Gidan Harka Mata Zallah WhatsApp Group
*GA INDA JOSEPH (JOHN) YA FARA HADUWA DA YASMINE, HADUWAR DATA ZAMA TA ƘADDARA WANDA WANI SANADI YA ZO YA GITTA HAKAN BAYAN YA AURETA MUTUWA TA RABA TSAKANI, SAI YA HAƊU DA HASALIN HASKEN NASA WATO *MALAMA HAFSAT MUHAMMAD ALIYU* (JANNEERH) shi kuma ya kira da *JANET*
Wani kalan jan birki yay ƙoƙarin yi amma ina hakan na neman gagaransa kasancewar an daɗe ba’a haɗu ba, don ba a barinsa yin driving da kansa koda kuwa zuwa ƙofar gida ne. A wani irin zuciye yajuya kan motar yana tsaida ita, amma duk da hakan seda car ɗin ta bugi matashiyar buduryar dake sanye cikin shijab kalan ash colour har ƙass.Farar ƙafarsa dake cikin baƙin takalminsa me shegen ƙyau ce ta fara bayyana, kafin blue dogon wandon outpit ɗin dake jikinsa. A kuma zafafe ya fito don baiga hurimin ubanda ya kawo ta saman kwaltan haka ba.
Ita kuwa wacce aka bige ɗin kamar ba zata juyo ba, sai kuma zuciyarta ta bata shawarar juyawa taga wane shahararran ƙwallan mara imanine da mutuncin ne haka .da ya nemi kaɗe ta. Idasa fitowar yay yana ƙarasowa har inda take duƙe da jikin motor ɗin. A gabanta ya tsaya yana hucin ɓacin rai shegen tsayinsa harna ƙaruwa yana ganin tsayin kansa da nata ba ɗaya ba, duk da kasancewar a duƙen take har yanzun kuwa. ♡ Soft fararen hannuwansa masu aji ya sanya kai tsaye yana kai hannun da nufin wurgar da ita daga jikin motar nashi. Se kuma aka sami akasi hannunsa kawai ya sauka saman shimar nata yana cilli dashi. Wani kalan waro manyan idanunta tay ganin an fusge dogon shimar ɗin dake jikin ta, saur̃in sáke ƙanƙame Alqur’anin dake rungume a hannunta tay, Zuciyarta na wani kalan tafasan ɓacin rai har tana jin yadda bugun ta ke fita fatt² haka da mugun ƙarfin gaske. Se kuma gaba ɗayanta ta juyo a fusace kai tsaye tana ɗauke wannan kyakykyawar fuskan nashi da wani lafiyayyen mari ta ɓangaren dama kana again ta sake juyowa ta kuma wanke shi da woni ta ɓangaren hagu….
♡
“Shin kai babu zuciyn a ƙirjinka ne hala!? kokuwa kana tunani da zuciyar takane bada ƙwaƙwalwa ba?.Amma kaikam duk ahalunka babu masu imani kuma bakusan menene daraja da muhimmancin ƴa mace ba?” Matashiyar budurwarn ta faɗi fuskanta ɗauke da mugun ɓacin rai, Kana ta bishi da kallo tun daga sama har ƙasa, wasu shegun riga da wando ne a jikinsa outpit kalan koɗaɗɗun nan masu ya ga² Se kuma sarƙan Cross na diamond ɗin dake saƙale a wuyansa, se bariman warin diamond ɗayan dake manne a kunnensa, se wani shegen kalan ɗan iskan askin dake kansa irin me kibiyar nan, ta ƙasa kuma ya tari gashin kan nasa ya tufke shi. iyaka su kaɗai sun isa tabbatar maka da cewan Ehhh lallai wannan ɗin ba musulmi bane Christian ne. Da wani kalan wulaƙantaccen kallo ta bishi kana taci gaba da furta. “Koda yake alamu sun gama nuna cewar musulumcinma kai baka da!, don da dukkan alamu arziƙinsa ma baka samu ba bare kuma har aje ga sanin daraja ɗan Adam. Amma duk da haka Kai mutum ne wadda ko acikin Christian ɗin ma kai baka da daraja daga kallonka na tabbata haka, duk iskancin da irinku masu addininku suke dashi basa taɓa wulaƙanta ɗan Adam irin haka”
A nutse ya janye idanuwansa daga kallonta yana rasa ma ta inda wanna ƴar filic ɗin yarinyarn ta sama kwarin gwiwan yi may maganganu har haka? Duk da kasancewar motsin da bakinta kaɗai keyi ne ya tabbatar may da cewan masifa take may bawai don yasan abinda take cewan ba kuwa.
Kallonta yake daga sama har ƙasa ta cikin eye glasess ɗin dake sanye a idonsa, ba tare da yama nuna alamar ya fahimta yaren da take maganar da shiba, ko nuna yama ji zafin marin data may ba ya raɓata zai wuce abinsa, saurin sake shan gabansa tay ganin kamar duk bayajin hausarn da tay maganan dashi, hakan ne ya sanya kai tsaye ta juye harshe zuwa English ta furta “To dan ma kaji Wllh² baka buge banza ba!, tun da kai baka da cikakken imani da kuma tausayi to kuwa wllh se na nuna maka hasalin yadda ake mutum ta mace da kuma darajantata!”
Wani kalan ɗan ware mata manyan idanunsa yay tare da ambatar “what? Hhhhh this girl is very stubborn and stopid shutter. stopid girl wannan wani kalan shashancine kodai ke baki da class ne? ko da yake naga ke mahaukaciyane ok you are deaf”
Yay maganan yana zare eye glasses ɗin dake sanye a cikin idonsa, Daidai da loƙacin da niƙab ɗin dake sakaye da fuskanta iska me ƙarfin dake kaɗawa ta yayeshi sama, daga saman kyakykyawan farar fuskarta, wani irin bugawa dummmm gabansa yay.
Don haɗewan da idanuwasu sukai wuri guda,Wanda wani kalan launinsu da hasken kwalliyar halittar da idanuwanta suka yi may tozali. Haka yaga gilmawar fararen idanuwan ta tamkar hasken farar zinariya mai ɗauke da tambarin Alkuki acikin ragayar fitilar kwai. Wani kalan ɗan dukan kansa yay yana tsurama kyawawan laɓɓanta da kai tsaye yake iya tantace kalan laushinsu. A mugun fusace ta sake fidda zara zaran yatsun ta biyar da ALLAH ya halatta mata ta sake ɗauke kyakykyawar fuskan shi da wani kalan arnen bahagon mari me gigita duniyar wanda aka yima shi.
A kuma daidai loƙacin ne bodyguard nashi da madame Victoria Osteen ta balbalesu da masifan barin shi fitan da yay shi kaɗai. Domin ba ƙaramin Mahaukacin S0 take ma Johseph ɗin ba, Ba tare da yasan da wanzuwar su wurin ba kattin arnan majiya ƙarfin kawai suka ma matashiyar budurwarn ƙawanya aka tamkar zasu cinye ta ɗan ya, Da wani irin mugun kallon baku da hankali ya shiga binsu dashi ɗaya bayan ɗayan.
Se kuma ko wannensu ya shiga yin baya da baya a mugun tsorace don sune kawai suka san ainihin ko wanene Johseph ɗin.
Ita kuwa wani irin nauyi ƙahon zuciyarta ya mata tamkar za ta faso ƙirjina ta fito haka taji ƙirjinta ya danne.A karo na biyu a kuma kausashe ta sake furta. “Kar ka yadda ko a rashin sani ne wannan ƙazamin hannun naka ya sake yinƙurin taɓa koda hijjabin jiki nane balle hannuwana Malam” tai maganar tana ƙara sa fusgo numfashinta da ƙyar da suke kokawa da juna wajen barazanar barin jikinta da yake shirin yi wajen fita baki ɗaya.
Wani kalan taɓune fuska yayi yana tsurama kyawawan laɓɓanta ido. Wanda suka yi matuƙar burgeshi sosai wajen yadda take balbala bala’in masifan, hakan ya sanya ba tare da tunanin komai ba ko dede ze aikata ko akasin hakan babu zata babu tsammani kawai taji sauƙar lisp nashi saman nata. A wani irin daskare ta tsaya chak da shirin tafiyan da take ƙoƙarin yi tamkar wacce akayi freezing nata. dan ko iya juyowa ba tayi ba balle tay tunanin meke faruwa da ita, Wani kalan rumtse idanunta tayi for the moment tana sauraran bugun zuciyarta, sharrr kuma hawayen tashin hankali suka wanke samar kyakkyawar fuskarta na tsantsan tashin hankali.
Shi kuwa John samm be san abinda ya aikata a gareta me girma bane duk da kasancewar dama samm can shiba Mutum bane ma’abocin irin hakan ko da kuwa da yake ba Musulmi ba. Amma samm hakan tsentseni yake bashi kuma da ƙazantane yake danganta hakan.
Amma se gashi yau da kansa shi Johseph Mr jef deefer ya aikata hakan ga wata? Watan ma Hausa gurl, shi ne ma sanadiyyar da har su Micheal suka janye shi daga gare ta be farga da hakan fa. Don ji yay Duniyar na juya masa yana jin tamkar shi kansa ba shi bane haka yake binsu, suna daɗa janshi ganinsa na ƙare nesa da ita har zuwa gaban Manyan motocin da suka zo dasu wajen guda biyar. Chark ya ja ya tsaya da shirin shiga car ɗin da yake yi, sakamakon sauƙar wani abu me nauyi da yaji a tsakiyar gadon bayansa. Su kuwa kattin arnan nan a 370 sukayi kanta da niyar su dagargaza ko wanne ƙashi da tsoka na jikinta. A wannan karon ma dakatar dasu yay ta hanyar ɗaga musu hannu. Cikin mugun azabar daya dirar masa lokaci guda ya juyo ga kallonta daidai tana shigewa cikin jibgegiyar car ɗin da ta taho ɗaukanta, Ba don ya soba don dole ya faɗa cikin car ɗin, yaransu najan motocin da shegen gudu na tsiya don sosai sukaji haushin hana musu raga raga da naman yarinyan da yay. Hakan yasa cikin mugun fushi ɗaya daga cikin yaran suka kira Madam Victoria Osteen tun kamin su Isa ga gidan suka sanar mata cewan wata Hausa girl ta jima John rauni.
A silo tarin motocin nasu suka lula zuwa haɗaɗɗiyar unguwar Banana Island, a katon get ɗin makeken gidansu sukayi Parking car nasu. Wani kalan mahaukacin hong suka shiga do ƙawa. Kai tsaye kutsa kansu cikin wargajejen katon get ɗin gidan sukai loƙacin da aka gama wangale musu shi. Baki ɗaya jama’ar gidan tun daga kan yaransu har manya suna kammale a ƙofar parlour’n shigowa, kasancewar Micheal yayi woya dasu kan cewar ai Johseph ɗin yayi faɗa da wata Hausa gurl ne, harma ta jimay ciwo, jin ambatar iyaka ciwon ne ya tashi duka hankalin madame itama tana tasar hankalin duk jama’ar gidan. Jin jirin tsaiwar motocin sune ya sanya su yowa Parking car ɗin dukansu barin ma jikin Madam Victoria osteen da har wani rawa² yake yi. Tun kamin ya ida fitowa ta shiga motar tana fitowa dashi kusan rungume a jikinta dukansa, duk ta cewan girman jikin da yake da amma samm ita bata gani idanunta sun rufe akan ƙaunar Shalelen ɗan nata.
A hankali a kuma nutse suke tafiya yana jingine da jikinta suke takowa zuwa cikin parlour’n. Dab da inda Papan shi yake zaune Madam Victoria ta zaunar da Johseph ɗin, itama tana zama gefensa suka sanya shi tsaƙiyansu. Sake tsumewayi yayi wuri guda jin yadda duk iyayen nashi suka bi suka ruɗe da ɗan bugun da besan ko miye ba yarin yan ta buga masa. A wani irin hankali yaji zuciyarsa tana narkewa tuno da waɗan nan mayun idon da bai taɓa ganin irin suba. A bayyane ya shiga furta.
“Meri har saash me tu ♥️_
_meri har Khushi me tu tere bina jindg_
_meri nhi kyu ki Meri jindagi hai tu ♥️😘 I love you, my sweet dreams baby_ As much ASI love you _
_I’ve finally accepted that it’s time to let you go_
_you will always hold a place in my heart ♥️ _
_but you no longer belong in my gurl _ more thant I accepted Mee_”
Baki ɗaya suka saki baki suna kallonshi cikin yanayi na ɗan tsoro. Papa ne ya sake sipping hannuwansa ya ɗago kan Johseph ɗin tare da furta.
“John what the problems?”
Kansa ya girgiza se kuma ya kamo hannun papa’n yana ɗorawa saitin Heart nashi tare da furta. “Nan ciwo kawai papah nan” yay maganan yana sake tura hannun paah cikin buɗaɗɗiyar rigarsa data buɗe kusan rabinta. Tashi tsaye madame Victoria Osteen tay tare da tafa hannuwanta tana furta “Ohhhh Lord I pray for.. Jesus jesu hoooooh John hooooh john, darling don me zakabar ƙanƙanin yaro kamar John fita shi kaɗai? Amma dai ai kasan bana barin shi koda yin driving ne ko? Bare fita shi dayan sa! Oh Jesus……
Mr jef deefer da madame Victoria Osteen ta ƙira da darling ne ya ɗago kanshi yana dubanta cikin faɗa ² da yarensu ya furta. “Amma dai ai kinsan baki fini son john ba ko?” Ihu tamay a ka ta dibilbele may baki take zuba masifanta. Domin kowa yasan madame Victoria Osteen bala’ice ita kanta, shi yasa kowa na gidan ke tsoronta fiye da kowa. Gata ƙaƙƙarfa mace tsananin riƙo da addinin ta ya sanya addininta na christian bata wani babban muƙami gareta a church, da di da ƙari gasu masu shegun kuɗi ne su gaba da baya wannan shi ne ya sake kankarota da sake babban matsayi.
♡
*YASMINE*
Tun da suka ɗauki hanya ta nutse a cikin kujerar motan tare da lafewa luff tana jin yadda bugun zuciyarta ke ta faman kai kawo har zuwa yanzun kuwa, hakan ya sanya bama tasan sun kawo katafaren dogon ginin gidan masu ba har saida driver ɗin ta ya mata magana tare da ɗan bubbuga gilashin motar kana ta firgigit ta dawo daga duniyar data lula. Fitowa tay ta fara tafiya cikin nutsuwar da tafi kama da jin kai da taƙama musamman yanda jikinta ke girgizar daukan hankalin me kallonta. Da wata maid service ta haɗu a gaban ƙofar parlour’n shiga gidan tana shanyar kayan data wanke na masu gidan. Shijab ɗin jikinta ta wurga mata saman fuska tare da dogon wandon uniforms ɗin Islamiyyar jikin nata. Kasancewar rigar irin duguwar nan ce har kusan gwiwar ta, Duk inda ta wuce sannu da dawowa ma’aikatan gidan ke mata amma bata kula kowa. Da mahaifinta Ambassador Kabeer Usman ta fara cin karo. Hakan ya sanya a guje tayi kansa tana faɗawa jikinsa tare da fashewa da kuka. “Ohh god waye kuma daga dawowan Ambasa baby zai taɓa min ita?” Fitowan Mahaifiyarta lowyer Khadijah Haroon ne ya sanyata haɗiye maganarta makut tana takurewa jikin mahaifin nata. Cikin muryan No nonsense ba tare data kalli ko inda take ba ta furta. “Oya get out of the here” sum sum ta miƙe tana yin sama se wani tattaro rigan jikinta take. Kai tsaye toilet ta shige tana sakar ma kanta shower, Bata fi 20 minute da shiga ba se gata ta fito ɗaure da fari ƙal ɗin towel me ɗan girma a jikinta.
Anutsenta tazauna gaban mirror kan stool, blow drying gashin kanta tayi tai parking nashi a ƙasan ƙeyarta, ta ɗauki wasu sprays masu tsada da ƙamshi ta feffesa ma gashin, sannan tashiga shafe shafen lotion masu sanya fata tayi laushi. Kafin ta feshe jikinta da tarin turarikanta, bayan ta mulke jikinta da Shu’umar humrarta. Cikin clothes na kayanta ta shige, wasu haɗaɗɗun simple ciffon riga da wando taciro tasaka nude, there’s no way idan ka kalleta baza kaso ɗauke Idonka daga kanta ba don wani masifar ƙyaun da kayan suka mata ko nace ta musu. Don kuwa tabbas YASMINE me ƙyau ce, idan nace ƙyau ina nufin maƙura ƙarshe.
Sake fitowa cikin parlour’n tay loƙacin an jima da idar da sallar maghriba. Ƙamshinta kawai da take fitarwa me yawa ne ya janyo hankalin duk wani dake zaune a parlour’n, ciki kuwa harda Omer da babu jimawa ya zo gidan ɗa ga yayan Hajiya Khadijah Haroon Mahaifiyar yasmine. Zama tay cike da gadara dajin kan daya kasance jininta ƙafarta ta ɗauka ta ɗora ɗaya kan daya, tana jan fruits table ɗin dake gaban daddy’nta. Tsawa Mafaiyarta da take ƙiranta da Maama t.a buga mata kan cewar bata iya gaida mutane bane? Kana maza tayi hanzarin maida fruits table ɗin data janye daga mahaifin nata. Hannun Ambassador Kabeer ya ɗagama Maama tare da girgiza mata kai alaman ta kyale mishi yarinya haka nan tayi abinda ranta yake so.
“Amma daddy’nta sau nawa zamuyi ta maimaita magana ɗaya kan Ambasajo eheeee? Yasmine fa har yanzu ba yarinyar goye bace gidan wani zata je. Don me ina kallon kusa kurai a cikin rayuwanta tana aikatawa amma da nayi yunƙurin gyarawa kace na dena kona bari? Haba Impossible wllh wannan bame yiyuwa bane bama dole na gyara rayuwar yarinyana da kaina wllh, don duk wata uwa data kasance ta gari ga ƴaƴanta dole zataso ganin ɗan ta cikin kyakykyawar nasaba ba wai a bauɗe irin Ambasajo ba!!!” Daga haka fuuuuu ta bar wurin bayan ta cillama yasmine wani mugun kallon zamu haɗe ne…..
*John*
A……….
_Washhh Hannuna ciwoooo!_
_To ya kuke ganin ko kuke tunanin wasan ze fara?, Nasan wasu zasu fara tunanin…… Ehhhhh ya neeeeee to koma dai miye mu haɗe a page na gaba lol 😄😍🥰 don jin yacce zata kaya_
_Anan ina son mu sani cewar komai na rayuwar ɗan Adam na tafiya ne bisa tsari da kuma ƙudurar ubangiji, komai kaga ya faru da bawa dama tun fil azal hakan na cikin rubutun kundin ƙaddararsa yake, Wala ƘADDARA me ƙyau ko akasin hakan, Se dai masu iya magana sukan ce ita ƘADDARA abace mara tabbas, nan take takan iya sanjawa. Ita kuma yarda da ƙaddarar kanta me kyau ko mara kyau na ɗaya daga cikin cikakken Imanin ko wanne bawa!…. A cikin Rayuwar ko wanne bawa kuma bai zama lallai ace saika amfana da wanda yake tare dakai ba, saboda wasu loƙutan ma ban banta akan sha wannan fama na kusa da kai da kake ma kallon Inuwar ka, ko Allon jinginarka, Tashin farko kwatsam se kaga kaine zaka kyautatawa na kusa da kai, Se kuma kaga sama ta ka wani shi ne zai shigo cikin rayuwarkan daga nesa ya zamo shi ne Haskenka ba wannan wanda kake ma kallon shi ne hasken naka na, bayan ka daɗe da linƙaya a cikin DUHU na DUKAN duhu’n. Duk da kasancewar tunaninsu iri ɗaya ne haka zalika Ma’amalar su iri ɗaya ce, duk da hakan bazai hana su saɓama junan suba wata rana, Amma da sun yi Haƙuri da juriya a cikin zaman takewarsun ta yau da kullum su duka se su tashi a ƙarƙashin Inuwar ita wannan Hasken Farin watan_
_Se dai kash…..
_Shin shin shinnm…… Kowa yaje yayi tunani ya ƙaraci tunaninsa don duk yacce kuke zata ko tunani to wasan ba haka yake ba lol 😄💃, don nayi ma kaina alƙawarin tabbas sena gindayar daku a wannan karon ma fiye da MIKIYA, koko TA DABAN, ko kuwa dai DUNIYARMU. koma nace fiye da komai ɗin ma hhhhhhhh, ciki kuwa harda RAMIN KURA……_
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐍𝐓𝐈𝐍𝐆 𝐀𝐍𝐃 𝐒𝐇𝐀𝐑𝐈𝐍𝐆
♡ “Papaah!!!”
Ya faɗi cikin muryan shogoɓa da sakalci yana karyar da wuyansa gefe har farar fuskarsan na dakunewa.
“Johseph?”
Mr jef deefer daya kasance mahaifi ga Joseph ɗin shima ya furta, Yana kallon yaron nashi cike da tsantsar son da yake jin kaff duniyar babu mai masa kalansa. tsaiwarsa ya gyare tare da ɗan karkatan da hulan daya kasance me zubi da irin malafar nan yay, cikin harshen English ya furta. “Yeah Johseph har yanzu kai ƙaramin yaro ne, ba ko ina ya kamata ace naka barinka kana shiga ba, dole driver ne zai kaika” wani kalan sake ɓata ransa yay yana komawa da baya tare da faɗawa ɗaya daga cikin saman 1str ɗin da suka zagaye parlour’n, yana kaiwa zaune tare da jingina da jikin kujeran.
Zama papan yay daga gefensa yana shafa sumarsa like woni baby’n goye nan. “To shikenan na yarda zaka fita ba guard’s Amma nima fa ina da sharaɗi akan hakan” ba tare dayay tunanin wanda sharaɗi bane ya furta.”Ohh papa problem” daƙuwa papan ya masa da dariya a fuskanshi “Na barka jeka dawo zamuyi magana akan Deepika” cike da zumuɗi ya miƙe harda ƴar rawansa na farin cikin zayyi driving da kansa yau, ze kuma fita ba tare da guard’s ko ɗaya ba, Wani tsallen farin ciki ya buga daidai da papan na cilla mishi trow pillows ɗin dake zagaye da lafayayyar kujeran da suka zagaya parlour’n. Da ɗan gudunsa ya bar parlour’n yana riƙe kunnuwansa alamun ya tuba.
Tunda ya fito kuma ya maida fuskan nan me ɗauke da kyakykyawan murmushin nan yana medata tamkar maɗaukar zunubi.
Cikin yanayi na kamewa yake takunsa cikin ƙarfin jiki da kuma izza, don kuwa duk wanda yasan Joseph yake kuma rayuwa dashi to kuwa tabbas yasan irin izzar da yake da. ♡
Hannunsa dake ɗauke da tsadaddar wayansa ƙirar iPhone x ce riƙe a hannunsa yana kamar duba woni abu ne me muhimmanci, haka ya ringa ratsa wuraren gidan daya kasance wani irin tsararre haɗaɗɗe kuma. Tun kamin ya ƙara sa isowa Micheal yay hanzarin isa Parking car na gidan,kai tsaye wata shahararriyar mota ƙirar zamani ash color da ta gaji da haɗuwa yay hanzarin fiddota compound na gidan. wacce kallo ɗaya zaka mata kai da kanka ka fidda ƙiyasin maƙudan kuɗaɗen data lasa kafin a mallaketa. Dan The car ɗin is so majestic, so elegant, so classy, so luxurious. ♡ Yana ƙoƙarin shiga mazaunin driver sit cikin wannan daƙilallar muryan ya cira masa hannunsa ɗaya tare da furta. “Uhmmm… uhmmmm” yana kuma bashi hannu alamun ya bashi car key na motarn. Cikin ɗari ɗari da tsoro da kuma rawan jiki Micheal ɗin ya furta “Amma Bo…..
A dake muryarsa har na ɗan tashi kaɗan ya furta “Ba buƙata” daga haka ya sanya kansa cikin haɗaɗɗar car ɗin, tare da yin reverse nata yana barin haraban gidan wanda hakan yay daidai da zazzaro idanu wojen da Micheal yay cike da ruɗin fitan da yay shi kaɗai. Don yasan wannan ɗin dokar paah ne baya taɓa barin Joseph ɗin fita shi kaɗai ɗin sa ba tare da guard’s ko driver nashi ba. Kasancewarsa pilot kuma dama hakan doka ce a kansu duk wani pilot baya taɓa driving da kansa sedai a ja shi… Paah dake tsaye daga samar benen dake kallon fitan Shalelen yaron nashi yay ƴar dariya cikin sautin da zaifita sosai yay ma Micheal ɗin magana kan cewan karya damu yasan da fitan. Woni kyakykyawan numfashi ya kawo yana kuma shan zuciya irin alamar na tsira ɗin nan da ƙyar. ꨄ Shi kuwa Johseph cike da nishaɗin daya gaza ɓoyuwa har saman kyakykyawar fuskanshi kai tsaye kana iya kallar hakan. Tunda ya hau saman kwaltan yake driving motan nashi very slowly, cikin ɗan tafiya tinanin papah’nshi kan rashin barinsa fita shi ɗaya ko yay driving Kamar haka shi kaɗai. Ɗan ɓata fuska yay tamkar yana gaban mahaifin nashi ya furta
“Ahh dad I’m anger so what about me which condition I’m in I have a difficulties something that happened to me papahh, everything happen to me like a young age, ahh seriously me I’m a big like any serious good human being I’m proud for my self for that hmm may be I will show him do to really understand, but I love you Papa so much I LOVE YOU paah!!”
Yay maganan yana wani lumshe kyawawan fararen idanunsa da kwayar cikin su ta kasance gold colour.
*Ambassadors kabeer house*
Gaba ɗaya mutanen gidan zaune suke cikin wani katafaren parlour na alfarma, Me ɗauke da wasu manya manyan sofa set guda masu numfashi wanda suka kasance masu launin blue da milk, Wanda kalan sukayi wani irin ƙawata parlour’n sosai suka sake fito da asalin kyaun sa, inda yaji komai da ake buƙata na rayuwa, wanda idan nace zan tsaya zayyana muku kyan parlour’n kaɗai ɓata ma juna time,A natse matashiyar yarinyar wacce take fara tas yanayin jikinta kuma kai tsaye na bayyana tsantsar hutu da jin daɗin da suke ciki ta ɗan saci kallar mamy’n nata tare da furta. “Aunty yasmine tana lafiya kuwa Mummy?, Har yanzun bata fito ɗinner ba. Ita da mahaifiyar nata suna sanye cikin shiga iri ɗaya na lace doguwan riga inda ita yarinyar nata a kasance fitet gown ne, ita kuma uwar normal doguwan rigawa esharp. Cakkk kuwa Abbin nasu ya dakata daga sipping coffee ɗin da yake yi, tare da dubar matashiyar yarinyar yana me furta. “Maza Husna je dubomin ko lafiyarta” yay maganan yana dire bowl ɗin dake hannunsa ya zubawa upsairs nata idanu tare da buga wani uban tagumi. Takun takarmin ta da kuma ƙamshin turarenta da baya taɓa ɓuya kawai mahaifin nata ya shaƙa ya sauƙe wata nannauyar ajiyar zuciya. Har zuwa lokacin data ƙara so cikin tsaƙiyar parlour’n ba a sake ba. “ALLAH sarki Ambasa Baby’n daddy’nta ƙaraso mana”,cewar mahaifin nata, wanda ya sata ƙarowa sum sum domin bata mata kashedin mahaifiyar nata ba da tace da ita zasu haɗe. Don duk iskancinta tana tsoron mamy’n nasu. Sum sum take tafiyar har ta kai gaban daddy’n, zaunar da ita yayi gefensa yana tura mata duka kayayyakin dake jere a gabansa. “Eat it ambasajo na” Murmushi ta masa tana gyaɗa kanta wanda babu ko band. “Ina ɗankwalin ki Hau’wa?” Haka ta tsinkayi muryan Mummy nata wacce tayi maganar da ɗan ƙarfi, tura ɗan ƙaramin bakinta gaba tayi, domin idan da sunan da yasmine ta tsani taji an ƙirata dashi to shi ne Hau’wa. Har ƙara ƙara yasmine ɗin ma amma ita a son samunta kowa ma ya dinga ƙiranta da ambasajo ɗin da mahaifinta ke ƙiranta dashi. “Ba magana na ke miki bane yasmine?” Ta sake wulla mata tambayar a karo na biyu. “Ambasajo ɗin Daddy’n ta maza tashi kije ki samo ko hula ne, Mummy naki bata son a zauna lafiya kinji”. Kanta ta ɗaga mishi tana tashi tana tashi,”yawwa that’s my girl” babu jimawa kuwa se gata ta dawod da Baby shijjab jikinta. _*HAUWA KABEER USMAN MAINA*_ kenan da akafi sani da suna _YASMINE HUTU_ ƙyaƙyƙyawar budurwa ce mai kimanin shekaru ashirin da biyu a duniya. Wacce ta kasance ɗiya da farko a wurin mahaifinta Ambassador kabeer Usman Maina, Mahaifinta sananne ne da kowa kusan duka duniyar ta sanshi kasancewar matakin ambassador ɗin daya riƙe.Bayan haka babban ɗan kasuwa ne kuma mamallakin duk wani company’n dake tashe a zagayen Lagos da ketarenta. Yasmine yarinya ce da batajin magana sammm, amma ga wanda be santa ba kai tsaye ze mata kallon nutsatstsiyar yarinya ne, Se dai sammm ba haka take ba. Wanda badan mahaifiyarta dake tsaye a kanta ba da tuni rayuwarta ta jima da taɓarɓarewa, domin kuwa mahaifin shike wuce mata gaba a duk wani rashin ji da kirki nata, Idan mahaifiyarta ta tilasta mata zuwa islamiyya setayi tafiyarta manyan club’s ko park. Se ta dedeci loƙacin tashi yayi kana ta nufo gida. kullum zaka kalleta idan zata tafi cikin shigar kayan islamiyya, wanda hakan yasa wasu ke mata kallon kamila kuma natsassiyar mace. gata masifaffiyar gaske ce lamba ɗaya ta bugawa a jarida. Ƴar gata ce shalele kuma ƴar shagwaɓa a gidansu, Musamman ma ga mahaifinta ambasador kabeer maina. Gatan data samu da rayuwar da take a cikin ta seta tashi tamkar renon turai,Inda ta samu zurfafa kanta harta samu wadataccen ilimin boko, sedai na addinin kuwa ko oho amma fa idan ka taɓa ta akan addinin ta bata barin ko ta kwana, wacce zaka ɗauka cewar ita ɗin irin wannan shahararrun yaran nan ce masu haddar Alqur’ani izu sittin a kansu, sedai ko rabin izu bata da. Karatunta kuwa gaba ɗaya a ƙasar ƙetare ta yisa, idan ka cire Nursery school datai a Nigeria kawai. Sam bata son harkar talauci ko haɗa hulɗa da mutanen da suka kasance talakawa, wannan dalilin nema yasa sammm ta tsani islamiyyar da Mahaifiyata ta saka ta. A cewar ta haɗa wurin zama tare da su harma da shaƙar numfashin juna kan iya taɓa ta itama, wai wataran ta zama irinsu kodai ta auri talakan, Wannan dabi’a tata yana taɓa mahaifiyarta kwarai da gaske. Abu ɗaya ne ALLAH ya taimaketa da nisantata da shi duk da rayuwar turai data tashi a ciki, shi ne kasancewa da namiji. Sedai takanyi irin su sking love haka don tace wannan kamm babu laifi, amma fa ba Inji AMMEY LAYLERH ba 🤗 🤣 ato. Inji yasmine lol 😄😍……..
“Ambasajo ku matso mu fara dinner, kamar Omer yana nan ma ko?” Yayi maganar da alaman tambaya. Husna ce ta ɗaga kanta ita kuwa yasmine ko motsi batayi ba, duk kuwa da cewar Omer ɗin dan ita yazo.tana ƙoƙarin buɗe kyakykyawan foodplask ɗin dake gabanta, sega Omer ɗin nan ma yana sauƙowa daga saman bene mai ɗan jiki kaɗan haka fari tas da shi. Wanda fuskarsa ke ƙawace da kwantatciyar saje da gemu mai ɗan tsawo, yana da manyan maganai kamar bull ga dogon hanci, wanda kallo ɗaya zaka masa ka kalla irin tsantsar kamar dake tsakanin sa da matar da suke kira da Mummy. A natse ya ƙara sa saukowa daga zuwa downstairs ɗin yana zama. Tare da furta. “Good evening Daddy”, “Good evening Omer how was your night?” Cewar Daddy ɗin Mummy na tura masa plate ɗin dake ɗauke da abinci. Husna ce ta fara gaida shi, yayin da yasmine ta sha kunu, domin ita yanzu tunda Mummy nata ta fara sako zancen aure tsakaninta da Yaya Omer ɗin ta dena sakar masa fuska. “Hala yasmine da dukkan alamu bata ga Omer ba ko?” Mummy ta faɗi cikin gatse. Fuskarta ta ɓata ita fa wllh shi yasa sammmm bata son zama kusa da Mummy’n, duk wasu hanyar kusheta seta fito mata dasu, da kuma diagata gaban ko su waye. Ranta a ɓace ba tare data kalle shi ba ta ce dashi. “Ya Omer good evening da “how was your night?” Ya amsata yana ɗan sakar mata murmushin sa me kyau. _I don’t like her_ ta faɗi a zuciyarta tana murguɗa masa baki, wanda hakan da tayi ya sanya Omer ɗin kallonta yana waro idanunsa sosai yana kallonta speechless. “Baby yadai? Nafa kina murguɗa min baki” Ya faɗi yana sake waro idanunsa akanta. “Malam wai ina ruwanka da nine ka fiye takura min fa Aha! Kana takura rayuwana.”
“Ya takura rahuwar taki yasmine!, Me ya sa ke samm baki da kirki ne idiot kawai” Mummy’n ta ta faɗi a fusace tana miƙewa tayo kanta. Wanda ya sa ta kwasa a mugun guju tana ce dashi zasu haɗu ne. Ta haye samanta tana sauƙe ijiyan zuciya, a gaban mirror taja ta tsaya tare da zare band tare da ribbon ɗin kanta, tana tsurama kanta Ido slowly ta tura hannayen ta cikin gashin kanta, ko me ta tuna kuma se ta wani daki kan nata kaɗan. Tana me furta “Ohhhh ALLAH!!!” A bayyane sakamakon gilmawar kyakykyawar face nashi data gani a cikin zuciyarta. Daidai kuma lokacin ne aka fara yayyafi, kafin a tsuge da ruwan saman sosai, yanayin yayi wani irin daɗin gaske, ga wata irin ni’imtacciyar iska wadacciyar da ta ga gauraye ko ina dake cikin garin. A daidai kuma wannan lokacin John ke zaune cikin motarsa yayi Parking nata a wani bakin masjid. Tin yana saka ran za’a dauke ruwan har ya cire. Don kuwa yaga abin bana ƙare bane, se yaji duk zaman motar ya gama gundirarsa. Don haka a natse a kuma wani irin Hankali ya fito daga cikin motar. Wata brander ya hango babu kowa a wurin, se yaji kamar hankalinsa ya ɗan nutsu da daya zauna a wurin. Umbrella ɗin dake bayan motar ya miƙa hannunsa yana ɗauka, kai tsaye yana yin wajen….
*DUHU NA DUKAN DUHU*
AMMEY LAYLERH ✍️



INA FATAN AHERI
Wow
Assalamualikum
nice