hangame ta ce. “to mene ne a ciki hasina? sana’a ce fa ba sata ko wani mugun abun ba.” kamar za ta yi kuka ta miƙe ta zari gyale tana faɗin. “duk da sana’a ce amma ai a ƙasƙance mutane suke kallon mai yin ta.” amma ta ce. “sai su yi ta yi, ni dai tunda allah ya gani neman halak ɗina nake ai shikenan.” za ta kuma magana amma ta katse ta a tsawace.

“ki je ki karɓo mini ba jan magana na nema ba, ke da idan ba ki yi musu ba ba kya jin daɗi a rayuwarki.”

baki ta tura gaba ta fice tana ƙunƙuni, tsabar jin haushin aiken ko kuɗin markaɗen ba ta tsaya ta karɓa ba. bayan ta je ta ɗauko a hanyar dawowa ta ji ana kiran sunanta, da sauri ta ajiye bokitin da ya fara sagar mata da hannu ta juya, wata ƙawarta da suke islamiyya ta gani tana bin ta da wani irin kallo mai kama da ƙyama, hakan ya sa ta ji duk ta muzanta, da rawar murya ta ce. “tas..tas…tasneem me ya kawo ki unguwar nan da sassafe haka?” kallon sama da ƙasa tasneem ta yi mata ta ce. “shekaran jiya muka dawo nan baya, ga gidanmu can da muka tare kina shan kwanar can.” ta nuna mata direction ɗin da hannunta sannan ta ci gaba da faɗin. “ke kuma fa? daga ina haka na ga kamar markaɗe ma kika ɗauko?” ta ƙarashe maganar tana leƙa bokitin da hasina take ta karewa a bayanta.

yaƙe hasina ta yi ta ce. “na zo gidan masu aikin gidanmu ne da muke ba su aikin yi mana ƙosain sadaka, saboda kwana biyu ba sa yi da wuri almajirai suna zuwa su cika a ƙofar gidanmu, shi ne dad ɗina ya ce na zo na yi musu magana akan haka, da na zo sai suke sanar mini yaron da yake kai markaɗen ne ba shi da lafiya, shi ne na kai musu da kaina saboda’ kar dad ya kuma magana.” wani murmushi tasneem ta yi ta ce. “gaskiya ne, amma kin yi ƙoƙari fa, kai markaɗe da kanki, da farko har na fara tunanin ko gidanku ne a nan har zan ce zan bi ki mu je na gani.” da sauri hasina ta ce. “a’a, ba gidanmu ba ne, mu muna can g.r.a ne na bayan unguwar nan.”

daga haka suka yi sallama tasneem ta juya ta tafi, ƙaƙƙafar ajiyar zuciya hasina ta sauke, ranta a ɓace ta ɗauki markaɗen ta ci gaba da tafiya, tana shiga gida ko sallama babu ta fara mita.

“wallahi daga yau ba zan ƙara kai markaɗen nan ba, da ba don allah ya taimake ni ba da tuni asirina gama ya tonuwa yau, shikenan kuma na kaɗe har ganyena.”

amma ba ta tanka mata ba ta girgiza kai kawai ta ci gaba da aikinta, a zuciye hasina ta koma inda ta tashi ta zauna tana ƙunƙuni, hangowa kawai take tasneem ta biyo ta ta zo ta ga amma a wannan cukurkuɗen da take, da ba ta san adadin kunyar da za ta kwasa ba a ce ga mahaifiyarta, mai ƙosai da kokon siyarwa da safe, da rana kuma shinkafa da wake da daddare kuma awara, hamdala ta yi ta janyo wayarta ta ci gaba da kallon status ɗin da take, a ranta tana taya su ameera murna da mamansu ta kasance kyakkyawa ƴar gayu ƴar boko da ba za su ji kunyar nuna ta a ko’ina ba ko kuma a zo gidansu a gan ta ba, saɓanin ita da amma kwata-kwata ba ta san wani abu gayu da wayewa ba, kodayaushe tana bakin murhu ko kuma tana kai kawo a aikace-aikacen gida. kamar wadda aka yi wa mutuwa haka ta rafka tagumi tana fatan da ma a ce bawa shi yake da ikon tsara rayuwarsa, da tabbas ko a kusa da unguwar masu siyar da ƙosai ba za ta zo ba bare kuma a ce mahaifiyarta ce take yi!

zeey kumurya✍🏻

09047871750

[9/15, 9:01 pm] +234 913 560 4817: *bara a kufai*

*zeey kumurya*

2.

bright pens 2026

yota id 003

bismillahir rahmanir rahim.

juraij

kaiwa da komowa kawai yake a cikin ƙaton bedroom ɗinsa cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa, lokaci ɗaya ya zauna a bakin gado kamar wanda aka tsikara tare da ɗaukar wayarsa da ya yasar ya latsa ya ƙura mata ido, gabaɗaya fuskarsa ta sauya, jijiyoyin kansa sun fito raɗa-raɗa, a hankali ya sauke numfashi tare da lumshe idanunsa da suka yi ja, yana jin yadda zafin wutar da ke ci a zuciyarsa yake karaɗe ko’ina na jikinsa.

a razane ramlah da ke kwance tana kallon shi da idanunta da ke cike da bacci ta tashi zaune, idanunta duka a waje ta ƙarasa kusa da shi tare da dafa kafaɗarsa, saboda gigicewar ganin yanayinsa bakinta har rawa yake gurin furta. “man! mine! me ya faru? me aka ce maka a wayar da assusuban nan na ga jikinka yana ta tsuma haka?” bai ba ta amsa ba sai idanunsa da ya buɗe ya zuba mata, yanayin yadda ta ga idanunsa ya sa ta saurin ja baya a firgice tare da furta. “innalillahiwa’inna’ilaihi raji’un!” a sukwane ya miƙe ya fara tafiya ba tare da ya amsa mata ko ɗaya daga cikin tambayoyinta ba, ta bi shi da kallo tare da sauraren takunsa da yake amsawa a duk ɗaga ƙafa da direnta da yake yi, dafe kai kawai ta yi cikin kaɗuwar rashin sanin damuwar mijin nata.

zuciyarsa a cunkushe ya fito parkour ya haura sama, direct ɗakin daddy ya nufa ya buɗe ya shiga.

yana nan a kwance a miƙe samɓal tamkar gawa kamar kullum da kodayaushe, wani irin faɗuwa gabansa ya yi, bai san ya aka yi ba sai tsintar kansa kawai ya yi a bakin gadon da daddy yake kai, jikinsa na tsuma ya kai hannu daidai saitin hancin daddy, ƙaƙƙafar ajiyar zuciya ya sauke tare da zamewa ya zauna. azkar ɗin safe ya fara karantawa a hankali yana tofawa a fuskar daddyn, bayan ya ida ya ɗora hannunsa a kan goshin daddy, murya a karye ya ce. “allah ya ba ka lafiya ya nuna mini ranar da zan ga ka miƙe kana tafiya da ƙafafunka.” daga haka ya miƙe ya gyara masa kansa sannan ya fice daga ɗakin a hanzarce.

a bakin steps ya tarar da ramlah a tsaye tana kallon inda zai ɓullo, kamar za ta kifa haka ta fara taka matattakalar tana faɗin. “me ya samu daddy? ba dai jikin nasa ba ne ko?” ta ƙarashe maganar tana hawaye.

cike da kulawa ya kama hannunta ya ce. “babu abin da ya same shi, yana nan a raye kamar yadda yake.” dogon numfashi ta sauke ta ce. “alhamdulillah! ubangiji ya tashi kafaɗunsa, amma har hankalina ya tashi ganin yanayinka, i thought wani abun ne ya same shi.” girgiza mata kai kawai ya yi.

“to me ya faru my na gan ka a haka? ka san bana son abin da zai taɓa mini kai ko kaɗan? bana ƙaunar ganin damuwa daidai da ƙwayar zarrah a kan fuskarka.”

sai da ya zagaye ta ya sauka daga kan steps ɗin gabaɗaya sannan ya ce. “damuwa da numfashina a yanzu sun zamo manyan amininai, saboda dalilai masu tarin yawa da kika sani da kuma ciwon daddy.” ya dakata daga tafiyar da yake ya juyo ya fuskance ta, fuska babu walwala ya ci gaba da faɗin. “kin taɓa ganin kifin da aka ciro shi daga cikin ruwa ya ci gaba da rayuwa?” ta girgiza masa kai a hankali, ya ce. “to tamkar haka lafiyar daddy da farincikin rayuwata suke, idan kin ga na koma kamar yadda kike so to na ga daddy ya fara takawa da ƙafafunsa, sannan kuma na cika burina akan abin da nake son cimmawa.” a raunane ta ce. “da yardar allah daddy zai warke ragal, burikanka ma gabaɗaya za su cika.” idanunsa da suka yi masa nauyi kawai ya lumshe ya ci gaba da tafiya. da sauri ta bi bayansa har tana tuntuɓe.

**** ****

ahayan

durƙushe take a bakin rijiya tana kuka mara sauti, jikinta sai karkarwa yake saboda sanyin da yake ratsa ta na ruwan da umma lantana ta kwara mata a jiki, saboda takaicin ba ta yi nasarar cilla ta cikin rijiyar ba kamar yadda ta so.

“amma dai lantana kin yi asara kin kuma cika mahaukaciya, haka kawai ki kama ki hankaɗa yarinya cikin rijiya, idan da tsautsayi ya sa ta faɗa ta mutu sai ki yi yaya kuma?”

baba da ya fito daga ɗakinsa a guje yana saɓa babbar riga ya faɗa a fusace kamar zai kai wa umma lantana duka.

tsaki ta ja ta ce. “to sai me don ta faɗa ta mutu? ka fi kowa sanin ba ta da gatan da za a bi ta kan gawar tata ma bare a ba da bayanin yadda aka yi ta mutun, idan na kashe ta na kashe banza, kuma ko ba komai an rage mugun iri ai.” baba ya kufula ya ce. “to shikenan tunda haka kika ce, don allah ki gwada ki gani idan za a bar ki da ranki, kar ki fasa, mahaukaciyar banza da wofi kawai wadda ba ta san abin da take ba!” inno ta saki murmushi cikin jin daɗin yadda yayan nata yake wanke umma lantana a gaban yaran gidan da ihun ahayan ya fito da su tsakar gidan. kamar umma lantana za ta yi kuka ta ce. “yanzu ni kake kira da mahaukaciya malam saboda wannan agolar?”

“ba saboda ita ba ne kawai, har da ja’injar da kika yi da zulai, kuma na sha faɗa miki duk abin da ta ce shi za a dinga yi a gidan nan, amma saboda kunnen ƙashi ne da ke kin ƙi ji.”

“ba zai yiwu ba ne shi ya sa na ƙi ji, ba yadda za a yi ina matar wanta a ce sai abin ta shimfiɗa zan bi, wallahi ba ta isa ba, ta yi kaɗan!”

ta ƙarashe maganar tana zullo kamar za ta kai masa duka.

inno ta yi ƙasaitaccen murmushi ta dubi baba ta ce. “rabu da ita baban zeenat, ita ce za ta wahala ai ba ni ba, don wallahi za ta janyo na cire hannuna a komai na gidan nan ne, sai na ga a inda za ta dinga samun abin da za ta ci har ta samu energyn yi mini haukan da take.” da sauri baba ya ce. “a’a ba ma za a yi haka ba.”

“ke lantana ba za ki ɓallo mini ruwa ina zaman zamana ba, saboda haka biyayya ga umarnin zulai ya zama wajibi a gare ki, tilas ne wannan, idan kuma ba haka ba na tattara ki ke da tsumman ƙazamin jikin ku bar mini gida.”

daga haka ya juya ya koma ɗakinsa a fusace, umma lantana ta rasa abin faɗa saboda tsabar takaici da baƙinciki, inno ta saki siririyar dariya cikin shaƙiyanci tana karkaɗa awarwaron hannunta yana bayar da sauti.

“dole ne a yi mini biyayya idan ana son a ci gaba da zama ana shan jar miya.”

harara kawai umma lantana ta iya zabga wa inno tare da jan ƙwafa, zeenat ta ja hannunta a zuciye suka koma ɗaki. inno ma ɗaki suka koma ita ‘yarta husnah bayan ta zabga wa ahayan mugun kallo. ummi da ke tsaye a bakin ƙofar ɗakin umma ta taɓe baki ta ja hannun raudah suka koma ɗakin.

ba tare da wani ya rarrashe ta ba ta goge hawayen fuskarta da hannunta ta miƙe ta janyo ruwa ta cika wa inno bakitin kamar yadda ta saka ta, ta ɗauka ta kai mata har kusa da ƙofar ɗakinta, sannan ta dawo ta tsugunna ta ƙarasa wankin tukunyar da ta fara.

tana ajiye tukunyar a ƙofar ɗakin umma laraba inda kwarfetonta yake ta ji kamar ana kallon ta, a hankali ta ɗaga kanta, gabanta ne ya yi mummunar faɗuwa lokacin da idanunta suka sauka a cikin nasa, saurin yin ƙasa da kanta ta yi tare da neman tsarin allah a cikin ranta.

kallon da ya saba bin ta da shi kamar sabon maye shi yake wulla mata a yanzu ma, muryarta na rawa saboda tsoro ta gaishe shi, da kai kawai ya amsa mata ya shige ɗakin inno yana waigen ta.

zeenat na duban umma lantana cikin damuwa ta ce. “na sha faɗa miki umma ki daina biye wa inno tana saka baba yana wulaƙanta ki a gidan nan amma kin ƙi ji, yanzu mene ne amfanin wannan zagin da kika janyo ya yi miki? kuma abin da kika so ɗin dai bai samu ba.”

“abin ne da ciwo zeenat, akwai tarin baƙinciki kuna rayuwa gida ɗaya da mace amma ta fi ka arziƙi da izza a gidan, abin takaicin ma wai ƙanwar mijinka.”

umma lantana ta faɗa kamar za ta yi kuka.

“ki kwantar da hankalinki ki daina damuwa umma, ba dai duk saboda ‘yarta tana auren mai kuɗi ba ne? to in sha allahu rabbi sai na auri wanda ya fi mijin aunty laure komai da komai, ai ba wata uwar ta fi mu ba.”

umma laraba ta yi ƙasa da murya ta ce. “shi ya sa nake son wanda babanku ya ce zai zo ya zaɓi mata a gidan nan ya zaɓe ki, saboda na ji yana faɗawa ita uwar jin kan ba ƙaramin hamshaƙi ba ne.” da sauri zeenat ta ce. “ni zai ma zaɓa umma, kar ma ki ɗaga zancen, ba dai kin ce malamin nan ya ce kina kawo kuɗin da ya buƙata zai yi mana aikin ba? to yanzu zan shirya na je gidansu furera na ranto miki kuɗin, can ma zan fara zuwa kafin na je makarantar.”

“yawwa ‘yar albarka, ‘ya ɗaya tamkar da dubu, ni na san ban yi haihuwar asara ba da ma, na san sai kin share mini duk wani hawayena.”

zeenat ta ce. “wannan rubutu ne akan dutse ummata, bari na yi maza na shirya.” umma lantana ta miƙe tana faɗin. “ni ma bari na leƙa idan yarinyar can ta hura wutar na ɗora miki ruwan shayin, ki samu ki karya kafin ki fita.” zeenat ta ce. “to farar uwata.” murmushi umma lantana ta yi ta fice daga ɗakin.

sai da goma na rana ta wuce sannan ta kammala wankin, a matuƙar gajiye ta yi shanya saboda yunwa da ke nuƙurƙusar hanjin cikinta, jikinta babu ƙwari ta tattare gurin ta shige ɗakinsu.

a kwance ta tarar da umma ta yi nisa a cikin tunanin da take, jiki a sanyaye ta tsugunna a gabanta ta ce. “sannu da hutawa umma.” kallon tsaf umma ta yi mata sannan ta sauke numfashi ta ce. “kin gama wankin duka?” kai ta gyaɗa a hankali.

“umma kina cikin gidan nan kuma idanunki biyu amma kina ji za a cilla ni rijiya ko fitowa ki duba ni ba ki yi ba bare ki tsawatar?”

“ahayan ba ni da zaɓi sama da na abin da na yi, dole fa sai kin yi haƙuri a zaman gidan nan, na samu an kara ki ana riƙe min ke idan ban yi biyayya ba ya zan yi? in kuma so kike na yi magana a kore mu to, tunda ke kin fi son a yi ta maimaita magana ɗaya.”

hawayen da suka zubo mata ta share ta ce. “amma umma maganar kisa fa ake, da na faɗa rijiyar nan wallahi mutuwa zan yi.” a fusace umma ta ce. “idan kin mutu allah ya ji ƙan ki, amma dai duk abin da zulai da lantana za su yi miki a gidan nan ba zan taɓa magana ba, saboda ina son zama ban shirya yankar ticket ɗin zawarci da wahala ba, ke idan kin ga ba za ki iya zama ba ƙofa a buɗe take sai ki nemi wani gurin ki koma.” kallon umma ta yi cike da rauni hawaye na tsere a kuncinta, tana jin yadda har yanzu zuciyarta ba ta daina bugawar tsoratar da ta yi ɗazu ba, rijiya fa? rijiyar ma irin tasu mai zurfi da ke cike da ruwa, amma shi ne umma za ta ce ta yi haƙuri saboda kawai kar baba ya sake ta? ta san har da rashin maganar umman yake saka su umma lantana yi mata kowanne irin cin kashi.

“ba tsare ni za ki yi da ido ba, duka zan ji a jikina kawai kin rufe ni da shi, shi ne zan san kin fusata.”

“allah ya ba ki haƙuri.”

ta faɗa da rawar murya tare da yin ƙasa da kanta.

kamar daga sama suka juyo baba yana zabga sababi a tsakar gida, da sauri suka miƙe a tare suka leƙa.

sabira ƴar autar umma ce a hannunsa ya murɗe mata kunne, tana ta kuka da son ya sake ta amma ya ƙi.

“sato kuɗin nake ko kuma haƙowa nake da za ku ishe ni da bani-bani? yaushe na biya kuɗin makarantar da har za ki zo ki ce mini an koro ki? shegiyar yarinya da ta yi gadon annamimanci a gurin uwarta, to ba zan bayar ba, daga yau ma kar ƙi ƙara zuwa makarantar tunda macuta ne kuma ɓarayi.” ya ƙarashe maganar tare da yin cilli da ita ta faɗi a ƙasa, tsawa ya buga mata akan ta yi shiru ko ya zane ta sannan ya koma ɗakinsa yana muzurai.

da sauri ahayan ta je ta rungume ta a jikinta tana rarrashinta, ko tari umma ba ta yi ba ta juya ta koma ɗaki, inno da umma lantana da ma ko leƙowa ba su yi ba tunda ba ɗansu ake duka ba, ahayan ta bi ta da kallo zuciyarta a cunkushe da wani irin abu mai zafi.

“aunty ahayan ina son makaranta, ina son na zama likita, don allah kar ki bari baba ya cire ni.”

“in sha allah za ki yi karatu har sai kin cika burinki, ki yi haƙuri ni zan samo kudi na biya miki school fees ɗin da yardar allah, tashi mu je ki ci abinci.” ta ƙarashe maganar tare da kama hannunta suka koma ɗakin umma, ta tambaye ta abin kari ta ce baba bai bayar ba ya ce ba shi da kuɗi, sai dai ta kai wankin da ta yi jiya da yamma gidan masu shi ta karɓo kuɗin sai ta siyo abin karin da shi.

har baba ya fita daga gidan bai daina banbamin faɗan kuɗin makarantar da sabira ta tambaya ba, umma na ta ba shi haƙuri kamar za ta yi kuka.

yana fita ya ga wani maƙocinsu a tsaye a ƙofar gida yana jiran shi, bayan sun gaisa mutumin ya risina ya ce. “alhaji taimakon dai da ka saba shi na ƙara zuwa a taimaka a yi mana, na tashi babu ko sisi ga gida ba abinci, yara ko makaranta ba su je ba.” da sauri baba ya ce. “kayya! abu bai yi kyau ba, har ta kai yara su ƙi zuwa makaranta?” mutumin ya ƙara rusinawa ya ce. “wallahi alhaji, shi ya sa ma na kasa haƙuri na zo na same ka ko za a yi abin da aka saba.” cike da alfahari baba ya zura hannu a aljihu ya ɗauko kuɗi ya ba shi, sai da mutumin ya tsugunna sannan ya karɓa yana ta zabga godiya kamar zai ari baki.

******

juraij

tsaye yake a gaban mudubi yana ƙarasa shiryawa, har lokacin yanayin tsantsar ɓacin ran da yake ciki da damuwa bai bar fuskarsa ba.

a hankali ramla take tafiya cikin yanga ta ƙarasa inda yake tsaye yana ɗaura agogo a tsintsiyar hannunsa. tsayawa ta yi a kusa da shi fuskarta ɗauke da yalwataccen murmushi tana ƙare masa kallo.

“good morning my man.”

ta faɗa tana ɗaukar turaren da ya buɗe ta fara fesa masa a jiki.

“morning.”

ya faɗa a taƙaice ba yabo ba fallasa.

“ka yi kyau sosai hubby!”

ya yi mata murmushi kaɗan kamar mai rowarsa.

“ba za ka yi breakfast ba ne wai na ga kana ta sauri da sassafen nan?”

hannunta ya kama cikin kulawa ya ce. “na faɗa miki ina nan ne kawai amma hankalina gabaɗaya ba ya tare da ni.” rausayar da kai ta yi ta ce shikenan, amma bari na haɗa maka kafin ka sauko daga gurin daddy, idan ka je office ɗin ka samu nutsuwa sai ka ci.” ya gyaɗa mata kai kawai don ba ya son doguwar magana, ya san halinta ita kuma ba za ta taɓa ƙyale shi da batun abincin nan ba idan bai bi yadda take so ba. zare hannunta ta yi daga nasa ta fice daga ɗakin. mintuna biyu ya ƙara ya bi bayanta shi ma. a dinning area ya hango ta ita da wata dattijuwa mai aikin gidan, kallo ɗaya ya yi musu ya ɗauke kai ya haura sama.

“wai ke don allah wacce irin dabbar mata ce? sau nawa zan faɗa miki da zarar kin ga mijina ki dinga gaggawar barin gurin ki tafi inda kika san ba zai gan ki ba?”

da rawar jiki dattijuwar ta rusuna ta ce. “don allah hajiya ki yi haƙuri, wallahi ban lura da shi ba ne, ban san ma ya fito ba sai yanzu da kika yi magana.”

ƙwafa ramlah ta ja ta wurga mata murfin flaks ɗin da yake hannunta ta ce. “munafukar banza kawai, sai an yi magana ki yi ta marairaicewa, na guji yara masu aiki ashe kuma tsofaffin an gudu ne ba a tsira ba, sai kun ga mijin mutum ku yi ta satar kallon shi.” ta ƙarasa maganar tare da jan dogon tsaki. dattijuwar ta yi ƙasa da kanta kawai ba ta ce komai ba.

a wulaƙance ta nuna ta da hannu.

“yau dai na ƙyale ki, amma wallahi idan irin haka ta sake faruwa a bakin aikinki.”

da sauri dattijuwar ta tsugunna tana mulmula goshinta inda murfin flaks ɗin ya same ta, ta ce. “na gode! na gode sosai hajiya! in sha allah zan kiyaye, hakan ba za ta kuma faruwa ba.”

tsaki ta ja tare da zabga mata harara ta bar gurin. matar ta raka ta da idanunta da ke cike da ƙwalla.

a hankali ya tura ƙofar ɗakin ya shiga bakinsa ɗauke da sallamar da ba ya fasa yin ta duk da ya san ba mai amsa masa, daga bakin ƙofa ya tsaya ya rungume hannayensa a ƙirji, ya ƙura wa daddy ido cikin tsantsar damuwa. ya ja sakanni a haka kafin ya ƙarasa bakin gadon cikin ƙarfin zuciya.

“allah ya ba ka lafiya.”

ya faɗa cikin sanyin murya da mutuwar jiki.

a bakin gadon ya zauna ya karanto addu’oi ya tofa a hannunsa ya shafa a fuskar daddy, sai da ya gyara masa pillow yadda zai fi jin daɗin kwanciyar kamar ɗazu sannan ya tashi ya fice daga ɗakin.

a gaban steps ya tarar da ramlah tana kallon matattakalar kamar ɗazu, murmushi ta sakar masa tare da kama hannunsa bayan ya gama saukowa.

“na kai maka abincin da briefcase ɗinka mota, saboda na ga kana sauri kar tsayawa ɗaukar su ya ɓata maka lokaci.”

numfashi ya ja ya fesar ya ɗaga mata kai.

“don allah hubby ka dinga rage wannan damuwar da kake yi, in sha allah daddy zai samu lafiya very soon, bana jin daɗi kullum idan ka je gurinsa na ga ka fito cikin wannan yanayin.”

hannunta da yake cikin nasa ya damƙe ya ce. “na kasa sabawa ne, a duk lokacin da na gan shi abun sabo yake dawo mini, duk farincikin da nake ciki ina tuno halin da daddy yake ciki sai na neme shi na rasa, idan kuma na shiga na gan shi sai na ji tamkar ban taɓa sanin wani abu nishaɗi ba a rayuwata!” gefen fuskarsa ta shafa ta ce. “na sani dear, amma dai ka dinga rage wannan damuwar don allah kar wani ciwon ya kama mini kai, kuma ko shi ma daddyn na san ba jin daɗin ganin ka a irin wannan yanayin yake ba, kawai don ba iya magana ne, amma na san da tuni ya furta maka.”

kai ya gyaɗa mata sannan ya zare hannunsa daga cikin nata ya nufi ƙofar fita daga parlourn, ta bi shi da kallo tana jin kamar ta tsaga zuciyarta ta saka shi a ciki ta ɗinke saboda yadda take jin shi a cikin ranta.

har ya kai bakin ƙofa ya juyo ya dube ta.

“kar ki manta da ba shi maganinsa akan lokaci.”

“abu ne da ba zai taɓa yiyuwa ba my man.”

ya yi murmushi kaɗan.

“na gode sosai da yadda kike kula da mahaifina ba tare da nuna gajiyawa ba.”

ta ɓata fuska ta ce. “mahaifinmu dai, kuma kar ka ƙara mun godiya na faɗa maka amma ka ƙi dainawa ko?” juyawa ya yi ya fice yana murmushi, murmushin da a irin wannan gaɓar kaɗai yake jin shi, ko a ina yake, ko me yake yana tuna ya bar mahaifinsa a hannun ramlah sai ya sake shi, musamman idan ya hango yadda take rawar jikin yi masa hidima da dukkan lafiyarta da jikinta, wanda ko shi da ya haifa ba ta bari ya yi masa rabin abin da take masa.

“marka! marka!

ramlah ta faɗa cikin ɗaga murya tana yatsina.

da sauri dattijuwar nan ta fito daga ƙasan steps inda ta rakuɓe ta zube a gaban ramlah.

“na’am hajiya.”

ramlah ta bi ta da wani matsiyacin kallo ta ce. “ki je waje ki zauna sai na kira ki, sannan duk wanda ya zo ki tare shi ki ce bana nan.”

“to hajiya in sha allah” dattijuwar ta furta da azarɓaɓi, da wani mugun kallo ramlah ta raka ta da shi tare da sakin tsaki ta bi bayanta da sassarfa ta rufe ƙofar da key, sai da ta kashe light ɗin parkourn sannan ta haura sama a hanzarce.

zeey kumurya ✍🏻

09047871750

[9/15, 9:01 pm] +234 913 560 4817: *bara a kufai*

*zeey kumurya*

3.

bright pens 2026

yota id 003

bismillahir rahmanir rahim.

fuskarsa a cunkushe yake takawa zuwa inda motarsa take, rauni da damuwar ciwon daddy da ya fito da su suka dishashe saboda tuno saƙon da ya yi karin kumullo da shi a ɗazu, ba ƙaramin daure zuciyarsa ya yi ba na yaƙar halin da ya shiga ganin yadda ramlah ta tayar da hankalinta, don ba ya son sanar da ita abin da yake faruwa sai ya gama tabbatar da abin da yake son sani, hatta yanayin takunsa sai da ya sauya ya koma na asalin juraij ɗinsa. tun kafin ya ƙarasa ɗaya daga cikin yaransa ya yi hanzarin buɗe masa mota bayan ya gaishe shi, da kai kawai ya amsa masa sannan ya shiga motar ya mayar ya rufe.

wani irin gudu yake yi da motar tamkar zai tashi sama, hakan ya sa cikin mintuna ƙalilan ya ƙarasa wani madaidaicin gida da ya ƙawatu da ginin zamani, daga waje ya yi parking ya tsaya yana kallon gidan da idanunsa da suka kaɗa suka yi jajur. a hankali ya furta “innalillahi wa’inna ilaihi raji’un!” tare da tattaro ragowar juriyar da ta rage masa ya buɗe motar ya fita ya shiga cikin gidan.

tun daga harabar gidan yake jiyo sautin kukan da ke ƙara dagargaje zuciyarsa, jikinsa ya fara tsuma, da sassarfa ya ƙarasa parkourn ya shiga kamar an cilla shi. idanunsa suka sauka akan hoton sheikh adnan bukhari da ke manne a bangon ɗakin yana fuskantar ƙofa, saurin kawar da kansa ya yi saboda bugawar da zuciyarsa ta yi, ya tsayar da idonsa akan matashiyar matar da ke ta kukan da ya cika gidan.

“sun kashe shi! sun kashe mana miji! sun mayar mana da ‘ya’ya marayu, sun raba ni da farincikina!”

kalaman da ta furta masa kenan a ɗimauce cikin tsantsar tashin hankali.

ɗauke idonsa ya yi daga kanta ya mayar kan uwargidanta da ke zaune ta ƙura wa waje ɗaya ido tamkar mutun-mutumi, idonta babu alamun hawaye, sai wata irin rawa da jikinta yake tamkar an jona mata shocking, ga yaran gidan gabaɗaya sun baibaye ta suna kuka mai taɓa zuciya.

a sanyaye ya tsugunna a gabansu tare da zare glasses ɗin idonsa, kamar wanda aka yiwa farraƙu da furta harafi haka ya rasa me zai ce musu, yana jin kamar duk kalmomin da zai yi amfani da su sun yi kaɗan wajen rarrashi da sanyaya musu zuciya. ƙaramar yarinyar gidan ya yi jarumtar ɗauka ganin tana ta rarrafe da kuka amma babu wanda ya bi ta kanta, ya rungume ta a jikinsa cikin tsantsar tausayin ta na rayuwar maraicin da ta same ta tun kafin ta san me duniyar take ciki.

“ina gawar take?” ya tsinci kansa da furta haka.

“tana sama, yanzu su yaya lawal suka wuce da ita, duk suna can, ummu ma tana can.”

amaryar ta ba shi amsa cikin kuka, kai kawai ya gyaɗa mata. ta ci gaba da magana cikin wani irin rauni da kukan da ta kasa tsayar da shi.

“sun hana mu zuwa wai sai an gama yi wa gawar gwaje-gwaje, yaya lawal kuma ya ce ko iyayenmu kar mu kuskura mu sanarwa a yanzu saboda wani babban dalili wai sai an gama bincike, na rasa ya zan yi, na ruɗe na rikice shi ya sa na yi maka text, don jikina ya ba ni ba mutuwar allah ba ce, akwai wani abu a ƙasa, akwai abin da ake ɓoyewa, na san kuma duk duniya kai kaɗai ne za ka iya ganowa, kai kaɗai ne za ka tsaya ka ƙwato mana haƙƙinmu, kai ne kawai hope ɗinmu a yanzu, ummu mace ce ba za ta iya komai ba, ga tsufa, duk yadda suka tsara mata yarda za ta yi, shi ya sa bayan sun hau sama na je na buɗa ƙofa don kar ka zo ka yi knocking su ji su san da zuwanka, wallahi kashe shi aka yi, amma suna so su binne komai, ka taimaka mana kar ka bari haƙansu ya cimma ruwa, ka taimake mu a gano ko su waye a bi mana haƙƙin mijinmu.” ta ƙarashe maganar tare da ɓarkewa da wani irin kuka.

a zafafe ya sauke yarinyar jikinsa ya miƙe ya nufi sama jikinsa na wani irin tsuma, kukan ummu ne ya sanar da shi dakin da suke, a sukwane ya tura ƙofar ya shiga.

a tare duk suka ɗaga kai suna kallon shi, ummu ta yunƙura za ta tashi a hanzarce amma ta kasa, ta koma sharaf ta zauna, hannunta na rawa ta nuna gawar ɗanta ɗaya tilo a duniya tana faɗin. “juraij mutuwa ta ɗauke mini adnan, ta raba ni da shi, ka gan shi, kalle shi, abokinka ne amma ya zama gawa! ya mutu! ya….” ta kasa ƙarasa abin da take son furtawa saboda wani irin gigitaccen kuka da ya ƙwace mata, da sauri ya ƙarasa ya riƙe ta amma ya gaza furta ko da harafi ɗaya ne, bayanta kawai yake bubbugawa alamar rarrashi, idonsa na kan gawar sheikh adnan da ko jiya da yamma sun haɗu, likitan da ke tsaye a kusa da yaya lawal yana rubuce-rubuce ya ce. “sai haƙuri hajiya, lokacin sheikh adnan da allah ya rubuta zai rayu a doron duniya ya riga ya ƙare, sai dai fatan ubangiji ya ji ƙan shi da gafara.” hawayen da ya sauko a kuncin yaya lawal ya goge ya ce. “rayuwa kenan, mutuwa ba ta da iyaka, ga ni ga ummu da sauran ƴan’uwanmu amma sai ƙaramin cikinmu ta ɗauka, innalillahi wa’inna ilaihi raji’un! idan na tuna jiya har dare muna tare da shi sai na ji tamkar mafarki nake, kamar za a tashe ni na farka na ga adnan tsaye akan duga-dugansa mu ci gaba da rayuwa…..” wani kallo juraij ya wurga masa ba tare da ya gama jin ƙarshen zancen nasa ba, shi ma kallon shi yake hakan ya sa idanunsu suka sarƙe da na juna, tsawon wasu sakanni suna haka kafin juraij ya janye nasa ya mayar kan gawar abokin nasa. sai da ya jingina ummu da jikin gado sannan ya ƙarasa ya yaye zanin da aka rufe sheikh adnan da shi, fuskarsa da ba ta motsin komai ta bayyana, idanunsa a rufe amma kamar za a yi masa magana ya amsa, yana ƙoƙarin janyo zanin ya mayar ya rufe fuskar idanunsa suka sauka akan wani abu da ya saka zuciyarsa doka wani uban tsalle, jikinsa ya kama tsumar da ta zarce ta baya, ya tsaya cak yana kallon abun cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa.

***** ****** ******

saudat

a kullum da kodayaushe idan ta kaɗaice babu abin da take yi sai tunanin masu matsalolin rayuwa da take ganin sun fi nata, musamman idan ta hasaso waɗanda iftila’in rayuwa na hatsari ko na gobara ya faɗa musu, a dalilin haka duka gidan su mutu su bar mutum ɗaya tak da ciwon kewa, ko kuma wanda ba za su mutun ba amma za su sha wahala ko su nakasa, ko kuma masu gudun hijira da ƙaddara ta tarwatsa garinsu da ahalinsu, ko waɗanda suka tashi a gidan marayu ba tare da sun san kowa nasu ba, da waɗanda linzamin ƙaddara ya ja su ga ƙare rayuwa a gidan kaso, wani ma bai aikata abin da ake tuhumar shi ba amma tunda ubangiji ya jarrabce shi babu yadda zai yi. duk da hakan ba ya rage mata komai na raɗaɗin da take ciki amma tana cewa “alhamdulillah!” tana samun ƙwarin gwiwar jurar duk wani ƙaluben rayuwa domin ta tuna akwai waɗanda suka fi ta shiga tasku. tana jin kamar watarana komai zai wuce kamar labarin wahalar rayuwar wasu da take ji, amma yaushe? me zai faru ta daina rayuwar bara a kufan da ta ginu tana yi? shi ne tambayar da take yiwa kanta a kullum da kodayaushe ba tare da ta san amsar ta ba. bugun ƙofar banɗakin da take ciki da aka yi ne ya sa ta miƙe ta goge hawayen fuskarta, wanda ba su damar zuba ne ya shigo da ita toilet ɗin. da nauyin da zuciyarta ta yi mata da ya bi dukkan jikinta ya sagar mata ta janyo butar gabanta da ƙyar ta ɗauraye fuskarta. sai da ta yi iya yin ta na ganin ta ɓoye halin da take ciki sannan ta buɗe ƙofar banɗakin kanta a ƙasa ta fice ba tare da ta bari sun haɗa ido da wadda take jiran nata ba.

“ni da dinkum-dinkum.”

ta ji an faɗa cikin izgili, ba ta tsaya ba bare ta san waye ta ci gaba da tafiya kanta a ƙasa, cikin fatan kar mutanen da suke hada-hada a tsakar gidan su gane ta.

wasu mata guda uku da suke zaune suna kallon ta suka kwashe da dariya, ta tsakiyar wadda ita ta taɓo su ta nuna musu ita ta ce. “allah ya raba mu da duhun kai ya ƙara ba mu wayewa, wannan dunkumewa haka har ina? ji fa yadda take tafiya kai a ƙasa saboda kawai kar ta yi wa kowa magana.”

“shi ya sa ai ga shi nan ƙannenta suna ta aure suna barin ta.”

“to wa zai ɗauki macen da ba ta da wayewa? kullum tana fama da hijabi kamar matar liman.”

ƙara kwashewa suka yi da dariya sannan wadda ta fara maganar ta ce. “to ita liman ɗin ma ya gagara samuwa ai.”

duk maganganun da suka yi a kunnenta amma hakan bai sa ta ɗago kanta ba bare ta kalle su, ta ci gaba da ratsawa ta cikin taron mutanen bikin da suka cika gidan nasu.

ta zo daidai ƙofar ɗakin mama ta ji ana ƙwala kiran sunanta, kamar ta share sai kuma ta tsaya ta juyo tana duban mai kiran nata, ganin shamsiyya ce ya sa ta ɗan ɓata fuska don kamar mai kiran ƴar cikinta haka ta cika gurin da hayagaga. tana ƙarasowa kusa da ita ta miƙa mata ɗan hannunta tare da faɗin. “affan za ki goya mini don allah, ina son na yi wanka na yi shirin zuwa bridal shower ɗin nan amma yana ta kuka ya ƙi zama shi sai goyo kawai yake so.” fuska a sake saudat ta ce. “bari na je na ji kiran da mama take yi mini tukunna, idan ba aiki za ta saka ni ba sai na karɓe shi.” ba ta jira cewar shamsiyyan ba ta shige ɗakin mama, da kallon takaici shamsiyya ta bi ta baki a sake, a kufule ta tallafe ɗanta da ya callara kuka ta bi bayan saudat.

saudat na shiga ɗakin mama ta rufe ta da faɗa ba tare da ta damu da mutanen da ke ɗakin ba.

“wai don iskanci na aika a kira ki tun ɗazu amma sai yanzu za ki zo? kin san kuma akwai abubuwa da yawa a gidan nan da suke jiran ki.”

“ki yi haƙuri mama banɗaki na shiga…” ba ta ƙarasa ba muryar shamsiyya da ta banko ɗakin ta katse ta a harzuƙe.

“mama wai na ba wa yaya saudat riƙon affan don na samu na shirya da wuri na tafi gurin bikin nan amma ta ƙi karɓar shi?”

“a saboda me kuma? karɓe shi dalla ki riƙe mata shi, ke da komai ba kya yin abin da ƙuda zai bi.”

a raunane saudat ta ce. “ni ma shiryawar nake son na yi ne saboda na ga yamma na yi, amma ba cewa na yi ba zan karɓe shi ba, na faɗa mata…”

“ki shirya ki je ina?” mama ta katse ta a tsawace sannan ta ci gaba da faɗin. “kunyar da kika saba ba ni ita kike so ki ƙara ba ni a gurin bikin ko me saudat? ina zaman zamana ina tarona cikin mutunci da girma ba za ki janyo mini ƙaranta a wajen surukai har biyu ba, musamman ma iyayen matar zubair da suke masu arziƙi da wayewa da ta amsa sunanta wayewa, to ba zai yiwu ba, babu inda za ki je kina yawo da hijabi zugwi-zugwi bare ki janyo mini abin faɗe.” sai da ta haɗiye wani abu da ya tsaya mata a maƙoshi sannan ta iya furta. “ba hijabi zan saka ba, fabric ɗin da kowa zai saka ni ma shi zan saka.” kallon sama da ƙasa shamsiyya ta yi mata ta tuntsire da dariya, cikin izgili ta ce. “to ai gara ma ki je da hijabin, don wallahi ɓata mana sha’ani kawai za ki yi, kin san jikinki ba ɗaukar kaya yake ba, wanka ba ya kama ki don haka gara ki haƙura kawai ki zauna ki taya masu su girki aiki shi ya fi dacewa da ke.”

“daina ma ɓata bakinki shamsiyya babu inda za ta je wallahi, ana sabgar arziƙi ba za ta ɓatan rai ba, salma ma idan ta gan ta ba za ta ji daɗi ba, don ko cikin ƙawayenta ba kowa ta gayyata ba gudun kar su ɓata mata taro, bare kuma ita da gara su ma suna ɗan gayun nan ko yaya ne.”

wata ƙanwar mama da ke zaune a ɗakin tana shiryawa ta ce. “to ai maman rasheeda da kin bari ta je, saboda idan tana shiga cikin mutane ne za a samu ta waye har ta samu mashinshini ko za a samu ta shiga daga ciki.” taɓe baki mama ta yi cike da takaici ta ce. “wallahi babu wani abu da za a yi wa saudat da zai saka ta waye, don babu haƙilo da ƙoƙarin da ban yi ba amma kullum jiya i yau, shi ya sa na tattara ta na watsar ta je ta ƙarata, indai duhun kai ne babu inda zai kai ta sai turbar da na sani.”

“gaskiya dai yadda kike da gayu da son kwalliya da sabgar girma ban taɓa tunanin za a samu irin saudat a ƴaƴanki ba.”

“hmm.” kawai mama ta ce ta ci gaba da laluben magi za ta bayar a zuba a miya ana jiran ta.

inda sabo saudat ta saba da irin waɗannan abubuwan da wariyar launin fata daga mahaifiyarta da ƴan’uwanta da kyarar da suke nuna mata, ba ma kamar yaya rasheeda, da ta tabbatar da tana nan sai ta saka ta kuka saboda maganganun da za ta caccaɓa mata kamar ba ciki ɗaya suka fito ba. jiki a sanyaye ta karɓi affan ta goya ta shiga jijjiga shi, tana tsaye har shamsiyya ta yo wanka ta zo ta shirya a gurguje cikin wani yadi da ya haska farar fatarta, rigar ta kama ta sosai ta bayyana komai na jikinta, amma maimakon mama ta yi mata faɗa sai ma koɗa kyan da ta yi take yi ita da ƙannenta.

baki a washe mama ta ce. “don ma ba ki yi make up ba da sai kin fi haka fitowa.” tana zira takalmi mai tsini a ƙafarta ta ce. “lokaci ya riga ya ƙure ne, amma gobe dinner ai dole na yi, kuma yau ɗin ma na ji har su yaya rasheeda suna cewa ba za su yi ba.”

saudat ta ɗauka za ta karɓi ɗanta ne, amma sai ta ji tana ba ta sallahun inda za ta ga diaper ta canza masa idan ya yi kashi da kuma madarar da za ta haɗa masa idan ya tashi. da mamaki yayar abbansu da ta shigo ɗaki a lokacin ta ce. “lallai shamsiyya, sai ka ce ba yayarki ba kike ba ta wannan umarnin ba ladabi ba komai?” da sauri ƙanwar mama ta ce. “to ai ta zama yayar yanzu tunda ta yi aure har ta ɗanɗani zafin haihuwa.”

da kallo saudat ta raka shamsiyya idanunta cike da ƙwalla, saboda kawai ta zaɓi saka hijabi ta suturta jikinta akan wannan shigar ta bayyana jiki ya sa kowa ya tsane ta? ko kuma tana da wani aibu ne bayan rashin iya gayu da duk inda ta je sai an kushe ta? tun tasowarta tun tana ƙarama ba ta da farinjini ko kaɗan, kyara da tsangwama su take samu a gurin mutane a kodayaushe, duk da nasu ba ya yi mata ciwo sosai kamar na mahaifiyar da ta tsugunna ta haife ta. ganin hawaye na ƙoƙarin zubo mata ya sa ta yi yunƙurin barin ɗakin, amma mama ta hana ta a tsawace da faɗin. “ina za ki je kuma? jira fa nake affan ɗin ya yi bacci ki kwantar da shi ki je ki ɗebo mana ruwa, tun ɗazu aka ce na tankin ya ƙare ga shi babu nepa ga almajirai ba su taso ba sai shida.” tsabar mamaki ba ta san lokacin da ta ƙame a inda take ba, ɗiban ruwa a shekarunta, ƙanwarta ta biyu fa ake aurarwa, ta tabbata ko cikin yaran da suka zo bikin ba za a rasa masu iya ɗebo ruwan ba.

“ba za ki je ba ne kika tsaya mini a ka?” mama ta faɗa cikin hargowar da take yi mata magana a kodayaushe.

kai ta girgiza ta dawo bakin gado ta sauke affan a hankali gudun kar ya farka sannan ta fice daga ɗakin zuciyarta a ƙuntace. kanta a ƙansa ta ƙara ratsawa ta cikin mutanen da suka cika tsakar gidan ta je ta ɗauki bokiti ta ɓoye a cikin zunbulelen hijabinta, tun kafin ta ɗauko ruwan har wata irin kunya ta rufe ta, addu’a kawai take allah ya sa babu wadatar mutane a wajen.

ta je ta bugo ruwan ta ɗauko ta dawo ta tarar ƙofar gidan a cike da abokan ya zubair suna ɗaukar hotuna tare da tsokanar shi irin wadda ake yi wa kowanne ango, shi kuma sai sakin fara’a yake da take ƙara tabbatar da farincikin da yake ciki, amma yana hango ta ya tamke fuska tamkar bai taɓa dariya ba, musamman da ya san wasu abokan nasa sun san ƙanwarsa ce.

ɗaya daga cikin abokan nasa ne ya zungure shi yana nuna saudat da hannu ya ce. “wannan ba ƙanwar nan taka ba ce?” kamar an yi masa dole ya ce. “ita ce mana.”

“kamar ba ƴar gidanku ba amma, duk kun fita kyau da fari da wayewa, ita kullum cikin burma hijabi kamar wadda ta zo daga ƙauye ba tashin birni ba.”

aminin zubair ɗin ne ya amshe zancen da faɗin. “ga shi an haɗa ta da ɗiban ruwa, ana bikin yayanta da ƙanwarta gaskiya ba a duba mata ba.” ya ƙarashe maganar yana sakin dariyar shaƙiyanci. daidai lokacin saudat ta zo gilmawa ta kusa da su a hanzarce don kauce wa idanuwansu da suke bin ta da shi kamar za su cinye ta, zubair da ke bin ta da kallon raini ya ja tsaki ya ce. “shegiya ai ɗiban ruwan ne ya dace da ita, kowa yana abin da ƙuda zai bi a duniya amma ban da yarinyar nan, wallahi har mama wani lokacin cewa take ko dai an canza mata ita ne a asibiti? saboda mu duk ba haka muke ba, ƙauyanci da gidadancin nata ya yi yawa.” duk yadda ta so daurewa sai da ta ɗaga kai ta kalle shi don kalmar shegiyar da ya kira ta ba ƙaramin dukan zuciyarta ta yi ba.

***** *****

zuciyar juraij na wani irin bugu ya yi parking a harabar ƙaton gidan da ya shiga, sai da ya jingina kansa a jikin kujera yana mayar da numfashi na wasu mintuna a ƙoƙarinsa na daidaita nutsuwarsa sannan ya fice daga cikin motar ya nufi cikin gidan.

bayan ya yi knocking an buɗe masa ya shiga parkourn bakinsa ɗauke da sallama, matar da ke tsaye suna shirya dinning ita da yaranta ƴanmata guda biyu suka amsa masa cikin mamakin ganin shi da safe haka.

“ina kwana hajiya.”

ya faɗa cikin girmamawa.

“lafiya ƙalau juraij.” ta amsa ba yabo ba fallasa tare da ci gaba da magana. “malam ɗin yana part ɗinsa ka shiga.” kai ya jinjina mata ya nufi ƙofar da za ta sada shi da ɓangaren maigidan, ganin haka ƴanmatan suka haɗa baki gurin gaishe shi da sauri, hannu kawai ya ɗaga musu ya shige. hajiya ta taɓe baki tare da faɗin. “faɗin ran yaron nan yana ƙona mini rai wallahi, shikenan kullum a cukule kamar wanda ya shiga gasar rashin fara’a.” murmushi muhibba ta yi ta ce. “ni kuma ba ƙaramin burge ni yake ba..”

“mtsss.” hajiya ta katse ta da jan tsaki sannan ta ce. “haka kuka iya, ba ku da aiki sai yabon shi ku da malam, kun manta abin da ya yi mana a gidan nan kamar bai taɓa sanin mu ba.” ta ƙarashe zancen tana jan ƙwafa.

“hajiya wannan daban, amma yaya juraij ba ruwansa, yana da kirki da…”

“na ji! zancen ya ishe ni haka, je ki ci gaba da kwaso sauran kayan a kitchen, na haɗa na malam ku kai masa, don tunda wannan mutumin ya zo kuma fitowar malam ba yanzu ba.”

sallamar juraij haɗe da buɗe ƙofar part ɗin malam ya saka shi ɗago kai daga duba wani littafin addini da yake, tattausan murmushi ya saki tare da amsa masa sallamar.

“lale maharbin da murucina.”

kai kawai juraij ya jinjina masa yana jin sassauci na tafarfasar da zuciyarsa take yi masa, hakan ya tabbatarwa malam da akwai wani abu.

tun kafin ya ƙarasa malam ya miƙe bayan ya ajiye littafin hannunsa ya miƙa wa juraij hannu suka yi musabaha.

“bismillah.” ya faɗa har lokacin da murmushi akan fuskarsa mai cike da haiba yana nuna wa juraij kusa da shi.

ƙasa kawai ya yi da kansa yana sauke numfashi da sauri da sauri, ya lumshe idonsa da suka sauya kala yana sauraren bugun da zuciyarsa take yi masa kamar za ta faso ƙirjinsa ta fito. cike da kulawa malam ya kama hannun juraij ya zaunar da shi ya fara bubbuga kafaɗarsa a hankali alamar rarrashi tare da furta. “subhanallah! lahaula-wala-ƙuwwata illa billah!” maimaitawa juraij ya shiga yi a hankali don ya fahimci me yake nufi, sun ɗauki mintuna a haka sannan malam ya sake shi ganin ya fara dawowa cikin nutsuwarsa ya koma kusa da shi ya zauna ya dube shi a tsanake ya ce. “yanzu lokacin kasancewarka a gurin aiki ne, a yadda na san ka kuma ba ƙaramin abu mai muhimmanci ba ne zai saka ka bar office ka zo nan, duk da yanayinka kaɗai ya alamta mini ba lafiya ba don ruwa ba ya tsami banza, ina fata dai ba jikin mahaifin naka ne ya…..” kwankwasa ƙofar parlon da aka yi ya katse malam, umarnin shigowa ya bayar, suhaila ta turo ƙofar bakinta ɗauke da sallama, bayan sun amsa ta ƙarasa ta ajiye tiren hannunta a kan centre table sannan ta juya ta fice.

malam ya ƙara duban juraij a karo na biyu ya ce. “ina sauraren ka, me ya faru?”

“sun kashe sheikh adnan!”

“innalillahi wa’inna ilaihi raji’un! sheik adnan din? yaushe? su waye? ya hayyu ya ƙayyum, hasbunallahu wa’ni’imal wakil!”

“a daren jiya! su suka kashe shi! azzaluman da suka saba ɗaiɗaita mana rayuwar al’umma.”

ya ba shi amsa a rarrabe ƙirjinsa na ɗagawa da komawa.

salati da sallallami malam kawai yake yi cikin tsananin razani da gigita, a rikice ya ce. “saboda lecture ɗin da ya yi a huɗuba ranar juma’a ne ko? tun a lokacin na kira shi na ce kar ya sake, mutanen nan ba imani ne da su ba, barin su da ubangijin da ya halicce su shi ne abin da ya dace mu yi tunda babu yadda muka iya da su.”

“har wanne lokaci za mu kai a ƙasar nan muna ƙin hoɓɓasawa mu ƙwaci kanmu? mutane ne fa su kamar mu, yadda suke yin duk abubuwan da suka ga dama haka mu ma za mu dinga ɗaukar mataki a kansu!”

cike da damuwa malam ya ce. “tabbas haka ne mutane ne su ma kamar mu, sai dai muna da banbanci da su ta kowacce fuska, su sun zaɓi duniya ne akan lahirarsu, sun zaɓi tsafi da shirka da zubar da jinin muminai don samun duniya, shi ya sa ubangiji yake yi musu talala ya ba su sa’a akan dukkan abubuwan da suke yi, wanda yake saka su ganin kamar wayonsu da dabararsu da isarsu ne suka ba su, shi ya s*bara a kufai*

cike da damuwa malam ya ce. “tabbas haka ne mutane ne su ma kamar mu, sai dai muna da banbanci da su ta kowacce fuska, su sun zaɓi duniya ne akan lahirarsu, sun zaɓi tsafi da shirka da zubar da jinin muminai don samun duniya, shi ya sa ubangiji yake yi musu talala ya ba su sa’a akan dukkan abubuwan da suke yi, wanda yake saka su ganin kamar wayonsu da dabararsu da isarsu ne suka ba su, shi ya sa da zarar mutum ya yi yunƙurin yaƙar su ko fallasa wani sirri nasu suke kawar da shi nan take…”

“haka za mu zauna a yi ta tafiya kenan malam? suna mayar mana da mata zaurawa, su mayar da ƙananun yara marayu? dole mu ma sai mun dage mun ƙwaci kanmu, idan ba haka ba watarana sai dai mu wayi gari mun zama bayinsu, numfashi ma sai sun so za mu yi, babban abin da yake ƙara baƙanta mini raina yadda duk wata ɓarna da suka yi sai sun bar alamar da za a gane su suka yi, suna yi mana izgili da nuna ba mu isa mun yi komai a kansu ba, tunda da suna yi a ɓoye, amma daga lokacin da hankali ya kai kansu aka farga da su suka fara bayyanawa, wanda hakan yake nuna sun yi ɗin mu yi duk abin da za mu yi, to za su gani! za mu yi abin da ba su taɓa zato ba da yardar allah!

numfashi malam ya sauke tare haɗe hannunsa guri guda ya tallafe haɓar fuskarsa, a raunane ya fara faɗin. “kar ka manta juraij ina daga cikin waɗanda suka fara farga da wannan ƙungiyar gami da yunƙurin yaƙar su, amma babbar illa da suka yi mini a matsayin barazana ya sa na janye ƙudirina ba don abin ya daina damu na ba, na koma gefe na zuba musu ido kawai ina kai ƙarar su gurin mai duka akan ya yi mana maganin su, tunda idan sun fi ƙarfinmu ba su fi ƙarfinsa ba shi.”

miƙewa juraij ya yi ya zura hannayensa a cikin aljihun wandonsa, sai da ya shaƙi iska ya fesar sannan ya fara magana cikin ɗacin rai.

“ba zan iya ci gaba da jurar yadda suke lahanta rayuwar al’umma da rushe musu farinciki a duk lokacin da suka so ba, rantsuwar da na yi kafin fara aikina ba za ta tashi a banza ba, da izinin allah yadda na kafa ƙudirina a kansu ba ja da baya sai na ga abin da ya ture wa buzu naɗi.” ya yi taku biyu tare da ƙara murtuke fuskarsa kamar yana gabansu, a kaushashe ya ce. “yanzu aka fara wasan da ni da su, domin tun lokacin da na yi arba da gawar sheikh adnan na yi wa kaina alƙawarin shi ne ɓarna ta ƙarshe da za su yi matuƙar ina numfashi in sha allah!” jinjina kai malam ya yi ya ce. “na san taurin ranka da nacinka akan duk abin da ka saka a gaba tun kana yaro, amma ka sani ba komai ba ne ake son ganin baya kuma ake gani ba, wani abun gobara ne daga kogi da maganinsa sai dai allah kawai, ba mu da sanin inda mutanen nan suke, ba ma sanin lokacin da suke aikata ɓarnarsu, ba mu da ƙarfin iko kamar su, manyan ƙasa ne da masu mulki da masu madafan iko da masu dukiyar da ba mai iya ja da su, kana kallon dai yadda duk malamin da ya fito ya yi magana ko yaya take a kansu suke sai sun yi masa kisan gilla, kai ma na san labarinka da ƙudurinka ya daɗe da zuwa gare su, don ciwon da mahaifinka yake yi na daɗe ina hasashen daga gare su ne.”

“duk da haka ba zan karaya ba malam, kai kaɗai ne hope ne, ka ba ni ƙwarin gwiwa kawai tare da ci gaba da yi mini addu’a don allah.”

takawa malam ya yi ya dafa kafaɗarsa tare da sakin murmushi, cike da ƙarfin zuciya ya ce. “in sha allahu ina tare da kai a kodayaushe juraij! ina ji a jikina wannan jajircewar taka za ta taka muhimmiyar rawa a cikin al’umma wajen inganta musu rayuwa, fatan nasara da sa’a murucina, ubangiji yana tare da kai gaskiya, in sha allah zai ba ka kariya da sa’a akan waɗannan azzaluman.” sai a lokacin fuskarsa ta ɗan saki, ya saki ajiyar zuciya a hankali ya ce. “na gode.” daga haka ya yi masa sallama ya tafi bayan malam ya yi masa tayin tsayawa ya karya ya ce masa sauri yake ana jiran shi a office.

tagumi malam ya rafka yana saƙa abubuwa da dama a cikin ransa na tsoron kar allura ta tono garma.

*note: ga masu cewa ba su gane ba saboda shimfiɗar da na saki tun a farko, labarin mairo da su ma’u shi ma a cikin bara a kufai yake, za mu koma gare shi, shi labari kamar tsani yake kowanne da matattakalar da ake hawa kafin a je ƙarshe, tun lokacin na faɗa doguwar tafiya ce mai ɗauke da labarin mutane daban-daban, ahayan; juraij; saudat da haseenah, kowa da labarin tasa rayuwar da ƙaddararsa, har yanzu sharar fage muke yi, amma da sannu za ku gane komai in sha allah!*

*09047871750*

*zeey kumurya ✍🏻*

About the author

mynovels

Leave a Comment