Boyon Sirri Hausa Novel Complete
ƁOYON SIRRI*
*Oum Hairan*
*1-2*
“Ina zamu samu budurwa da bata taɓa tsayawa da namiji ba Waziri?” Kalmar da ta fito daga Bakin Mai martaba Dikko kenan wanda ke zaune bisa wani gado na alfarma ya zuro kyawawan ƙafafunsa ƙasa ya azasu bisa wani farin tumtum, wani Gwauron numfashi Waziriy Ya sauke yace “Allah ya ƙara maka lafiya baxan ce ga inda za’a samu ba amma dole mu tashi tsaye mu bincika saidai wannan aikin yana buƙatar sirri kuma yana buƙatar shiga cikin talakawa domin jin abinda suke cewa ta wannan hanyar zamu iya gano abinda muke nema” fuskarsa babu wata alama ta jin daɗi ko akasin haka yace “Idan har zan samu biyan buƙata zan iya yin komai Waziriy Saidai kiyaye siffar da Bokan ya fasalta mana wajibi ne sannan kiyaye tonuwar asirin ma wajibi ne”
Jinjina kai Waziriy yayi yace “Wannan duk me sauƙi ne Indai Umma zata samu lafiya zamuyi komai” da wannan ya sallami Waziriy shi kuma ya tashi ya shiga bathroom ya sakarwa kansa ruwa zuciyarsa na cike da ƙuna, baitaɓa kallon sarauta a matsayin wani abu da zai zame masa barazana ga kwanciyar hankalinsa da farin cikinsa, Lumshe idanunsa yayi tabbas zuwa yanzu yana buƙatar Abokiyar rayuwa wadda zasu rayu har abada wacce bazata tafi ta barsa ba saidai Ya Zaiyi da waɗannan sharruɗan da aka gindaya masa kafin kaiwa ga wannan matakin Mace biyar ya aura a cikin shekarar da bata wuce biyu ba dukkansu babu wacce ya samu damar keɓewa da ita sai guda ɗaya tak wato Nanah a ranar da yayi kwanan amarci da Nanah a ranar ta mutu kuma a ranar Mahaifiyarsa umma ta kamu da matsanancin ciwon haukan da yanzu haka ko ganinta ba’a bari ayi kullum tana ɗaure cikin sarƙa.
Shafa mararsa yayi cikin damuwa ya ɗauki towel ya naɗe ruwan dake jikinsa ya shanya ya ɗaura wani a ƙugunsa ya fito ya zauna saman stool yana kallon kansa, babu ta inda Allah ya rage shi sai ta fannin iyali to wai shi Meye matsalarsa? Meyasa kowa cikin yan uwansa yayi aure yana tare da iyalansa shi kuma aure yake neman gagararsa? Wanne irin sirri ne ɓoyayye game da rayuwarsa da duk wajen me maganin da aka turashi yake sanar dashi akwai wani ɓoyon sirri da akayi akan rayuwarsa wanda bazai taɓa kwancewa ba har sai ranar da wata gimgimemiyar ƙaddara ta faɗo rayuwarsa, shin wacce ƙaddara ce wannan?”
Lumshe idanunsa yayi yana sharce ruwa daga sumarsa ya mike da sauri ya sanya doguwar riga ya ɗauki wani rawani irin nasu na buzaye ya naɗe kansa ya dauki takobi ya rataya a bayansa da salkar ruwa ya sanya takalmin fata saboda yau ya kudurce Zaiyi tafiya me tsayi a ƙafarsa domin haɗuwa da Ƙaddararsa…….
Bayason bi ta hanyar da za’a Ganshi saboda haka ya fita ta ɓoyayyar hanyar sirri ta gidan wacce babu wanda yasan da ita sai wanda yake amsa sunan sarki a wannan babbar Masarauta, tafiya yayi me tsayi a wannan hanya kafin ya fito bayan gidan ya raɓa bango ya wucce kamar wani haske ya juya ya kalli gefe da gefensa bai tsinci kowa ba don haka yaci gaba da tafiya kamar wani talakan bafatake a ƙasa cikin rana da sahara tafiya ta tsayin klomiters kafin ya hango wani raƙumi yana jan ruwa a wata rijiya ya sauke ajiyar zuciya domin yasan ya tunkari inda mutane suke, ya gaji sosai dalilin da ya sanyashi ƙara sauri ya isa ga inda rijiyar take tun daga nesa zaratan samarin suka zare takubban su dake cikin kube suna jiran ƙarasowarsa…….
: *💔ƁOYON SIRRI💔*
*Oum Hairan*
*page 3-4*
Cikin taku irin na wanda ya gaji da tafiya Dikko ya isa ga wa’yannan matasan da suke jan ruwa a rijiya ya daga musu hannu tare da gaishesu cikin Harshen buzanci abinda yasa dukkan suka maida takubbansu suka fuskance shi ya fara bin garin da kallo yar ƙaramar ruga ce kamar ta Fulanin tashi ya sauke numfashi tare da cewa “Ni baƙone matafiyi daga Arlit Nayi zango me tsayi babu ruwa babu abinci babu wajen sauka ina buƙatar a kaini masauki domin na huta” wani cikin matasan yace “Kayya Samari mu wannan ruga muna da tsoron mutumen birni saboda basuda amana kuma suna zuwa su amre mamu kyawawan yammata su Barmu muna cika Buje da kaya babu wajen sakawa da wannan muka daina barin baƙo ya sauka a Rugarmu gaskiya” cikin tausayin kansa da wannan tafiya daya kwararo ta kusan klomiters yace “Ba ɗaya da zai faru daga gareni Ni Nazo ne kuma zan wucce” fir waɗannan samari sukaƙi aminta da su bawa Dikko masauki har Saida suka fuskanci gskyrsa sannan suka ce akwai gidan Sarkin rugar Mal Buba duk garin shine yake da wajen sauke baƙi shima saboda masu zuwa neman magani gareshi ne” ji Dikko yayi kansa ya sara da jin an ambaci sunan daya jima yana ji ana ambata masa a wajen bokayen daya jima yana bibiya don neman sauƙi daga lalurarsa.
Da sauri yace “Ku kaini na nemi izinin zama dashi daga yau zuwa gobe” wani cikin samarin ne ya jagoranceshi suna tafe yace masa “Saidai akwai wata doka ɗaya da zuwa gidan Mal Buba yana da ɗiyarsa guda ɗaya me suna Mairama A bisa sharaɗin shiga gidansa ba’a kallon Mairama sau biyu duk kallon da zakayi mata ka kalleta a kallo ɗaya sannan ba’a magana da Mairama Ko mu da muke cikin garin nan bamu taɓa ganin fuskar Mairamah ba kullum cikin sanya niƙabi take sannan bata taɓa magana da wani namiji ba a rayuwarta” Wani Gwauron numfashi Dikko yayi Yanajin wata nutsuwa na kwarararsa yace “Meyesa ba’a magana da ita kuma ba’a ganin fuskar ta?” murmushi Samarin yayi yace “To mudai bamu sani ba Amma Mal Mudi me ƙarangiya yace “Akwai wata ƙaddara da zata faɗawa Mairamah da Ubanta Mal Buba yake kokarin kareta daga ita wannan dalilin yasa ya kulle mata bakinta kuma yake ɓoye mata fuskarta A hasashen Mal Moddi ya tabbatar da cewa duk lokacin da Bakin Mairamah ya buɗe to wannan Ƙaddarar tana gaf da faruwa koma ta faru” Shiru Dikko yayi yana tunani wasu kalmomi da Bokan daya bashi aikin daya fito dashi ya faɗa masa lokacin da yake ce masa shi Baisan inda zai nemi budurwar da bata taɓa magana da namiji ba kuma Baisan inda zai nemi wannan siffar daya fasalta masa ba, A lokacin Bokan Tsauni yayi dariya yace masa “Yaro ko a wahale ko a gajiye kuma ko a jikkace sai kaje inda wannan yarinya take domin bata kasance budurwa kawai ba ta kasance wata ɓangare na hargitsin rayuwarka tabbas sai ka kwanta da wannan yarinyar ko kana cikin hayyaci ko baka cikin hayyaci ko kana so ko bakaso wannan a rubuce yake kuma bazai zama kwanciyar sunnah ba kuma bayan kwanciyar wasu manyan kaddarori zasu faru da zasu iya tafiya da rayuka da yawa amma dai tabbas buƙatarka zata biya ta samun lafiyar mahaifiyarka kuma zakayi aure ka kwanta da Matarka ku rayuwa cikin aminci saidai kuma bazan iya faɗa maka halin da zaka kasance ba bayan cikar wannan muradan tabbas su sun ɓuya sunƙi bayyanuwa gareni” ………
: *👑ƁOYON SIRRI👑*
*_(Royalty & Romantics)_*
*Oum Hairan*
*Free page 5-6*
Girgiza kansa yayi da sauri yana tuna wannan kalamai gabansa na faɗuwa tabbas akan mulkinsa da samun lafiyar mahaifiyarsa da kuma tabbatar kwanciyar hankalinsa babu abinda bazai iya yi ba da wannan samarin dake masa Rakiya ya nuna masa gidan daga nesa yace “To Samari nan shine gidan Mal Buba Ka sallama masa in yana ciki zai fito yayi maka gurbi” da wannan Dikko ya isa kofar gidan yayi sallama ta cikin gidan yajiyo wata zazzaƙar murya ta amsa masa tare da cewa dashi Ana zuwa, Babu jimawa Mallam Bubah ya fito sanye da kayansa na buzaye yasha naɗi na iya idanunsa kawai ake gani ya miƙa masa hannu suka gaisa cikin girmamawa yayi masa bayanin cewa shi baƙo ne wanda yazo daga wani guri me nisa yazo wuccewa ne dare yayi masa yake neman masauki sannan kuma yaji labarin yana duba marasa lafiya wannan ya ƙara masa ƙarfin gwiwar zuwa” mirmushi Mal Buba yayi yace “Ba shakka Samari shigo akwai masauki” gaba yayi yana biye dashi suka isa ga wata bukka suka duƙa suka shiga gurin zama Mallam Buba ya nunawa Dikko ya fice bai jima ba ya dawo ɗauke da wani kwano me kyau ya ajiye a gaban Dikko ya zauna suka ƙara gaisawa yana masa tambayoyi daidai lokacin Mairamah ta bankaɗo labulen ta shigo fuskarta naɗe cikin naɗi irin na buzaye babu komai a waje sai iyakar Idanunta Kafa mata Idanu Dikko yayi ƙirjinsa ya buga da ƙarfi ganin fuskar dake cikin naɗin ta bayyana gareshi kamar yanda bokan Tsauni ya ya sanar dashi babu ko shakka wannan ita ce yarinyar da aka umarce shi da kwanciya da ita, wani ajiyar zuciya ta sauke ta duƙa cikin ladabi ta aje ƙwaryan Damammiyar furar da Mahaifinta yayi mata umarnin kawowa da kuma ruwa ta tashi ta fice har yanzu idanun Dikko na satar Kallonta, Muryar Mallam Buba ta katseshi da cewa “Kaci abinci ka huta zan ɗan fita zuwa Masallaci” jinjina kai yayi ya ja ƙwaryar furar ya fara sha tare da Lumshe idanunsa tunda yake bai taɓa jin fura me daɗin wannan ba”
Yasha sosai amma rabin hankalinsa yana kan yanda Zaiyi ya cika ƙudurin daya baro dashi gida shin ta wacce hanya zaisamu yayi abinda ya kawo shi? sauri yayi ya gama yayi alwala ya fito domin tafiya masallaci ya itama Mairamah fitowa tayi ta juye ruwan data ɗora a murhu ta shiga bayi tayi wanka ta fito ta koma dakinta ta zauna domin babu sallah a yau ɗinta sai gobe take tunanin zata fara sallah hakan ya bata damar daukar wani littafin addini tana dubawa taji shigowar Mal Buba da baƙonsa tayi maza ta dauki niƙab ɗinta ta sanya duk da tasan Mal ko zai leƙota sai anjima hakan yasa ta gyara mashimfiɗinta tayi addu’a ta kashe fitilar aci balbal ta kwanta baccinta na kwanciyar hankali ya ɗauke ta, da asuba Mal ya tasheta ta fito ta wanke Idanunta ta shirya cikin dogon Hijjab har ƙasa ta ɗora niƙab ta fito domin zuwa makarantar da suke yi ita ke koyar da yammata da matan aure na wannan ƙauye nasu Yau da shauƙi take karatun yau innarta zata dawo daga Damagaran tasan duk inda suke sunyi nisa yanzu da tafiya, inda suke karatun babu maza amma hakan bai sa mal Buba ya amincewa Mairamah cire shingen fuskarta ba basu tashi ba sai tara na rana duk mazajen garin sun tafi gona shima Mal Buba yana komawa gida yayi shiri don tafiya gonar ya ishe Dikko kwance yana bacci ya fice ya isa dakin Mairamah yace in ta haɗa abin karyawa ta kaiwa bako shi zaije gona” fatan nasara tayi masa ya fita ita kuma ta fito kamar yanda dokar gidan take sanye da Hijjab nata ta shiga madafi ta haɗa abin karin kumallo daidai nasu na talakawa ta ɗauki na bakon ta isa ƙofar ɗakin tayi sallama daga ciki aka amsa mata ta buɗa labulen ta shiga ta duƙa ta ajiye tare da gaisheshi ta mike domin fita yayi gyaran murya ta tsaya Cak tana jiran taji me zaice ya tashi yana gyara zaman takobinsa yace “Yaushe zaki fara cire wannan shingen da kike ɓoyewa mutane fuskarki dashi Maryam?” gabanta ne ya faɗi ta juyo da sauri zatayi magana yayi maza yace “Ba dole bane amma rayuwa da ɓoye baiwar da Allah yayi Miki akwai wahala shin sai yaushe za’a baki damar fallasa sirrinki ga abokan rayuwarki?”
: *👑ƁOYON SIRRI👑*
*_(Royalty & Romantics)_*
*Oum Hairan*
*Free page 7-8*
Da sauri ta fice daga ɗakin gabanta na faɗuwa Badan ta rasa abin faɗa ga wannan baƙo ba sai don Batada ikon magana dashi bayan Gaisuwa da wannan ta shiga dakinta ta zauna ta tusa abincin data girka a gaba tana turawa yana tuna kalmar baƙon a ranta tana tambayar kanta meye yasa shima fuskarsa take a ɓoye tunda yazo? ɗiban kunun gyaɗar tayi ta kai bakinta ta rufe ta ajiye ta koma ta kwanta baccin safenta data saba bata san lokaci ya tafi ba saida taji ana tashinta ta tashi da ambaton sunan Allah ta buɗe Idanunta kan Mahaifiyarta tayi tsalle ta Rungumeta tana cewa “Nayi kewarki Innatu nayi fama da kaɗaici saboda rashinki ashe dai da gaske abinda fataken burtali suka faɗine ne yau kina tahe lale Innatu ya su gwaggo yasu yafendi?” zama Innatu tayi tana ƙara kallon ɗiyar Tata tace “Kowa yana lafiya hayyan suna Gaisuwa a gareki Jibir ma yace a gaisoki yace zaizo ku tamtamna a tsaida maganar amre” fara’ar fuskar Mairamah ce ta ɗauke gabadaya ta Turo baki tana cewa “Nifa Innatu idan Jibir be bari ba zai rasa damarsa ki hwaɗi masa ya hita ijiyata ya huta ni ba sa’ar amrensa bace”
Daƙuwa Innatu tayi mata tace “Ungo nan ja’ira yo saki a gaba zamuyi muna kallo kin isa amfani ai dole kitai ki amfanawa Mijinki Kema ki samar da halwarki” tashi tayi tana ƙunƙuni ta saki mayanin fuskarta ta fice a gidan dama in da sabo Innatu ta saba ganin wannan a wajen ɗiyar Tata Indai za’ayi maganar aure yanzu zata birkice mata, batayi yunƙurin tsayar da ita ba tasan bai wuce gidansu Jaru ƙawarta zata ba.
Murmushi Innatu tayi ta fara tattare kayan data gani a dakin ta gyattashi ta fito ta fara sharar tsakar gidan ta share shi tsaf sai yanzu ne ma tasan akwai baƙo a gidan mal yayi sauka kenan shima fitowar Dikko ne cikin shirinsa na zagaya gari ya rusuna da ladabinsa irin na kare ya gaisheta ta amsa tana cewa dashi sannu samari kaji” fita yayi yana mamakin zallar kyawu na wannan ahlin yana tafe tunaninsa na rabuwa biyu zuciyarsa ta imani tana faɗa masa wannan abin da yake shirin aikatawa ba ƙaramin cin amana bane kuma kuskure ne me girma wata ɓangare kuma tana tunzurashi tare da faɗa masa to menene ma don yayi amfani da ita sau ɗaya tak tabbas ita ce domin jiya yayi magana da Bokan Tsauni ya tabbatar masa kar ya sake ya bar wannan ƙauye ba tare da yayi amfani da wannan yarinya ba idan kuwa yayi gangancin haka to duk wani burinsa zai rushe har abada ne, yayi tafiya me tsayi kafin su haɗu da Waziree suka kalli juna sosai Dikko ya kalli dukkan kusurwar dake Saharar yace “Na samu wata yarinya da tayi daidai da abinda muke nema saidai zuciyata ta karye” nan ya kwashe dukkan labarin Mairamah da uwayenta ya sanar dashi, sukayi shiru na dogon lokaci kafin Waziri ya kalli Dikko yace masa “Ka kawar da tausayin da yake hararo zuciyarka ka turmushe wannan yarinyar a cikin daren nan Ranka ya daɗe bamu da lokaci idan komai ya kammala akwai damar tuba idan kuma kaƙi cika sharaɗin wannan aiki akwai tarin damuwowi” dago manyan idanunsa da izza da miskilanci ya shanye yayi ya zuba su kan Waziri yace “Bantaba aikata zina ba tun Jiya nake tunanin Meyasa sai nayi zina kuma da ɗiya me tsarki sannan buruka na zasu cika?” dariya Waziri yayi yace “Wani kisa zaace yayi kafin burukansa su cika kai iya zinar ce kawai don Allah ga kayan aikinka wannan layar ka kasance cikin bata kariya kuma duk yanda za’ayi karkayi yunkurin ci musu ƴa a gidansu gidansu akwai tsaro kasan yanda zaka yi ka fakaici fitarta kayi amfani da damar ka haurata kana gamawa ka matsa wannan layar zaka ganka a masarautarka”
*👑ƁOYON SIRRI👑*
*_(Royalty & Romantics)_*
*Oum Hairan*
*Free page 9-10*
Damƙe layar yayi zuciyarsa na kai kawo a ƙirjinsa ya mike yace “Ka kula da komai bansan adadin lokacin da zan ɗauka wajen jiran dama ba amma lallai zanyi bakin ƙoƙari na naga bata kufcemin ba” da wannan ya juya ya nufi hanyar da zata maidashi Gurbin Mal Buba ya isheshi a ƙofar gida suna karatu ya zauna a wajen shima ya fara daukar karatun Saida aka tashi sannan Mal Buba ya dubeshi yace “Samari zaka ɗauki lokaci ne anan?” sunkuyar da kai yayi yana kurɓar shayinsu na buzaye yace “Zan iya tafiya kowanne lokaci akwai abokan tafiya ta da nake jira na sanar dasu su isheni a nan” jinjina kai mal Buba yayi yace “Nima zanyi wata tafiya gobe idan Allah ya tashemu da rayuwa zanje wajen wani malamina dake Katsinan Nigeria akan matsalar Maryama” Da sauri ya dubeshi yace “Meye matsalarta?” Murmushi Mal Buba yayi yace “Tun tana ƙarama Allah ya jarabceta da ciwon gudun maza ko a lokacin ƙuruciyarta bata yarda da abokai maza abin ya zarme mata har girmanta bata amincewa ko kalma ta haɗata da namiji bayan Gaisuwa idan kuwa aka sanar Dani akace ana sonta to ranar bazamuyi bacci ba kwana zatayi tana iskokai abin tana girma abin yana ƙara tsanani a wannan lokacin tana iya daukan makami ta nufi duk wanda yace yana sonta shine dalilin da yasa dukkan ƙawayenta anyi masu amre wasu harda yaransu ita kuwa ko zance baayi mutane sunata zunɗe na a gari suna kallon kamar akwai nufi a cikin wannan abu wanda Allah ne shaida nafi kowa son naga Maryamu tayi amre”
Jinjina kai Dikko yake yi gabansa na faɗuwa da abinda yake zuwar masa saidai yasan ko giyar wake yasha bazai fara ba shi yafi Maryamu hatsari domin shi murus duk wata mace data shigo rayuwarsa take mutuwa har lahira. Da wannan suka tashi suka shiga ciki yau ma da Innatu ta gama girki Mairamah ce ta kaiwa baƙo tana kaiwa bata tsaya komi ba ta fito da sauri ya bita da kallo yana ƙissima yan lokutan da suka rage ya cimma muradinsa a kanta,
Bai iya cin abincin ba saboda tunanin abinda ke gabansa haka sukayi sallama da Mal Buba ya tafi bayan ya raka mal ya dawo ne ya ishe Innatu a tsakar gida tana shara yayi mata sannu tare da tambayar ta Mairamah ta sanar dashi ta tafi gonar Baffanta don cire ciyawa ya numfasa a gareshi wannan dama ce saidai Baisan gonar ba, amma bazai sare ba zai bincika fita yayi cikin samari daiɗaiku da basu wuce gona ba ya zauna yana tsintar abubuwa sai yamma liƙis sannan Mairamah ta dawo daga nesa ya hango ta tana tafe cikin takunta na nutsuwa yanzu ma fuskarta naɗe take da mayafi shikam ya ƙosa yaga wannan fuska ya kuma san dalilin da yasa ake rufe ta taɓe baki yayi yana kallon agogonshi ya gama daidaita saarsa yau ko zai rasa rayuwarsa sai ya cimma burinsa bata ƙaraso ba ya koma gida itama data ƙaraso bata saurareshi ba ta debi ruwa a madafi ta shiga wanka Innatu batanan ta shiga maƙota karɓo kuɓewar kaɗi hakan ya bawa Dikko sa’ar zuba wani magani cikin ruwan miyar yayi maza ya koma dakinsa ya zauna.
Aka gama tuwo aka malmale harda yanka zabo aka burge a miya aka kaiwa Baƙo nasa yau Innatu da kanta takai masa saboda ta lura Mairamah Batada kuzari tunaninta ko yunwa takeji, ta zubo musu abincin ta dauko man shanu da yajin daddawa ta zuba musu tayi mata magana ta tashi ta sauko sukayi Bismillah suka fara cin tuwon Innatu na lura da ɗiyat tata yinin yau gabaɗaya babu walwalarta suna tsaka da cin abincin Innatu tace “Mairamah akwai abinda ke damunki ne?” ɗagowa tayi ta kalli uwarta Idanunta ya ciko da ƙwalla tace “Bansan meye zai faru Dani ba amma tun daren jiya nake wasu mugayen mafarkai yau kuma na tashi da faɗuwar gaba sannan Anamin kuwwa a kunne ana faɗamin wani abu zai faru Dani da bazan iya guje masa ba” sanin halin Ɗiyar Tata yasa bata ɗauka abin serious ba tace “Insha Allahu Khairan” tana maganar tana miƙa tare da Hamma tace “Ni Kinga bacci ma Nakeji da wuri tuwon nan da naci ya kashemin jiki” itama Hamma tayi tace “Nima Naji kaina yayimin nauyi ga gajiyar gona bacci zanyi da wuri Innatu” wani rubutu ta dauko ta ta dafa a tukunyar ƙasa ta bata tace “Ki shanye wannan sai ki kwanta” karɓa tayi ta shanye ta haye yar katifar tasu ta yayi ta naɗe da bargo tana addu’a bata ƙarasa ba wani bacci me nauyi ya ɗauketa itama Innatu a inda tayi shafa’i da wuturi baccin ya ɗauketa me mugun nauyi……….l


