Muradin Zuci Hausa Novels Complete
MURADIN ZUCI
Bintu Musa ✍️
Wannan Littafin qirqirarren labari ne, banyi dan wani ko wata ba, in yazo dai dai da rayuwar ku, kumin afuwa a bisa kuskure ne. Ban kuma yi dan cin zarafin wani ko wata ba, in sabanin hakan ya gifta, shima ayi min afuwa bisa kuskure ne.
A Blurb for you…
KADDARA….Itace sanadin da yasa ta tsinci kanta acikinsu. Daga lokacin da ta fara mallakar hankalinta ta fahimci banbancin ta da ahalin da ta daukesu jininta.
“Amma menene laifinta dan kaddararta tazo a hakan?”
“Shin me tayi da yasa take fuskantar kalubale daga garesu?”
Wannan sune tunanin FADWA a kullum. Amma kuma duk hakan tana daukansu da sauqi wani lokacin in aka hada da zafin da takeji na yadda kaddara ta hado ta cikin ahali daya da SHI.
Ta aminta da cewar har abada batada babban maqiyi kamarsa. Tana jin har abada zuciyarta bazata taba sauqowa akan abunda ya mata ba.
Saidai abunda bata sani ba shine kaddarar rayuwar ta tana manne da tashi. Ya zatayi Idan ya zamo shine qarshen bangon majinginar ta a lokacin da ta rasa madafa?
Labarin Muradin zuci zai tabo wani bangare ne na sabanin fahimta da ake samu a rayuwa. Kuma zamuga shin har tsawon wane lokaci zuciya take iya danne son wanda take matuqar so? Shin soyayyar da aka rayu da ita acikin zuciya takan iya boyuwa?
Har zuwa yaushe?
Assalamualaikum Everyone, Bintu ta dawo muku da sabuwar tafiya da take muradin ayi tare daku.
Littafin Muradin zuci zaizo muku a paid book ne wannan karon. Akan 500 kadai. ku tuntubeni ta wannan line din 08134692758
Sannan zaku samu sameshi akan manhajar AREWAPEN.
Ga wa’inda mukayi tafiyar KUNCIN ZUCI babu su kuma you’re welcome on board in this journey, masu neman Littafin Kuncin zuci kuma zaku iya samunsa a Arewapen ko Wattpad for FREE. ko kuma ku tuntubeni ta numbern dana rubuta a sama dan samun complete document.
Nagode.
Love, Bintu Musa.
https://www.arewapen.com/book?id=6a284ace1fd5770fa0dc53fa
Ina miqa godiyata sosai ga qunguyar mu ta Wow (women of words) Association.
Da kuma godiya ta musamman ga:
Ramlat (Mai Dambu)
Sayyid (Legends pen)
Nusaiba Rimi (Nusy Bee)
Thank you so much for been there for me when i need you, Allah ya bar zumunci.
Fatima Dahiru
Hajara Usaini
Ina matuqar godiya agareku for your support, My sisters from another mother, Allah ya saka da alkhairi da dukkan qwarin gwiwan da kuke bani a koda yaushe.
MURADIN ZUCI📖📚
Bintu Musa ✍️
Chapter 01
Free page
Houston, United States.
25th October.
Daren Talata, 9:00 pm.
Hankali a tashe matashiyar balarabiyar take tuqin motarta qirar Honda prelude, wadda ta kasance daya daga cikin motocin da suke tashe a wannan lokacin. Tafiya take ba tareda itama ta san inda ta nufa ba, idanunta na kan titi tunda ta fara tuqin taqi juyawa ta kalli seat din dake gefenta. Hannunta da suke riqe da steering wheel din ta kalla ganin yanda suke rawa sai ta sake damqe sitayarin tana mai qara gudun motan a yayin da zuciyarta ke kadawa da wani irin yanayi da yasa idonta kawo kwalla. Tafi awa daya tana yawo acikin garin kuma har sannan bata tsaida inda ta nufa ba sai zagaye take acikin wata makekiyar unguwa ta rasa a wane taqamaiman gida zata tsaya, gashi har sannan jikinta sai rawa yake, can kawai ta samu kanta da tsaida motan a gefen hanya ta kifa kanta akan sitiyarin da hannunta duka biyu ke riqe dashi har sannan. Hawaye masu zafi taji suna zuwa mata idanunta ba tareda ta sharesu ba ta dago kanta tana bin gurin da ta faka motan nata da kallo, ganinta tayi gaban wani babban gida mai cike da alatun rayuwa ga haske a ko’ina tar, samun kanta tayi da qurawa compound din gidan ido ganinsa dauke da gajeran gate irin wanda yawancin ‘yan qasar suke amafani dashi a gidajensu, nan kuma idonta yakai kan shukokin compound din da take hangowa daga inda take zaune cikin motan. Sai kuma ta kai hannu ta fara share hawayen da ya sauqa a fuskanta, ahankali ta juya ta kalli seat din dake gafenta ganin har sannan babu wani motsi da basket din dake ajiye a gurin yayi, sai ta kai hannunta ahankali ta yaye farin towel din dake lullube akai tana kallon kyakkyawar jinjirar dake baccinta hankali kwance sai tashin qamshin turaren babies take mai dadi, kuka ne yazo wa matashiyar da sauri ta kai hannunta ta rufe bakinta gudin kar ta tada Babyn. Aqalla ta kai minti biyar tana kallonta sannan cike da jarumta ta maida towel din ta rufe yarinyar, da haka ta jawo baqin gyalen kanta ta rufe fuskanta sannan ta juya ta duban street din unguwar, kasancewar kebababbiyar unguwa ce ta masu hannu shuni sosai sai ya zamtoh babu kowa a daidai street din da take, ganin haka yasa ta bude motan ta fice tareda zagayawa daya bangaren domin daukan jinjirar. Ahankali ta dauko basket din ta juya tana waige waige ganin ko ana kallonta sannan ta fara tafiya a sannu ta tura qaramin gate din and to her luck kuma ba’a datse yake ba, da sauri ta nufi gefen shukokin ta duqa ta ajiye basket din hawayenta na diga kan towel din amma haka ta miqe ta fice da gudu gudu tana sake waigawa ko da wani ya ganta har ta qarasa ga motarta ta shige da wuri ta tayar. Sai da ta kai qarshen layin sannan ta faka motan ta juya tana kallon gidan ta madubi sai kuma kuka mai qarfi ya kwace mata, wani irin zafi takeji a zuciyarta kamar wuta a wannan lokacin tana kukan ahankali take ambaton sunan jinjirar. Can kuma ta kasa daurewa tayi saurin bude motan da nufin ta koma ta dauko yarinyar dan ji take duk wani jarumtar da ta fito dashi kuma ya watse, bazata iya ba…bazata iya ba.
Fitan ta ke da wuya ta hango fitowan wani magidancin mutum daga gidan tareda wasu yara guda biyu suna tafe a jere dashi zasu fita daga compound din gidan, da sauri ta sake komawa cikin motan ta tayar tareda figanta ta bar arean da gudunta.
Tasani..Lokaci ya qure mata..Ya qure mata har abada kuma..
A yayin da magidancin ya fito daga gidansa tareda yaransa maza da suka kasance ‘yan biyu kuma ‘yan kimanin shekaru sha biyu, hankalinsa naga fita kwata kwata bai lura da abunda aka ajiye masa a compound din gidansa ba sai daya daga cikin yaran ne ya riqe masa gefen riga domin jawo hankalinsa yace “Papa look..A basket” sai ya juya shida dayan yaron nasa suka kalli gurin da IMRAN ke nunawa da yatsansa ya sake cewa “Papa menene?” a sannu shi Papan ya fara nufan gurin cikin kaffa kaffa yaran na biye dashi a baya, kafin ya qarasa kawai dayan yaron nasa dake bayansa ya tafi kansa tsaye ya tsugunna zai bude, da sauri Papa yace “Kash. IMAM meyasa bak..” kafin ma ya qarasa maganan Imam ya bude towel din suka kalli cikin basket din a tare, Imran dake boye a bayan mahaifin nasu shima ya leqo kansa, dago kai Imam yayi yace “Papa it’s a Baby” daskarewa Baban nasu yayi yana kallon kyakkyawar Babyn dake bacci hankali kwance ga kuma kayan sanyi na yara mata mai kalan ruwan hoda a jikinta dauke da zanen flowers wanda hakan ke nuni da kasancewar babyn ‘ya mace, hannu Imam ya kai zai dauketa sai Papa ya janye hannun nasa still yana kallon jinjirar da kana ganinta kasan farinta ba na ‘ya’yan mu hausawa bane, Imran ya duqa kusa da dan’uwansa shima yana kallon yarinyar sai ya dago kai yana murmushi yace “Papa let’s keep it” shidai Papa har sannan baice komai ba gashi alamun tashin hankali ya bayyana qarara a fuskarsa sai kuma ya miqe ya fara bin arean wajen gidan nasu da kallo ko da zai hango wanda ya musu wannan ajiyar a daren nan, can kuma ya juyo yace “Ku tashi mu koma ciki akwai sanyi” sai Imran yace “Papa anan zamu bar Babyn?” Imam dai yanata kallonta har sannan bai sake cewa komai ba, sai Papa yace “No, we’re taking her with us” da haka ya sunkuya ya dauki jinjirar tareda furta duk addu’an da tazo bakinsa, sai twins suka miqe suma Imam ya dauki empty basket din suka fara tafiya a gaba while mahaifin nasu yana biye dasu a baya riqe da babyn a qirjinsa suka koma cikin gidan nasu.
A lokacin da suka shiga babban falon gidan nasu suka samu Momma zaune a inda suka barta ga jakadiyarta mai suna Habiba na matsa mata kafafunta da suka kumbura dalilin tsohon cikin dake jikinta, dago kai tayi tace “Ha’a, har kun dawo?. Da mota kuka fita ne?” sai Imran ya qaraso gurin ta da saurinsa yace “Momma we found a Baby” sai ta dan hade gira ta juya tana bin mijin nata da kallo ganin yana riqe da nannadadden towel a qirjinsa, qarasowa Papa yayi tareda zama a gefenta atake kuma Habiba ta miqe kanta a duqe cikin ladabi ta matsa gefe, sai ya duqo ya bude wa Matar tasa towel din tana ganin yarinyar kamar idanunta zasu fado, sai ta dago kai tana kallonsa tace “Menene wannan din?” yana kallonta shima yace “Jinjirace Fatima, anan cikin compound dinmu aka ajiyeta” sai ta dafa cikinta ta fara qoqarin miqewa yana kallonta, da sauri Habiba ta matso zata taimaka mata amma ta daga mata hannu da nufin ta barta sannan ta qarasa miqewan da kyar duk suna kallonta ta kalli Imam dake riqe da basket din har sannan, fuska a hade tace “Bani abun nan” sai ya matso ahankali ya bata ta karba tana kallon mijin nata tace “Kawo ta mu fitar da ita daga gidan nan tun kafin ta jawo mana masifa muna zaman zaman mu” da mamaki Papa yake kallonta yace “Meye haka kike cewa ne Fatima, clearly dai kina gani jinjirace alamun bata sha iskan duniya sosai ba, meye nata kuma?” Momma tayi qanqan da ido tace “Shiyasa zamu mayar da ita inda muka ganta sannan mu kira police da social services, we are not keeping a stranger’s Baby in this house wallahi” da mamaki Papa yace “Haba Fatima, ki nutsu da Allah. Ta yaya zamu maida baiwar Allahn nan out there in this cold weather kawai dan kina tsoron abunda hukuma zasuyi, kin manta akwai CCTV a street din ne? Anan zasu gani su kuma shaida ajiye mana ita akayi ai” a fusace tace “Ni ba hukuma nake gudu ba, qananun maganan da hakan zai jawo mana acan gida nake gudu, ya muna zaune qalau zaka jawo mana masifa har cikin gida” sai ya dan girgiza kai ya miqe tareda miqa mata yarinyar yace “Dan Allah ki riqeta, ki kula da ita kafin insan ta inda zan bullowa al’amarin, the mother might come back, bakisan yanda nake burin hakan a raina ba, it’s too cruel for the baby, social services will just be passing her from one home to another in the name of adoption, she’s innocent” tsayawa Momma tayi tana kallon yarinyar yayin da duk wani annurin fuskanta ya gushe, idonsa a kanta ya sake miqo hannunsa “Riqeta mana Fatima” sai lokacin Imam ya matso tareda dan miqa hannu zai karbeta ai da sauri Momma ta tureshi har sai da ya fadi, rai a bace take kallonsa tace “Uban ‘yan karfin zuciya, inna gaura ma mari ba” kafin Papa ya dagosa ya riga ya miqe yana kallon mahaifiyar tasa dake harararsa, sai Papan ya juyo gareta yace “Wai me yake damunki ne Fatima, Lafiyan ki kuwa?” tace “Ba lafiya nake ba, ta yaya muna zaune lafiya zaka shigomin gida da jinjira sabon haihuwa har kana fadin in riqeta, wallahi ka koma da ita duk inda ka daukota tun wuri” da haka ta juya tana riqe da cikinta da yayi nauyi sosai ta wuce dakinta dake nan downstairs wanda tun zuwansu gidan take zama acikinsa dalilin bata iya hawa stairs taje asalin dakinta dake can sama, sai duk suka bita da kallo yayin da Habiba tabi bayanta da hanzari gudun kar ta mata masifan da ta saba.
Wannan littafin Paid ne akan Naira dari biyar (500), masu buqatan kasancewa cikin wannan tafiyan zasu iya biya ta wannan layin.
8134692758 Opay
Fatima Musa Maina
Shaidar biyar ta wannan layin. 08134692758
Sandar Girma Hausa Novels
MURADIN ZUCI📖
Bintu Musa ✍️
Chapter 02
Free page.
Papa daskarewa yayi anan tsaye a falon ya gagara zama yana bin matar tasa da kallo, ya sani wannan din ba sabon abu bane sanin masifa da fitinar matar tasa da yake fama dashi tun fil azal wanda kowa ya shaida a kaf danginsa cewa Fatiman fitinanniya ce kuma in bataso zaman lafiya ba toh ba wanda zai zauna lafiya a can gidansu dake Nigeria. Sai ya koma ya zauna kan kujerar a hankali ya duqar da kansa yana kallon Babyn wadda kamar hadin baki itama ta bude idanunta a hankali, dan stiff yayi yana kallon kwayar idanunta da suka kasance grey color, duk da kasancewar ta jinjira hakan bai hana manyan idanunta fitowa fili ba a lokacin da take kallonsa. Duk yanda yake jin nauyin tashin hankalin dake tunkarosa hakan bai hanasa samun kansa da yi mata murmushi ba, sai ya kwantar da murya ahankali yace mata “Assalamualaiki” nan twins suka matso suna kallonta, Imran yace “Papa please let’s keep it” sai ya dago kai yace “She’s a girl Imran”. Imam kuwa sai kallonta yake baice komai ba shima, sai Papa ya sake duqawa ya kalleta yanajin tausayinta na shiga kowane sashi na zuciyarsa, tayaya wannan innocent being din zata zamo masifa bayan in za’a bata zabi itama bazata so abunda ya faru da ita ba ko kadan, har sannan bata dauke idanunta daga kan Papan ba sai can kuma ta fara motsi tana dan bata fuska alamun zatayi kuka nan ya hau jijjigata yana kallon kayan sanyin dake jikinta, mamakinsa daya a wannan lokacin shine ta yanda kayan jikin jinjirar yake fes da kyau ga wani tashin qamshi da takeyi, sai ya dan dago ta yana sake duba kayan dan ko daga texture din mutum zai fahimci ba daga cikin wahala ta fito ba. Idonsa ne yakai kan wani rubutu ajikin farin towel din nata sai ya kai hannu ya yaye kadan yana ganin sunan da akayi engraving kamar saqa ajiki da harafin larabci “FADWA” ya maimaita sunan a fili, sai lokacin Imam yace “Papa sunanta ne?” ya gyada kai “Sunanta Fadwa” Imran yayi murmushi ya duqa kansa gareta yace “Hi Fadwa” sai Papa ya shafa kansa bai bar murmushin qarfin halin ba, yace “Yes.. Her name is Fadwa” ya qarasa fadi yana danne duk wani tashin hankalin da ke kokarin taso masa a zuciya.
Rai a bace Momma ta shiga dakinta Habiba na biye a bayanta, cikin kwantar da hankali tace “Ranki shi dade kiyi hakuri kar hakan ya ja miki matsala ga lafiyarki” ta juyo a fusace tace “Sai an fitar da yarinyar nan daga gidan nan, ke yanzu yarinyar nan bata miki kama da aljana ba?” Habiba ta dan duqar da kanta tace “Ki gafarceni ranki shi dade, amma yarinyar ba lallai ta kasance aljana ba sai dai asalinta ne zai iya zama da tangarda” Momma tayi saurin cewa “Dama batun shegiya kam shegiya ce, kuma wallahi ba zan raini ‘yar cikin shege tareda ‘ya’yana ba” kafin Habiba tayi magana suka jiyo tashin kukan yarinyar Momman ‘yar kimanin shekara biyar dake kwance akan gadon tana bacci, sai Momman ta juya gareta da sauri tace “Jidda na kin tashi” yarinyar ta gyada kai tana murza idanunta sai uwar ta miqa mata hannu da nufin ta iso gareta. Tana shafa bayan Jiddan ta juya zata fadi magana a Habiban aka turo kofan dakin Imran ya shigo a daddare, qin qarasowa yayi cikin dakin yayi sai ya tsaya anan bakin kofar yace “Mama Habiba kije Papa na kiranki” da sauri tace da Momma “Ranki shi dade bari naje” gyada kai kawai Momma tayi batace komai ba tana kallon Imran din dake tsaye a bakin kofan yaqi shigowa, dan hararansa tayi sannan tace “Meye na tsayawa a bakin kofan toh?” sai yayi murmushi ya juya while Habiba na biye dashi suke fice tana kallonsu, sai can kuma tayi tsuka ta cigaba da shafa bayan Jidda dake shirin komawa wani baccin.
Fitan Habiba falon ta samu Papa na tsaye yana jijjiga Fadwa dake kuka a hannunsa, cikin ladabi ta duqar da kanta tace “Ranka shi dade akwai abunda kake buqata ayi ne?” sai ya juyo yace “Kuka take bansan me takeso ba ko zaki gwada lallabata” nan ta miqa hannu ya bata ita ta cigaba da lallabatan, amma har zuwa karfe goma na dare Fadwa bata bar kukan ba duk da ruwan dumin da Habiba ta bata tasha, har zuwa sannan kuma Momma bata sake fitowa daga dakinta ba duk da kukan jinjirar da take jiyowa ya karade gidan. Hankalin Papa in yayi dubu ya tashi a wannan lokacin ya rasa me ke masa dadi. Sai bayan Habiba ta danyi dabarunta ta gano ciwon ciki ne ke damunta sannan ta fada masa, aikuwa nan da nan ya dauki car key twins na biye dashi zasu fice siyo mata maganin sai Habiba ta sake tuna masa yarinyar na buqatan madara da kayan sakawa har dasu pampers ya gyada kai tareda ficewan. A daren Papa suka fita zuwa super market don nemo madaran nata, yana tafe a motan yana tunani har sai da Imam dake seat din gefensa ya ankarar da shi isowarsu gurin ganin zasu wuce sannan ya dakata, daga nan kuma suka biya boutique na saida kayan yara amma kuma sai suka samu a kulle, haka ya hakura ya biya dasu pharmacy ya siyo maganin ciwon ciki na daidai jinjiri sabon haihuwa sannan suka koma gida.
Bayan Habiba ta bata maganin cikin sa’a suka samu ta fara bacci sannan Papa ya sake dubasu kasancewan suna cikin daya daga cikin dakunan dake nan downstairs, ganin Fadwan tayi bacci yasa shi ficewa sannan ya nufi dakin matarsa, anutse ya bude kofan sai ya sameta a zaune a bakin gado sanye cikin kayan bacci tana dan dafa cikin ta dake dan mata ciwo kadan, da sauri ya qarasa yana mata sannu amma bata ko dago kanta ba sai ya zauna kusa da ita ya sake cewa “Sannu, ko in taimaka miki ki kwanta?” nan ma ta girgiza kai bata ce komai, shiru sukayi sai can yayi qasa da murya yace “Fatima, yarinyar nan itama batada zabi akan abunda ya faru da ita” sai sannan ta dago kai tana kallonsa tace “Ni bance laifinta bane daman, kawai bazan riqe yarinyar da bansan asalinta bane, ya kawai daga ganin yarinya a yashe zaka dauko ka qaqabamin nima inaji da kaina” sai yayi murmushi tareda kamo hannunta yace “Haba mana Binta na, ai ba lallai sai ke zaki raine ta ba, ga hadimanki dayawa da duk abunda kikace shi zasuyi, Ina laifi in kin taimaki yarinyar da batada gata ayanzu sai na Allah da namu, ki tuna fa muma ba dabarar mu bane ya bar mana namu ‘ya’yan cikin gata kuma a gaban mu” sai ta kwace hannunta tana hade fuska tace “Ni ka daina dangantamin yarana da irin wannan maganganun, kuma ai ba mu kadai bane mutanen da zamu iya riqeta, akwai orphanages dayawa ai” Papa na kallonta yace “Then..Menene makomar yarinyar kenan? what if..” kafin ya qarasa ta fara qoqarin gyara kwanciya tace “Ni kawai banaso, nace banaso ana dole ne? naji yau ta kwana a gidan amma zuwa gobe bazan lamunci zamanta a gidan nan ba” da haka ta kwanta ta juya masa baya yana kallonta, can ya sauqe numfashi ya miqe ya fice. Dakin twins ya tafi a upstairs dan tabbatar da ko sunyi bacci sai ya samu Imran nata munsharin bacci abunsa while Imam na zane a takarda anan zaune kan upper bunk dinsa dake saman na Imran din, murmushi Papa yayi yace “Imam bazaka bar zanen nan haka ba kayi bacci?” sai ya dago kansa, ahankali yace “Saura kadan” yace “No son, it’s late..ka kwanta haka nan sai gobe ka qarasa” da haka ya qaraso bakin gadon ya fara tattare masa takardun, sai ya dago takarda guda daya yana gani a zuciyarsa yana mamakin baiwar yaron a kullum in yaga abubuwan da yake zanawa kala kala. Sai da ya tabbatar ya kwanta sannan ya nufi switch din dakin zai kashe wutan yaji Imam din yace “Papa, cikin ya daina mata ciwon?” sai ya juyo yace “You mean Fadwa?” ya gyada kai ahankali, sai Papa yayi murmushi yace “Eh ya daina har tayi bacci, now sleep….saida safe” da haka ya kashe wutan sannan ya fice tareda rufo musu kofan..
Tunda ya koma dakin kwanansu Momma bata juyo ta kallesa ba duk da idonta biyu har sannan, har ya gama shirin baccinsa yazo ya zauna a gefen gadon bata motsa ba kuma idanunta a bude tana kallon wall din dakin ta bashi baya, sai ya juyo yana kallonta yace “Kinyi bacci?” shiru tayi bata amsa ba, qasa qasa ya sake cewa “Ya cikin naki?” nan ma tayi shiru, ganin halin nata ne ya motsa yasashi kwanciya shima ya juya bayansa yana jin zafin hali irin na matar aurensa.
Bintu ✍️
Paid Book (500)
8134692758
Fatima Musa Maina Opay
Shaidar biya: 08134692758
MURADIN ZUCI📖
Bintu Musa ✍️
Chapter 03
Free page..
Washegari tun da lokacin sallahn asuba yayi Papa ya kwankwasa dakin su Habiban dan jin lafiyan yanda suka kwana. Bayan ta bude sai ta sunkuya ta fara gaisheshi cikin ladabi sannan ta fito daga dakin domin bashi guri, da ya amsa mata sai ya shiga cikin dakin direct ya nufi gadon inda Babyn ke kwance tareda Jidda, bacci ya samu tanayi kamar ba ita ta tada musu hankali jiya da kuka ba, sai ya maida towel din ya rufe tareda gyarawa Jidda duvet dinda take lullube itama sannan ya juya ya fice daga dakin. A falon ya tadda Habiban tana jiran fitowansa sai yace “Ya cikin nata?” kai a duqe tace “Da sauki, bata sake wani kukan ba ranka shi dade” ya gyada kai sannan ya nufi upstairs gurin ‘yan samarin yaran nasu. Tare da twins din yayi sallah anan falon suna biye dashi ya jagoranci sallahn dalilin rashin yawaitan masallatai a kasar a wannan shekarun. Har Habiba ta gama hada breakfast Momma bata fito ba, da Papan ya leqata ya mata magana ma bata kulasa ba sai ya dawo dinning area din suka cigaba da cin abincin da yaransa wanda suma a daddare suka gaisa da mahaifiyar tasu a wannan safiyar.
Habiba dai ita take tsaka mai wuya, fushin Momma uwargijiyar tata take tsoro matuqa gashi tasan ko giyar wake tasha bazata tsallake maganar Papa ba. To wa ya isa ya tsallake magana ko umarnin Yarima mai jiran gado bayan sarki Abdulfatah, sahun giwa ne ya taka na raqumi shiyasa babu yanda ta iya ta amshi kulawan jinjirar ta hada da aikinta na kula da uwargijiyar ta da tazo yi takanas a qasar.
Da Papa ya shirya fita gurin aiki ne Habiban ta sake tuna masa batun tufafin Babyn sannan ya sake shiga dakin dan dubota, nan ma ya samu ta koma wani baccin bayan Habiba ta bata madaran tasha kadan. Duqawa yayi idonsa akanta zuciyarsa na qara karyewa, sai ya kai hannu ya kama qananun fingers dinta duk bata motsa ba, wani irin nauyi yaji zuciyarsa nayi akanta, what a cruel world! This beautiful innocent child didn’t deserve this, wane mara imanin ne zai yasar da wannan yarinya?.. Da wannan maganganun zucin ya miqe cikin sanyin jiki sai twins suka shigo dakin Imran na gaba suka qaraso bakin gadon suna kallonta. Sai Imran ya hau gadon ya kai hannu yana taba fuskanta yace “Papa bacci take har yanzu?” ya gyada kai yanajin nauyin yin maganan kar suga gazawarsa, sai ya juya yana kallon Imam ganin ya tsaya dan nesa da gadon idonsa quri akan babyn baice komai ba, dan murmushi Papan yayi sannan yace “Daga nan zaka gaisa da ita kuma Imam?” sai ya girgiza kai ya qaraso bakin gadon amma bai hau ba, cikin nutsuwarsa da ta zame masa jiki dukda yarintarsa yace “Papa ya cikin nata?” sai Papan ya amsa da “Ta samu sauqin, gashi har baccin ta takeyi ma” ya gyada kai bai sake cewa komai ba sai Imran dinne yake wasa da hannunta suna magana da Papan, sai da suka dauki lokaci a dakin sannan suka fice while Papan yayi kiran Habiba dake wajen Momma, bayan ta fito a hanzarce yace mata “Kayan sakawa ne kadai ya saura acikin abubuwan da take da buqatan ko?” tace “Eh ranka shi dade, da dai mayukan yara irin wanda kuka siyo kwanaki da Gimbiya” ya gyada kai sannan ya dauki qaramar jakansa dake dauke da takardun da zai buqata a wajen aikin nasa sannan ya sake leqawa dakin matar tasa suyi sallama. Tana hakimce a bakin gadon hannunta riqe da plate Habiban ta kawo mata nata breakfast din, ganinsa yasa jidda baro gurin mahaifiyarta ta qaraso garesa tana maqalqale kafansa, sai yayi murmushi tareda shafa kanta yace “Where is my little pumpkin?” tana dariya tace “Mee Papa” da haka suka qarasa gurin Momman da idanunta ke kan plate din bata dago ba har sannan, saida ya zauna a kusa da ita ya umarci jidda da taje gurin yayunta sannan ya sake maida hankali gareta yace “How are you feeling?” a nutse tace “Na dauka samun ‘yar tsintuwar yasa ka mantawa dani da kuma jininka dake jikina” madadin ya nuna haushin kalaman nata sai ya danne tareda dan yin murmushi yace “Jiya kadai dan ban bi abunda kikeso ba yaci ki zamo me fahimta ta Fatima, i thought ko bance ki kula da ita ba ke me jin tausayin tane, cikin sanyin nan akayi dumping dinta batareda tausayi ba, menene nata aciki, sannan menene laifi na dan na nemi kulawa da ita, ke kanki kin sani babu yanda za’ayi in fitar da yarinyar nan waje a jiya, in kaita Ina? Haba Fatima, Ina imaninki ya tafi?” sai lokacin ta dago kai tana kallonsa, nan hawaye suka fara taruwa mata a Idanu sannan tace “Wato dan na nemi kare mutuncin ka shine rashin imani, yarinyar da kana gani kasan ‘yar qazanta ce, wane irin maganganu kake son jawo mana da mutuncin ka, daraja da kuma kimarka?” nan kuma ransa ya fara baci yace “Kina gurin ne da aka sameta ta hanyar qazantar, wai me yake damunki ne Fatima, da kike maganar kima da daraja kina tsammanin mahaifan nawa zasuyi alfahari da cewar na yardar da yarinyar ba tareda na bata shelter bane?” Tayi shiru bata basa amsa ba sai ya sake cewa “Zan zamo jagora bisa mulkin iyayena da kakanni da zan karbi ragama kuma ace tun yanzu bazan iya kwatanta jinqai ba me na zamo kenan? will you be proud of that man?” nan ma tayi shiru batace komai ba, sauqe numfashi yayi sai ya nutsar da muryarsa wannan karon cikin lallashi ya kuma fadin “Ki tayani mu samu ladanta koda na qanqanin lokaci ne Fatima, tunda baki amince da mu riqetan ba zan samo mafita tunda wannan ba qaramin case bane a qasar nan. But before that, please ki ban hadin kai mu kula da baiwar Allahn nan, gidaje dayawa acikin estate dinnan amma sai Allah ya kawota garemu, bamu san me ya boye a cikin lamarin nan ba” ta gyada kai nan ma bata amsa ba sannan ta cigaba da cin abincinta, ganin tayi shiru yasa shi yi mata sallama tareda miqewa ya nufi kofa ta bisa da kallo sannan ta dan tabe baki tana qara hade fuska.
Papa bai dawo gidan ba sai karfe sha daya na safen ya shigo gidan hannunsa niqi niqi da kaya. A dan gigice ya shigo falon sanadin jiyo kukan Fadwa da yayi tun kafin ya bude kofan, sai ya samu su Imam da Imran din tsaye a dan nesa da dakin da Fadwan ke kwance tana ta tsala ihu sun kasa shiga ciki. Da sauri ya ajiye kayan akan table sannan ya nufi dakin ya shiga nan ya sameta har fuskar nan tata tayi jaa abunka da farin fata, cikin hanzari ya dauketa dalilin wani irin tausayi da ta basa ya dorata a kafadansa ya hau jijjaga ta, baiwar Allah sai ta tsaida kukan ta fara ajiyan zuciya jin ta ajikin mutum, sai ya juyo yana kallon twins da suke kallonsa a bakin kofan, idon Imran tsuru tsuru dayake yafi dan’uwansa Imam din tsoro a tarin lokuta, da sauri yayi magana ganin yanda baban nasu ke kallonsu “Momma tace kar mu shiga” ya sake cewa “Imam ya shiga ta dakeshi” sai Papan ya kalli Imam din da ya sunkuyar da kai baice komai ba, da haka ya fito ya wucesu yana kiran Habiban, da saurinta ta fito daga dakin Momman tana sunkuyar da kai jikinta na dan rawa na sanin me tayi, amma kuma ba laifinta bane tunda itama uwar dakin nata ce ta umarceta da tayi mata wasu ayyukan tabar yarinyar, ganin yanda take a tsoracen sai Papa ya fahimci wani abu, ya fara kokarin danne bacin ran nasa yace “Ya kika barta tana kuka, bayan na bar miki kulawanta” da sauri tace “Ka gafarceni yallabai, hakan bazai sake faruwa ba” sai ya gyada kai tareda sauqo da Fadwan daga kafansa yana kallon yanda ta fara kokarin komawa bacci, ya miqota ga Habiban yace “Ki mata wanka, ga kayanta can na kawo, ki tabbatar ta qoshi sosai kafin ta koma baccin, banason abunda ya faru yau ya sake maimaituwa” jiki na bari Habiba ta amsa da “Kayi hakuri yallabai ka gafarceni, bazai sake faruwa ba” sannan ta miqe tareda karban Fadwan ta nufi dakin kwanan su da ita, da dan hanzari Imam ya dauki kayan da Papan ya siyo wa Fadwan yabi bayan Habiban Imran na biye dashi da wasu a hannu suka shige dakin dukansu. Sauke numfashi Papa yayi yanajin bacin ran abunda matar tasa ta aikata bayan ko awanni uku masu kyau ba’ayi ba ya gama neman alfarman tallafinta gurin kula da marainiyar Allah, sai ya girgiza kai kawai ya nufi dakin nata aransa yana tunanin yanda halinta ke sake banbanta a kullum sabanin yanda ya santa baya.
Sai 12 ya shirya tafiya wajen aikinsa bayan ya tabbatar da Fadwan ta samu kulawan da take buqata sannan yayi sallama da iyalinsa ya fice, bayan ya gamo ayyukansa wajen 4 o’clock bai koma gida ba ya nufi gidan Abokinsa me suna Ladan dake living anan Houston din shima da familynsa, dan zuwa sannan duk tunanin da zeyi yayi akan lamarin nan and it’s all leading him to one option, shine dole ya bada jinjira nan ga child services, dole yayi reporting ga police, duk yanda yake son yarinyar da kuma son samun ladanta dole haka zai hakura saboda jalala irinta matar da Allah ya hadasa da ita.
Paid Book 500
8134692758
Fatima Musa Maina Opay
Shaidar biya: 08134692858
From the writer of KUNCIN ZUCI…And now
MURADIN ZUCI📖
Bintu Musa ✍️
Chapter 04
Free page
Papa bai dade ba ya isa gidan Abokin nasa mai suna Ladan, wanda ya kasance citizen din qasar dalilin iyayensa da suka kasance Nigerian immigrants and living in the united states for a long time, a yayinda kuma abota ta hadosa da Papa tun samartakarsu a sanadiyar degree dinsu da suka yi tare a makaranta daya.
Iso Ladan ya masa zuwa dan qaramin garden dinsa dake backyard na gidan suka zauna bisa kujeru na shan iska sannan matarsa mai suna Zulaiha ta kawo musu abun sha ta kuma gaisa da Papan. Sun dau lokaci suna hiran rayuwa da kuma businesses dinsu a inda Ladan din yace dashi “Kargi is high time ka fara tunanin expanding cooperation dinnan naku zuwa Atlanta, there’s alot of business potentials there, inda ni nakeda irin privilege dinka na rayuwa da wuya in zauna a guri daya haka sai dai wani ikon Allah. Duniyar matsawa take da gudu yanzu. There will come a time that zuwa America zai zamo abu mafi sauqi ga mutane unlike yanda ake wahalar samun zuwa yanzu” sai Papa ya ajiye cup din hannunsa ya kallesa “Abunda nake ta tunani yanzu haka kenan, in sha Allah zanyi maganan da mai martaba sai muyi shawara, dan kaga yanzu hankalina yafi karkata ga haihuwan mai dakina tukunna, da kuma passport din Babyn, amma zamuyi hakan da yardar Allah” Ladan ya gyada kai cikin gamsuwa sannan yace “Hakane, Allah ya sauketa lafiya” ya amsa da Amin suka danyi shiru while nursing their drinks, can Papa yace “Ladan, nazo neman shawararka akan wani al’amari daya tunkaromu nida iyalina, nayi tunanin iya tunani amma kaina ya kulle akan ta yadda zan bullowa lamarin” nan Ladan ya dan gyara zama yana kallonsa, sai ya hau bashi labarin abubuwan da suka farun daga daren da aka ajiye musu babyn har zuwa wannan ranan, kafin ya gama maganan Ladan yace “Abdulaziz meyesa zaka saka kanka acikin irin wannan matsalan?” sai Papan ya dan hade gira yace “Bakaji me nace bane? Ce maka nayi fa har cikin compound aka ajiye mana ita, ya kakeso inyi? left her in this cold freezing weather?” Ladan ya sauqe numfashi yayi shiru na wasu sakkani tukunna, can yace “Ai lamarin qasar nan dinne, bakayi bama kamar jira suke balle issue irin haka ya faru? But you should’ve call the police Kargi, nan da Nigeria akwai banbancin mai matuqar yawa” Papa yace “Nasani, shiyasa nazo ka bani shawara ai, raina nason riqe yarinyar nan Ladan, wani irin protectiveness nake ji akanta banason ta fada wani mugun hannun wallahi, Inason riqeta in bata duk wani kulawan rayuwa ta yanda bazata rasa duk wani gatan da ake tunanin yara kamarta suke rashi ba” Ladan yace “Me matarka tace akan haka? ta amince da ku riqetan ne?” ya girgiza kai yace “A’a, as a matter of fact a ganinta na farko da yarinyar ta qi komai dangane da ita, can you believe har hana hadimarta kula da yarinyar tayi, haka na dawo gidan nasamu tanata kuka abun tausayi” sai Ladan yace “Toh kaga matsala ta farko kenan Kargi, dan wannan matsalace babba, the best idea shine ka bada yarinyar nan ga child services, tunda Fatima bataso babu ta yanda zaka taba jin dadin kula da yarinyar nan, Happy wife Happy home” Papa ya girgiza kai “Na dade bama fuskantar same angle nida Fatima, it’s always the opposite Ladan, she never understands where I’m heading, yara irin wannan ba qaramin lada ake samu da riqonsu ba. Allah ya gani Ina tausayinta” sai Ladan yayi shiru yana kallonsa baice komai ba, ganin haka sai Papa yace “Amma tunda kaima hakan kace shikenan zan bada itan, addu’ana daya kar Allah yasa ta fada mugun hannun ko kuma ta taso cikin Christianity, Qasar nan ba ruwansu da wannan in suka tashi bada yaro, Allah ya dubeta duk inda take” a sanyaye Ladan ya amsa da Amin sannan suka koma wani batun daban.
Da wannan tunanin ya koma gida, amma abun mamaki yana dosar gidan nasa ya samu motoci biyu a fake a daidai bakin gate. A kallo na farko ya gane daya data kasance ta police daya kuma bazai shaida ta waye ba, duk yanda yakai ga taurin zuciya sai da yaji hantarsa ta kada, tunaninsa a wannan lokacin kodai neighbors dinsu sunsan me yake faruwa toh?. Da haka yayi parking a gefensu yana fitowa sai daya daga cikin polisawan ya qaraso garesa suka gaisa ya qara da “Sir, we need to have a few words with you” shima yace “Let’s go inside then” da haka ya musu jagora zuwa cikin gidan suka shiga tare yana gaba.
A falo ya tadda Momma zaune kusada wata middle age woman wacce ke riqe da folders a hannunta tana nazarin bayanin da Momman ke mata, ta gefe dasu kuma Habiba ce tsaye riqe da Fadwan a hannunta ga twins tsaye a gefenta suma, sai bayan su Papan sun zazzauna matar ta kallesa ta fara magana cikin harshen turanci kamar haka “Matarka ta kira office dinmu akan yarinyar da aka ajiye muku jiya, shine muka zo saboda akwai buqatar zamu riqe yarinyar a hannun mu Mr. Kargi” sai police daya ya karbi maganan shima “Amma kafin nan munada buqatar muje station kayi cike cike, mun duba cameras na street dinku mun tabbatar ajiyeta akayi amma dole sai mun tafi dakai dan buqatar bayani daga bakinka” jiki a sanyaye Papa ya juya yana kallon Momma da taqi kallon idonsa, duk yanda yakai ga danne bacin ransa saida hakan ya bayyana akan fuskarsa, sai matar can din ta sake cewa “Ka fahimcemu Mr Kargi, bamu zo da tashin hankali ba aikin mu muka zo yi, yara irin wa’innan daman aikinmu ne na tabbatar da sun samu kulawan da suke buqata” nan Papa ya gyada kai ahankali, a turance yace “I understand…Miss??” tayi saurin cewa “Eva..It’s Eva Hollaway, from Texas Department of Family and Protective services” ya gyada kai “Okay, Miss Eva..I understand” da haka suka mimmiqe sai ta juya tayi godiya a Momma da ta kirasun, a nutse ta amsa da “Thank you Miss Eva” Papa na kallonta, Har suka fice kuma taqi kallonshi sai sunkuyar da kai take tana wani ciccin magani.
Papa bai dauki wani dogon lokaci a station din ba ya gama cike ciken da ake buqata daga garesa, amma da aka nanu masa clip na record din matar da ta ajiye jinjirar sai da ya qame a zaune dan mamakin ganin motar da ta fito daga cikinta, kansa ne ya kulle ganin babu wani alamun talauci a tattare da matar duk da yanda ta rufe fuskarta, hasali ma irin motar da yake hawa tazo da ita sannan daga yanayin kayan da ya gani jikin yarinyar tun farkon ganinsa da ita ya shaida cewan duk inda ta fito babu talauci a ahalin. Anan suka sanar dashi plate numbern motan matar was not registered kwata kwata duk iya tracing din da sukayi, ya gyada kai cikin fahimta yana jin wani tausayin jinjirar na sake shigansa a wannan lokacin amma haka ya danne komai har ya gama abun suke buqata daga garesa a station din.
Kasancewan maghrib ta masa a nan din sai bai je social service office din ba, sukayi agreement da miss Eva dake tare dasu a station akan zai dawo washegarin ranan.
Fitowa sukayi a tare da ita tana riqe da Fadwan sannan ta nufi motan ta ta sakata suka tafi da ita yana kallonsu wanda hakan ba qaramin karya zuciyar sa ya sake yi ba. Ga tsananin bacin ran abunda matarsa ta masa wanda har sannan yana jin dacin rashin ganin mutuncinsa da batayi ba tayi abu gaban kanta batare da shawararsa ba, haka ya hadiye komai ya nemi taxin da zata kaisa gida. Da ya isa gidan yana bude falon Momma ta dago kai tana kallonsa sai ya dauke kansa ya nufi dakinsu dan yayi sallah, saida ya zo wucewa ta gabanta ta fara kokarin miqewa da kyar dan Habiba da twins basa falon, tana kallonsa tace “Baban Jidda i had to do what is safe for us, this is the only way and you’re not making any effort to do so” sai ya juyo a nutse yace “Kinji nace wani abu ne?” tayi shiru tana kallonsa batace komai ba, ya juya tareda nufan dakin yana danne duk wani abunda ke taso masa a zuciya. Har suka zo kwanciya Papa baice mata qala game da abunda tayin ba, itama ganin haka sai taqi kulasa aganinta duk inda aka samu kwana biyu komai zai wuce, zasu dawo yanda suke a baya dan sanin da tayiwa mijin nata mai hakuri ne da kuma rashin riqe abu arai…Saidai abunda bata sani ba shine wannan karon tayi kuskure, ta kuma tura shi har zuwa maqurar da ya dau damarar nuna mata matsayinta na macen dake qarqashinsa.
The following day beyi qasa a gwiwa ba ya tafi office dinsu Eva da safe. Da isarsa ya fara neman izinin yaga Fadwan amma suka qi barinsa acewarsu hakan “It’s not allowed” sai aka kaisa office din shugaban sashen a inda shima shugaban yayi kiran na qasa dashi a qaramin meeting room wanda a nan Papa ya sake musu bayanin duk abunda ya farun, bayan sun gama paperwork sai ya nemi magana da over roll shugaban nasu a office dinsa. Sanin co-operation companyn su Papan ba boyayye bane a Houston yasa shugaban bashi girman sa har da kawo masa ruwa amma bai sha ba, ya gyara zama tareda dan matsar da glass cup din gefe yace “What are the necessary requirements that I’ll need to fulfill before adopting this child legally?”.
Sai shugaban me suna Carl yace masa abune me sauqi tunda duk wani qualities din da ake nema na wanda zeyi adopting yaro shi Papan ya cikesu, kawai za’a bi legal paperwork ne for court approval amma kuma akwai abu guda daya, sai da consent din both married couple din which means sai lallai da amincewar ita Momman sannan za’a basu yarinyar, Jan aiki.
A farkon satin da ya fara going through process din ko bin ta kan Momman beyi ba ganin yanda ta manta da batun ma ta cigaba da rayuwar ta cikin kwanciyar hankali a gidan, duk yanda hankalin twins yake kan Fadwan more especially Imam haka ya danne in sun tambayesa inda take sai yace musu “Tananan lafiya”. Habiba ma taji zafin uwargijiyar tata amma babu yanda ta iya balle tayi magana, haka ta cigaba da abunda ya kawota gidan tana ganin yanda Momman ta kama sabgoginta kamar ba uwa ba. Papa na iya kokarinsa na danne komai dukda tana ganin coldness dinsa lokaci lokaci dan abune da ya quduri niyya a ransa na sai ya bata mamaki akan abunda tayin. Zata sha mamakinsa matuqa.
A wani dare ya yanke shawaran kiran mahaifin sa dan sanar dashi duk da yasan ko bai fada masa ba abunda yake shirin yi din daidai ne. A lokacin da ya gama isar da bayanin nasa ta waya, sai Dattijon ya nutsar da muryarsa gurin cewa “Abu ne mai kyau hakan, kuma Allah zai muku jagora matuqar niyyarku akan yarinyar tsaftatacciya ce” yace “In sha Allah. Nagode, Allah ya qara girma” sai mahaifin nasa ya sake cewa “Mai dakin taka ce zata riqeta?” Ya amsa da “Muna shawara akan wannan din tukunna” sai yace “Yayi, Allah yayi albarka” ya amsa da Amin yanajin nauyin abun da yake shirin yi din na sauqa daga zuciyar sa.
Sati biyun da suka biyo baya ya cigaba da cukucukun adoption din tareda Eva kuma zuwa sannan suna barinsa yaga Fadwan in yaje office din nasu, atarin lokuta in aka kawo masa ita sai yaji kamar ya tafi gida da ita a lokacin, wani irin iko na ubangiji sai ya saka masa so da tausayin yarinyar matuqa aransa, da ita yake kwana arai most days saboda tunanin yanda batada kowa da kuma gata a wannan lokacin sai inda aka miqata. Da akazo batun lallai ana buqatan consent din Momma sai yayi confiding da Eva akan halin da yake ciki da me dakin nasa, itama taji ba dadi sosai amma cikin qarfafa gwiwa tace “Mr Kargi, Ina ganin soyayyar yarinyar nan a idanunka da kuma actions dinka, wanda hakan ya nuna min cewa Fadwa is safe with you, zata samu dukkannin gatan da muke fatan duk yaron da muka bada shi ya samu, abun da zakayi yanzu shine ka nemo qwararren lawyer da zai shige maka gaba akan hakan, Ina tabbatar maka da in process din ya tafi daidai ba sai matarka tayi signing komai ba zaka tafi gida da ‘yarka” ta qarasa tana murmushin bashi qwarin gwiwa, godiya ya mata sosai yana jin dadin shawaran nata sannan ya bar office din. Da wannan Papa yayi wining case din a kotu a ranan Thursday, 15th of November. A yayinda qwararren lawyernsa da ya shige masa gaba ya jajirce sosai dan ba qaramin kudi ya zubar akan case din ba duk dan saboda suyi winning case din…And right there agaban su Ladan da sauran jama’an dake zaune cikin kotun Alkalin ya qaddamar da cewar Fadwa ta zama ‘yarsa halak malak.
Paid Book 500
8134692758
Fatima Musa Maina Opay
Shaidar biya: 08134692758
MURADIN ZUCI 📖
Bintu Musa ✍️
Chapter 05
Free page
Bayan kwana biyu da gama zamansu na kotu sai department of child services din suka yi masa duk wasu cike cike na takardu da yake buqata akan Fadwan wanda bayan nan har asibiti sai da suka kaita tare dashi akayi mata duk wasu gwaje gwajen da ya kamata kuma Alhamdulillah sai results dinta suka fito “Disease free”, ba qaramin dadi Papa ya ji ba more especially da ya ga genotype dinta was excellent. Da fari su Eva sun nemi zabinsa na canja mata sunanta in yanada buqatan hakan amma bai amince ba. Sai da akazo cike mata surname ya nemi su cire Kargi daga cikin sunanta su saka mata “Fadwa A. Abdulfatah” akan wasu dalilai nasa da bai bayyana musu ba, har Ladan dake zaune a gefensa sai da ya kallesa a wannan lokacin amma baice komai ba.
A kwana na uku.
Yana riqe da ita suka fito daga social service office din Eva na biye dasu, sai da suka qarasa ga motarsa sannan ya juyo ya fara godiya a Eva, tana murmushi tace “This child is lucky to have you, Mr Kargi” yayi murmushi “Thank you once again Miss Eva” da haka ya bude motan sai Ladan ya nemi yi masa rakiya sanin me zai tarar a gidan nasa, girgiza kai yayi yace masa “Ba damuwa, zan kiraka” ya qarasa maganan yana saka Fadwa acikin baby stroller da yayi attaching da car seat dinsa wanda takanas ya siyo guda biyu, daya nata dayan kuma na upcoming babyn da za’a haifa masa.
Bai dauki lokaci ba ya isa gidan sannan ya zagaya ya sake daukanta a hankali yana murmushi ganin yanda ko motsin tashi batayi daga baccinta. A compound din ya tadda su Imran na wasa da bingirar ruwa, Imran din na gudu Imam na biye dashi yana jiqashi suna dariya, ganin Papa da Baby hannu yasa suka nufesa da saurinsu, Imran yace “Papa, ka dawo mana da Fadwa?” ya gyada kai yana murmushi “She’s back, as your sister” Imam yayi murmushi yafara kokarin karbanta sai Papan ya basa ita ya dora ta a kafadansa har da dan jijjagata kadan duk Papan na kallonsa, da haka kuma sannan suka shiga cikin gidan. Basu samu Momman a falon ba sai Habiba da take ta goge goge, tana ganinsa ta tsugunna suka gaisa sannan yace “Karbi yarinyar nan a mata wanka, akwai madaranta ko sai an siyo?” da sauri ta kalli hannun Imam ta kasa amsawa saida Papa ya sake maimaita maganan sannan ta amsa da “Eh ranka shi dade, akwai” da haka ta karbi Fadwan jiki a sanyaye tana hasko rikicin da za’a kwasa da uwardakinta.
Maganarta Dutse….Momma na zaune a bakin mirror’n ta Papa ya shigo dakin, ta juyo ta kallesa sau daya ta dauke kai dalilin har sannan suna ‘yar sama sama da juna, amma ga mamakinta sai taga ya zauna a bakin gadonta yayi patting gefensa yace “Zo ki zauna zamuyi magana” asannu ta tashi sannan ta qaraso kusada shi din ta zauna. Saida suka dauki wasu mintuna sannan cikin nutsuwa ya fara jefa mata tambaya “Fatima, Inason ki fadamin ko da akwai abunda na rageki dashi a iya zamanmu?” sai ta kallesa tana hade fuska tace “Meya kawo wannan maganan kuma?” yace “Inason ki bani amsata” ta girgiza kai tana kawar da fuskanta, ya sake cewa “Akwai ta inda na sabo a zamanmu? ko ta furuci..ko kuma ta yanda nake mu’amalantarki da yasa kike yawan daukana ba’a komai ba” nan kuma ta dan ware ido tace “Ni yaushe na dauke ka ba ba’a komai ba?” “In akan maganan ‘yar tsintuwar can ce yasa kake fadan hakan ai nayi abunda ya dace ne” cike da bacin rai yace “Kina nufin kin fini sanin abunda ya dace kenan Fatima?, ace Ina mijinki amma kullum maganata ce zata zamo abun tsallakewarki, abun takawarki yanda kika ga dama, a kullum ke sai kinyi qoqarin defying dina a duk abunda zance kenan” a zafafe itama tace “Ya Ina matarka zakace sai kayi forcing dina akan abunda banaso. Tun kawowar yarinyar nan gidan nan nace maka ka fitar da ita kaqi to ya kake so in maka in ban kira an fitar min da ita daga gidana ba” Papa baisan lokacin da ya miqe ba yana munata da yatsa yace “Baki isa ba Fatima, baki isa ki juyani yanda kika ga dama ba in kyaleki. Bamu gaji haka a gidanmu ba kuma baza’a fara daga kaina ba kina jina?” “Yarinya kuma gatacan na kawota gidan nan a matsayin ‘yata halak malak sai inga abunda zakiyi. Ta zama ‘yata da tayi taking sunana a bayan sunanta na matsayin ubanta sai in gani ko ni da ke waye yafi wani sanin abunda ya dace” da haka ya juya tareda ficewa a zafafe ya barta nan zaune bakin gadon a daskare.
Yana kaiwa tsakiyar falon yaji ta jawo hannun rigar sa da qarfi tana huci, ya juyo yana kallonta shima ransa na quna, cikin qwayar idanunsa take kallo tace “Wallahi bazan riqeta ba Abdulaziz, saidai ka zaba koni ko ita, kuma ayau ba gobe ba nakeson komawa gida na fasa haihuwa a qasar nan, ka maidani gida… ko zan haihu a jirgi yau bazan kwana a gidan nan yarinyar nan tana cikinsa ba” ta qarasa maganar qirjinta na hawa da sauqa. Shi mamakin qarfin halin ta ma yake matuqa, ace tana mace amma zuciyarta kamar ta mutanen fari wannan wace irin mace ce ita. A hankali ya zare hannunsa daga riqon da ta masa yace “Ba inda zakije daga gidan nan har sai kin haihu” sai kawai gani yayi ta nufi dakin da Fadwan ke kwance da hanzarinta kamar ba tsohon ciki ne a jikinta ba, ta tura kofar da qarfi tareda shigewa yabi bayanta da saurinsa, Imam ta samu a kusada Fadwan yana rainon ta kafin Habiban ta gama hado madaranta acan kitchen
A zafafe ta qarasa bakin gadon Papan yana qoqarin riqota amma kafin ta duqa ga Fadwan Imam yayi saurin yi mata rumfa akanta da nufin kareta, cikin bacin rai ta hau dukan bayansa Papa na riqeta tana fadin “Wallahi sai an fitar da ita daga gidan nan” bai tsaya sauraronta ba ya matsar da Imam din tareda daukan Fadwan zai fice daga dakin, sai kawai Momman ta fashe da kuka me qarfi tana fadin “Ni ka maidani gidanmu ni da abunda ke cikina tunda ka samu wadda ta fimu a wajenka” bai kulata ba ya fice daga dakin Imam yayi saurin bin bayansa suka nufi upstairs. Dakin boys din ya kaita ya ajiye ta a upper bunk din Imam dan Imran yayi bacci akan nasa, sannan ya juya ga Imam din yace “Ka kula da ita karta fado” ya gyada kai tareda hawa gadon, da haka Papan ya sake ficewa amma kuma sauqansa downstairs din sai bai samu matar tasa a dakin daya barta ba, ya juya zuwa dakinta tareda murda handle din amma yaji a kulle kuma yana jiyo kukanta acikin dakin. Habiba ce ta fito daga kitchen din jiki a sanyaye dan ta jiyo komai sai ya kalleta yace “Kije dakinsu Imam tana can, in kin bata sai ku dawo dakin naku” ahankali ta amsa da Toh sannan ta wuce saman ba kuzari. Har dare Momma taki bude dakinta ga Jidda ma ta tashi daga bacci tana kuka duk Papan na jiyosu amma ba yanda beyi da ita ta bude kofan ba taqi. Habiba ma tayi iya kwankwasawanta amma Momma tayi biris dasu, ganin har karfe takwas na dare bata bude ba yasa Papa dauko landline phone dinsu na gidan dan kiran mutum daya da yasan zata iya tankwara masa ita, duk da yasan tsakiyar dare ne acan gida Nigeria amma haka ya danna kira ga layin da yasan zai samu yayar matar tasa mai suna Aina’u. A bugu na biyu mijinta ya amsa kiran cikin muryarsa dake cike da bacci sai Papan ya bashi hakurin tashinsa da yayi, yace “Ba damuwa Yarima ai kafi haka, mai dakin ta samu sauqa kenan” anutse Papa yace “Har yanzu da sauran lokaci, na kiraka bisa wani uzurin ne daban” sai yace “Ina jinka Yarima” nan Papa ya fara masa bayani a nutse duk da yanda kira yake matuqar tsada a wannan lokacin bai dameshi ba, burinsa daya a wannan lokacin shine yanda zai seta barakar da ta fara kunnowa a gidansa. Sun dauki lokaci me tsaho suna magana wanda iya adadin kudin da suka bata a wannan kiran in aka baiwa wani faqirin zai iya fitar dashi daga talauci na har abada, amma Papa baibi ta kan wannan batun ba har saida ya tabbatar ya isar da duk maganganun da suke bakinsa ga Alhaji Saminu mijin Anty Aina’u, a inda daga qarshe shima ya miqa wayan ga Aina’un ta cigaba da magana dashi Papan.
Jim kadan da gama wayan nasu aka sake kira sai be dauka ba ya tafi daidai kofar dakin Momma yace “Fatima ki bude kofan nan ga Maman Kasim akan waya zakiyi magana da ita” shiru tayi daga farko bata kulasa ba har saida telephone din ta sake yin wani qaran alamun kira sannan ta murda key din kofan tareda miqo hannunta ya dora mata a tafin hannunta sannan ta maida kofan ta rufe.
Momma bata dauki kiran ba sai da ta sake zama a bakin gado, aikuwa tana dauka ta fara cin karo da maganan Anti Aina’u a zafafe “Meye hakan kuma kikeyi kamar wata qaramar yarinya Binta?” tana shirin yin wani hawayen tace “Amma kinsan dai bai kyautamin bako?” Aina’u tace “To dan bai kyauta miki ba shine zaki bi lamarin ta kulle kanki a daki, da kikaje kan yarinyar dukanta zakiyi ko me?” “Kefa bakida hankali wani lokacin wallahi, ai ta nanata miki magana amma yana bi ta bayan kunnenki, banda ma Yarima yana matuqar sonki ai da baku kawo iyar haka ba da wannan banzan halin naki, toh wallahi tun wuri ki dawo hayyacinki in ba so kike in kira Mama ba a goben nan, ke har Mai Martaba zan kira yasan abunda kikeyi tunda ke baki isa a miki magana kiji ba, ki na abu kamar bakya tuna inda kika fito, meyasa ke kullum sai anyi ta miki bita akan sha’anin zaman duniya ne wai?” nan kuma Momma ta fashe da kukan cin rai, jin wai har iyayenta za’a kira akan abunda aka mata dole tun fari, jin ta kasa magana yasa Aina’un cewa “Ki nutsu ki san me kike yi Binta, dan mijinki ya nemi taimakon marainiyar Allah ba hakan yana nufin ya shiga hakkinki bane, a yanda kika tara hadimai suna miki duk wani bauta ai kula da yarinyar nan bazai zamo abun damuwanki ba. Mijinki babban mutum ne dole ko bai riqe na waje ba zai riqe wasu na cikin gida ma, kuma nasha fada miki ba haka ake zaman duniya ba, da salo ake tafiyar da abubuwa irin haka. Koda bakya sonta ai bazaki nuna masa ba” ta dan dakata da maganan tareda sauqe numfashi sannan ta cigaba “Kin taso gidan mulki gaba da baya amma har yau bakida wayon yin dabarun iya zaman duniya” sai sannan Momman ta share hawayenta tace “Toh Adda me kikeson inyi ?” tace “Ki ajiye komai ki riqe mijinki, wannan yarinyar bata kai ta saka muku matsala a tsakaninku ba sai dai in ke kikaso, kuma wani batun kinason dawowa gida bai taso ba. You will born that child in good condition and come back home safe kina jina?” ahankali tace “Naji” da haka Aina’un tace “Sai gobe da azahar zan kira kafin nan garinku ya waye, banason inji wani batu sabanin wanda muka zanta dake yanzu kinji” ta gyada kai tareda fadin “Toh, saida safe” tace “Amin, kici abinci kuma ki bude kofan yanzu” nan ma ta amsa da Toh sannan sukayi sallama.


