WhatsApp Join WhatsApp Channel
Hausa Novels

Labule Asirin Mai Daki Hausa Novel Complete

Written by mynovels

Labule Asirin Mai Daki Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

“Wacece Maryam Sa’id?”

Tana aji uku ne taci karo da wannan tambayar a cikin slam book da ake ta zagayawa dashi tsakanin ‘yan ajin, haka suka dinga kallon juna ita da littafin nan,  saboda ita dai tun asali ba gwanar bada labari bace ba, ko film ne ta kalla in kace ta baka labarin abinda ya faru saita rasa ta inda zata fara, akwai lokacin da suke kallon wani indian series mai suna “saloni ka safar”, haka suke binshi kafa da kafa, in babu wuta za’a kunna generator, kamar wanda akayiwa asiri. Wani episode mai zafi akayi, duk basa nan sun tafi wajen sunan matar Khalifa da ita ba’aje da itaba saboda tana karambau, haka suka zagayeta suna jiran tayi musu bayani, data fara kamo tsakiya tana jonawa da farko, haka Shukra taja tsaki

“Wallahi da gangan ma mukayi asarar lokacinmu muna tambayarki Maryam, ke an taba kulla abin kirki dake daman? In dai labaranki mutum zai jira ya hadu da takaici”

Kuma tasan da gaske ne, tunda a ranar ta rasa ta inda zata fara amsa wannan tambayar, to wacece ita ta wacce fuska? Halaye? Tarihi? Halaye dai ai ba masu yawa bane ba, ba kuma boyayyu bane, tunda kowa za’a tambaya tashin farko zaice ita din mafadaciya ce ta kwatance, dan ko a lokacin da take primary ba’a cacar baki da ita, kafin ka numfasa ta sauke maka mari in yaso a kacame da dambe, wanda yafi wani karfi ya kwaci kanshi, tunda har wanda suka wuceta aji saida suka kiyayeta, haka ake cewa yanda take lange-lange kamar za’a iya kaita kasa, kashi dayane da ita. Haka ‘yan gidansu in suka fadi wannan zasu kara da wani hali nata guda daya, kishi, tsananin kishin da har Hajjarsu take roka mata sauki akanshi.

Dan kishine irin wanda bata kaunar taga wani ya rabi ko da ‘yan uwantane, dan akansu nema Hajjar ta fara gane kishin da Maryam take dashi har takan ce

“Allaah Ya rabaki da wannan kishin Maryam, ‘yan uwanki ma kenan, inaga mijinki?”

Kawayen Khairi kuwa da take ganin suna kusan sa’anni da ita sun sha wahala a wajenta, musamman na cikin unguwarsu, balle kuma a makaranta, baka isa a fito break ta ganku kuna cin abinci da ita ba, saita turmusaka cikin kasa, gashi ko taron dangi akayi mata sai anyi da gaske ake iya kaita kasa, shisa duk suka hakura da kawancen da Khairi, idan Hajja ta daketa kan abinda tayi kuwa saita je ta rama akansu, tunda halinta na uku taurin kaine, inta kafe ko kasheta za’ayi ba zata daina abinda takeyi ba, shisa ma Alhajinsu ya hana dukanta saiya kama dole

“Kar yarinyar nan ta kangare muku, yara irinsu ja ajiki, soyayya da fahimta suke so ba kyara ba, ku fahimci abinda bataso din, idan abune da zai iya cutar da ita a gaba sai ayi kokarin fahimtar da ita a hankali…”

Hakan kuwa aka cigaba da tafiya, amman kuma ai tana ganin yanda take kara girma tsoron halayen nata na cika idanuwan Hajja, amman kuma ai kamar kowa ba zata rasa halaye nagari bako? Kuma tana da yakinin sune suka rinjayi wanda suke hadata fada da kowa na gidan suka sakata shiga ransu sosai, wani abu da take alfahari dashi a ko ina, tunda yanzun zuciyar Maryam babu kowa a cikinta banda iyaye da ‘yan uwa. Ita kawaye basu dameta ba, kawai ‘yan uwanta su hadu su sota fiye da kowa, ko da wani zai rabesu tofa kar su damu dashi yanda suka damu da ita, kai gabaki dayama su din kar wani ya nuna yana sonsu fiye da ita, shine matsalarta.

To duk ya zata takaita wannan tunda a hakama kadan ne a cikin halayenta ta sakasu a wannan slum book din da aka bata shafuka biyu kacal a ciki, idan kuma asali ake nufi ta ina zata fara? Ai asalinta ba zai cika batare da iyayenta ba, tushensu shine nata, babu ta inda zata bada tarihinta bata hada dasu a ciki ba. Alhaji Sa’id shine mahaifinta, kuma dan asalin kauyen Matazu ne ta jihar Katsina, su tara mahaifiyarsu ta haifa, amman su biyu suka rayu, dan tanayin wabi ne, sauran yaran duk rasuwa sukeyi kafin ayi suna, har a lokacin abinka da kauye akace watakila ta zagi mayya ne da take ganiyar kuruciya, shine take bibiyarta, wasu kuma suce ko asiri ne, kowa da abinda yake fada. Sa’id ne ya fara tsayawa, bayanshi ta kara guda biyu sannan Murtala, dagashi kuma sai haihuwar ta tsaya mata.

Masu karamin karfine matuka, tunda gonar gado ce mahaifinsu da gabaki daya danginshi ake nomawa, a ciki ake duk wata hidima ta yau da kullum, annobar amai da gudawa da ta shiga garin a wata shekara, ana tsananin zafi, itace tayi ajalin mahaifinsu Sa’idu, inda mahaifiyarsu tabi shi kwanaki sha biyu tsakani, sai rikonsu ya koma hannun Kanin mahaifinsu Ya’u, shikuma duk karamin karfinshi mata hudune dashi, yara maza duk wanda yakai shekara biyar sai a watsa shi almajiranci, dan haka aka hada da Sa’idu da yake da shekara bakwai lokacin, da kuma Murtala da bai karasa cika hudu ba tunda shi kanshi Ya’u yasan cikin matanshi babu wadda zata dauki wahalar Murtalan.

Da aka tashi kuma duk kukan da suka dingayi sai aka rarrabasu, shi Sa’idu akayi Zaria dashi, Murtala kuma garin Kano. Da yake Sa’id irin yaran nan ne masu shiga rai, yana da wani sanyi a tare dashi idan ka kalle shi, baiyi wahalar abokai da suke fita yawon bara tare ba, bai kuma rufa wata uku ba ya zamana ko shi kadai ma saiya fita yawonshi, tunda sunyi sa’a Malamin nasu nagari ne, banda karatu baya sakasu irin aikace-aikacen gona da wasu Malaman sukeyi. A irin yawon ne yaje wani gida a cikin unguwar samaru yawon bara, da aka bashi abinci, yaga shinkafa da miya harda salak, rabon da yaci abinci ya koshi irin ranar tun iyayenshi na da rai, yana gamawa saiya rabe kasan wata bishiya da take kofar gidan ya kwanta.

Bacci ya kwashe shi, wani bacci da ya zame masa silar alkhairai masu tarin yawa, dan a wannan kwanciyar da yayi ne maigidan ya dawo ya same shi, kuma kankantarshi saita bashi tausayi matuka, ya shiga gidan nashi dashi, ya cewa matarshi kullum zai dinga zuwa ana bashi abinci, batayi musu ba ta amsa. Safe, rana, dare haka Sa’id yake zuwa karbar abinci, ya taba zuwa ya samu ganyayyaki duk sun zubo a harabar gidan yace ta bashi tsintsiya ya share, da taki tunda almajirin da yake zuwa yanayi mata wannan aikin a lokacin Babba ne, zazzabi yake fama dashi kwana biyu.

Sai dai nacin da Sa’id ya saka saita bashi, tayi mamakin ganin ya share gidan kwal, sai gashi yana dan yi mata kananun aikace-aikace, sai aiken da ba’a rasa ba, a hakan kuma yayi sabo da dan gidan Mustafa, har iyayen saida suka dinga mamaki, tunda Mustafa kowa yasan kamar dage yake wajen fada, shisa duk ya kore abokan harna cikin unguwa, amman a ranakun da babu islamiyya, alhamis da juma’a har sautin dariyarshi zaka dinga jiyowa suna labari da Sa’id, akace mai da wawa, sannan su Alhaji Usman mutanen kirkine kwarai, irin kirkin da baya wahalar samu a zamaninsu, kirkin nan na maida dan wani naka, sai son inganta rayuwar Sa’id ta shiga rayukansu, da kanshi ya taka har makarantarsu Sa’id sukayi magana da Malaminshi, ya dauke shi ya sakashi a makarantar boko.

Ajiya A Duhu Hausa Novel Complete

Wannan shine mafarin samun ingantacciyar rayuwa. Sa’id, amman duk da haka yasan iyakarshi, yanda duk suke janshi a jiki yana kama kanshi na sanin fa har abada shidin almajirin gidansu ne, ya samu karatu har matakin NCE inda baisha wahalar samun aikin koyarwa ba a lokacin, sai dai ya samu aikin ne a garin Kaduna, shikuma Mustafa da yake yana da wata irin kwanya, kuma gurbin karatu a Ahmadu Bello ya samu, sai gashi ya samu scholarship zuwa kasar Ingila inda ya dora karatunshi, yayi dabarar yin duk wani aiki da ya samu yana adana kudadenshi, yana da burika masu yawan gaske, babban burinshi shine zama hamshakin mai kudi.

Lokacin daya dawo har Sa’id yayi aure, ya auri Asma’u da kannenta dalibai ne a makarantar da yake koyarwa, a lokacin ita tana makarantar kwana ne aji uku, kuma sun taka har Matazu domin tabbatar da gaskiyar asalin Sa’id kafin su bashi aurenta. Haka dan uwanshi Murtala bayan gwagwarmaya daya sha, tunda shi karancin shekaru yasa kamar ba zai rayu ba a almajirancin da aka kaishi, ya fada harkar garuwa, ya samu nasibi a cikinta, dan da wannan sana’ar yayi aure, yana kama haya anan cikin kwaryar Kano, kafin daga baya ya bude gidan ruwan shi, inda ake dandazon dibar ruwa duk rana.

Yanzun haka yaranshi biyar ne da matarshi Furaira data saka yaran suna kiranta da Mummy, dan kuwa macece da batayi ilimin boko ba, na addinin ma an samu na bautawa Ubangiji, amman tana matukar son harkar gayu, kullum gidanta tsaf zaka ganshi, haka ma yaranta guda biyar ne kacal, tunda taji labarin tsarin iyali ta karbe shi da hannu bibbiyu, so takeyi su samu ingantacciyar rayuwa irin wadda ta gani a tare da yaran Alhaji Sa’id lokacin da takai musu ziyara a garin Kaduna. Suyi ilimi na boko dana addini. Sunayensu ma itace take shigewa ‘yan gayu tana adana duk sunan da yayi mata dadi, Asaad ta farayi, sannan Aminatu da taci sunan mahaifiyarta suna ce mata Minal, Ishaq, Hibba, sai Autarta da Murtala ya sakawa sunan mahaifiyarshi Zainab suke ce mata Khairi. Wannan sune iyalan Murtala kanin Alhaji Sa’id.

A filin jirgi Mustafa ya hadu da Rumana da babban wanta, da kuma matarshi, tun daga kallon farko yaji cewar yaga abokiyar rayuwa, Kanuri ce, yar Maiduguri, baka kyakkyawa ta gaske. Duk da yaji dar saboda fuskantar da yayi na cewa ‘yar masu kudi ce, haka dai yayi jarumtar karbar katin dan uwanta da yagansu tare. Kuma da yake akace matar mutum kabarinshi, bai samu wata matsala ba, saiga Bafullatanin usuli ya taka har Maiduguri neman aure,dan Mustafa farine kal, ko sumar kanshi ka kalla zaka san cewa bafulatani ne, iyayenshi tsatsonsu fulanin Yola ne. Anyi shagali dai-dai da zamanin, tunda bayan aiki daya samu a shekarar da aka bude gidan man NNPC, wato 1977, duk da baya fatan aiki a karkashin kowa, suka tare a garin Abuja.

Ya fara binciken yanda zai kafa business dinshi na siyar da motoci da tun asali shine plan din da yake dashi. Da taimakon Allaah da kuma tsantsar naci irin na Mustafa ya kafa AU motors, inda daga baya ma ya ajiye aikin nashi da kudi suka fara zauna masa, kuma ya tattara ya baro garin Abuja ya dawo Kaduna ya kara kafa wani branch din na AU motors, yanzun haka yana da branches uku ne, Abuja, Kaduna, Kano, sai dai na Kadunan ma duk yafisu karfi. Jinkirin haihuwa suka samu shi da Rumana, wani abu daya saka iyayenshi matsa masa karin aure ganin irin dukiyar da yake ta tarawa babu magaji a fadarsu.

‘Yar uwarshi ya aura Fadime, bayan tarin rikicin da suka sha da Rumana, dan macece ita mai izza da ji da kai, sannan tana matukar kaunarshi. A shekarar Fadime ta samu ciki, kuma saida tayi yara uku sannan Allaah Ya bawa Rumana ciki itama. A yanzun haka, Rumana na da suke kira Mami, na da yara uku ne, Munira, Anisa, sai Haris. Inda Fadime (Umma) take da guda bakwai, Aliya, Halima, Kubra, Shatu, Mukhtar, sai Ibrahim.

Kuma Maryama da duk ‘yan uwanta sunsan amintar da take tsakanin babansu Sa’id da kuma Mustafa, dan karin karfin arzikin Sa’id din kowa yasan sanadin Mustafa ne daya kara fadawa harkar noma, sai kuma ya zamana Sa’id din shine yake kula masa da wannan bangaren, in ba haka ba, da basu taso cikin rufin asirin da suke dashi ba, dan aikin koyarwar da yakeyi ba wani kudi bane da za’ace za’ayi hidimar yau da gobe a ciki har a adana wani abu. Dan rufin asirin da Sa’id din ya samu a lokacin, ya kuma karasa ginin daya daukeshi shekaru takwas yanayi, sai ‘yan uwan da suka watsar dashi a baya suka dawo sunaji dashi, ciki kuwa harda Murtala da Sa’id din shine yake bibiyarshi sosai da zumuncin nasu ya jima da watsewa. Saima da akaji ya tafi aikin Hajji, bayan dawowarshi kuma Asma’u da suke kira da Hajja tun asali saboda Hajiyayye ake ce mata a gidansu da yake an haifeta ranar arfa, su sai suka takaita shi zuwa Hajja, sai dangi sukace dawa Allaah Ya hadasu ya dinga biya musu bukatu in ba Alhaji Sa’id ba.

Su bakwai Asma’u ta haifa, Ahmad, Khalifa, AbdulKarim, Zahra, Yazid, Asiya sai auta Maryam. Amman tun tasowarsu kullum gidansu cikin jama’a yake, yaran dangi da sukazo hutu daga Matazu, wasu kuma na wajen Baba Murtala da sukazo daga Kano. A cikinsu kuwa wasu ma nan suka kwaso kayansu suka dawo da zama, su bakwai sai suka samu karin mutum biyar, Maimunatu, Sagir, Adnan, Saifullahi, da kuma Khairiyya da ‘yar gidan Baba Murtala ce, kuma shekara daya da rabi ta bawa Maryam. Hajja duk ta hadasu ta rike kamar daga cikinta suka fito, tun tana samun matsala da wasu a cikinsu har suka warware suka saki jiki suna mata rikon uwa kamar yanda takeyi musu na ‘ya’ya.

A irin amincin da yake tsakanin Alhaji Sa’id da kuma Alhaji Mustafa da Zahra ce ta makala masa Baban Tudun Wada, saboda acan unguwar yayi katafaren gidanshi a garin Kaduna, sunan saiya bishi. Ya kamata ace matansu ma suna wannan amincin, amman babu, saboda Hajiya Rumana bata bada wannan damar ba, musamman da taji labarin wanene Alhaji Sa’id a bakin ‘Yan gidansu Alhaji Mustafa, a raine take kallonshi, saboda har a zuciyarta ta kasa aminta dashi a matsayin aminin mijinta bayan yaronshi ya kamata ace ya zama. A karkashin shifa yake ci yana sha. Ita kuwa a irin izzarta me zaija mata kawance da matarshi.

Shisa itama Hajjan ta kama kanta, duk kirki da hakurinta tana da gudun wulakanci, sannan daga ita har mijinta dabi’ar cusa kai ba halayyarsu bace ba, yanda duk Alhaji Mustafa yaso ya juya Hajiya Rumana akan sha’anin gidan aminin nashi dole ya gaji ya kyaleta, garama Fadime ita duk wata hidima da zata taso a gidan Alhaji Sa’id da ita ake wuni anayi har a kammala, duk da Hajja ta girmeta saita zame mata kamar wata Yayaa da bata da ita a kusa tunda duk yan uwanta suna can Yola. Wannan zumunci nasu yayiwa Hajiya Rumana tsaye a wuya yana kara saka mata tsanar duk wani abu daya danganci Alhaji Sa’id da ahalinshi.

A lokacin bata hango wata alaka zata shiga tsakaninta da iyalan Alhaji Sa’id data wuce tunaninta ba.

In su Maryam sunje gidan Alhaji Mustafa, in zasu karaci buga bangaren Hajiya Rumana dansu gaisheta, ba zata taba bude musu kofa ba, daga bayama sai suka daina zuwa, suyi zamansu bangaren Fadime, har su gama abinda ya kaisu a mayar dasu gida. Wannan shine tarihin da Maryama zatace nata, tunda ya hada duk wani abu kama daga asalinta, da kuma duk wasu mutane masu muhimmanci da suke da alaka ta kusa data nesa da ita. Maryam taso ace ta samu Kakanninta, tunda a halin yanzun Malam Ya’u kawun mahaifinta ya jima da rasuwa, sai matarshi Hajiya Inna, kuma sosai Maryam takejin dadin zama a wajenta duk idan sukaje Matazu, saboda labaran da take basu masu abin dariya da ban al’ajabi.

Tana aji uku na a makarnatar Sakandire Hajiya Inna ta rasu, kusan tafi kowa jin mutuwar ‘yar tsohuwar a gidansu, ta jima tana kuka, har saida kowa ya dinga mamakinta. Kuma kusan Maryam zatace a wannan lokacin ne mutuwar ta bude mata ido, tasa ta fara fahimtar rayuwar gabaki daya dama abinda ta kunsa. Dan a lokacin ana gab da bikin Adda Maimunatu ne, tunda ita taki karatun, dakyar tayi diploma, tunda ta hadu da Yasir dashi sojane, ta rufe idonta, sonshi takeyi har bata iya boyewa a gaban kowa, haka Maryam zata dinga lekensu idan yazo zance, labarin Hajiya Inna na fado mata.

Wani labari da yaki barinta har yau, lokacin tana aji daya a sakandire Hajiya Innar ta basu shi, amman ko yau ta rufe idanuwanta tar muryar Hajiyar ke dawo mata

“Ai mu da Allaah Yayiwa tsahon rai muna ganin abinda ya ishemu, mu lokacinmu ai sai kayi sa’a ne ma za’a fada maka anyi maka miji, koni nan bansan kalar Alhaji ba sai bayan an daura mana aure, saboda yanda iyayenmu suka san cewa sun isa damu, ba zamu koyi numfashi mai karfi ba balle muyi musu kan hukuncin da suka yanke mana”

Da yake maganar ta zauna mata, duk da karancin shekarunta haka ta dinga juya zancen duk lokacin da zataji an saka rana ko kuma anyi aure, tana kara hankali tana mamakin yanda za’a daura maka aure da mutumin da baka taba gani ba

Ta ina zaku fara zaman?
Ya zakuyi a haduwar farko?
Me zakace masa?
Shi ma kuma fa?
Idan ita akayiwa irin auren nan ya zatayi
To wai idanma aka daura sai ta ganshi baki kato irin mazan da basa burgeta sai yaya kenan?

Dan ita duk a cikin abubuwan data dinga tunani, mafi muninsu shine ace namijin ya kasance baki, haka kawai bakaken maza basa burgeta, watakila dan mazan farko-farko da ta farajin sun kwanta mata a rai farare ne, fararen ma indiyawa, tunda gidansu mayun kallon indian films dinne harma da series. Duk sanda zata ga manyan matan gidan na zance in taga saurayin baki saita tabe baki, inta ganshi fari kuwa ta dinga fara’a kenan kamar wajenta akazo. Shisa a yau da ta hangi Adda Maimunatu da Yasir sai take jin inda ace yafi haka haske da anyi namiji mai kyau, da Addanta ta more miji, to wanda ya auri fari ai shiya more, ko wajen hotunan biki saima sunfi haskawa.

Ace dai farine kamar Hamma Ishaq din Baba Murtala, murmushi ya kwacewa Maryama, duka shekara daya da wani abu kenan da Ishaq din ya samu gurbin karatu a Zaria, taji ance Injiniya zai zama, da yake ba zata tuna fuskarshi ba sosai, Khairi dai bata cika hasken fata ba, kusan ita Maryam dinma ta fita haske, sai gashi ya biyo ‘yan gidan da suke ABU din suma sunzo hutun karshen mako, Ishaq farine har wani dorawa-dorawa yakeyi, da gashin kanshi kamar ya kara tirawa, dogone amman bashi da jiki, ‘yan gidansu sunce wai Khairi tafishi kyau, duk gidan Baba Murtala ma babu wanda aka tarawa muni irin Ishaq, saboda shi guntun hanci gare shi, sai wasu jajayen labba shi ba bature ba. Haka ta dinga kallonsu kamar basu san abinda sukeyi ba.

Ta ina za’a hada Khairi da Hamma Ishaq? Anya a wankan farko na jarirantaka an wanke musu idanuwansu da kyau kuwa? To ai a idanuwan Maryam duk wanda yazo a fari, musamman namiji, to cikin kaso dari na kyau dai ya tafi da tis’in, sauran goman kuwa ai ba wani abu bane ba, ballantana shifa ga gayu, ga kamshi, ga labbanshi irin na indiyawan da take gani a fina-finai. A zuwanshi na karshe gidansu, wajen satar kallonshi duk ana zaune a falo, ta dibo kunun aya, tayi tuntube tana shekawa Adnan shi a saman kai, ya kuwa kai mata wani duka da Ishaq ya tare mata yana fadin

“Ya za’ayi ka kaiwa mace irin wannan dukan Adnan? Ai sai kaji mata ciwo”

Shikuma Adnan din yaja tsaki yana mikewa, baiko ce musu komai ba

“Dawo nan kinji kanwata…”

Ta kalle shi, yanda ya ajiye kalmar kanwata din na zauna mata a wasu sassa na jikinta, shine abinda ya kashe mata jiki ya hanata mayarwa da Adnan maganar da tasan babu abinda zata janyo mata a wajenshi sai duka, a wannan ranar inda ace Maryam tasan cikakkiyar ma’anar kalmar da bature yake kira da “crush” da tace abinda ya faru da ita kenan akan Ishaq

Ya samu wani waje da yafi ko’ina laushi a zuciyarta yayi zaune batare dama ya sani ba…

#LubnaSufyan ✨
#WomenOfWords
#09035723778 (WhatsApp)

Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram ne kawai 20/06/2025 In Shaa Allaah, bayan mun kammala shafukan dandano.

Zaku iya biya ta: 9035723778 Opay, Lubabatu Sufyan.

NAGODE.

*

LABULE…Asirin mai daki

2

Yau Alhaji Sa’id yaje makarantar yaran ne ya biya musu kudi, wannan aikine da mazan gidan sukaso sauke masa tunda jimawa, amman yaki, har yau duk wani PTA da za’ayi, in ba uzuri na rashin lafiya ba da kanshi yake zuwa musu makaranta. Haka yakan ware wasu ranaku ya dauke su da safe ya sauke kowa a tashi motar, ko kuma yayi musu bazata ta hanyar zuwa ya daukosu, wani abu da baya gajiya da jin dadin yi, ko dan irin farin cikin da yake gani a fuskokin yaran nashi. Kowane da nagari baya bukatar dalilin da zaiso iyayenshi, da ace ana da bukatar wannan dalilin, Alhaji Sa’id zai kasance cikin iyayen da ba zasu taba gajiyawa ba.

Tun yana makarantar yake ganin kiran Hajiya Rumana, yasan ba zai wuce kara ta kawo masa ba, a lokutta da dama har mamakinta yakeyi, yasan inda zata iya rabashi da Alhaji Mustafa, data jima da yin hakan, sannan kuma bashi da wata daraja da kima a idanuwanta, ko yaranta in dai zasu hadu haka suke gaishe dashi kamar an cusa musu tsumma a baki, da yake sunyi gadon dagawa da jin kai irin nata. Amman kuma duk randa Alhaji Mustafa ya murde mata, bata da wanda zata kira sai shi. Saida ya gama abinda yakeyi, niyyarshi ma saiya koma gida ya karya, amman yanda ta dinga jera masa kira bayan kira ya tabbatar matsalar babba ce, shisa ya daga, aikuwa kuka takeyi kamar anyi mutuwa, har saida gabanshi ya fadi, bai ma fahimci abinda take fada ba, ya daiji Haris ya kuma ji Mustafa, sai yace mata gashi nan zuwa gidan.

Ya kuwa karya mota yana nufar hanyar Tudun Wada, da yake akwai ‘yar tafiya, makarantar yaran na wajen Rabah Road. Yana isa, baima shigar da motarshi ciki ba, ya dai juyata yanda in yazo tafiya ba sai yayi hakan ba, kanshi tsaye bayan ya shiga gidan ya wuce bangaren Alhaji Mustafa, ya kwankwasa da sallama a bakinshi, da kanshi ya taso ya bude masa kofar yana dariya

“Yanzun nake zancenka a raina fa”

Cewar Alhaji Mustafa, sukayi musabaha, suna kara gaisawa kamar wadanda sukayi shekaru basu hadu da juna ba, kallo daya zakayi musu ka fuskanci irin shakuwar da take tsakaninsu

“Yanzun dinma kararka aka kawomun”

Alhaji Mustafa yaja tsaki mai karfi

“Karma ka fara shiga maganar nan Sa’idu, na riga na rantse saiya koma inda ya fito, in taga ba zata zauna ba itama zata iya tattara nata kayan ta bishi”

Ya karashe maganar yana haki saboda yanda ranshi ya kara baci lokaci daya

“Azumi uku dai, ai bansanka da raki ba”

Hararashi Alhaji Mustafa yayi

“Bafa wasa nakeyi ba…”

Ido ya dauka ya sakawa Hajiya Rumanan, daman jiranta yakeyi daga ita har Haris din. Tun lokacin da ya aureta ya fara gane halinta na jin kai da nuna isa, sannan da ace shi din namiji ne mai sanyi, ba karamin raini zatayi masa ba. Halinshi na kin daukar da yawa daga dabi’unta yasa ta dinga kokarin sauke kadan daga ciki, musamman akan danginshi da take ganin basu kai su rabesu ba. Duk da haka in sunzo din ba dadinta sukeji ba, akace shimfidar fuska ma wani abune, to harsu tafi in ba magana takeyi ba, babu wanda zaiga hakoranta.

‘Yan uwanshi basu fara jin dadin kawo masa ziyara ba sai bayan daya kara aure, sai kuma ta tsiro da wani abu na kai masa korafi cewa yanzun duk wani nashi ya juya mata baya, basa ma sauka bangarenta saboda ya auro tasu, kuma suna ganin ita bata haihu ba, wani zubin ma kuka take sakashi a gaba ta dingayi, ai sunzo gidan taga sunayi mata dariya akan rashin haihuwarta, bai huta da wannan fitinar ba sai da ta samu cikin Munira, sai kuma bayan ta haihu ya zamana hankalinta kacokan ya koma kan yarinyar, kamar shi dinma bata da wani lokacinshi saina yarinyar, da yake yana samun duk wani abu da yake bukata a tare da Fadime sai bai wani damu ba.

Gwarne tayi tsakanin Munira da Anisa, duka shekara daya da wata hudu ne tsakaninsu, har a danginta saida aka nuna a dauke mata Munirar sai taji da rainon Anisa, in yaso idan tayi kwari sai a dawo da ita, tace bata bukata duk zata iya hadasu tayi rainonsu. Sun fara samun matsala da ita ne akan yaran, lokacin Munira na da shekara biyar, ta dauki kofin shayin data gama sha tana bugawa a jikin TV, yana zaune sai yayi mata tsawa, yanda Hajiya Rumana ta karaso ta dauke yarinyar da ta fashe da kuka, idan wani ya hango daga nesa zaiyi zaton makami ne a hannun Alhaji Mustafa

“Ya za’ayi kayiwa yarinya karama irin wannan tsawar? Ai saika firgitata”

Kallon mamaki kawai ya dinga binta dashi a lokacin saboda yama rasa abinda zaice mata, a hankali kuma saiya kula da itafa akan yaran nan harshi bai isa ba, baisan abinda ya kamata dasu ba sai ita, kowanne irin hukuncine akansu in dai ba ita ta yanke ba to baiyi ba. Cikin danginta ma kafarta kafarsu, haka gidan iyayenshi, in dai ba tare da itaba, to yaran basa zuwa, yaran Fadime ma da yake tsoranta sukeji basa shiga bangarenta sam, saiya zamana tashin hankalin da Alhaji Mustafa ya dingayi akan ganin yaran sun shaku ya tashi a banza, shi dai ba wuni yakeyi dasu ba, wani zubinma sai yafi satika biyu baya garin. Sannan akan yaran Hajiya Rumana dai duk wata tufka da zaiyi yana barin gidan zatabi ta warware.

Da ta haifi Haris kuma sai abin ya kara ninkuwa, saboda soyayyar da take nunawa yaron ya wuce yanda za’a misalta. Haka aka cigaba da rayuwar, ya rasa yanda zaiyi da ita akan yaran, ga abin yana damunshi sosai, ko yanda su Munira suke mu’amala da danginshi a darare kadai ya isa abin takaici a wajenshi. A hankali kuma ya yarda Hajiya Rumana na daga cikin kaddararshi ne da babu yanda zaiyi da ita, abinda ya faru gaban idonshi dai zai tsawatar, shisa babu ma wata shakuwa a tsakaninshi da yaran, da yawan lokutta in suka gaishe dashi duk sai su bar falon, musamman Haris da yafisu sangarta, sai rashin jituwarsu yafi yawa da Alhaji Mustafa, tunda su Munira in fada yayi musu zasuyi shiru, harma su bashi hakuri.

Amman Haris sai yayi magana, sai yayi kokarin yin bayani ko dai ya fadi wani abin, duk zafin Alhaji Mustafa akan Haris ya fara dukan yaranshi, sukayi wata rigima da Hajiya Rumana har tayi yaji ta kwashi yaran ta tafi Maiduguri, rigima akayi sosai, tunda danginta sun goya mata bayane a fadan, dakyar Alhaji Sa’id yayi ruwa yayi tsaki ya shawo kan aminin nashi sannan aka samu dai-daito. Da yake a lokacin ma Haris din ya kammala primary dinshi, sai kawai ta nuna masa wata makarantar kwana ta kudi take so Haris din ya tafi, makaranta ce mai tsadar gaske da take a garin Kano. Da yaki amincewa dan yana ganin alamar kangara a tare da Haris din.

Yana gudun idan yayi nisa da idanuwanshi abin zai iya fin haka, da taga alamar kamar yana neman yaki amincewa, ya tafi Abuja, ya dawo ya samu Haris baya gidan, taje da kanta tayi masa duk wani abu daya kamata ta kuma biya kudin. Suka sake wani rikicin kamar zai saketa, nan ma dai Alhaji Sa’id ta samu, ya lallaba mata shi, sai dai har kasan ranshi bayason wannan makarantar kwanan da aka kai Haris, tunda ga ‘yan uwanshi nan a Kaduna suke karatunsu, Mukhtar da Haris din ya ba shekara biyu, alamu sun nuna ma lokaci daya zai hada da gama primary din da kuma haddar Al-Qur’ani.

Kuma yawan misalin da Alhaji Mustafa yake yiwa Haris da Mukhtar idan yanayi masa fada ko yayi laifine abinda yasa Haris din baya kaunar ya bude ido yaga Mukhtar, saiya zamana in zai hadu dashi sau goma saiya kwade shi sau goma, ko da kuwa Alhaji Mustafa zai karyashi ne, Mukhtar dinma daya hangoshi yake neman maboya, babu jituwa ko kadan a tsakaninsu. Mukhtar bai samu salama ba sai bayan tafiyar Haris makarantar kwanan nan. Kuma duk wani tsoro da Alhaji Mustafa yake dashi akan nisan Haris shine yake faruwa acan makarantar.

Tun satin da aka kaishi, maganar da Hausawa sukayi na sai hali yazo daya ake abota ta tabbata akan Haris, da yake aji dayane su dukansu sababbin dalibai ne, lokacin ake kokarin fahimtar juna. A satin ya hadu da, Idris, Sulaiman da Yakub, kuma sai aka hadasy daki daya, haka suka samu sukayi musayar gadaje da wasu a cikin dakin yanda suka koma makotaka da juna. Basu hada wata a makarantar ba duk wani Malami daya kwana ya tashi saida ya sansu, shugaban makaranta ya haddace fuskokinsu, suka kafa tarihin kasancewa ‘yan aji daya da suka gagari seniors dinsu. Idan wani laifin suka aikata, makaranta bata da contact din kowa saina Hajiya Rumana, idan ma aka nemi ganin mahaifinshi sai tace baya kasar.

Ita kuma ba fada take iya yiwa Haris din ba, duka yaran bakar fatarta suka biyo, gara Munira ita kai tsaye ba zaka kirata da baka ba, sannan fuskarta sak irin ta Alhaji Mustafa ce, hakama Anisa duk da bakinta dashi take kama, Haris ne duk yanda ake cewa ba’a gane kamannin jariri, a asibiti ma Nurses suka fara maganar yanda yake kama da ita. Hasken fatar da jarirai sukanyi Haris baiyi ba, da duhunshi ta haifoshi, kunnuwanshi bakikirin, aikuwa kafin ma ayi arba’in yayi baki, irin wannan duhun fatar Hajiya Rumana daya hadu da hutu yasa take wani irin kyalli, da yake tana da cikar gashin gira, sannan gashin kanta ma duk da bamai tsayi bane sosai a cike yake, ya kwanta luf har gaban goshinta, haka gashin idanuwanta ma, tana da irin kyawun da idan wasu manyan fashion houses din zasu ganta zasu kafa mata nacin zame musu model.

Wannan kalar fatar Haris ya biyo, cikar gashin da kuma kyan daga kallon farko. Yanda idanuwanta suke haka nashi suke, kamar da ruwa a cikinsu, in yayi dariya zaka ga ta isa har cikinsu, haka idan ranshi ya baci zaka ga kyallin bacin ran nan a cikin idanuwanshi, yana da irin idanuwan nan na kalilan mutane, idanuwa masu tonon asiri, wanda zasu haska maka har kasan zuciyarshi inka natsu a cikinsu. Shisa ko yayi kokarin kama bakinshi sai su fada maka duk wata kalma da bai furta ba. Wani irin so Hajiya Rumana takeyi masa da ita kanta bata san iyakarshi ba. Sone daya makantar da ita daga ganin laifukanshi, a wajenta kome Haris zaiyi kuruciya ce, zai bari idan yayi hankali. A wannan bigiren ya kammala ajinshi uku, ya kuma shiga aji daya inda ya zabi bangaren Art, tunda bason karatun yakeyi ba, yama fara kokartawa ne tun wani zagi da aka hadu akayi musu a staff room.

Wata Malama ta kirasu da

“Dakikai”

Kalmar nan tayi masa ciwo matuka, da yayiwa su Sulaiman magana kan ya kamata su fara maida hankali sai abin ya basu dariya, shi dai ya kyalesu ne tunda ba’a dole, ya dai fara canzawa ta bangaren karatun, shisa ya zabi Art din, a tunaninshi zaifi mishi sauki tunda akwai saukin lissafi a duka subjects din. Wannan shekarar itace tazo musu da sauyi daga shi har abokanshi, Idris duk yafisu girma, suna kiranshi da Barde, sai Yakub da soyayyar da yakeyiwa wani sanannen mawaki 2Pac yasa lakabinshi ya koma haka. Sulaiman daman ana kiranshi Lalaye ne tun suna aji daya. A lokacin Haris ne bashi da wani sunan banza.

Lokacin da suka dawo hutun first term na aji hudu a Sakandiri ne suka ga canji mai yawa tare da 2Pac, da yake su mahaifiyarsu bata tare da Babansu, tun suna primary suka rabu, gallazawar da mahaifinsu ya kula suna fuskanta ne ma yasa duk ya daukesu yana rarrabasu a makarantun kwana, sai dai babban wanshi da aka tura kasar Amurka, haka ya dawo ya zama rikakken dan shaye-shaye, yanzun haka wannan komawa hutun da 2Pac yayi ma an kai yayan Rehab saboda kwakwalwarshi ta fara samun matsala. Wani abu da iyayen 2Pac da ma abokanshi basu sani ba tun yana aji daya ya fara sha, daga maganin tari, saiya koma sato kwayoyin daya ke gani wajen yayan nashi, kuma sai kowa yayi bacci yake dauko daya ya rabata wajen gida takwas, saiya totse kashi daya yake iya samun bacci.

Kamar yanda dabi’ar masu shaye-shaye take, suna girma abin yana gaba, saiya zamana a hankali yake kara dosage din, wannan hutun daya koma kuma ya hadu da wasu abokan da suka girmi kanshi sai suka koya masa shan wiwi, da yake Baban 2Pac na tunanin zai cike musu gurbin rashinshi da na mahaifiyarsu hadi da gallazawar matarshi sai yake sakar musu kudi sosai da sosai, harma baisan abinda zaiyi da kudadenshi ba lokutta da dama, sai yanzun daya fara amfani dasu yana siyan wiwi. Itace yayi sneaking dinta da yawa, da yake abokan sun koya masa yanda ake boyonta, kasan takalman makarantarshi. Sai dare ya raba in ya nada saiya boye da lighter dinshi ya tafi bandakin makaranta ya zuqa.

Haris shiya fara kamashi, da farko ya tsorata, har saida sukayi fada da 2Pac din, amman abu na kuruciya, sai yanda 2Pac din yake nada wiwin ya kuma kunnata yana zuqa ya fara burge Haris, harya gwada shima, ranar farko kara daya ya zuqe bayan tarin daya dingayi a zuka wajen biyar kamar zai shide amman yaki hakura, sai dai maimakon cajin da yake ta kwadaita masa, sai yaji kamar kawai wani abune yake dan yawo a kanshi, bai bugu yanda ya kamata ace yayi ba. Kafin term ya kare saiya zamana sun janyo Barde da Lalaye sun fara wannan muguwar ta’adar. Waje suka gano ma cikin makarantar inda suke zuwa susha kayansu, data kare sai 2Pac ya kwanta ciwon karya, ya dingayi kamar wanda jinnu suka shafa, dole aka mayar dashi gida da permit na kwana uku zuwa sati daya in har bai samu sauki ba.

Kwananshi uku yayo musu kayanta ya dawo musu da ita makaranta, har shayi idan aka basu sai Haris ya faki ido ya marmasa ganyen a ciki, lokacin ne ya samu sunanshi na Ganja, dan ba karamin burge abokanshi yakeyi ba, sunce babban kai yake dashi. Kuma Hajiya Rumana ta kara kankaro masa mutunci data siya masa wata tsadaddiyar waya, haka yayi sneaking dinta zuwa makaranta, aikam ranar ko wani dan sarki ba zai nuna ma Haris jin kai ba. Inda ace Hajiya Rumana ta nutsu ta saka idanuwa akan Haris, data kula da canjin da ya samu, a lokacin kuma data ga duhun da labbanshi sukayi fiye da sauran fatarshi saboda yawan hayakin da yake bankawa cikinshi.

A lokacin yazo hutu, wanda daga shine zasu shiga aji shidda, Alhaji Mustafa ya jima bai saka shi a ido ba, kamar boye masa Haris din yakeyi, sannan Hajiya Rumana ma tana tayashi wannan boyon. Idan da yamma ya dawo gidan sai tace masa Haris na Islamiyya inya tambaya, idan da daddare ne kuma ace ya tafi sallar isha’i, ko kuma ya riga ya kwanta, shi dai bai karyata ba, amman basu taba haduwa da Haris a masallaci ba, duk da unguwar cike take da masallatai, amman ai na kusa shi duk suke zuwa. Sannan yaushe rabon Haris da wata Islamiyya? Ya kan leka dai in ance ya kwanta, har dakinshi, kuma yana samunshi a kwance din, ya dan tsaya sai yayi masa addu’ar shiriya da neman kariya kawai yaja masa kofar.

Sai ya yanke hukunci sai yaga Haris a ranar zai ma fita daga gidan, da yake girkin Hajiya Rumana ne, yayi zamanshi a falo, fushi take tayi masa da baima san dalili ba, yara ne suke yawan hadasu fada, kuma ai ya gaji ya hakura, ya yarda tafi karfinshi akansu, tunda da yace ba zai biyawa su Munira su tafi kasar waje ba, sai tace ita zata biya, nan ne ma ya nuna bata isa ba, sai dai in ya yafe mata su gabaki daya, dole ta hakura, amman yanaji yana gani duk sukayi applying Jami’ar Maiduguri, suka koma wajen danginta, sai dai suzo hutu, a lokacin ma ana maganar auren Munira dinne da wani abokin wasanta na bangaren Hajiya Rumana din, wanda haihuwar kasar Ingila ne, kasancewar mahaifinshi yana aiki acan, akwai ‘yan uwan Hajiya Rumana da yawa a kasashen waje. Yaron yanzun haka Likita ne, yana aiki a Birmingham ta kasar Ingila, can dinma zasu tafi, itama sai ta cigaba da karatunta dan ta kusan kammalawa inda take karantar fannin magunguna wato Pharmacy.

Lokacin da Haris ya shigo falon, wando ne dogo a jikinshi, ruwan toka mai cizawa, sai farar t-shirt, sumar da ya dan tara kadan bakikirin da ita, tasha gyara sai daukar ido takeyi, kallo daya Alhaji Mustafa yayi masa yaji gabanshi yayi mummunar faduwa, ya kafe shi da ido bayan sun gaisa yana dorawa da

“Zo nan Haris”

Bai musa ba ya karasa, da yake akan doguwar kujera Alhaji Mustafa yake, shi Haris saiya zauna akan hannun kujerar

“Ya makarantar?”

Ya tsinci kanshi da tambaya

“Alhamdulillah”

Cewar Haris, wata irin rashin natsuwa ce take ta shigar Alhaji Mustafa game da Haris din, bai kawo wani abu guda daya a ranshi ba, ya dai tabbatar akwai wani abu da ba dai-dai ba a tare da yaron nashi, anya kuwa Allaah ba zai kamashi akan sakaci da ‘ya’yan Hajiya Rumana ba? Ya kamata ma ace ya gaji ya hakura ya bar mata su? To ta ina ma zai fara yanzun, inda Mukhtar ne ko wani a cikin yaran Fadime da yanzun sun zagaye shi kowa nason bashi labari, amman kalli yanzun yanda kalamai sukayi musu karanci tsakaninshi da Haris, kamar wasu bakin juna.

“Yaushe zaka koma makaranta?”

Haris din ya dan numfasa

“Ranar Monday”

Saiya jinjina kai, kudi yake sakawa Hajiya Rumana na duk wata hidima data danganci yaran, amman yau sai yace

“To ka shirya gobe sai muje muyi siyayyar komawa makarantar ko?”

Cike da mamaki Haris ya kalle shi, saboda abune da bai saba ba,

“Mami ma ta gama saimun komai da nake bukata”

Sukayi shiru na wani lokaci

“Karfe nawa zaku wuce ran Monday din?”

Haris yasan basa wuce karfe goma, direba ne yake kaisu shi da Hajiya Rumana

“Wajen tara da rabi zuwa goma haka muke fita”

Kafin ma Alhaji Mustafa yace wani abu Haris din ya mike

“Ina dan shirya kayana ne Baba, saida safe”

Bai kuma jira amsar shi ba ya wuce abinshi, Alhaji Mustafa yaji wani abu ya takure a cikin kirjinshi, haka ya kwanta da wannan rashin natsuwar, itace kuma ta zame masa wata abokiya a kwanakin har zuwa Monday, da saida su Haris din suka ganshi a shirye tsaf, kallo daya zakayiwa Hajiya Rumana kagane bataji dadin wannan bazata na mijin nata ba. Akan dole akayi tafiyar dashi, har makarantarsu Haris, duk wani report card dinshi da take fada masa wai a makaranta ake ajiyewa sun dai fada mata grade dinshi yasa aka dauko, yaji dan sauki ganin Haris din ya fara kokari, ko a term din da aka fita na bakwai yazo. Ya dai kalli Hajiya Rumana da yaji cewa duk sanda za’a nemeshi yana kasar waje, da alama shugaban makarantar yaji dadin zuwanshi.

Sukayi musayar Lamba, Hajiya Rumana na sakawa a ranta, suna koma gida zata faki idon Alhaji Sa’id ta rufe lambar ta yanda shugaban makarantar ba zai iya kira ba, shikuma ta sauya lamba daya a ciki yanda inya kira ma sai daiya samu wani. Ba zata bari Haris na gab da gama makarantar nan sujawo mata wata fitina da Alhaji Mustafa ba, so takeyi akan Haris ta shawo kanshi ya fitar da yaron kasar waje, a gaban idonta yake maganar watakila Mukhtar na da rabon komawa Madina, tunda su kananun duk sunje Umra, manyan kuma sun hadane harda Hajj, acan zaiyi karatunshi, da tayi magana sai yace mata

“Bafa ni zan kaishi ba, kwakwalwarshi ce zatayi masa sanadi”

Wai ita zai ninke a bai-bai, ta dauki idone ta saka masa, dan ba karamin tashin hankali za’ayi ba ace wani a cikin yaran Fadime ya tsallaka wata kasa da sunan karatu, in har ya nuna mata ba zai fitar da Haris ba, sannan ta riga tayi rantsuwa sai dai yayi abinda zaiyi, amman ko da yardashi ko babu, Haris ba zaiyi karatu a Najeriya ba, haka suka dawo gida. Aikuwa abinda tayi niyya shi tayi data samu ta dauki wayar Alhaji Mustafa.

Sai dai har ranta bataso a kirashi ne akan irin rashin ji da rigimar da Haris yakeyi
Ko a mugun tunani batayi hasashen kiran da za’ayi ma Alhaji Mustafa har akan Haris har ita saiya girgiza…

About the author

mynovels

Leave a Comment