Auren Adashe Hausa Novels Complete
AUREN ADASHE💅🏻*
Na
Fatima Isa Manu
( Sahiba / Dr. teema✍🏻 )
💪 *JAJIRTATTU WRITER’S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al’umma cikin sauƙi_.✏️*
*Page 📄1*
Kano unguwar Dorayi, ƙarfe goma na dare…….
A buge yake tafiya har yana had’a hanya, hannunsa rike da taba yana zuk’a yana fuzgar da iskar ta hanci da baki alamun dai ya dad’e a harkan, sannan kuma k’wararrai ne.
Tafiya yake yana sambatu cike da fad’a da zafin rai, duk abunda ya samu a hanyar yana bugewa ya wuce, haka har ya iso k’ofar gidan da yake son k’arasawa.
Buga k’ofan ya shiga yi kamar ba gobe yana faman masifa, “ Zubairu ka fito ka bani kuuuuudina dan ummarun uwarka,”
Makwabta suka shiga fitowa dan ganewa idanunsu wa yake dura ashar da cikin daren nan.
Wani ne mai suna Malam Hamisu Limamin unguwar ya ce, “ Bawan Allah kayi hak’uri kila yayi bacci ka tafi ko gobe ka dawo…” Bai kai da k’arasawa ba ya lalumu wata ashar yana fad’in, “ Dan tselan uwarka na maka magana ne, shege mai zubin Aljanun lahira, magulmatan banza da hofi,”
Tsit mutanen gurin suka yi, yaron Malam Hamisu wanda suke kira da Khalid yaja hannun Mahaifinsa ya dubi inda yake ya ce, “ Allah ya shirye ka, bazan tsaya na maka wa’azi ba dan ba ji zakayi ba,” Suka shige ciki suna rufe k’ofan su.
Ya cigaba da buga k’ofan da k’arfi, “ Zubairu zan fasa k’ofan nan idan baka bud’e ba, kana ji na ba wai baka ji ba shege tsinanne dan kusun uwa, ni nace ka shiga adashe baka da kud’i,”
Ummah ta jawo Torch da ke gefen ta, ta dalla idon Baba dashi tana cewa, “ Ka tashi kaje ka biya bashin da kaci, kaji dai yanda yake tsinewa Mahaifanka,”
“ Ina ruwanki? Ai ba kaina farau ba kuma ba kaina gamau ba, dan haka ya balla k’ofan bazan bud’e ba,”
“ Amma kasan akwai ƴa mace a cikin giɗan nan ko? kana zubarwa da ƴarmu mutunci ne fa,”
Dan jim Baba yayi yana nazari sannan ya tashi ya fito waje, Ummah ma ta fito ta shiga d’akin da ke gefe tana haskawa.
Cike da tsoro ta firgita tana janyo bargo ta dukunkule jikinta, bakinta har rawa yake dan tsoro.
Ummah da ta lura da yanda ta tsorata ta ce, “ Yusrah ni ce ba wani ba,”
Da gudu ta taso ta rungume ta tana fashewa da wata raunanniyar kuka wanda yake fitowa daga k’asan zuciyarta, Ummah ta shiga shafa mata baya alamun rarrashi, ihun da suka jiyo ne ya saka su fitowa da sauri.
Wawan mari ya wanka masa yana hura masa hayaki a fuska yana fad’in, “ Zaka bani kudina ko sai na guntile maka harshe Zubairu,”
Baba ya ɗurkusa a k’asa yana roƙon su, “ Ka tausaya min bani da kuɗin zubin adashen nan, idan na….”
“ Bura uba da larabci, idan na yarda in tafi a tsaye Zubairu, kai kasan baka da kudi zaka shiga adashen mu, duk ka gama zubawa kowa sai da yazo kaina sannan kace baka da kudi?, lallai kai dan iska ne,”
Halak Dina Romantic Love Story
Baba ya kama k’afansa yana rokon shi, “ Zan baka wallahi idan na samu,”
“ Idan kuma baka samu ba fa?”
Ya juyo ya kalli Yusrah da Ummah sannan ya sunkuyar da kai, “ Ka ɗauki yarinyata a matsayin kuɗinka,”
Da sauri Yusrah ta kalli Baba tana kallon shi suka had’a ido, taji zuciyarta ya tsinke lokacin da ya zuba mata idanunsa masu firgitarwa wanda suka koma ja dan shaye shaye.
Ummah tayi saurin cewa, “ Haba Malam, Ahh ba dai yarinyata ba wallahi sai dai wata,”
Tabe baki yayi yana janye k’afansa daga rik’on da Baba ya masa ya juya zai tafi ya tsaya ya ce, “ Ina jiranka daga yau zuwa wayewar gobe, idan banga kudina ba zan turo yarana sun dauki wancan abar” Ya nuna Yusrah sannan ya fice yana wak’a yana hura hayaki, mutanen da suke bakin k’ofan suka watse.
Baba ya tashi daga durkushen da yake yana rufe k’ofan gidan ya dafe zuci, “ Na maida wallahi yaransa ya turo ashe shi da kansa ne yazo, na shiga uku ni Zubairu,”
Ummah rai a bace ta ce, “ Kasan mai ka aikata kuwa Malam?”
“ Ko ma menene ke kika sani,”
“ Malam yarinyarka fa ka bada a matsayin kudin adashe,”
“ Wani abu take min a gidan dama? Ai irin haka ne ranar su ranar amfanin su kenan, Allah ma yasa idan ya d’auke ta ya yafe min kudin adashen,” Yana gamawa yayi wucewar shi d’aki.
Yusrah tayi shuru tana kallon Baba har ya shige d’aki, zuciyarta cike da wasi wasi akan lamarin Baba, idan yana mata wani abun sai tana kallon kamar ba shi ne Mahaifinta ba.
Ummah ta dafata cikin kulawa tana fad’in, “ Yusrah babu abun da zai faru ki shiga d’akinki ki ƙwanta,” Ta gyaɗa kai sannan ta shige.
Shuru Ummah tayi tana nazarin kalaman Baba sannan ta shiga d’aki ita ma.
Haka ya k’araso inda yake kwana ya tarar da yaransa tsastsaye da alama shi suke nema, kallo daya ya musu yana jan tsuki ya ce, “ Ƴan iska shegu sai kace da gaske kuna so na, har da wani tsayuwa ku hana idanunku bacci,”
“ Oga ina ka shiga ne haka babu dan rakiya?”
“ Dakin uwarka naje? da kuka bugun ne zan d’auki dan rakiya,” Shuru yayi yana bata fuska yana jin wani wari yana buso shi, ya kallesu su ukun, sannan ya ce, “ Ina Bash?”
Shuru suka yi, a tsawace ya kuma cewa, “ Dan uwarku ina Bash?”
Da sauri Faisal ya ce, “ Yana ciki a kwance,”
Ya bisu da kallon tuhuma yana fad’in, “ Me kuka masa?,” Suka yi shuru sai kallon kallon da suka shiga yi, a fusace ya tashi ya shiga d’akin nasu yana zuge labulen, idanunsa ya sauk’a akan shi a kwance kamar gawa sai hakin mutuwa yake.
Da sauri ya dubi inda suke ajiye kwalaban yana shinshinawa, a furgice yayi cilli da kwalban yana nufo Bash da sauri ya fara jijjiga shi, tashi yayi da sauri ya fito ya shiga d’akin da yake mallakinsa ya bud’e akwatinsa yana ciro syringing, ya d’auko wani k’walban magani ya zuk’o a ciki sannan ya koma d’akin da sauri.
Ba tare da ya tsaya wasa ba ya choka masa a bayansa, sannan ya fito da sauri ya mik’awa Lukman dari biyu yana cewa, “ Siyo ruwan sanyi da gudu,” Ya amsa ya tafi dan cika aikan.
Yabi su Faisal da kallon sannan yayi kwafa ya koma wurin Bash ya shiga yi masa fifita.
Lukman ya kawo ruwan sanyi yana mik’a masa ya koma gefe ya tsaya kamar yanda sauran suke a tsaye suna jiran hukunci.
Bula pure water yayi ya shiga dura masa a baki yana jik’a masa riga, ya sake bula wani ya zuba masa a tsakiyan kai, kusan guda biyar ya bula sannan Bash ya fara dawowa cikin hayyacinsa.
Sai da yaga ya dawo normal sannan ya tashi ya zuba musu wani banzan kallon ya fice daga d’akin nasu ya koma nashi.
Ajiyar zuciya Faruq yayi haɗe da lumshe ido ya ce, “ Ya barmu yau,”
Faisal ya girgiza kai, “ Hmm!!! Ya shirya muguntar da zai mana dai,”
Lukman da ko a jikinsa ya ce, “ Ku kunsan dama sai yaci ubanku yau ai, sanin kanku ne ya hana mu shan giya amma bakwa ji,” Ya nuna Bash da hannu yana cewa, “ Shi kuma wannn da ke dabba ne yasan bashi da lafiya kuma ya sha, ko da yake kune tsinannu da kuka bashi ai,”
Bash dai binsu da ido yake bai ce komai ba, dan sai yanzu yasan ana rayuwa a duniya amma dazu ya kusa ziyartar lahira.
Da tunanin hukuncin da zai yanke musu suka yi bacci.
*Washe gari*
Sai guraren ƙarfe takwas din safe sannan ya banko k’ofan shi ya fito yana mik’a, hasken rana ya dalle masa ido, bata fuska yayi yana shafa sumar kansa da yayi yawa zuwa sajensa.
Aljuhunsa ya shafa yaji ba kud’i, lebensa da suka koma baki dan shaye shaye ya ciza sannan ya nufi d’akinsu yana zuge labulen.
Duk suna zaune sunyi zurum zurum kamar wanda ruwa yaci, idan aka cire Lukman da hankalinsa kwance.
Suna kallon shi suka tsorata, Bash ya matsa kusa da Lukman yana hadiye wani mugun yawu.
Inda Faisal suke ya gani sannan ya ce, “ Munafukai, kamar mutanen arziki ashe duk rainon fir’auna ne! anya kun gaishe da Ubangijinku kuwa?” Ya bisu da kallo.
Faruq ya mik’e da sauri amma sai hajijjiya ya dibe shi ya koma.
“ Ba dole ka koma ba, kun cika cikinku da giya wanda Allah ya hana, zaku kashe wancan jakin da yasan shi bashi da lafiya!!! Ni ba na hanaku ba? ya akayi kuka samu kudi kuka siya? a ina kuka samu kudi? Wa ya siyar muku? wa ya siyo muku?”
Bash kamar zaiyi kuka ya nuna Faisal da hannu, “ Babban Yaya wallahi shi ya siyo, kasan bana maka karya, idan nayi karya na mutu yanzu,”
Inda Faisal yake ya iso yana cikumo rigarsa ya mik’ar dashi tsaye, idanunsa da suke kamar na damisa ya zuba masa wanda yasa jikinsa ya fara rawa, da kaukausar murya yake magana “ A ina ka samu kud’in siyan giya!”
Tsabar tsorata gagara kiran sunan nasa yayi sai faman cewa yake, “ Bab babba babban Yaya….”
Sakinsa yayi yana jijjiga kai, “ Shagon waye ka shiga? gidan waye ka haura? waye ka yiwa barazana?”
“ Babban Yaya kud’in wani yaro na kwace dubu biyar na siyo mana…” Bai idda ba ya wanka masa mari, kafin ya ankara ya sake wanka masa wani yana cewa, “ Ka kyauta gobe ma kayi!!! Ba na hanaku taba kayan mutane ba?”
Dukansu suka had’a baki gurin fad’in, “ Ka hana”
“ Good, kuma shine suka yi ko?”
“ Kayi hakuri mun tuba!!!” Nan ma a tare suka fad’a.
Jijjiga kai yayi zai fita ya tsaya ya juyo, “ Kuje gidan Zubairu ku amso min kud’ina, idan bai baku ba ku d’auko min wancan kwailal,” Daga haka ya fice.
Lukman ya matso kusa da Faisal yana cewa, “ Kai kasan ya hanamu shan abun nan, mesa ka siyo to? sanin kanmu ne kaf duniya bayaso a tabamu ko wani abu ya same mu, ba re kuma ace na bacin rai, ya dauke mu tamkar wanda suka fito ciki daya, ya bamu gurin zama, ya bamu rayuwar inci, ya hana cikinsa abinci ya bamu, ya hana kansa farin ciki ya bamu, a sanadinmu yasha zuwa police station, daukan laifin da bashi yayi ba yayi duk saboda mu, yayi abubbuwa dayawa duk saboda rayuwarmu, shi zai sha wiwi da taba amma mu zai hanamu, duk da kuwa idan bai sha ba bayajin dadi, baya bacci,,,,, wannan duk bai isa ya ganar da ku cewa yana sanmu fiye da kansa ba, rayuwarsa dayawa ya sadaukar duk saboda mu, har ya koyawa kansa zama dan daba saboda mu.” Ya kai karshe yana cewa, “ To mesa idan ya hana mu bazamu hanu ba? ya zama uwa, uba a garemu, shi din garguwarmu ne, shi ne bangon mu, dole idan muka nemi sanyi zamuje izuwa gare shi mu jingina, haka kuma duk wanda ya taba shi dole ne mu koma yan daba.”
Faruq ya matso yana cewa, “ Ni dai daga yau na daina shan giya, amma shaye shaye kam zanna yi, kuma dabanci dama shine namu sai munyi muke samun kudi,”
Murmushi Bash yayi yana tashi zaune ya cije lebe dan har yanzu cikinsa yana ciwo, sannan ya daura hannu akan na Faruq ya ce, “ Nima haka,”
Lukman ma ya daura hannu, sannan Faisal ya daura yana murmushi.
“ Babban Yaya ya samu aiki fa zamuje karbo kud’inmu,” Cewan Faruq yana mikewa ya d’auko wukansa ya gyara mekyau yana fad’in, “ Ko ya bamu kud’in Yayanmu ko mu masa sabon kaciya,”
Faisal ya saki dariyar gefe yana fad’in, “ Gyaramin nawa ni ma, idan dare ya danyi sai muje.”
Haka wayewar ranar tayi shi ba dad’i duk hankalinta a tashe, dan tasan halin Baba ba kudi ne dashi ba kuma tunda yace ita ce a matsayin kud’in tasan baja da baya.
Guraren karfe biyu ta shirya cikin kayan islamiyya blue da fari, hijab dinta har k’asa, sannan ta saka nikab, ta saka safa ta dauki Al-qu’anin ta ta fito.
Dakin Ummah ta shiga tana cewa, “ Ummah zanje Islamiya sai na dawo!”
“ A dawo lafiya Yusrah, ki kula da kanki, Allah ya bada sa’a”
“ Amen,” Sannan ta fito bayan tayi addu’ar fita daga gida, tafiya take kanta a k’asa tana muraja’anta a zuciya, duk majalisan da ta wuce sai mazan sunyi gulmanta, wasu suce har yau ba’a taba ganin fuskarta ba kila bata da kyau ne, wasu kuwa sai zagin Babanta suke a cewan su bata samu uba na gari ba.
Taji ba wai bata ji ba, kuma maganar su ya kona mata zuciya amma babu yanda zata yi sai hakuri, haka har ta isa islamiyan su, nan ma dai gulman ake, tayi banza dasu ta samu seat ta zauna ta bude qur’ani ta soma karantawa.
Sai kusan karfe shida da rabi suka tashi, lokacin garin har ya fara duhu, sauri sauri take dan ta shiga gida, dan unguwar ba kyau sai tarin yan shaye shaye da kwarata da yan sari, haka har ta isa gida lokacin ana fitowa a sallan magrib.
Ummah ta samu a tsakar gida ta gama girki tana tattarewa, gaishe ta tayi ta shiga d’aki ta cire kayan jikinta ta cire nikab sannan ta fito, alwala ta daura ta koma ta dauki himar tayi sallah.
Ummah ta zubo musu abinci suka soma ci suna dan taba hira, Baba ya shigo yana cewa, “ Ni fa a halin yanzu ko shaidan bai kaini hakuri ba,”
Ta gaishe shi cikin siririyar muryanta, “ Baba ina wuni?”
“ Klau nake!!” Sannan ya samu wuri ya zauna yana kallon cikin kwanon abincin nasu ya ce, “ A ina aka samu tuwo har aka girka?”
“ Dazu na siyo masara dama akwai kuka sai na dafa,” Cewan Ummah tana tashi ta kawo masa nasa.
“ Ke yanzu ban da bakin hali irin naki, akwai kudi a wurinki ki kawo na biya bashin adashe ne kika ki,”
“ Dubu daya ne fa Malam!!!,”
“ To mai maraban danbe da fada? idan aka k’ara dubu tara akai ba an samu goman ba,”
“ Ni dai bani da shi,”
“ Kar Allah yasa ki samu, ina zaune da mahassada yan bukulu….”
Kofan gidan suka shiga bugawa, a razane Yusrah ta mike zuciyarta na tsinkewa tana kallon kofan shigowa gidan, Ummah na fad’in, “ Ka kai musu kudin su, ina da tabbacin su ne suka dawo,”
“ Ai na fada miki bani da kudi sai dai su dauki Yusrah wallahi…..” Bai k’arasa ba suka shigo hannunsu rike da wuk’a Faisal na cewa, “ Zubairu kudinmu…
*COMMENTS*
*LIKES 👍*
*SHARE 📖*
*FISABILILLAH🙏*
_*SAHIBA CE✍🏻*_
[7/17, 7:51 AM] +234 902 730 8227: *AUREN ADASHE💅🏻*
Na
Fatima Isa Manu
( Sahibar Jajirtattu ✍🏻 )
💪 *JAJIRTATTU WRITER’S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al’umma cikin sauƙi_.✏️*
Page 📄2
“ Ai na faɗa miki bani da kuɗi sai dai su ɗauki Yusrah Wallahi…..” Bai k’arasa ba suka shigo hannunsu riƙe da wuk’a Faisal na cewa, “ Zubairu kuɗinmu,”
Da sauri Baba yayi bayan Ummah yana faman salati, “ Inna’illahi!!! Astagfirullah!!! Subhanallah!!! A’uzubillahi minal shaiɗanin rahim!!!”
Wani dariyan rainin hankali Faruq yayi yana gyara wuk’ansa ya ce, “ Wato dai mu ne shaidanun ko Zubairu? To ai hikenan bari mu nuna maka aikin shaidanun asali,”
Faisal ya nufo wurin Baba yana jawo shi ya durkuso shi a tsakiya suka zagaye shi, Bash ya rike sandan shi mekyau yana cewa, “ Zaka bamu kud’inmu ko sai mun maka aiki yanzu,”
Faruq yayi dariya yana nuna Lukman ya ce, “ Luku luku ka masa wa’azi akan cin bashin adashe kafin mu masa aika aika!!! Zubairu kasan mu muna da Malami a cikinmu,”
Yusrah ta fashe da kuka mai cin rai wanda ke nuni da zallan Allah wadai da halin Mahaifinta, kukanta ya janyo hankalin Faisal ya nuna ta da wuk’a, “ Wannan ba ita bace Babban Yaya yace a d’auko idan bai bada kudinmu ba?”
“ Kwarai kuwa ita ce, ni da farko ma na d’auka Aljana ce, ashe mutum ce,” Bash ya fada yana janyo ta da k’arfi daga jikin Ummah har sai da ta fad’i.
Ummah ta saki wani kukan takaici tana fad’in, “ Dan Allah ku barmin yarinyata, idan yaso shi sai ku d’auke shi ko yanka shi ma zakuyi kuyi, amma ku barmin yarinyata,”
Lukman ya danyi gyaran murya na yan iska ya soma cewa, “ Hajiya bama jayayya da aikin Babban Yaya, shi tsohon nan da baisan hadith ba uban me zamuyi da shi, kuma wallahi bari kaji Zubairu idan baka bamu kud’inmu ba zaman unguwan nan sai ya gagare ka, tsohon bahanmage kawai,” Ya zungure shi da k’asan wuk’an.
Faisal ya ce, “ Ni fa da niyar yi masa duka nazo, yaci ace na dan lafki keyarsa,”
“ Babban Yaya bai ce a masa illa ba, kawai cewa yayi mu amso kud’inmu ko mu d’auko kwailan nan,” Cewan Faruq yana nuna Yusrah da ta gagara tabuk’a komai dan haushi.
Sa k’afa Bash yayi ya hankad’a shi gefe yana fuzgo Yusrah da k’arfi har sai da hannunta yayi k’ara, ta saki wani kukan azaba tana tauna lebe da sauri.
Ummah taje zata riketa Faisal ya shiga tsakani yana saita wuk’an dai-dai wuyan Ummah ya ce, “ Kina sake taku daya a nan sai kin bakwanci lahira billahil lazi,”
Baba yayi shuru yana addu’an su d’auki Yusran su tafi ya samu ya shiga band’aki, idanun Bash ya sauk’a akan shi, dariya ya saki yana fad’in, “ Hala dai tunanin wani adashen kake?,” A firgice ya girgiza kai yana fad’in, “ Aa na daina daga yau,”
Lukman ya saka Yusrah a gaba yana fad’in, “ Ki wuce mu tafi ustaziya, gwara ki bini mu tafi, idan kuma su Faisal ne zasu sakaki a hanya bismillah,”
Tana rike da hannunta wanda yaji ciwo saboda janta da k’arfin da Bash yayi, ta dubi inda Ummah take tsaye tana kuka ta ce, “ Ummah ki ce su barni dan Allah, wallahi tsoron su nake,”
Faisal ya bugawa Baba k’asan wuk’an a tsakiyar kai, wani k’ara Baba ya saki yana rik’e wurin, kafin kace me sai ga jini ya fara zuba, Yusrah ta ware ido tana fad’in, “ Baba!!!” Ta nufe shi amma sai Faruq ya janyo ta da sauri yana cewa, “ Mu ware!!!!” Lukman ya bud’e musu k’ofa suka fita, Ummah ta durkushe a gurin tana kuka.
Sauri suke dan su bar cikin mutane, ga kukan da Yusrah take ya cika musu kunne.
Haushi ya sa Faisal buge bakinta da k’arfi, nan take ya fashe jini ya fara zuba, tayi saurin dafe bakin nata tana lumshe ido, hannunta ya baci da jini har jikin hijab nata.
Lukman na cewa, “ Ka fasa mata baki fa!!!”
“ Ita ta janyo,” Cewan Faruq yana cigaba da tafiya,
Bash ya kalli yanda jinin ke zuba ya ce, “ Faisal kai abun ka duk zuciya, ka ji wa Zubairu rauni yanzu ma ka fasa bakin Ustaziya,”
“ Bakaji damun mu tayi da kuka ba, tana so ta tara mana jama’a cikin daren nan, dama gashi neman mu police suke,”
“ Zaku zo mu tafi ne ko kun tsaya sai anzo anci ubanku mai lasisi,” Faruq ya fad’a yana mai cigaba da tafiya.
Lukman yayi gaba abun shi, Bash ma yaja tsuki yana rike da sandan shi ya yi tafiyar shi, ganin taki tafiya ne, haushi yasa Faisal d’aukanta a kafad’a suka tafi.
An tafi an bar Baba da rauni a kai, sai surutai yake yana ja wa Faisal Allah ya isa yana tsinewa Babban Yaya.
Ummah kuwa kuka take tana tuna halin da Yusrah zata shiga, dan tasan sai dai ita ta nemo kudi ta biya bashin adashen kafin su bar mata yarta, amma Baba ba zai taba biya ba, ya gwammace ta mutu a chan.
Jiki ba kwari ta tashi zata shiga ciki Baba ya ce, “ Kizo ki taimaka min ki kaini kemis, dan ina da tabbacin kaina fashewa yayi.”
A kufule ta ce, “ Allah yasa ya rabe gida biyu ma, idan ni ce zan kai ka kemis ka mutu a wajen, Wallahi ban taba nadamar auren ka ba sai yau, da irin auren ka gwara auren dan iskan gari.”
“ Munafukar mata ince ke ma da kud’in adashen na aure ki, dan yau an biyo ni gida karban kudi shine zaki na gayamin magana, yarki dai sai dai ta mutu a chan amma bani da kudin karbo ta, ni yanzu ma wani adashen nake son shiga,” Ya karashe yana mik’ewa hannunsa dafe da kansa.
Tsuki Ummah taja ta shige ciki, Baba na fad’in, “ Nan gani nan bari dumamen mayya,”
*UNGUWAR SULTAN ROAD*
Kana shigowa line gidan zaka ga signboard anyi rubutu da manyan harufa *ZAYYAN’S MANSION* wanda ke nuni da mamallakin gidan babba ne, kuma sananne ne.
Babban gida ne wanda ke cike da security’s ta ko’ina, tun daga bakin gate har wajen parking lot duk security ne masu sanye da bak’aken kaya.
Gidan yana dauke da Apartments dayawa, amma g dukkan alamu guda uku ake amfani dashi kuma suna jere, amma duk na tsakiyar yafi babba, haka kuma an fi k’awatashi.
Tun daga bakin k’ofan falon zaka ji yanda ake hayaniya ana masifa, muryan wata budurwa ce yafi tashi inda take cewa, “ Ko ma mene kuyi, amma ku sani babu wanda ya isa ya tursasani abunda banyi niya ba!!” Bata jira cewan su ba ta dauki mukullin motanta ta fito kamar zata tashi sama, har mayafin kanta na zarewa gashin kanta ya bayyana wanda yasha gyara.
Doguwa ce fara sol, abayan dake jikinta wanda ya kwanta ne zai tabbatar maka da tana da diri, shape kamar 8, tana da dara daran ido kamar na mage, ga hanci dogo da bakinta karami pink, Hidaya kenan, mace mai ji da kanta da kuma daukar wanka, wanda saboda daukar wankanta ne kawayenta suke kiranta da Dawisu 🦚.
A 360 ta fizgi motar aka bud’e mata k’ofa ta fice.
A falon kuwa, Mata ne guda uku da babbar mace guda daya ta zauna tayi tagumi, kallo daya zaka mata ka gane suna kama da Hidaya sosai.
Na kusa da itan ne ta zauna gefenta tana cewa, “ Mamiee when zaki daina damuwa da halin Anuty Hidaya ne? by the way ita bata damuwa da halin da zaku shiga daga ke har Dad,”
Mamiee ta d’ago ta ce, “ Samha sanadiyar Hidaya ce har yau dangin Babanku basa sona, ina k’ok’ari na duk dan ta sauya amma taki,”
Tabe baki wacce ke tsaye tayi tana fad’in, “ Mamiee idan an fara hayaniyarku da Hidaya kuna tafiya ko kitchen dan in samu ina bacci kuna damuna,”
Dariyan rainin hankali na zaunen tayi tana gyara glass din dake idanunta, wanda ke nuni da na rashin lafiyan ido ne, sannan ta ce, “ Ai Mamiee bazata iya rayuwa babu Hidaya ba, ke Amrah hanaki bacci ake ni kuma hanani karatu ake,”
Mamiee ta girgiza kai ta kira sunan su, “ Amrah, Najma ni kuke cewa na dame ku!”
Amrah ta kwashi laptop dinta da wayarta ta ce, “ Ni fa magana nayi amma nasan sai yanzu fada ya dawo,” Tayi sauri ta shige d’akinta da yake kusa da kitchen.
Najma ta gyara headphone 🎧 dinta ta kure kida ta shige dakinta dake kusa da na Amrah.
Samha ta rike hannun Mamiee tana cewa, “ Sorry Mamiee, kije ki kwanta ki huta,” Mamiee ta tashi ta wuce d’akinta. Shuru Samha tayi tana mamakin yayuntan nan.
*WAYE DAD*
Alhaji Zayyan Barde shine asalin sunan Dad, iyayensu su uku suka haifa da Yusuf wanda suke kira da uncle Yusuf, sai Jamila wacce suke kira da Mom.
Iyayensu duk sun rasu hakan yasa Dad ya zame musu uwa uba, yake basu kulawa sosai har ya aurar da Jamila, wanda yanzu take da yara biyu maza Khashim da Othma.
Allah ya budawa Zayyan sosai inda yake sana’ar fitar da karafuna zuwa kasashen waje, inda ya daura kaninsa a matsayin manaja na babban campany shi, arzikinsa ya sake bunk’asa, nan yayi gini a unguwar sultan dake garin Kano.
Ya buk’aci Yusuf da yayi aure, haka kuwa akayi Yusuf ya auro wata bafulatanan Adamawa wato Jidda suna kiranta da Anuty, cikin shekara Allah ya azurtasu da samun yaro namiji wanda Yusuf ya sawa Dad takwara wato Zayyan, ana kiransa da Maheer.
Dad ya dukufa kan kasuwancin shi gadan gadan baya wasa, duk inda ake samun kudi Dad yana wajen, cikin shekaru kadan Dad ya zama hamshakin mai kudi na bugawa a jarida.
Lokacin Yusuf yaransa biyu da Maheer da Ma’eesha, nan kuma Dad ya samo matar aure a unguwar Hotoro, inda ba’aja magana ba aka daura musu aure shi da Aisha wato Mamiee.
Sai dai tsana mai karfi Jamila da Jidda suke mata, a ganin Jamila yanzu zata mallake mata Yaya, ita kuma Jidda gani take Dad zai kwace dukiyarsa daga hannun mijinta.
Tun da Aisha ta shigo gidan Maheer ya dawo wurinta da zama, idan aka nemeshi aka rasa ana zuwa part din Aisha za’a sameshi yana bacci ko game, shakuwar da yake tsakanin shi da Aisha yayi yawa dan shi ya fara kiranta da Mamiee.
Bayan wasu shekaru, Yusuf da Jidda suna da yara hudu Maheer 28yrs, Sameer 26yr Ma’eesha 24yrs tayi aure a Adamawa da yaro daya amma an sakota ta dawo, sai Fadil 22yrs…
Jamila kuma biyu Khashim 31yr yayi aure, da Othuma 29.
Zayyan da Aisha yaransu hudu wato Amrah, Najma, Hidaya da Samha….
*COMMENTS*
*LIKES 👍*
*SHARE 📖*
*FISABILILLAH🙏*
_*SAHIBA CE✍🏻*_
[7/18, 9:45 AM] +234 902 730 8227: *AUREN ADASHE💅🏻*
Na
Fatima Isa Manu
( Sahiba / Dr. teema ✍🏻 )
💪 *JAJIRTATTU WRITER’S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al’umma cikin sauƙi_.✏️*
Page 📄3
Zayyan da Aisha yaransu hud’u wato Amrah, Najma, Hidaya da Samha.
Amrah ce Babba, tana da shekara 25, slim ce sosai dan idan ba fad’a maka akayi ba zaka tsammanin ita ce karama, chocolate color ce ga kyau dan kaman su daya da Mahaifinta, yanzu tana karantar law, tun da aka haifeta take da ciwon ido har sai da aka siya mata glass, ita karatunta kawai ta sani bata damuwa da kowa.
Najma ce na biyu, tana da shekara 23, tana da jiki sosai dan ita suke kira da Ajebo, ga kyau dan ta d’auko na duka bangaren iyayenta ne, ita kawai a barta da kida da zuwa chasu, da chatting da samari, tana part 3 a university, tana karanta business.
Hidaya ce na uku wacce ake kira da Dawisu, shekaranta 20 cib, kyakkyawar mace wacce ko wani namiji yakeson mallaka, ga haske ga diri ga kyau uwa uba ga gashi da tsayi, tana karatun midwifery, bata shiga harkan kowa amma akwai rawar kai ga son yawo, idan ta fice da karfe uku sai kusan sha daya take dawowa, tun Dad na fada har ya gaji dan baji take ba, kuma ba damar ka mata magana ta hau gaya maka bakar magana, babu wanda take tsoro sai cousin nasu Yaya Maheer wanda a gidan yake amma yanzu yayi tafiya baya k’asan kusan shekara daya, sai dai ita duk rawar kanta bata kula samari a cewarta bata lokaci ne a matsayinta na wacce take karatun lafiya, haka kuma kaf family anfi tsanarta a cikin yaran Mamiee dan ita ta fito daban cikin yaran gidan, akan Hidaya har fad’a Mamiee da Jamila sukayi, amma Hidaya ko a jikinta karshe ma cewa tayi chan ta matse musu.
Samha ce k’arama wacce suke kira da Auta, shekaranta sha takwas 18 a duniya, da ita fara ce bazaka iya banbance ta da Hidaya ba, yanzu take rubuta WAEC AND NECO, kaf duniya babu wanda take tsoro sama da Hidaya, ba ita kadai ba har sauran kowa tsoron masifar Hidaya yake, idan kanaso kaga bacin ranta, to ka taba mata iyayenta, shiyasa har yau basa shiri da matar Uncle Yusuf wato Jidda wanda ke zaune shi da iyalansa a gidan.
*MUN DAWO DAGA LABARI*
Ma’eesha ce ta hangi fitan ta a fusace da motan, tsuki taja ta koma bangaren su tana kiran Mahaifiyarta, “ Anuty yau an taba wancan Aljanan,”
Jidda ta fito tana fad’in, “ Ita da waye kuma?”
“ Ina ga ita da uwarta ne, kinga yanda ta fita a fusace kuwa kamar wacce zata tashi sama, yarinya sai zuciya gashi ba damar kaje ka tunkareta, ita kanta ma abun tsoro ce barin ma ta maka magana a tsawace,”
Fadil ne ya fito daga d’akinsa hannunsa rike da yaro yana cewa, “ Anuty Eeesha ki karbi yaronkin nan ko na mayar dashi inda ya fito,” Ya rike shi da hannu daya.
Da gudu Ma’eesha tazo ta karbi danta tana daka masa harara tana cewa, “ Dake ba kai ka haifeshi ba dole ka rike shi da hannu daya, baka san zafin haihuwan bane,”
“ Ina zan sani kuwa, naji kina gulman Hidaya mai ta miki?”Fadil ya fad’a yana mai zama kusa da Anuty.
“ Babu abunda yarinya ta tare muku amma kullum kuna cikin zaginta ko dura mata ashar, gashi ke kin gagara zaman gidan auren kin dawo gidan Faza.” Suka ji muryan Sameer daga kitchen hannunsa rike da mock yana siping tea.
Anuty ta saki baki galala tana kallon shi, Fadil yayi dariyan mugunta yana gyad’a k’afa alamun dai maganar ya masa dad’i, Ma’eesha idanunta suka ciko fal da kwalla, ta share tana rungumar danta ta koma d’akinta ta rufe k’ofa.
Anuty ta ce, “ Nikam Sameer ko son Hidaya kake ne ban sani ba?”
Girgiza kai yayi, “ Ko kad’an, gaskiya ce dai bakwa so, ni banga laifin Mamiee ba amma tun da na taso a gidan nan ke da Mom kullum sai kun zage ta, ko me ta muku oho,”
“ Ni kake fad’awa bak’aken maganganu Sameer?,” Anuty ta nuna kanta cike da mamaki duk da kuwa ba sabon abu bane, Sameer da Maheer basa kunyar gaya mata gaskiya duk d’acinta kuwa, a wani bangaren ma gwara Sameer din akan Maheer.
“ Ni dai gaskiya na fad’a, is better ma ku daina ko Allah zai gyara lamurukan ku,” Daga haka yayi wucewarsa waje zuwa bangaren Mamiee.
Anuty ta juyo da zummar yi wa Fadil magana, amma sai ya tashi da sauri ya fice yana wayar karya.
*HIDAYA (DAWISU)*
Bata zarce ko’ina ba sai school nasu, direct hostel nasu ta shige tana faman surutu, “ An bar musu gidan su dafa su cinye,” Ta shiga bubbuga k’ofan dan ta baro key bata a gida.
Wata budurwa ce wacce zasuyi sa’a ta bud’e kofan, bangaje ta Hidaya tayi ta shige ciki, da kallo budurwar ta bita kafin ta rufe k’ofan ta shigo ciki.
A tsastsaye ta same su Hidaya sai masifa take, “ Shi ne daga barin d’akin nan har an haye gadona!!!” Ta kalli yanda bedsheet nata yayi sucuznig, a fusace ta juyi tana kallon su tana cewa, “ Marwat nasan ke zakiyi wannan iskancin, to a gyaramin gadona bana son datti,”
Azima ta girgiza kai tana cewa, “ Hidaya wai ke da waye haka duk kin gagara yin shuru?”
Marwat ta ce, “ Ni ai tun da ta bangaje ni a bakin k’ofa nasan yau kan ba dadi, duba fa ko mayafi babu akanta, Allah ya rufa asiri kar aljanu su kai miki hari,”
Tura baki tayi tana shafa kan nata taji ba mayafin, kwafa tayi sannan ta zauna akan gadon Azima tana cewa, “ Mamiee ne da yaran nan suka kusa samin ciwon kai yau, wai a rasa wanda zaiyi girki sai ni, girkin ma wai na Ya Maheer dan zai dawo daga tafiya, ince yana da uwa ai kuma yana da bazawarar kanwarsa why not su su masa,”
Marwat ta dafe kai bayan ta gyara bedsheet din, sannan ta zauna kusa da su tana cewa, “ Kila ko naki yake son ci,”
“ Yunwa ta kashe shi to, in dai ni zan masa girki to yunwa ta kashe shi,”
Shuru suka yi suna zuba mata ido, yanda take maganar ya isa ya sanar dasu cewa ta tsane shi.
*YUSRAH*
Suna shigowa gidan suka tarar da Babban Yaya zaune akan taburma yana busa taba, kallo daya ya musu ya dauke kai.
Akan taburman Faisal ya direta yana cewa, “ Babban Yaya, Zubairu yaki ya bamu kud’inmu fa shi ne kawai muka yi ram da ustaziya kamar yanda ka bada umarni,”
Ya kalli inda take ta wani dunkule a gefe dasu ta hade kai da gwiwa, sheshekan kukanta ne kawai yake nuni da tana da rai, tsuki yaja yana kallon su ya ce, “Na ajiye muku abinci a dakinku,,,” Sannan ya dubi Bash yana cewa, “ Kai mai zubin tsaka ka samu kaci abinci fa, dan wallahi idan yau ka biye su kasha wani abu, to ina mai tabbatar maka zaka ziyarci lahira ne babu ruwana dan ubanka,”
Suka yi dariya Bash na bata rai ya ce, “ Babban Yaya yau fa bani da kudi dry ne,”
“ To dama kai kana da kudi ne, ai baka ake dama tun da a tsiyace kake!” Sannan ya mayar da hankalinsa kan Faisal yana fad’in, “ Ina shi Zubairun yake dan uwarsa, da ya bamu wancan kwailan a matsayin kudinmu dafata zamuyi ko soyata, dawainiya ya daura min ai aradu,”
Yusrah ta d’ago da kanta, hasken watan da ya dallo ne yasa duk suke kallon junansu kamar rana, ta bude baki cike da radadin da yake mata da tsoro tana cewa, “ Zan sha ruwa”
Muryanta ya daki dodan kunnensa, ya kalle ta lokaci daya yana dauke kai, da farko ya tsorata amma sanin cewa ko da wasa bata taba fita babu nikab bane yasa ya yarda ita ce, a zuciyarsa kuwa cewa yayi, ‘ Dole ki saka sunnah a fuska, wai wai jar uban nan, Al-arshi ya zuba halilta a nan wurin,’ Muryan Faisal ya katsai shi inda ke cewa, “ Bamu da ruwan sha Ustaziya,”
Babban Yaya ya dauki pure water dake gefensa ya cilla mata, da sauri ta dauka ta fara sha duk jini ya bata gaban hijab nata, da mamaki ya kalli Lukman yana cewa, “ Dan uwarku me kuka mata? ko kun aikata wani abu ne?”
Lukman ya girgiza kai yana cewa, “ Kuka take mana shine aka dan buge bakinta kadan, amma dake fake one ce har ya fas…” Bai karasa ba yaji naushi a baki.
Da sauri Bash yayi bayan Faruq yana rike shi, Faisal ya sha jinin jikinsa dan yasan karshe shi zaici ubansa, Lukman ya rike bakinsa kansa a k’asa.
Yusrah da take gefe ta zuba musu na mujiya tana jira taji me ya faru.
Rai a matuk’ar bace ya shiga zazzaga musu masifa hade da zagi, “ A in kuka ji ance ku daki mace dan durun uwarku? ni fa aiken ku kawai nayi bance ayi duka ko zubar da jini ba, ita me tayi da zaku fasa mata baki har yayi jini haka, ku abunda aka hanaku shi kuke yi dan kun rainani ko;” Ya sauke numfashi yana shafa gashin kansa sannan ya ce, “ A cikin ku wa ya daki mace?”
Muryan Faisal na rawa ya ce, “ Ni…. ni ne,”
“ Na sani, nasan kai zaka aikata,” Bai jira ba ya shiga daki da sauri sauri, Lukman yayi saurin shigewa d’akin su, Faruq na mara masa baya da gudu, kafin kace me Faisal da Bash sun shige an rufo k’ofa da karfi an saka sakata, labulen an barshi a waje.
Ya fito da wata zabgegiyar sanda yaje bakin k’ofan yana fad’in, “ Zaku bude ko sai na cilla muku wuta kun kone dan uwarku,” Suka yi tsit kamar ba mutane a dakin.
Yusrah tsoro ya rufeta sai waro ido take tana kallon shi, yayi kwafa ya juya zai shiga d’aki sai kuma ya tsaya ya juyo ya ganta, a tsawace ya furta, “ Zaki shiga dakin ko sai na rufe k’ofan,” Bata san lokacin da ta tashi ta shiga dakin nasa da sauri ba jikinta na bari…
*COMMENTS*
*LIKES 👍*
*SHARE 📖*
*FISABILILLAH🙏*
_*SAHIBA CE✍🏻*_



GASKIYA NE
Gsky yayi dadi