WhatsApp Join WhatsApp Channel
Littafan Hausa Novels

Matar Gida Hausa Novel Complete

Written by mynovels

Matar Gida Hausa Novel Complete

 

 

YOTA ID/022

YOTA ID/022

 

P1

Safiyar lahadi karfe 11:24am na safe,zaune take cikin kitchen kan wata karamar kugerar ruba hannunta riƙe da wata farar roba cikin robar shinkafa ce ƴar gwamnati,cike da nitsuwa take cire wasu kananun kwari dake cikin shinkafar,ƴarta ƴar shekara ɗaya da wata biyar ce ta shigo kitchen hannunta riƙe da wata karamar kofi cikin hausarta da bai fita da kyau ta ce ”Mumy in ca tea” murmushi Amirah ta yi tare da ajiye robar shinkafar kan carbin ɗin kitchen,har sannan fuskarta dauke da murmushi ta dauke ƴarta mai suna Fauziyya ta ce ”yunwa ki ke ji?” alama Fauziyya ta yi wa mahaifiyarta alamar eh hakan yasa Amira faɗin ”sorry yanzu zan maki tea ko autar Dady” nan Amira ta shiga haɗawa Fauziyya tea daidai lokacin da ta zuba ruwan zafi cikin kofi ta dauke tea spoon tana juyawa Fauziyya tea mijinta mai suna Ɗalhat ya shigo kitchen ɗin fuskar nan tamau babu fara’a wata farar takarda ya miƙo mata ɗan jimm Amirah ta yi kafin ta sa hannu ta ƙarɓa takardar amma ta ƙasa buɗe saboda fargaba da kuma tsananin tsoron,kafe sa ta yi da idanunta alamar tambaya shima ita yake kallo kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce ”ki je gida na sawwaƙe maki,bazan iya cigaba da zama da ke ba,ƙazantar ki da rashin iya kula miji sun ishe ni ba a kan ki aka fara haihuwa ba,mata da yawa sun haifi ƴaƴa sama da 7 amma basu sake jiki sun sawa kansu lalace da rashin tsafta kamar ki ba”shiru ya yi kamar bazai ce komai ba sai kuma ya ja wani dogon numfashi kafin ya ce ”tun ba yau nake faɗa maki cewar zan iya rabuwa dake kan rashin tsafta amma kin ƙi gyara hali” nan ma wani shirun ya kuma yi kafin ya ɗan yi ƙasa da murya yana shafa kasimba dake fuskarsa ya ce ”nan da sati uku za’a daura min aure” yana gama faɗin haka ya fita daga kitchen ɗin

 

 

Amirah ta dauki a ƙalla mintina goma tsaye cikin kitchen kamar wacce aka dasa lokaci ɗaya tunaninta ya tsaya cak da gaske yake all this while da yake ce mata zai rabu da ita ya auro wata,me yasa wasu mazan basu da lissafi ne auren ta da Ɗalha shekaru 9 cikin shekarun nan ta haifi ƴaƴa 7 maza huɗu mata uku kusan duk shekara take haihuwa,babu kalar planing ɗinda bata yi ba amma da yaro ya cika watanni takwas zuwa tara sai wani ciki hakan yasa ta hakura daina yin planing ɗin gaba ɗaya, tana iya bakin ƙokarinta waje ganin ta kula da gidan da yara har shima Ɗalha amma gaba ɗaya abubuwa sun ƙi mata saiti tayi ta roƙon Ɗalha ya sama mata ƴar aiki amma yaƙi duk sanda ta yi masa maganar ƴar aiki cewa yake sai da ya ƙaro mata kishiya da zasu riƙa raba kwana hakan zai sa ta sami sauƙin ayyukan cikin wasa yake faɗa mata haka ita ma sai ta biye masa ta ce ta amince ya auro koma wace ita bata da matsala,ƙarancin shekaru da kuma auren wuri da aka yi mata yasa har yanzu ta ƙasa saita gidanta,mahaifiyarta ta rasu tun tana ƴar shekara goma duk ƴan uwanta maza ne su shidda mazaje sai ita kaɗai mace,da su take shawarwarin rayuwarta, bata taɓa kawo zai iya sakinta da gaske ba duba da irin soyayyar da suka yi kafin aure cike da ƙidima zuciyarta ta yi mata nauyi sosai ji take kamar an daura mata dutse a ƙirji,kukan Fauziyya ne ya dawo da ita hayyacin ta hakan yasa ta nufi inda firiji yake ta buɗe firijin tare da daukan ruwar gora ta xubawa Fauziyya ruwan cikin tea yadda zafin tea zai yi mata daidai sha,ta mikawa Fauziyya kofin ta ce ”maza je ki parlour” babu musu Fauziyya ta karɓi kofin zuwa parlour wasu hawaye masu zafi suka rinƙa zuba daga idanun Amira haka ta daure ta gama dafa abinci saboda yaranta bayan ta gama girkin ne ta zuba masu sun ci ta kuma yi masu wanka babban ɗanta Muhammad Sudais da me bin sa Afef suka yiwa kansu wanka,bayan ta gama masu wanka ne ta zuba kayan wanke su cikin injin wanken kaya ta cewa Sudais da injin ya gama wanke kayan ya kwashe ya baza su ƙara shan iska daman shi ke yi kullum,duk abinda take Ɗalha na zaune cikin parlour yana danna wayarsa kallo ɗaya zaka yi masa ka fahimci chat yake kuma yana jin dadin chat ɗin,Amirah ta haɗa yaranta duka cikin ɗakinta ta yi masu nasiha ta ce za ta yi tafiya saboda haka su kula da ƙansu sosai ta yi masu nasiha,Rayyan ɗan shekara shidda ya fara kuka ya ce ”Mumy ni zan bi ki” nan ta shiga rarrashinsa da ƙar ta samu ya daina kuka,Allah ya taimaka tuni Fauziyya ta yi barci hakan yasa Amirah daukar jakarta da ta zuba kaya kala huɗu a ciki ta fita zuwa parlour sai a sannan ne Ɗalha ya kalle direction ɗinta ganin tana shirin fita ita kaɗai ba tare da ce masa komai ba yasa ya ce ”wa zai kula da Fauziyya?” ya kare magana fuskarsa babu alamar wasa” murmushin takaice Amirah ta yi ta ce ”aiy kana nan zaka kula da ita” cike da ɓacin rai Ɗalha ya tashi zaune daga kwanciyar da ya yi kan kugera 3 siter ya ce ”nono gare ni da zan bata yarinyar da ba ki yaye ta ba” a takaice Amira ta ce ”na yaye ta ɗazu”daga haka ta fita daga parlour cike mamaki Ɗalha ya bi bayan Amirah da ido baki buɗe

 

 

YOT/022
*MATAR GIDA* 🩵002

 

YOTA ID/022

 

P2

 

Karfe hudu na la’asar Amirah ce zaune cikin wani ɗakin hotel laptop daure kan cinyarta tana rubuta letter,so take ta tura letter a wajen aiki, annual leave take son dauka,hutun kwanaki talatin na ranakun aiki, bayan ta gama lissafin kwanakin ta ga ya fita mata kusan wata ɗaya sati biyu,bayan ta gama drafting letter ne ta yi editing kafin ta turawa oganta ta e-mail,wayarta dake gefinta ta dauko dalilin kira da ake mata ganin me kiran yasa ta kashe wayar gaba ɗaya Ɗalha ne ke kira,daga lokacin da ta fita daga yanzu ya yi mata miss called kusan sau hamsin dalilin kiran nasa bai wuce Fauziyya ba,bayan ta kashe wayar ne ta fita harabar hotel ɗin cikin fita ta mutumci sanye take ciki wata doguwar riga egyptain abaya ligth blue yadda ta yi rolling farin gyale kafafunta sanye da simple black shoe,fita daga hotel ɗin ta yi gaba ɗaya yadda ta kama hanyar cikin gari,ta tare abin hawa ta faɗa masa sunan pharmercy dake kusa da hotel ɗin,tafiyar mintina goma sha biyar ne daga hotel ɗin zuwa pharmercy,bayan ta sallame ɗan sahu ne ta shiga cikin pharmercy ɗin yadda ta sami ɗaya daga phamarcist ɗin wata babbar mace ce da a ƙalla zata kai shekaru 50 a duniya bayan Amirah ta gaishi matar ne ta cewa matar ta yi yaye ta bata maganin zazzaɓi da kuma wanda zai rage mata zugin nono,ba tare da ɓata lokaci ba matar ta haɗawa Amirah magunguna,ATM card ɗinta ta ciro daga hand bag ta biya ƙudi magunguna kafin ta bar phamarcy ɗin,wani resturant dake can tsallakin titi Amirah ta nufa inda ta siya abinci har take away biyu

 

 

 

 

 

Bayan komawarta hotel ta rage kayan jikinta kafin ta samu waje ta zauna kan resting chair dake cikin ɗakin hotel ɗin ta dauki take away ɗaya ta buɗe ta fara cin abinci nan take wani kuka ya taho mata tun barinta gida take kukan zuci sai yanzu ta samu damar buɗe baki ta fara kuka gwanin ban tausayi,tunawa ta yi da ƴaƴanta,abincin da ta girka masu ta sani bazai kai su ci har dare ba,cikin muryar kuka ta ce ”ya Allah ka tsare min ƴaƴana ya Rabbi ka kulan min da su Allah ka bani hakuri da juriya” tana kaiwa nan kuka ya ci karfin ta saida ta yi mai tsafta kafin daga bisani ta tashi ta shiga bathroom dake ɗakin hotel ɗin wanka ta yi sannan ta dauro alwala a lokacin har an tayar da sallah kasancewar hotel ɗin tana sabuwar unguwa ce so akwai gidajen mutane da kuma masallatai a layin,bata tashin kan dardumar ba saida ta yi sallar isha’ai ta dauki lokaci mai tsawo zaune kan darduma tana jero addu’oi kafin daga bisani ta shafa,da kyar ta samu ta ci abinci rabin take away shima ɗin dan tana son shan magani ne shi yasa,kwanciya ta yi lamo kan king size bed ta takure kanta waje ɗaya tun sanda ta yi aure yau shine rana na farko da zata kwanta ita kaɗai ba tare da ƴaƴanta a gefinta ba,babban abinda yafi damunta shine Fauziyya bata san halin da take ba,so take ta ƙoyawa Ɗalha hankali kullum cikin kushi ta yake bai taɓa yabon ta ba duk wani ƙokarin da take wajen kula da ƴaƴanta baya gani kullum cikin ƙorafi yake,tun sanda ta aure shi bai taɓa yin sati ba tare da ya ce mata zai saketa ba,a ranar ta cika kwanaki takwas a gidansa ya dawo gida ya tarar ta yi barci bata rufe ƙofa ba ya tambaye ta dalilin da yasa bata rufe ƙofa ta ce masa bata san sanda barci ya dauke ta ba,saboda uni ranar ɓaƙi sun yi ta zuwa ganin ɗakin amarya hakan yasa ta gaji bata san sanda barci ya dauke ta ba ,ta daura da ”kasan ban saba ayyuka masu yawa ba,a gidanmu bana aikin komai sai dafa abinci shima kuma ba kullum ba” ta yi magana cikin wasa,buɗar bakinsa sai cewa ya yi ”tunda ba ki saba aikin karɓar baƙi ba sai ki koma gidanku aiy in baza ki iya ba”tun daga wannan ranar Ɗalha ke mata baraza kullum nuna mata yake shi zai iya rayuwa ba tare da ita ba,ita kuma babu abinda take tsoro kamar rabuwa da Ɗalha da ya fahimci hakan sai ya rinƙa mata barazanar rabuwa da ita ba ƙaramin kuka ta yi cikin wannan daren ba,dalilin zuwanta hotel so take Ɗalha ya ga amfani ta a gidansa shi yasa ta tafi hotel ta kama ɗaki,ba da niyyar iskanci ba,ta kama ɗaki ne dan bata son iyayenta su kira Ɗalha su bashi hakuri kan ya maida ta,da gangan ta bar masa yara har Fauziyya,ta barsu ne dan ya yi reno yaji yadda mata ke ji,Amirah da Ɗalha baƙi ne garin aiki ne ya kawo Ɗalha Lafia asalinsa ɗan Zamfara ne iyayensa da kowa nasa a can duke ita kuma Amirah bafulatana ce ƴan asalin Chad zama ya kawo iyayenta ƙaramar hukumar keffi dake jahar Nasarawa,ta hadu da Ɗalha ne a garin Lafai lokacin ta samu addimision a Fulafai,bayan auren su mahaifinta ya sama mata aiki a state wani babban kamfani a garin Lafia,babu abinda ta nema ta rasa wajen Ɗalha matsalar sa ɗaya rashin iya magana da kuma rashin sanin darajar ɗan adam,mai da sabulun wankanta kaɗai take siya da albashinta sai ƴan abubuwan da ba’a rasa ba haka yasa ta tara ƙuɗaɗe masu yawan gaske cikin asusun bankinta a wannan dare barci ɓarawo ne ya dauke ta

 

 

 

 

A can wajen Ɗalha kuwa tun azahar Fauziyya ki aikin kuka ya yi rarrashi har ya gode Allah,gashi ta ƙi yarɗa ƴan uwanta su riƙeta ida Dady kawai duk motsin da ya yi sai ta kira sunansa duk inda ya sa ƙafa Fauziyya na manne da shi,da kyar ya samu ta sha tea,bayan ta gama sha tea ta sa wani sabon kuka tana kiran Mumy alamar tana son shan nono,zuwa wannan lokaci Ɗalha ya fara fita hayyacinsa ga kukan Fauziyya ya ƙarwaɗe gida ga hayaniyan da ƴan uwanta ke yi yadda yaran maza su huɗu ke ta bugun ball,matan biyu kuwa sun mayar da hankali kan bebin roba dake gabansu sai faman surutu suke su kaɗai,wani tunani ya faɗowa Ɗalha nan take ya cire wayarsa cikin aljihu ya buga layin ƙanin Amirah Kabir,bayan Kabir ya amsa kiran Ɗalha ya fara jansa da hira suna cikin hira Fauziyya ta sake kuka nan Ɗalha ya shiga rarrashinsa hankalinsa ya rabo biyu hakan yasa Kabir faɗin ”ina mamanta? kaita wajen mamanta mana” shiru Ɗalha ya yi,a tunaninsa Amirah ta je gidan mahaifinta maganar Kabir yasa shi fahimtar bata gidan mahaifinta to ina ta tafi?” maganar Kabir ne ya katse wa Ɗalha tunani inda ya ce ”hello.. hello kana jina Yayanmu?” Ɗalha ya ce ”ta zaga ne yanzu zata fito”Kabir ya ce ”yauwa Yayanmu pls in ta fito ka ce mata tun ɗazu nake kiran layinta a kashe akwai maganar da nake son yi da ita ne” cike da tsantsan mamaki Ɗalha ya ce ”ok zan faɗa mata” tsabar mamaki Ɗalha ya ji gaba ɗaya bazai iya cigaba da magana da Kabir hakan yasa ya ce ”zan kiraka anjima Kabir” daga hakan suka yi sallama bayan Ɗalha ya kashe waye ya faɗa duniyar tunani mamaki ne ya cika shi bai taɓa kawo Amirah zata iya tafiya ta bar yaranta ba a tunaninsa tare da yaran zata tafi gidansu,amma sai yaga har Fauziyya ta bari me hakan ke nufi? ba yau ya fara yi mata barazana da saki ba,da sai ta yi ta basa hakuri har da kuka,sai yaga ta daina bashi hakuri duk sanda ya ce zai saki ta sai ta ce kana sakina zan tafi da yarana bazan bar ƴaƴana sun sha wahala wajen matarka ba,amma abin mamaki sai gashi yau ya mata saki ɗaya ta tafi ta bar yaran gaba ɗaya yana cikin wannan tunani ne ya ji wani ruwa mai ɗumi ya gangaro masa cikin wando nan ya fara kalle kalle so yake ya gano daga inda ruwa yake ƴarsa Sumayya ƴar shekaru biyu da rabi ta ce ”lah Dady Fauziyya ta yi maka fitsari a jiki” ta kare magana tana babbaƙa dariya wani irin zabura Ɗalha ya yi ya ce ”what fitsari,a ina?” har sannan Sumayya na dariya ta ce ”wallahi Dady fitsari ta yi maka,in ba’a sa mata pampers ba bamu daukanta har Mumy ma bata daukan ta,kullum sai Mu ta ce mata in zata yi fitsari ta yi magana amma bata ji”wani mugun kallo Ɗalha ke yiwa Fauziyya ta ƙi yarda ta kallesa ta sa kai ƙasa kamar munafuka Ɗalha ya yi magana cikin ɗan fushi ya ce ”wuce ki je toilet” har sannan kanta ƙasa a hankali ta sauko daga kafarsa ta nufi hanyar ɗakin mahaifiyarta,daidai kofar ɗakin ta sake wani kuka cikin Hausar ta da bai fita da kyau ta ce ”Mumy fiyaye” wani mugun kallo Ɗalha ya bi bayanta kafin ya kira babban ɗansa ɗan shekara takwas Sudais ya ce ya je ya yiwa Fauziyya tsarki

 

 

Karfe uku da wasu ƴan mintina na rana Ɗalha ne tsaye cikin ɗakinsa cikin shirin zuwa zance wajen masoyiyarsa Unisa Sudai ne ya shigo ɗakin cikin uniform ɗin islamiyya,bakinsa dauke da sallama Ɗalha ya amsa masa sallama cike da girmamawa Sudai ya ce ”Dady kaga Haydar yaƙi sa uniform ɗinsa kullum sai ya sa mun yi lattin zuwa islamiyya,kuma bulala ake mana in mun yi latti” shiru Sudais ya yi yana wasa da gefin rigarsa ya ce Ummu Abiha kuma ta ƙi wankin plate ɗinda muka ci abinci” wata doguwar numfashi Ɗalha ya sauke kafin ya ce ”ka je ka ce masu in na fito basu gama shire ba sai na zane su” da to Sudais ya amsa kafin ya fita daga ɗakin ita dai Fauziyya har sannan tana manne da Dadynta, karfe huɗu saura mintina goma Ɗalha ya fito daga ɗakinsa tsayawa ya yi a parlour yaga duk sun ɓata ko ina gaba ɗaya sun hargitsa gidan nan ya fara kwala masu kira duk suka fito amma banda Rayyan har Ɗalhat ya tada mota Rayyan ya fito da gudu hannusa riƙe da rigar islamiyya ɗaya hannu yana riƙe da robar ruwa,daga shi sai gajeren wando wani irin tuƙiƙin bakin ciki ne ya tasowa Ɗalha cike da ɓacin rai ya fita mota ya ce ”me ka ke tuntuni me ya hanaka sa uniform ɗinka?”nan take Rayyan ya fara kuka cikin muryar kuka ya ce ”banga wando islamiyya na ba” baki buɗe Ɗalha ke kallon sa cikin zuciyarsa ya ce ”haka Amirah ke fama da yaran nan kullum ya ilahi”

 

 

YOTA ID/022
*MATAR GIDA* 003

 

YOTA ID/022

 

P3

Sudais ne ya fito daga mota yazo ya tsaya kusa da Fauziyya dake tsaye gefin Ɗalha ya ƙarewa Rayyan kallo kafin ya ce ”kullum haka ya ke duk sanda zamu ji islamiyya sai ya ce baiga rigarsa ba ko wando wata rana sai Mumy ta kaimu islamiyya zai ce ya manta Ƙur’ani a gida, uniform ɗinsa yana ɗakin Mumy cikin saif ɗinta har Kur’anin sa duk a can take ajiye masa” shi dai Rayyan banda kuka babu abinda ya ke wani tsawa Ɗalha ya daka masa ya ce ”ka yiwa mutane shiru kafin na make ka” nan take Rayyan ya yi shiru yayin da Sudais ya koma cikin gida ɗakin mahifiyaru ya kwasowa Rayyan uniform da kur’ani,bayan Ɗalha ya sauke su islamiyya ne Fauziyya ta fara kuka ita sam baza ta zauna ba wajen Mumy take son zuwa nan Ɗalha ya shiga aikin rarrashinta,wata malamar islamiyya ce ta karɓi Fauziyya hannun Ɗalha,tana faɗin ”ƴar Mumy yau Dady ne ya kawo ki?”ita dai Fauziyya sai faman kuka take tana ƙokarin zillewa daga hannun Malamar,malamar ta kai hannu kunci Fauziyya ta ji ya yi zafi hakan yasa ta mayar da dubanta ga Ɗalha ta ce ”jikinta ya yi zafi kamar bata da lafiya” Ɗalha ya sosa kai ya ce ”eh rashin nono ne yau aka yaye ta” baki buɗe malamar ke kallon Ɗalha kafin ta ce ”bai kamata ka kawo ta makaranta ba,sai ta yi zamanta a gida ko zuwa jibi ne sai tazo in jikin ya yi mata sauƙi,mamarta bata ji zafin jikin yarinyar bane?ta shirya ta” nan Ɗalha ya fara kame kame ya rasa me zai cewa malamar sai kawai ya ce ”itama bata ji daɗe bani tana asibiti” nan malamar ta jajanta masa,daga haka ta miƙo masa Fauziyya ta ce ya maida ta gida a siya mata maganin zazzaɓi da kuma wanda zai sata cin abinci,Ɗalha ya yi mata godiya kafin ya bar kofar makarantar bai tsaya ko ina ba sai wani pharmercy inda ya yiwa mai pharmercy bayanin condition ɗin Fauziyya mai pharmercy ɗin ne ya bawa Ɗalha shawarar siyawa Fauziyya maganin barci wanda da ta kwanta sai safe amma ya tabbata ya ɗaga ta cikin dare ya bata wani abu ta ci ko da ruwa ne,Ɗalha ya yi na’am da shawarar ana cikin haɗa masa magunguna ne wayarsa ta fara ƙara alamar shigar kira a tunaninsa Amirah ce ke kiransa sai yaga Unaisa ce ke kira rejecting kiran ya yi kafin ya yi silencing wayar,shagon provission dake gefin pharmercy ɗin ya shiga,shopping ɗin kayan ciye ciye sosai ya yiwa Fauziyya da sauran yara daga nan ya kama hanyar gidan su Unaisa daidai juction ɗin gidan su Unaisa Fauziyya ta fasa kashi cikin mota,wari ne ya cika motar lokaci guda, hakan yasa Ɗalha faka mota gefin titi ya fara ƴan dube cikin mota yana faɗin ”wannan warin na meye ne” ita dai Fauziyya ta yi shiru tasa kai ƙasa bata ce masa komai ba,shiru ya yi yana dubanta kamar zai yi kuka ya ce ”what the hell is wrong with you Fauziyya ba ki iya magana bane?” Fauziyya ta yi wiƙi wiƙi da ido tana shirin kuka wani irin tsawa Ɗalha ya mata nan take ta haɗe kuka,sai kuma ta basa tausayi hakan yasa ya yi ƙasa da murya ya ce ”princess” haka ya ke kiranta wani lokaci duk yaran ita kaɗai ta fita Amirah sak babu inda ta baro Amirah hakan yasa duk cikin yaran Ɗalha ya fi sonta cike da kulawa Ɗalha ya ce ”duk sanda za ki popo ki yi magana kin ji?” Fauziyya ta ce ”umm” daga haka Ɗalha ya tada mota,a daidai kofar gidan su Unaisa ya yi parking mota,gida ne na masu rufin asiri ɗakuna huɗu jire sai kitchen da banɗaki daga can gefi,farfajiyar gida bata da wata girma sosai bishiyar lemo dake tsakar gidan da aka kewaye da randunar ƙasa ya baiwa farfajiyar gidan inuwa mai sanyi da dadin zama,Unaisa ce zaune karkashin bishiyar hannunta riƙe da wayarta tana kallon video a tik tok,daga can kofar kitchen mahaifiyarta ce zaune tare da wata makwabciyarsu suna hira,magana suke kan bikin Uanaisa,Ɗalha ya jingina bayansa da kujerar mota,daga azahar zuwa yanzu gaba ɗaya ya gaji har ya fara tunanin anya kuwa zai iya riƙon yaran nan kafin lokacin auren sa,warin kashin Fauziyya ne ya fara ɗaga masa hankali hakan yasa ya buɗe kofar motar dan iska ya samu damar shiga ya zira ƙafarsa ɗaya waje,layin Unaisa ya kira sai da kiran ya kusa tsinke kafin Unaisa ta amsa a takaice Ɗalha ya ce ”ki fito ina jiranki” ba tare da ɓata lokaci ba Unaisa ta fito daman zaman jiransa take tun safe ya ce zai zo ya kaita ice cream planet su sha ice cream su dauki hotuna

 

 

 

 

Unaisa kyakkyawar yarinya ce ajin farka Allah ya yi mata baiwar kyawun fuska da kuma dire komai a jikinta masha Allah tana da haske daidai gwargwaɗu,kyawunta yasa Ɗalha kara macewa cikin soyayyarta,sanye take cikin wata doguwar riga materail gray colour anyi masa ado da fararen fulawa fuskarta dauke da murmushi ta fito,tun daga nisa Ɗalha ya kafeta da ido kamar zai cinye ta,ji yake kamar ya maida ta ciki tsabar so,bakinta dauke da sallama ta iso wajen Ɗalha ya amsa mata sallama nan ta gaida shi ya amsa mata har sannan idonsa a kanta sai wani binta yake da ido,wani wari wari ne ya dake hancin Unaisa nan take ta fara rufe hanci tana bin wajen kallo tana neman daga ina warin yake,bayan ta gama dube dube ta mayar da dubanta kan Ɗalha ta ce ”beby kana jin warin nan kuwa?” numfasawa Ɗalha ya yi kafin ya ce ”ƴar ki ce ta ɓata jiki da popo” sai a sannan hankali Unaisa ya kai kan Fauziyya dake barci hankali kwance gaban mota,da sauri ta cire hannu daga hanci ta ce ”kamata ya yi ka kaita gida couze babu yadda za’a yi mu fita da ita alhali ta ɓata jiki,babu wanda Ɗalha ya faɗawa ya saki Amirah har Unaisa,shiru ya yi na wasu ƴan sakkani kafin ya ce ”mamansu bata nan” Unaisa ta yi saurin tarar numfashi sa ta ce ”ina ta je?” Ɗalha ya gyara zama ya ce ”na turata gidansu ɗazu da safe,and l don’t think zan dawo da ita nan kusa maybe sai mun gama cin amarci” ya kare magana yana sakarwa Unaisa murmushi,nan take annuri dake fuskar Unaisa ya ɓace fuskarta babu alamar wasa ta ce ”wani amarci za’a ci? amarci da ƴaƴa bakwai? “magana ta gaskiya ka maida matarka saboda ni ba zan iya reno ba” cike da mamaki Ɗalha ke kallon Unaisa,kamar bazai yi magana ba sai kuma ya ce ”munyi magana da ke last week kin ce za ki riƙe min yara tamkar ke kika haifi su” Unaisa ta yi magana cikin gatse ta ce ”sai na ce ka saki uwarsu? yara da mahaifiyarsu ka maida su marayu ba fa zai yiwu ba,tun wuri ka je ka yi bikon matarka” ta yi magana tare da kawar da kai gefe,shiru ne ya biyo baya kowanne su da tunanin da yake,sosai Ɗalha ya yi mamakin yadda Unaisa ta nuna sam baza ta riƙe masa yara ba,a tunaninsa zata yi farin ciki bayan ya sanar da ita ya saki Amirah amma sai ya ga akasin haka,Unaisa ta shirya za su sha soyayya sosai bayan aurensu,ga kuma alƙawarin da Ɗalha ya mata na tafiya kasar Poland cin amarci,yanzu ya saki matarsa ba lallai ya kaita Poland ba ita da ko airport bata taɓa zuwa ba,hakan yasa ta ci burin tafiyar sosai gashi duk ƙawayenta ta yi masu hiran za su poland honeymoon shikenan sai ta ƙare honeymoon a hidimar yara,sam haka ba zai yiwu ba

 

 

 

Ɗalha ya mayar da dubansa ga Unaisa ya ce ”je ki gyara mata jiki daga nan sai mu wuce na siya maki ice cream ɗin” galala Unaisa ta yi ta buɗe baki tana kallonsa ta saki wani irin murmushi kafin ta ce ”da wa ka ke magana? wai ni?” ta kare magana tana nuna kanta zuwa yanzu Ɗalha ya gama karaya da lamarin Unaisa hakan yasa ya yi shiru bai ce mata komai ba kawai ya rinƙa kallon ta can ya ce ”what is really wrong with you Unaisa ɗa fa na kowa ne beside Fauziyya ƴata ce and nan da wasu ƴan kwanaki za’a daura mana aure da ke me matsalar ki,pls bana son jin wata magana ki dauki yarinyar ki je ki gyara mata jiki ban son jin komai” wani irin dariya Unaisa ta yi harda shewa kafin ta ce ”ka yi hakuri bazan iya ba” Ɗalha na shirin magana ya jiyo muryar Aisha inda ta ce ”barka da yamma ango” fita Ɗalha ya yi daga mota ya nufi inda Aisha ke tsaye cike da girmamawa suka gaisa inda Aisha ta tambaye sa ya yara ya ci mata duk suna lafiya daidai lokacin idonta ya kai kan Fauziyya dake barci hankali kwance cikin mota amma kana ganinta zaka san barcin wahala take daga yadda ta kwanta,Aisha ta ce ”tare kuke da yaran?Ɗalha ya ɗan sosa kai kafin ya ce ”a’a bata jin daɗi ne shi yasa na fito da ita” Aisha ta ce ”allah sarki, Ubangiji ya bata lafiya,in babu damuwa zan yi mata shimfiɗa cikin gida kafin ku gama” Ɗalha ya ƙirkire murmushi kafin ya fara magana cikin in’ina ya ce ”daman..daman ta ɓata jikinta ne” Aisha ta ce ”to Unaisa ki shiga da ita ciki sai a gyara mata jiki” wani kallo Unaisa ta yiwa Aisha da yasa Aisha faɗin ”ba ki ji ba?” cikin sanyin murya Ɗalha ya ce ”ta ɓata jiki da bayan gida ne” cike da mamaki Aisha ta kalle Unaisa kafin ta ce ”saboda ta ɓata jiki da bayan gida shine baza ki dauke ta ba?” shiru Unaisa ta yi,ta kawar da kai gefe tana ƙananun maganganu ita kaɗai gudun kar a yi abin kunya yasa Aisha daukan Fauziyya bayan Ɗalha ya buɗe mata kofar mota cike da dabara ta fidda Fauziyya daga cikin mota,sallama dauke a bakinta ta shigo gidan,a tare Mama da makwabciyarsu suke amsa sallamar da ido Mama ta bi Aisha daidai lokacin da Aisha ta dire Fauziyya bakin fanfo Mama ta ce ”wannan kuma fa daga ina kika samu ta duk ta ɓata jiki da kashi?” numfasawa Aisha ta yi kafin ta ce ”ƴar Ɗalhatu ce wai bata jin daɗe shine ya taho da ita zance suna hanya ta ɓata jiki da kashi”

 

 

YOTA ID/022
*MATAR GIDA* 004

YOTA ID /022

 

P4

 

Shiru Aisha ta yi na wasu ƴan sakkani kafin ta ce ”Mama ki yiwa Unaisa nasiha da alama bata san abinda ta ke ba, wai yarinyarnan na ce mata ta dauki ƴarinya ta wanke mata jiki amma Unaisa ko motsawa bata yi ba daga inda take na yi mamaki sosai walh a gaskiya za’a samu matsala da Unaisa ya za’a yi ki so uba ki ƙi ƴaƴansa a ina aka taɓa yin haka,wlha Mama ƙi ja mata kunne gwara tun wuri ta gyara kar tasa ya fara tunanin bata son ƴaƴansa” tun sanda Aisha ta fara magana Mama kallon ta kamar baza ta yi magana ba sai kuma ta ce ”shirmen Unaisa ya yi yawa amma da ta shigo zan mata magana na ji dalilin da yasa ta yi hakan” ita dai Aisha bata sake cewa komai ba ta mayar da hankali kan wankewa Fauziyya jiki ita ko Fauziyya sai tsala ihu take tana kiran Mumy haka Aisha ta wanke mata jiki tsaf har wanka ta yi mata soso da sabulu ta wanke ta tsaf,ta shirya ta cikin kayan ƴarta Nana ƴar 2 years ta fesa mata turare mara ƙarfi,zafin da jikin Fauziyya ya yi yasa Aisha kiran ɗanta Auwal mai shekaru sha uku da shigan sa kenan daga shago ta ce ”kaita wajen babanta a waje ka ce masa jikinta ya yi zafi sosai ko zai maida ta gida wajen mamanta ta bata magani,kuma ya aiko gobe a ƙarɓo uniform ɗinta” ta kare magana tare da kunna fanfo inda ta fara wanke uniform ɗin Fauziyya

 

 

 

 

Kamar yadda mahaifiyarsa ta faɗa masa hakan ya yi,Fauziyya ko da gudu ta nufi inda Ɗalha ke tsaye ta ɗaga masa hannu alamar ya dauke ta,daukan ta ya yi yana shafa fuskar jin yadda jikinta ya yi zafi sosai ya mayar da dubansa ga Unaisa ya ce ”l think zan wuce kawai she is runnig temperature” da kyar Unaisa ta iya buɗe baki ta basa amsa tsabar yadda ranta ya ɓace ita da ta shirya daukan hotuna ta sa a status amma wannan yarinya mai ido kamar ƙwai da shegen fari kamar uwarta ta ɓata masa plan duk wannan magana cikin zuciyarta take muryar Ɗalha ne ya ya katse mata tunani inda ya ce ”kar ki ji komai zan tura maki ƙudin sai ki siya kwai” bai jira cewar ta ba ya buɗe motarsa ya shiga Fauziyya ta yi lamo jikinsa yana jin yadda zafin jikinta na ƙaruwa,bai tsaya ko ina ba sai kofar gate ɗin gidansa lokacin karfe biyar da mintina goma ledar magani ya dauko ya fita daga motar,ya kulle motar ba tare da ɓata lokaci ba ya cire key daga aljihunsa rigarsa ya buɗe kofar entrance,nan parlour ya samu waje ya zauna ya shimfiɗa Fauziyya kan ɗaya daga cikin kujerun parlourn zuwa yanzu jikinta ya fara week,Ɗalha ya buɗe ledar magunguna kenan ya ji alamar zuban ruwa daga ɗakin Sumayya da Ummu Abiha tashi ya yi ya nufi hanyar ɗakin bayan shigar sa ɗakin ne ya buɗe kofar bathroom, idonsa ya sauka kan bathtub dake cike da ruwa ga wani kumfa dake saman ruwan,wani doguwar ajiyar zuciya Ɗalha ya sauke kafin ya shiga cikin bathroom ɗin ya kashe famfo bathtub,hannun rigarsa ya naɗe daga nan ya zura hannusa cikin bathtub ya ɗaga stopper nan take ruwan dake cikin bathtub ya fara raguwa,yana shirin barin bathroom ɗin ne idonsa ya sauka kan siter yaga duk sun ɓata da kashi ko flushing basu yi ba,bai bar bathroom ɗinba sai da ya tsaftace shi tsaf kafin ya fito yana share zufa,fitar da magunguna ya yi ya ɗiba kowanne kamar yadda aka rubuta jikin kwalin maganin a hankali ya ɗaga Fauziyya ya zaunar da ita,idonta ne ya sauka kan magunguna,nan ta sake wani kuka ta fara magana cikin hausarta da bai fita ta ce ”Dady ban ca a’a ban ca” nan Ɗalha ya shiga rarrashinta yana faɗin ”no..no.. no my princess za ki sha ba ki da lafiya jikin ki ya yi zafi you have take your medicaton” ita dai banda kuka babu abinda take sai faɗin Dady ban ca take,ganin da gaske baza ta sha ba yasa Ɗalha daura ta kafarsa inda ya riƙe hannayen ta da hunnusa ɗaya,ɗaya hannu kuma yana riƙe da magani,ya daura ƙafarsa ɗaya kan kafafunta duka biyu yana faɗin ”buɗe bakin ki,comm on open your mouth my girl” ko da wasa Fauziyya ta ƙi buɗe baki hakan yasa Ɗalha ya sakin hannunta ya matse mata baki da kyar ya samu ta buɗe bakin bai tsaya ɓata lokaci ba ya zuba mata magani a baki,har cikin zuciyarsa ya ji ɗadi ganin ya samu ya zuba mata magani a baki,yana shirin daukan dayar magani Fauziyya ta fesar da maganin da ya zuba nan ƙasan tiles,wani irin zafi zuciyar Ɗalha ya yi ji ya yi kamar ya kai mata duka amma sai ya fasa ganin yadda idanunta suka yi ja sosai numfashinnta na fita da zafi,nan take wani irin tausayinta ya ziyarcesa bai san sanda ya fara magana shi kaɗai ba kamar wani zararre ”yanzu ya ya zan yi da ke Fauziyya ba ki da lafiya amma kin ƙi shan magani wannan wata irin musiba ce? Amirah ba ki kyauta min ba ki kyauta wa yaran nan ba innalillahi wa inna ilaihi raji’un ya rabbi” ya ƙare magana cikin karayar murya bai hakura ba ya sake gyarawa Fauziyya zama ya dauki ɗaya daga cikin murfin magunguna ya sake ɗura mata a baki nan ma ta fesar wannan karon a fuskarsa ta fesar,cike da jin haushi ya kuma daukan ɗaya ya ɗura mata,da sauri ya kama lips ɗinta duka biyu a dole sai ta haɗe maganin Fauziyya taga azabar da bata gani ba sai mutsu mutsu take da kafafunta Ɗalha ya ƙi sakar mata baki,bayan wani ɗan lokaci ya samu ta haɗe maganin,a hankali ya sake lips ɗinta cike da jin daɗin shan maganin da Fauziyya ta yi ya saki wata murmushi ya ce ”that’s good my princess” bai gama rufe baki ba Fauziyya ta fara wani irin tari,kafin Ɗalha ya ankare ta kwarara amai nan ƙasan parlour ta ɓata gaba ɗaya jikinta har shi ta ɓata masa jiki,ji ya yi kamar ya zai yi hauka harda rashin lafiya take tsabar ɓacin rai Ɗalha bai san sanda ya ɗaga hannu ya duke ta ba nan ta ƙara kwala wani uban ihu tsabar yadda marin ya yi mata zafi bata san sanda ta miƙe tsaye ba ta shiga zaga parlour tana ihu tana kuka,ko kallo bata ishe shi ba ya tashi zuwa bedroom ɗinsa ya gyara jikinsa,bayan fitarsa daga bedroom ne yaga Fauziyya kwance ƙasan parlour har ta yi barci nan kusa da amai da ta yi,shiru ya yi yana tunanin ta ina zai fara,ɗazu kafin Amirah ta bar gidan saida ta gyara ko ina har turare ta kunna cikin burner amma in few hours yaran sun ɓata gidan gaba ɗaya,gida ya koma kamar anyi sati ba’a share ba,tun daga parlour har ɗakunansu sun ɓata ko ina ko ina kaca kaca wasan da suka fita ɗazu ne sun kwaso datti a kafafunsu ko ina alamar kafarsu haɗe da datti,ga kayan wasa ta ko ina,kusan duka toys ɗinsu suka watsar a parlour

 

 

 

Bayan dogon nazari Ɗalha ya dauke Fauziyya ya kai ta bathroom ya gyara mata jikin barinta ya yi cikin bedroom ɗinsa saboda sosai take runnig temperature,gyaran gidan ya fara,da parlour ya fara bayan ya gama share parlour ne yana shirin moping wayarsa ta fara ƙara alamar shigar kira,ganin shugaban islamiyyar su Sudais ke kira murya can ƙasa ya ce ”shirt l almost forgot about them”daga haka ya masa kiran bayan sun gaisa ne shugaba islamiyyar ya ce ”Alhaji ba’a dauke yara ba muna shirin ƙulle makaranta magriba ta ƙarato” nan Ɗalha ya fara kame kame sai kuma ya ce ”motata ce ta samu matsala amma ina hanya” bai jira cewar shugaban makaranta ba ya katse kiran tare da yin wurgi da mopper murya can ƙasa ”da ni ki ke Amirah a tunanin ki zan ƙaraya ne na dawo da ke? dan kawai kin bar min yara bazan taɓa dawo dake ba” yana gama faɗin haka ya wuce ɗaki daukan Fauziyya ya yi ya fita ya sata a mota lokaci guda wani mugun wari ya ziyarce hancin sa sai yanzu ya tuna bai wanke inda Fauziyya ta ɓata da bayangida ba ɗazu,hakan yasa ya mayar da ita back seat,daidai lokacin da aka fara kiran sallar magrib Ɗalha ya yi parking kofar islamiyya Sudais tare da ƴan uwansa suka nufi motar Dadynsu yadda shugaban islamiyya ya ba Ɗalha hannu suka yi musabaha cike da mutuntawa Ɗalha ya ce ”a yi mana afuwa Mallam” Malamin ya ce ”a’a babu komai Allah ya kiyaye gaba Ɗalha ya amsa da ameen,bayan komawarsu gida Ɗalha ya cewa yaran su shiga ciki shi kuma ya tsaya wanke seat ɗinda Fauziyya ta ɓata ɗazu,ya dauki kusan mintuna ashirin kafin ya gama wanke seat ɗin,daga haka ya shiga gida dan gabatar da sallar magrib,idonsa ne ya sauka kan tiles ɗin parlour da ya gama share moping kaɗai ya rage masa so yake ya yi magana amma ya ƙasa furta komai wani tunani ya faɗo masa hakan yasa ya yi shiru ya yi wucewar sa bedroom ɗinsa,ya gabatar da sallar magrib,ya so ya zauna ya yi azkar ɗin yamma da ya saba yi kullum amma gaba ɗaya ya ji bashi da nitsuwa gani ya ke in ya ƙara koda minti ɗaya ne za su iya ɓata gidan gaba ɗaya hakan yasa ya shafe addu’a ya fito parlour wani irin tsawa ya yi masu duk suka natsu sun mayar da duban su garesa,fuskarsa babu alamar wasa ya ce ”maza kuji ku yi alwala ku yi sallah babu musu suka yu hanyar ɗakunan su,kwalbar maganin da ya siyawa Fauziyya wanda aka ce masa na barci da sa cin abinci ya gani a ƙasa kwalbar ta fashe duka maganin da ke cikin kwalbar ya zuba dafe kansa ya yi zuwa yanzu ya fara karaya gani yake kafin safe yaran za su iya yin ajalinsa,ba tare da ya yi magana ya dauke tsintsiya ya share kwalbar ya sa mopper ya goge wajen zama ya yi kan ɗaya daga cikin kujerun parlourn ya na tunanin ta ina zai fara abinci zai dafa masu ko gyaran gida,ga Fauziyya ta ƙi shan magani kuma ga dukkan alamu akwai yunwa a cikinta,wani tunani ya faɗo masa hakan yasa ya dauki Fauziyya tare da sauran magungunan ta ya fita daga gidan,ya nufi hanyar gidan Mama Uwani makwabciyarsu,zaman mutunci suke da Amirah, da Mama Amirha da yaranta ke kiran Mama Uwani,sallama Ɗalha ya fara yi tare da kwankwasa kofar gidan Mama Uwani,ya dauki a ƙalla mintuna shidda tsaye kafin Mama Uwani ta buɗe masa kofa ganin Ɗalha yasa Mama Uwani faɗaɗa fara’arta tana faɗin ”sannu da zuwa son” haka take kiran Ɗalha ta ce ”bismillah shigo” har cikin parlourn Mama Uwani Ɗalha ya shiga

 

 

YOTA ID/022

About the author

mynovels

Leave a Comment